← Book details Indo Sarƙa Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 76

Sashe 36

Indo Sarƙa Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ajiyar zuciya Alhaji ya sauke ya ce, "Lallai Allah ya taƙaita wahala kuma Addu'a tayi tasiri, mun godewa Ubangiji da yarinyar nan ta faɗa hannu na gari. Allah ya tsare ya ƙara shirya mana zuri'a, tabbas Indo tayi ƙuruciya amma mungode Allah, da Allah ya kawo lamarin cikin sauƙi. Kai kuwa Fahad Allah ya saka maka da mafificin alheri, tabbas kayi ƙoƙari kuma hakan da kayi shine dai-dai" su Daddy ba ƙaramin daɗin maganganun Alhaji suka ji ba, Baba Huwaila ce ta kalli Fahad ta ce, "Amma kuwa wannan yaro Allah ya saka maka da mafificin alheri da kayi sanadiyyar dawowar Indo ta, tabbas duk abinda Indo ta sanar da ku gaskiya ne kuma nima yanzu yan ƙara muku haska akan abin da ta sanar da ku" Baba Huwaila na zuwa nan Jamilu yayi sallama yana shigowa cikin falon. Cikin girmamawa ya gaishesu ƙur Yaseer ya kafeshi da kallo, har ya juya zai fita Baba Huwaila ta ce, "Jamilu ina zaka zo nan kaima ayi da kai man, kaga ƙanwarka Indo ta dawo" Zaro Ido Indo yayi yaja wani irin numfashi sannan ya sauke shi da ƙyar cikin wata Irin murya ya ce, "Indo ina kika tafi kika barmu" Indo sunkuyar da kai ƙasa tayi tana wata irin dariya sannan ta ce, "To Ya Jamil ba gani andawo dani ba" Maganar Indo har tsakiyar kansa ta riskeshi mamaki ne ƙarara bayyane akan fuskarsa jin yadda Indo take magana, wai yau har shi take cewa Yaya. Koma yayi ya zama cen jikin bango yana fuskantar Indo, A fakaice Yaseer sai watsawa Jamilu harara yake yana jin wani irin haushi a zuciyarsa.

Baba Huwaila ce ta cigaba da cewa, "Tun ranar da Indo ta so tafiya nayi niyyar nuna mata wani abu da bata san da shi ba, wanda Goggo ta bani saura kwana biyu ta rasu. Ta ce mun kar insanarwa da Indo matsayinta har sai bayan Aurenta kuma a lokacin ya dace na ɗauko wannan abun na damƙa mata shi da ƙarin bayani. A lokacin da ta nunamin zata tafi na ɗauka wasa take mun saboda bata taɓa mun irin wannan maganar ba, lokacin da ta fita nayi niyyar na kiranta na miƙa mata kayan da Goggo ta bani, daga nan mu ɗunguma zuwa gidan Maigari domin mu san abinda zai aiwatar ga wanda ya tono da wannan maganar sai dai ban sameta ba" Baba huwaila janye Indo tayi daga jikinta ta ce, "Bari na je na kwaso muku kayan na saukewa kaina nauyi, saboda ban sani ba ko ina da ikon ganin lokacin auren Indo ko akasin haka, tun da daga ni babu wanda yasan da wannan kayan ko Jamilu bai san da su ba" Baba Huwaila na gama faɗa ta fice daga falon, gabaɗaya shiru sukayi banda ƙarar fanka babu abinda yake tashi a ciki.

Baba Huwaila shigowa tayi hannunta ɗauke da wata baƙar leda, zama tayi ta kwance ledar ta fito da wasu ƙananan kayan harirai ta ce, "Wanaan riga da siket da kuke gani Goggo ta ce mun sune a jikin Indo lokacin da ta tsince ta, tare da wannan shawul ɗin. ajiye su tayi a gefe ta ɗauko wata ƴar mitsitsiyar azurfa ta zobe da ɗan kunne tare da abin hannu ta ci gaba da cewa, "Wannan ɗan kunne sune suke jikin kunne Indo, sai zobenta da ɗan awarwaronta." suma ajiyesu tayi a gefe ta kuma zaro wasu tsofaffun hotuna guda biyu ta ce, " Ga kuma waɗannan hotunan ta ce mun acikin pampars ɗin Indo ta same su" suma ajiyesu tayi a gefe ta ciro wata ƴar duƙunƙunanniyar takarda ta ce, "Wannan takardar itama ta ce a cikin pampars ɗinta take sai dai ta jiƙe har wasu daga cikin lambobin lambar wayar da aka rubuta sun goge" Alhaji kallan karɓar kayan yayi ya fara miƙawa Daddy, tunda Baba Huwaila ta fara fito da kayan Mommy da Momma jikinsu yayi sanyi hoton jiki Daddy ya hango da sauri ya miƙa hannu ya ce, "Alhaji bani hoton nan mu gani wa nake gani a jiki kamar hoton Khaleel" yana rufe baki Momma ta ce, "Bani Muga wannan Azurfar" Daddy na ƙarewa hoton kallo ya fara jinjina kai a fili ya furta, "Ashe harsashen da nake bai tashi a banza ba, tabbas Humaira ke jinimu ce Allah ya dawowa da Khaleel Ɗiyarsa Aisha"

A KAFTA🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️

SHIN A HARSASHEN KU SU WAYE IYAYEN INDO A CIKI???? MU HAƊE A COMMENTS🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️

_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

*ÆŠAN ÆŠANO DAGA LITTAFIN SIRRIN MU*

Yadda kake tunanin rayuwa ba haka take ba,da lokota da dama kana iya gane SIRRIN wasu, Amma wani lokaci naka SIRRIN dake bibiyar Rayuwarka wahalar gane masa kake,Yau Uban daya haifesa ya kawosa Duniya shine da gansa ya masa sharri,Shi ne ya saka za'a kai shi gidan yari,Matar da yafi so fiye da komai nasa,wacce ta zame masa Uwa,Uba,Yaya,Ƙanwa,Aboki yau itace Mahaifinsa ya kwanta da ita har ta ɗauki cikinsa,Kuma yanzu shine ake cewa shi yay mata CIKIN,da me zaiji? Da nakasar da take damunsa?ko kuma da BAƘON YANAYIN daya tunkaro sa?Wannan SIRRIN MU ne bai kamata ace kowa ya jishi ba,SIRRIN MU ne nida mahaifi na,SIRRIN MU ne nida Matar da nakeso, SIRRIN MU ni da Aljanun da suke tare da ita.

_JAMA'A WANNAN MARUBUCIYAR CE DAI WACCE TA NISHAƊANTAR DAKU A LITTAFIN *MOON* DA *UNCLE NE* GA KUMA *THE NEW EMIR* SBD NIN DAƊIN MASOYA YASA SAI TA GAMA PART ONE ZATA FARA SAKINSA WANDA ZATA NA BAWA ƳAN *VIP* POSTING 2 KULLUM A RANA ƳAN *NRML GRP* KUMA POSTING ƊAYA A RANA NASAN KUSAN *NIMCYLUV* TAURARUWAR MARUBUCIYA MAI TASHE😂

ZAKU IYA PAYMENT TA WANNAN ACCOUNT ÆŠIN

0116886423
Sulaiman Naima s union bank evidence of payment 08119237616

400 for nrml grp
600 for vip

Nima AMEERA ADAM na shiryar tsaf domin karanta littafin *SIRRIN MU*
[19/08, 18:53] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

*INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️
*BY*
*AMEERA ADAM*

*FOLLOW ME @WATTPAD*
_*AmeeraAdam60*_

GARGAÆŠI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.

_*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_

_SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._

*Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.*

63&64

Gabaɗaya kallo ne ya koma kan Daddy, da mamaki su Baba Huwaika suka bi shi da kallo, Alhaji na shirin magana Baba Huwaila ta ce, "Kai yaro kada kamun alaye, ban fahimci ƴar Khaleel ba?" Momma ta ɗago ta ce, "Allahu Akbar kabiran tabbas Safna ta samu labarin nan yau ko bacci bazata iya runtsawa ba, dama tun da na ga taɓon dake kanki Humaira nake ta wasu wasi a zuciyata, ashe ke ɗin jinina ce" Da mamaki Fahad ya ce, "Momma wai me yake faruwa ne kun sa mu a duhu? Wai kuna nufin Aishan Aunty Safna dai tamu wacce a ka sace?" Daddy ya ce, "Ƙwarai kuwa Ya zama dole na tunasar da ku alaƙarmu da Humaira idan kun manta" Indo dake kwance akan cinyar Baba Huwaila ta taso tana bin su Momma da kallo, Momma ware mata hannu tayi ta ce, "Zo Humaira ta" sororo tayi kamar bazata tashi ba, amma sai ta yunƙura da kyar ta ƙarasa gurin Momma da sauri Momma ta rungumota tana fashewa da kuka, sai da tayi mai isarta sannan ta ce, "Gabaɗayan mu babu wanda baiji ɓatanki ba Humaira, ashe Allah zai ƙara sada fuskokinmu" sai a lokacin Mommy ta ce, "Tun ranar da na fara tozali da ke naji wani yanayi a jikina, tabbas ina ganinki sai da gaba na ya faɗi kuma tashin farko Safna ce ta faɗo mun, saboda wasu abubuwa da na gani masu fasalin na Safna" Alhaji ɗan gidan Baba Huwaila yayi gyaran murya ya ce, "Alhamdullahi ga dukkan alamu faɗuwa ce tazo dai-dai da zama, amma har yanzu kanmu a cikin duhu yake muna buƙatar ƙarin haske, kuma bazamu gasgata abin da kuke faɗa ba dole sai munyi arba da su waɗannan mutanen da kuke magana akai" murmushi Daddy yayi ya ce, "Alhaji kenan! Ai da zamu riƙe Humaira to da bamu tako tun da garin Abuja mun kawo ta ba, kuma ko da acen muka gano cewar Humaira ƴar mu ce to zamu zo nan, domin karamcin ku agurinmu bazai taɓa musaltuwa ba" Baba Huwaila ta ce, "Nikam har yanzu ban gama gasgata maganar ku ba, kawai dai so kuke ku raba ni da Indo" Baba Huwaila na zuwa nan ta rushe da kuka tana faɗin, "Allah ya jiƙanki Goggo, mutuniyar ƙwarai, ta ƙaunaci Indo fiye da tunanin mai tunani. Ta gaya mun babu irin bincike da cigiyar da bata kai ba, amma ba'a samu mutum ɗaya da ya ce ya san ko da makamancin Indo ba. Ta sha tsangwama da ƙyara kala-kala Maigari kai ne shaida, ina ce har sai da ka sanya doka akan Indo sannan lamarin ya daidaita, amma rana ɗaya ku ce mun wai Indo ƴar ku kai jama'a, ina murna Indo na ta dawo kuke neman rabani da ita."

Momma tausayin Baba Huwaila tayi saboda ga daga maganganunta zaka fahimci irin ƙaunar da take yi wa Indo, kuma ko ita da bata wani daɗe da Indo ba sai da taji babu daɗi lokacin da suka ɗauko hanyar dawowa da ita ga mariƙanta,bare kuma Baba Huwaila da suka kwana biyu da Indo. Momma kallan Baba Huwaila tayi ta fara mata bayani a nutse.
Chapter 36 · 0% Book details