← Book details Indo Sarƙa Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 76

Sashe 66

Indo Sarƙa Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokacin da ya shiga cikin falon bata nan kai tsaye ɗakin ya tura ƙofa ya shiga, bakinsa ɗauke da sallama ya shiga da sauri ta durƙushe a gurin daga ita sai towel ɗaurin ƙirji da alama daga wanka ta fito, bakinta har rawa yake ta ce. "Dan Allah ka fita kayana zan sa" tsayawa yayi yaga yadda duk da takure guri ɗaya juyawa yayi batare da ya furta komai yana rintse idanu, cen ɗakinsa ya wuce shima toilet ya faɗa ya yi wanka ya sako doguwar jallabiyya, cen ɗakin Indo ya wuce ya sameta kwance a kan gado ta takure guri ɗaya zama yayi a gafen gadon ya ce, "Ki tashi ki ɗauro alwala muyi sallah" a taƙaice Indo ta ce, "Nayi tawa" shima ya mayar mata da martani, "Nafila zamuyi" bata amsa masa ba ta tashi taje ta ɗauro alwala ta saka hijabi sannan suka gabatar da sallar nafila, ya jima yana kwararo musu addu'a tun Indo na amsawa a zuciyarta har ta gaji tayi shiru sai da ya idar sannan suka shafa gabaɗaya.

Yana shirin miƙewa murya a raunane Indo ta ce, "Ya Jamil ɗazu kamun alƙawari." murmushi yayi yace, "Ina zuwa" yana gama faɗa ya fice daga ɗakin kai tsaye ya wuce firji ya ɗebo musu fresh milk da kofuna ya dawo ya zaune, a inda ya barta anan ya dawo ya sameta, zuba musu yayi ya miƙa mata ya ce, "Ki sha wannan idan muka gama sai muyi magana" karɓa tayi tana sha tana ɗan danna waya har suka kammala sha, kwashe kwanukan yayi ya fita da su Indo tun tana jiran dawowarsa har ta gaji ta haye gado ta kwanta.

Bacci har ya fara kwashe Indo taji alamar shigowarsa, hasken fitilar ya rage musu sannan ya zagaya ta gefen Indo ya bargon da take ciki ya kwanta. A hankali ta fara janye jikinta yayi karaf ya ce, "Wacce magana kike yi ɗazu" a sanyaye tace, "Dama akan wannan..." ya katse da faɗin, "Akan me" zaro idanu taji saƙon daya fara aika mata.

KUYI HKR BAN TACE SHI BA

_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉

GA TALLAN LITTAFIN SISTER NA😊😊👇🏻👇🏻👇🏻

👑 *KARAGAR MULKI*

*MALLAKIN*
*REAL EESHOW*

_*HOME OF QUALITIES WRITERS ASSOCIATION*_

_Dasunan Allah me Rahama mejinƙai_

*PAGE* 0️⃣1️⃣➡️0️⃣2⃣

*MASARAUTAR MURISHIYOS* babbar Masarauta cemai cikakken iko wadda kaf nahiyar babu wata Masarauta wacce ta kaita kuɗi taƙama izza zalinci da rashin sanin darajar bayinsu sarki idan ya zartar da hukunci dole abi ba'ah jayayya sunada riƙo al'adun su akwai kananun masarautu goma dake ƙarƙashin babbar masarautar wa'inda suke a ƙarƙashinta.

Zaune suke da kayan bayi suna cin abinci É—aya daga cikin Æ´ammatan ce tace" Maryam muyi sauri mu gama cin abincinnan mu wuce dan naga har rana tayi sosai".
"eh wlh muyi sauri Khadija nike nikejiyewa ma karki riski Assultana Fatimah tasa ayimiki hukunci kinsan halinta abu kaÉ—an zakayi akaika É—akin duhu".
"wlh kuwa nina ƙoshima bara na tafi saboda tsaro".
"toh sekin dawo nima bara na ƙarasa na fita".
"toh".
nan Khadija ta tafi tabar Maryam tana ƙarasa cin abinci tana cikin ci wata mata tashigo tare da cewa"ɗiyata har yau baki tafiba kinsan dai halin masarautar nan daiko damma kina guri me dama-dama ke yi ki tafi da Allah".
"toh Ummah".
nanta taƙarasa cin abincinta ta tafi part ɗin Assultana Hindu.

Cikin sauri ta isa ɓangaren ta tarar da sauran kuyangi wasu na aikinsu wasu kuma sun kammala nata portion ɗin ta wuce wato cikin ɗakin Assultana Hindu samunta tayi wani falo tana waya duƙawa tayi harta idda wayarta sannan Maryam tace"Ina kwana ranki shidaɗe".
harar Maryam Assultana Hindu tayi tare da cewa"lafiya ƙlau Maryam tin ɗazu niketa zuba idon ganinki nina ɗaukama bakida lafiya shiyasa bakizo ba".
"lafiyata ƙlau ranki shidaɗe makara mukayine".
"okay amma kuma tin É—azu naga uwar bayi tana aikinta".
kame-kame Maryam tashigayi kamar kullum hakan yasa Assultana Hindu yin murmushi tace"Allah ya shiryeki kidena wannan makarar ki wuce kifara aikinki".
duƙar dakanta tayi tare da yin dariya murmushi itama tayi nanta wuce tashiga gyaran ɗakin.

"Salamu Alaikum".
"wa'alaiki salam Jakadiya ce".
"eh nice uwar bayi yakike".
"lafiya ƙlau".
"masha Allah dama ba wani abun ne yakawoni ba se akan Maryam tadena tsaya ƙawarta Khadija saboda kinga watarana ba fata akeba karta haɗu da Yarima Ahmad ya ɓatamata rayuwa a banza a wofi yanzu naganta tana tsaye tana jiran Khadija".
"to Jakadiya kullum inzata fita senayimata faÉ—an haka bataji ko ita Khadija batason take zuwa tsayata saboda karta haÉ—u dashi".
"toh ni zan koma kar a nemeni".
"nagode sosai Allah yabar zumunci".
"Ameen".
nan Jakadiya ta tafi koda su Maryam suka dawo sosai Ummansu tayi musu faÉ—a kan abinda Jakadiya ta sanarmata.

Assultana Hindu na zaune taji anbada sanarwar shigowar Jakadiya ɓangarenta bada iso tayi jakadiya ce tashigo jiki na rawa cikin girmamawa tace"barka da hutawa Assultana".
murmushin ƙasaita Assultana Hindu tayi dake nuni da itaɗin jinin sarauta ce tace"barka Jakadiya meke tafe dake".
duƙar dakai Jakadiya tayi tare da cewa"Sultan ne yace akiraki cikin gaggawa".
"toh kicemasa ina zuwa".
"godiya nake ranki shidaÉ—e nabarki lafiya".
Jakadiya taƙarasa zancenta cikin girmamawa ta tafi bayan tafiyarta Assultana Hindu ta gyara Alkyabbar dake jikinta ta tafara tafiya cikin takun ƙasaita harta isa babban falonta tadda bayin da zasuyimata rakiya na sunkuye suna jiran fitowarta murmushi tayi tare da yin gaba suka bita a baya har suka isa ɓangaren Sultana a bakin babbar ƙofar suka dakata itakuma ta wuce tashiga.

Samun Sultana tayi da Assultana Fatimah se Ashraf dake dake kusa kusa da mahaifiyarshi yana danna waya gefe guda kuma me gayya me aikice Assultana Ummuh Hauwa'uh ke hakince kan wata KARAGA ƙarasawa tayi tare da duƙawa gaban Assultana Ummuh Hauwa'uh cikin girmamawa tace"barka da hutawa ranki shidaɗe".
cikin izza dattijuwar matar tace"barka".
a ɗan taƙaice waigawa tayi gaban Sultana Abdallah tace"barka da hutawa Sultan gani".
"yauwa magana zamuyi me matuƙar mahimmanci".
murmushi tayi tare da zama kusa da Assultana Fatima gyaran murya Sultan yayi tare da cewa"ba wani abu bane yasa na taraku ananba face akan Aliyu dole ya dawo yayi aure domin ina matuƙar jin takaici a duniya idan na tuna duk faɗin masarautar nan bani da magaji *KARAGATA* inajin ba daɗi yau da safe bokan masarauta ya dubamun cewa muddum Aliyu ya dawo cikin gobe zuwa jibi za'ah iya samun rabon ɗa namiji kamar yadda aka yiwa Ashraf wato Saɗaka hima haka boka ya umarta dan haka dole sannan idan aka yimasa Saɗaka tasamu ciki za'ah kaita gidan Saɗaka har Allah ya sauketa tabamu yaron tayi nesa da masarautar nan sannan Boka Kiriyanu ya shedamun dakaina zan rife ido in jefa sanda kan Kuyangar daya tsaya ita za'ayi Saɗa kan da ita dan haka dole ya dawo kafin na mutu inason ganin magajin KARAGAR MULKIN masarautar nan".

A razane Assultana Hindu ta kalli Sultana murya na rawa zatayi magana Assultana Ummuh Hauwa'uh ta ɗagamata hannu tace"wannan hukuncin yayi ko nima naji daɗinshi dan kana aikin soja sekaƙi aure amma kuma Sultan ɗiyar wa'inne masarautun ne suke neman haɗa zuri'ah da Aliyu gadanga ƙusar yaƙi a wannan shekarar nan ni banga tsarin jadawalinba".
"masarautu Shida ne suka aiko da wasiƙa da hotunan ƴammatan na zaɓarmishi ɗiyar Sarki Muhammad wato gimbiya Usaina saboda ɗiyar aminiyar Assultana Fatimah ce kuma yarinyar tanada tarbiyya".
"masha Allah ke seki kirawoshi ki sanar dashi".
jin wadda Sultana ze aurawa Aliyu gadanga ƙusar yaƙi baƙaramun tashin hankali Assultana Hindu tashiga dakyar ta saita kanta tace"toh shikenan zan sanar dashi".
"yauwa kekuma Assultana Fatimah ki aika da wasiƙa Aliyu zeje yaga gimbiya Usaina".
cikin ƙissa Assultana tace"toh godiya nike ranka shidaɗe".
nansuka tashi kowa yakoma ɓangarensa.

Assultana Fatimah na shiga ɓangarenta ta tadda Ashraf yanata zabga uban tsaki ƙarasawa tayi ta zauna kusa dashi cikin kulawa tace"Ashraf wai meyasa bazaka kwantar da hankalinka kabarmun komai a hannuna bane".
"haba Mamah tin yaushe nacemiki nafison a kauda wannan tsinanne Aliyun me gadara kina cemun akyaleshi kuma kullum mahaifinmu ƙara nuna banbanci yake akamu kamar bakya gani haba Mamah a wannan karon inyadawo itace dawowarshi ta ƙarshe domin sena zama ajalinsa".
"kai da Allah mahaukacin banza bakaji abinda bokan masarauta yace abinda bazan taɓa bari yafaru ba kenan danaga randa Aliyu ze haifi magajin *KARAGAR MULKI* gwara naga mutuwata domin bazan taɓa bari hakan ta faruba koda zan rasa zanin ɗaurawata kuma kai inbanda sakaraine kai ai abinda yasa nabari gimbiya Usaina ina taga wata tarbiyya shiyasa na zuga Sultan a auramishi ita kadena damun kanka ninasan mezanyi wannan karon zakasha mamaki domin sede ayi mutuwar kasko shima in anyimishi Saɗakan itama tahaifi macen".
"toh amma Mamah meze hana ki sanarwa da gidansu Usaina dukda Sultan ya hana".
"kaifa banza ne ninasan abinda zanyi bara kawai ka wuce gurin iyalinka".
tsaki yayi cikin rashin tarbiyya yace"kan wannan KARAGAR banƙi inbata da uban kowa ba ato ko kece wlh".don nikisan ihar inason abu tobawanda ya isayayimin shamakidashi bangabayansaba kokece "banjimekaceba koniceko to sainakƴaleka"ainasan bazaki iyaba
yaƙarasa tare da ficewa daga part ɗin ba alamun jin haushi tayi dialing number aminiyarta Gimbiya Kareemah bugu ɗaya ta ɗauka tare da cewa"ƙawata albishirinki".
"goro fari tass shaƙamun".
"ai ina me tabbatarmiki jibi zakiga wannan yaron mara tarbiyya yazo gurin Usaina".
"wow amma gaskiya naji daÉ—i burika na sun fara cika".
nansukayita kulla abubuwansu daga ƙarshe sukayi sallama.

Bayan ta kashe wayarta ne Khadijat data gama aikinta tazo wucewa Assultana Fatimah tace"keeeh zonan".
jiki na ɓari ta ƙarasa inda take tare da duƙawa murya na rawa tace"gani ranki shidaɗe".
"ki kiramun Saratu ".
"toh".
jiki na ɓari taje ta sanarwa da Saratu cikin rawar jiki Saratu ta nufi ɓangaren Assultana Fatimah ta zube a gabanta cikin izza Assultana Fatimah tace"gurin boka( ba'ah zuwa da wando) zamuje".
"toh Assultana Ummuh Fatiman gobe ƙarya suke su ja dake faɗa da aljani bakyau".
murmushin jindaɗi tayi tare da cire sarƙar wuyanta tace"ga tukuicinki muje".
"godiya nike Allah yaja zamananinki".
"Ameen".
nan ta rifa alkƴabba cikin sirri sukabi ta ƙofar baya su ka nufi wani guri da yike duk kukoki suna zuwa daidai kukokin suka tuɓe wandunansu sannan suka shiga wata bukka guda ɗaya dake gurin.
Chapter 66 · 0% Book details