Sashe 69
Indo Sarƙa Complete Hausa Novel · about 7 min read
Janyo hannunta ya ƙarayi har sai da ta faɗo jikinsa yace, "Wai baki da hankali idan kinje me zaki ce musu, kuma da izininwa zaki fita" cikin tsiwa ta ce, "Ni kake cewa banda hankali aikasan ba'a mara hankali ɗaya sai dai idan agurinka na koyi haukan..." tun bata rufe ba Jamilu ya ɗauketa da mari cikin wata irin murya yace, "Me yake damunki ne?" Indo sakin baki tayi tana yi masa wani irin kallo kamar wata sakarya, cikin wata irin murya ta ce, "Ni ka mara?" tausayin Indo ne ya kamashi amma ganin tsiwa kwance a fuskar Indo yasa ya kuma tamke fuska yace, "Indai bazaki dinga sanin abinda zaki dinga faɗa mun ba ranki sai ya dinga ɓaci..." Tun bai ƙarasa zancen ba ta ce, "Wallahi wallahi sai na rama ra rantse da girman Allah babu wani ƙato da zai dake ni ya daki banza" Jamilu mamaki ne ya kamashi azuciyarsa yace, "Ashe har yanzu halin Indo na nan?" matsawa yayi kusa da ita yace, "Ni kike kira da ƙato? Bismillah rama kinji ko ba ni zaki mara ba?" wani murmushi Indo tayi kamar wacce aka farantawa rai da ido ya bita da kallo lokaci ɗaya yaji ya tuntsure da wata irin dariya, sakin baki yayi yana kallonta kamar ba ita take sharɓar kuka ba dariya take sosai harda ɗan durƙusawa, sai da tayi mai isarta sannan ta kalleshi fuska a sake ta ce, "Tun da na rantse sai na rama wallahi sai na rama da sannu gaggawar me kakeyi? Bari kaji Ya Jamil wallahi nama fasa tafiya idan zaka fita kabar gidanan a buɗe wallahi babu inda zani, ai bahaushe yace jiki magayi" tana gama faɗa da ƙarfin gwiwarta ta ja akwatinta ta koma cikin gidan, Jamilu tsoro ne ya ɗan ɗarsu a zuciyarsa saboda yafi kowa da wacece Indo indai ta kafe akan abu sai ta aiwatar dashi, bare wani abu ya haɗaku da ita ko ya shekara da faruwa sai ta fanshe abinta, tsoronsa ɗaya baisan wane ɗanyan aiki zata shuka masa ba, gyara tsayuwa yayi yana ayyana a ransa bazai taɓa nunawa Indo tsoron hukuncin da zata yanke ba. Lokacin da ya shiga falon har ta bararraje ta fara cin wainar ƙwai da shayin da ya ajiye musu, bai tanka mata ba ya nemi guri ya zauna shima suka cigaba da karyawa.
Tun daga lokacin babu wata doguwar magana data ƙara shiga tsakanin Indo da Jamilu, banda gaisuwa babu abinda yake haɗasu itama sai ta ga dama, washegarin ranar da ya fasa mata waya da yamma ya siyo mata wata sabuwa da sabon layi a ciki lambobi huɗu ne kawai a ciki, daga ta iyayenta sai tashi da ta Baba Huwaila, lokacin da ya bata wayar ko godiya batayi masa ba saboda a ganinta biyanta tata yayi wacce ya fasa mata.
A haka suka shafe kwana biyar acikin gidan daga gaisuwa shikenan, Jamilu tun yana ɗari-ɗari da Indo akan furucinta har ya fara sakin jiki dan itama ta saki jikinta kamar ba abinda yake damunta, sai dai har lokacin babu wata kykkyawar mu'amala a tsakaninsu, a ranarsu ta shida da tarewa Jamilu na kwance a kan kujera ya faɗa nazarin rayuwa yaji fitowarwa, ɗagowa yayi ya ganta ta fito cikin doguwar rigar leshi hannunta ɗaya ɗauke da ƙatuwar akwatunta tana janta, tashi yayi zaune yana zurawa sarautar Allah Ido dan a tunaninsa cewa zatayi zata tafi gida, da ƙyar ta dinga jan akwatin tana nishi kamar wacce aka sata dole. Tana tafe tana wata waƙa da Jamilu bai tama jinta a bakin kowanne mawaƙi ba, dan yadda yaji waƙar na fita ba wata isarshiyar ƙafiya da alama Indo ce ta haɗa abarta, sai da ta fitar da jakar har cen gate ɗin gidan kamar Jamilu zai bita sai ya tsaya yaga iya gudun ruwanta dan babu hijabi ko mayafi a jikinta.
Yana nan zaune yaji dawowarta tana tafe tana cigaba da waƙarta, duk baiti ɗaya na waƙar na ƙara tsoratar da Jamilu saboda miyagun kalmomin da suke ciki.
"In farke cikin hallita, in tsarge hanjin hallita in kama gabana a sauƙi batare da kuskure ba, naci kamar ƙuda ga rashin zuciya amma hakan bazai hanani kwakwale hanjin mutum ba, da sabuwar wuƙata..." haka tayi ta shige da fice tana waƙarta ba kai ba fasali harta faɗa kitchen, hargitsa kayan kitchen ɗin tayi da ƙyar ta samo saitin wuƙaƙarta, sharɓa-sharɓa biyu ta ɗauko da kowanne hannuwanta wani plate ɗinta na tangaran ta ɗora akan sink sai da ta ɗan leƙa Jamilu, taga duk yayi wani zuru-zuru ƙasa-ƙasa taji yace, "Yarinyar nan shirin me take anya ba wani mugun abun take ƙullawa ba" dariya ce ta subce mata ta fara murmushi a hankali, wayarta ta zaro ta fara wayar ƙarya.
"Hello eh komai na tafiya dai-dai nan da ɗan lokaci sai dai wani bashi ba" tana gama faɗar haka ta haɗa farantannan ji kake taassss, da gudu ta fito daga kitchen ɗin ta fara kai sara da wuƙa, wani throw pillows ɗinta na kujera ta fisgoshi wani kukan kura tayi ta farke shi da wuƙa abinka da sabuwar wuƙa, nan take ya tarwatse. Jamilu na ganin haka ya ɗan ja da baya yace, "Ke meyake damunki ne..." bai rufe baki ba ta fisgo wani throw pillows ɗin na kusa da wanda Jamilu yake zaune, Jamilu na niyyar magana ta luma masa wuƙa tana cewa, "Zan farke hanjin pillow kafin nazo kan na uban gayya" tana gama faɗa ta wurgar ta buga wani uban tsalle tana ɗaga hannunta me ɗauke da wuƙar sama, kafin ta sauke da gudu Jamilu ya zuba a guje ya banka ɗaki da gudu.
Indo dariya take harda riƙe ciki da sauri tabi bayansa tana cewa, "Yau idan ban farke ka ba hankalina bazai kwanta ba" tana shiga Jamilu ya rafka Ihu yana cewa.
"Dan Allah Sarƙa karki farkeni ko me kike so zanyi miki"
SU JAMILU YAU ANMANTA DA AYUSHER AKE CEWA SARƘA🤣🤣🤣
KUYI MALEJI DA WANNAN🤥
_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
[03/10, 19:15] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀ï¸
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share
*INDO SARƘA*🤸ðŸ¼â€â™€ï¸
*BY*
*AMEERA ADAM*
*FOLLOW ME @WATTPAD*
_*AmeeraAdam60*_
GARGAÆŠI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.
_*WANNAN LITTAFIN GABA ÆŠAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE UðŸ¤*_
99&100
🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚
Indo bata saurareshi ba ta ci gaba da kaiwa iska suka da wuƙa tana cewa, "Gwara na kawo ƙarshen komai kowa ma ya huta, yadda na farke hanjin filon nan sai na farke hanjinka." Jamilu cen saman gado ya ɗare ya janyo ƙaton bargo ya kare da shi yana yiwa Indo magiya" sun ɗan jima a haka sannan Indo ta tunkaro shi gadan-gadan, daga cen ƙofar gida suka ji ana bubbugawa da ƙarfin gaske Indo ce ta juya ta fara takawa har zuwa falo, Jamilu na ganin tayi gaba ya diro daga gado cikin shammata ya fita a guje banda haki da gumi babu abinda yakeyi, Indo daga bakin ƙofar falon ta tsaya tana ƙyalƙyala dariya, bugu ake kamar za'a ɓalle ƙofar har Jamilu ya ƙarasa bakin ƙofar ba'a daina bugawa ba, sai da ya tsaya ya ɗan saita nutsuwarsa amma dukda haka kallo ɗaya zaka masa ka fahimci yana cikin wani hali, sai gumi yake yi ta ko'ina ga hakin da yakeyi.
A hankali ya zare sakatar gate ɗin ya fita, maƙocinsa Malam Inuwa ya gani wanda gidansa yake jikin gidansu Indo, saita nutsuwarsa yayi ya miƙa masa hannu suka gaisa yana ɗan ƙoƙarin kawar da yanayin da yake ciki, Inuwa ya ɗan fahimci wani abu sai yace, "Malam Jamilu muna zaune da Iyalina muka fara jiyo ihu sama-sama, da farko na so na share amma kuma bisa ga koyarwar addininmu daya nusar damu haƙƙin maƙotaka, nace bari nazo naji ko lafiya? " Jamilu duburburcewa yayi ya ce, "Am dama ai dama muna ɗan wasanni ne irin na masoya to bamu zaci sautin na fita waje ba" Malam Inuwa sam bai yarda da abinda Jamilu ya faɗa ba amma sai yace, "Ah lallai haka ake san irin wannan soyayya, kasan dake katangarmu ɗaya ana iya jin hayaniya idan akayi magana da ƙarfi "murmushin yaƙe Jamilu yayi ya ce, "Ai fa dama haka ne" cikin zolaya Malam Inuwa yace, "Zan turo madam nima tayi course muma mu dinga wasan farke-farken" Jamilu dariya ya sa saboda ya lura da Malam Inuwa tun tariyarsa mutum ne me barkwanci, Jamilu yace. "Amma sai ka biya dan ba'a aikin banza a Kano, yauwa anjima dama zata shigo su gaisa kasan gajiyar biki bata samu ta leƙa maƙota ba" hira suka ɗan taɓa sannan sukayi sallama.