Sashe 4
Indo Sarƙa Complete Hausa Novel · about 8 min read
Indo ɗaga kanta sama tayi kamar mai tunani aikuwa tai farat tace, " Yauwa Allah ya taimakeka Ina kadarorina na gurunka da Goggo ta baka kafin ta rasu to kawai a saida gonar bayan gidan Idi mai Nama dama bata da girma abiya da ita sauran kuɗin ka bawa Baba Huwaila ta ja jari " Wata tsawa Mai Gari ya bugawa Indo ya ce, " Ke baki da mutumci ko? a yaushe Kakarki ta bani wasu takardu? Baƙin sharri zaki ƙullamun " Daga Indo, Jamliu har Baba Huwaila Mamaki ne ya kamasu, lokaci guda aka fara kus-kus kowa da abinda yake tofawa agurin, Baba Huwaila ce ta taɓo Indo ta ce, " Karna ƙara jin bakinki Indo kinji "
Indo badan taso ba ta ja baki ta rufe, Baba Huwaila ta cewa Mai Gari, " A gaskiya Ranka shi daɗe dubu biyu zan bayar idan zasu karɓa shikenan idan kuma sun raina na riƙe abuna" Mlm Sani ganin da gaske Baba Huwaila take yasa ya amince gudun kar yayi biyu babu, atake Jamilu ya zaro dubu guda ya basu yace su biyoshi gida su karɓi sauran, haka Fada ta watse kowa yayi nasa gurin.
Tun a hanya Jamilu ya rufe Indo da faɗa ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba kamar zai dake ta har suka je gida, ganin Faɗan yaƙi ci yaƙi ƙarewa yasa Baba Huwaila itama ta fara nata bambamin faɗan, " Wai yanxu Jamilu akan naira dubu biyu ka sa Marainiyar Allah a gaba da masifa kamar ka cinyeta ɗanya, wallahi da nasan haka zakayi daka riƙe abinka tunda kasan dai nafi ƙarfin dubu biyu bare kamana san iyawa " jin irin faɗan da Baba Huwaila take yi yasa ya ɗebi takalmansa ya fice daga gidan, sai da taga ya fita sannan ta sa Indo a gaba da rarrashi tana mata nasiha akan abinda ta aikata ba dai-dai bane.
*DA DADDARE*
Tun yamma Indo ta zaƙulo wasu kayan Goggo waɗanda aka bata da zummar za'a rage mata su ta dinga sawa, wani zumbulelen farin hijabin Goggo na sallah ta fito dashi fili, ɗaga ƙasan filo tayi ta sasu ciki tana jiran dare yayi, ana sallar Isha'i Indo tayiwa Baba Huwaila sallama dan har saƙo ta barmata idan su Saude sun biyo mata zuwa dandali bazata ba, Baba Huwaila ba ƙaramin mamaki tayi ba najin haka amma sai tayi tunanin ko gajiya ce ta sa Indo zata kwanta da wuri.
Cikin dare lokacin ƙafa duk ta ɗauke banda kukan tsuntsaye ba abunda yake tashi, alokacin ta farka daga bacci kayan wajen Goggo tasa ta ɗauko zumbulelen farin hijabin tasa, kwandon kayan kwalliyarta da shafe sati bata buɗeshi ba, ta buɗe ta ɗauko hoda ta zazzaga ta shafe fuskarta, hannu da ƙafafuwa Ludayin miyar Baba Huwaila da tun rana ta ɓoyeshi ta ɗauka ta sa a hijabi, ƴar fitilarta ta ɗauka ta fito daga ɗaki saɗaf-saɗaf ta je wajen bakin ƙofa ahankali ta zare sakata ta fice, kamar Aljana ita kaɗai ce a waje haka ta samu ta ƙarasa bayan katangar gidan Mai Gari ( _Dake gida huɗu ne tsakanin gidana Baba Huwaila da na Mai Gari_) ta kamata ta ɗane ta dirga.
A hankali ta ɗaga labulen ɗakin Mai Gari ta shiga ta same shi a kwance baccinsa yake hankali kwance, toshe bakinta tayi tana dariya ƙasa-ƙasa musamman da ta tuna irin muguntar da zata yiwa Mai Gari, sai da tayi ta gama ta koma saitin kan Mai Gari ta zaro ludayin miyar ta dai-dai ci kan sa ta bashi ƙwaaal, azabure Mai Gari ya tashi yana susar gurin baya yaja ganin mutum tsaye cikin fararen kaya.
Indo canja murya tayi shigen ta Goggo sannan ta fara magana, " Ni ce Goggo Kakar Indo Sarƙa nazo tafiya kai cen makwancina tunda cin Amana zakayi " Mai Gari cikinsa ne ya juya baiyi aune ba sai ji yayi ɗumi na bin wandonsa, Indo na ganin Fitsari na bin ƙafar Mai Gari ta gimtse Dariyarta ta kuma cewa.....🥱
_Ummou Aslam Bint Adam_😉
[17/06, 03:31] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀ï¸
*INDO SARƘA*🤸ðŸ¼â€â™€ï¸
*BY*
*AMEERA ADAM*
*FOLLOW ME @WATTPAD*
_*AmeeraAdam60*_
https://chat.whatsapp.com/HqkJ9DNdj356ipogZ4Sldt
GARGAÆŠI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.
_*WANNAN LITTAFIN GABA ÆŠAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE UðŸ¤*_
7&8
Indo na ganin fitsarin na bin ƙafar Mai gari ta gimtse dariyarta ta kuma cewa, " Bani kaɗai na taho ba da sauran Abokan zamana muke tafe amma na dakatar dasu a tsakar gida domin aikin nawa ne " ɗan ɗingisawa Indo tayi irin yanda Goggo take tafiya tana shirin sake magana Maigari yace, " Ki dubi Allah da Muhammadu Rasulillahi Goggo karki tafi dani wallahi duk abinda kike so ki faɗa Goggo zanyi miki shi " shiru Indo tayi ta nufi hanyar bakin ƙofar ɗakin tana tafe tana ɗingiwa sannan ta ce, " Kaaaaaai karka gaya mana maganar banza ba makawa sai mun tafi da wata gaɓa daga jikinka acikin daren nan domin kaci amanar marainiyar Allah, zaɓi ya rage gareka shin ƙafarka zamun fara cira ko hannunka? Domin mu fatalwa muddun muka ziyarci mutum bama tafiya sai mun bar masa wata shaida " Mai gari kamar wani ƙaramin yaro yana jin haka ya fashe da kuka gwiwa bibbiyu ya tsugunna yana baiwa Indo haƙuri, ganin duk ya firgice ya fita hayyacinsa yasa Indo ta ce, " Munyi maka afuwa mun fasa tafiya da gaɓɓan jikinka, nemi guri ka kwanta kayi rufda ciki zamuyi maka irin alfarmarmu "
Tun Indo bata rufe baki ba Mai gari yayi sufa ya kwanta jikinsa banda ƙyarma ba abinda yake yi, ganin ya juyo yana kallonta ta ce masa, " Idan ka kuma kallonmu zamu tafi da ƙwayar idanunka " aikuwa ba shiri Maigari ya sunkuyar da kansa ƙasa, Indo kusurwan bangon ɗakinsa ta kallah ta fara magana ita kaɗai, " Au Marka mai waina shigowa kika yi tafiya da Ɗan naki, ay ya nemi afuwa da kinyi zamanki inkika ce mun kina san ganinsa ba sai mu taho miki da shi ba " gaban Mai gari yankewa yayi ya ƙara faɗuwa jin an ambaci Marka mai waina, shi dai a iya saninsa Mahaifiyarsa ce take amsa sunan Marka mai waina duk cikin ƙauyensu kuma ta rasu wajen shekara guda rabi da suka wuce, juye-juye yake da kai yana san ɗagowa aikuwa Indo na ganin haka ta ce, " Marka mai waina Ƙwaƙulomin idanunsa kinga ma bawa Muzammilu mai Icce ya wuce mana dashi kafin mu ƙarasa tafiya da mutanen da ya kamata mu tsitstsinta acikin daren nan "
Mai gari rintse idanunsa yayi gam yana yiwa Indo magiya da ban haƙuri, Indo fakar idon Mai gari tayi ta ɗan sunkuyo ta kuma bashi ƙwaaaal da ludayin miyar hannunta, Mai gari Zabura yayi zai tashi kuma ko me ya tuna da sauri ya koma ya kwanta yana sosa gurin. Indo takawa tayi a hankalin tana faɗin haba Ramma ya kika fara ɗaukan fansa tun bamu tafi dashi cem cikin jinsin mu ba? " Ludayin hanunta ta sa a jikin kofar langalangar ɗakin Maigari ta fara ƙoƙawa ji kake ƙiƙar-ƙiƙar sai ta sa ƙafarta ta fara buga ƙasa zuwa cen sai ta fara wani irin nishi da gurnani hmmmmmm kamar wata rago, duk inda tashin hankali ya kai Maigari yaje cen gaba ɗaya jikinsa ya jiƙe sharkaf da gumi, wandonsa duk ya fitsareshi da fitsari, zura kanta tayi tsakar gida da ke da hasken farin wata ta hango wani ƙaton buhun geron Mai gari wani murmushi tayi da ta tuno irin mugunta da zata yi masa da shi idan ta kuma dawowa a wani daren, wata sanda ta hango ta zura hannu ta ɗauko tana shigo da ita da sauri ta ɗaga ta makawa Maigari a gadon baya tare da ranƙwala masa ludayin a goshinsa, a zabure ya tashi yana buga ihu da neman ɗauki cikin magiya ya fara magana, " Dan Allah Goggo ku faɗi duk abinda kuke so zanyi muku wallahi kome kuke so zanyi shi ku daina azabtar dani dan Allah kuyimun rai " Indo na daga gurin da take ta fara bubbuga hijabinta kamar mai shirin tashi sama tana wani irin ɗan gurnani, sannan ta ce masa, " Zamu koma makwancinmu amma ka sani zamu ƙara dawowa, zamu baka saƙo idan ka wani gari gobe duk wanda ka gayawa abinda ya faru abakin ranka, tashi ka shige ƙarƙashin gado har sai anyi assalatu sannan ka fito " tun bata rufe baki ba Maigari ya ɗaga zanin gado ya shige ciki dake irin kadon ƙarfen nan ne mai rumfa.
Indo fitowa tayi daga ɗakin Mai gari alokacin Baraka ta fito hannunta ɗauke da buta ihun Maigarin da taji ne ya tashe ta, sam bata kawo Maigari bane tayi tunanin ƴan kwamati ne suka kama ɓarayi, mutum ta gani da farin hijabi da sauri taja baya ganin haka yasa Indo ta ce, " bururururu bum bum bum bum kuzo maza ga wata ta fito ku janyota mu tafi da ita " Baraka sakin butar tayi ta koma ɗaki da gudun gaske tana banko ƙofa.
Indo na ganin haka ta tsugunna ta fara tafiya da rarrafe tana tafe tana baza ƙasa dan gudun kar aga sawun tafiyar mutum da safe asirinta ya tonu idan zata ƙara komawa.
Tun ta da samu ta kama katanga ta dirga take tafe tana waige kamar mara gaskiya, da sauri ta samu ta tura ƙofar gidansu ta shiga buta taci karo da ita a ƙofar ɗakin Baba Huwaila da sauri ta ɗauka ta fara wanke fuskarta da hannuwanta xuwa ƙafarta, tana gamawa ta faɗa ɗakinta kan katifa ta fashe da dariya, Indo dariya take yi harda riƙe ciki sai da tayi mai isarta sannan ta kwashe kayan Goggo ta cusa cen cikin jakarta ta koma ta kwanta.
*A CEN GIDAN MAI GARI*
Tunda Maigari ya shige ƙarƙashin gado ko motsin kirki ya kasa yi, lokacin da yaji Indo ta buga ƙara tana cewa a tafi da Baraka luff ya ƙarayi gabansa na dukan uku-uku, yanda yaga rana haka ya ga ƙarshen darensa, har akayi Assalatu Maigari kasa fitowa yayi saboda yana gudun kar ya fito ya kuma gamuwa da fatalwar Goggon Indo.