← Book details Indo Sarƙa Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 76

Sashe 24

Indo Sarƙa Complete Hausa Novel · about 6 min read

Lokacin da suka sauka garin Abuja Magriba ta kawo kai,SUWAIT HOTEL acen suka yada zango ɗakinsu ƙayatacce ne mai ɗauke da kayan alatu kala-kala, Honourable zaune yake a gefen gado yana cire babbar riga, Indo zaune take akan kujera one siter miƙewa tayi zata fita ya ce, " Cutie ina zaki haka? " cikin yanayin gajiya ta ce, " So nake na kama ruwa " murmushi yayi ya ce, " Ga Toilet nan muje na rakaki ki watsa ruwa " da mamaki Indo ta ce, " Honey kaine zaka rakani na watsa ruwan? " Honourable tunowa yayi da suɓutar bakin da yayi, cikin wayancewa ya ce, " Ina nufin na rakaki bakin banɗakin ki shiga ki watsa ruwa " Indo gyaɗa masa kai tayi cikin nuna yarda da abinda ya furta, matsawa yayi kaɗan tana biye da shi ya nuna mata Toilet ɗin, shiga tayi a ɗarare saboda yanda taga yanayin gurin tunda take bata taɓa taka ko makamancin wannan gurin ba, tsaye tayi ta rasa gurin da zatayi fitsari daga ƙarshe ta yanke shawarar tsugunnawa a ƙasa tayi abinta, famfo ta kunna tayi tsarki ta ɗauro alwala, tana fitowa ta sameshi zaune daga ahi sai singlet da gajeren wando, yi tayi kamar bata ganshi ba ta wuce ta fara duba jakarta ko zata samu babban mayafin da zata iyayin sallah da shi, duk cikin kayanta matafi ɗaya ne sai kayan sawarta shawara ta yanke ta ɗauki babbar rigar Honourable ta yafa kamar mayafi ta tayar da sallah,ajere ta rama sallar la'asar da magariba bayan ta idar ta fara Addu'ar Allah ya cika mata burin abinda ta fito nema,Baba Huwaila ce ta faɗo mata take ta fara zubda kwalla musamman da ta san halin Baba Huwaila da sa abu arai, kuka take harda shashsheƙa tanajin inama ta koma ta cigaba da zama da Baba Huwaila,agefe ɗaya tunowa tayi da irin gorin da Baraka tayi mata,wani sabon kukan ne ya ƙara zuwar mata,Honourable ne ya tako a hankali ya tsugunno gurinta ya dafa kafaɗarta ya ce, " Haba Cutie kukan me kike yi? Me zai dameki kina tare da Honey? " Indo janye jikinta tayi sannan ta ce, " Gaskiya Honey ka ɗaukeni daga gurin nan ka kaini gidan rediyo ka kai musu cigiya " a fakaice Honourable ya ɗan yamutsa fuska sannan ya ce, " Haba Cutie nace miki ki ɗaukeni tamkar mahaifinki kina tunanin zan cutar da ke ne? " Kafin Indo ta bashi amsa sukaji nocking a bakin ƙofa Honourable ne ya buɗe, abinci ne aka kawo musu tun daga bakin ƙofa Honourable ya karɓa ya ajiye, dawowa yayi gurin Indo alokacin ta ajiye Babbar rigarsa ta ɗauki mayafinta ya yafa ta koma cen gefe ta takure,kusa da ita ya zauna har suna iya jin numfashin juna ɗan matsawa Indo tayi gabanta na faɗuwa, kamo hannunta yayi ya ce," Haba Cutie ki bani haɗin kai mana akan abinda bai taka kara ya karya ba muyita kewaye-kewaye " ƙara matsawa yayi ya cigaba da cewa, " Zakiji daɗin haɗuwarmu domin Allah kaɗai yasan alherin da zaki samu agurina, idan har kika amincemun a yau ba sai gobe ba zan mallaka miki tsadaddiyar mota, kuma sai..." Indo ce ta katseshi tana fisge hannunta daga cikin nasa tana ƙyaƙyacewa da wata irin dariya, Honourable murmushi yayi a tunaninsa maganarsa ce ta faranta ran Indo har yana tsammanin yayi nasara akanta,cikin zuciyarsa ya ke faɗin, " Yarinya ai nasan za'a rina waɗanda suka fiki taurin kai ma mun buga dasu kuma sunyi biyayya..." wata sabuwar dariyar tata ce ta ƙara katse masa tunaninsa, kallanta yayi da mamaki ganin tana ta ɓaɓɓaka dariya ba kyaakykyautawa ga wani irin juya idanu da takeyi kamar mai yin fari,yana shirin yin magana zumbur Indo ta miƙe tsaye tana ƙwambare ƴan yatsunta tana cigaba da dariya haɗe da zare idanu tana kalle-kalle.

Cikin Honourable ne ya kaɗa tsoro ya fara kamashi yana daga zaune ya fara ja da baya,Indo taku uku ta ƙara ta ɗanyi baya da shi girgiza kanta ta farayi take ɗan kwalinta ya fita gashin kanta ya ware cikin wata irin murya ta fara magana, " A yau basai gobe ba zamu fyeɗeka tabbasa hanjin cikinka dashi zamuyi kalaci wuuuuuuuuuuuu gurururu kai ku kwantar mun da shi " Honourable najin ance a kwantar dashi a zabure yaja baya tumbinsa banda rawa ba abinda yakeyi, cikin tashin Hankali ya ce, " Humaira dan girman Allah kiyi haƙuri wallahi bansan haka kike ba,tsautsayi ne da sharrin shaiɗan..." Wawan Ihun da Indo ta kwara ne ya katse shi wani irin gumi na daɗa kaiyo masa, tsaye tayi ta dira kan plate ɗin abincin da Honourable ya ajiye take abincin ya watse a tsakar ɗakin,ɗaukan ɗayan Plate ɗin tayi ta ƙaso gurin Honourable ta juye masa a ka sannan ta fara nunoshi da plate ɗin tana cewa, " Idan kanasan ka fanshi kanka sai ka cinye farantin nan idan ba haka ba sai mun daddatseka " jiki na rawa Honourable yace, " A dai canjamun wani abun amma ina ni ina iya cinye plate hukuncin yayi tsauri..." kafin ya rufe baki Indo tsalle tayi tun iya ƙarfinta tana dira ta buga masa Plate ɗin a saman kansa, wani irin Ihu Honourable ya kwara ya faɗi cen gefe yana maida numfashi, Indo dariya ta sa ta cigaba da cewa, " Kuzo mu farke ƴaƴan cikinsa ku bawa ƴaƴanmu su cinye " yana daga kwance ya fara ja da baya yana ɗaga hannu alamar roƙo, Indo wani tsallen ta buga ta haye saman gado ta fara kwaso fulallika da zanin gadon tana jefawa Honourable,ilahirin jikinsa banda rawa babu abinda yakeyi tunani yayi kawai akan yaje ya murɗeta yasa abu ya ɗaureta, yunƙurawa yayi ya tashi yana tunanin ta inda zai fara kamo Indo, a gefe ɗaya kuma yana fargabar taɓa shi karta masa illah,Indo kamar ta shiga zuciyarsa tana ganin tashinsa jikinta ya bata da sauri ta sauka daga kan gadon ta kurma wani uban ihu haɗe da tafiya da gudu taba fisgo Plasma Tv dake jikin bango, tana ɗaukota ta hau zaro ido tana kalle-kalle wata irin dariya ta fashe da ita ta buga Television ɗin a ƙasa, da sauri Honourable ya ja baya yana dafe ƙirji Tv stand ɗin ta fizgo ta jefawa Honourable da sauri ta fisgo wayar jikin Tv da ƙarfin gaske, ihu tayi ta fara buɗe baki kamar mai shirin kai cizo ta fara shauɗawa Honourable bulala ta ko'ina.

KUYI MANAGE DA WANNAN SABODA RASHIN CAJI🤒

_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
[18/07, 18:28] Ameera Adam: *FOLLOW ME @WATTPAD*
_*AmeeraAdam60*_

GARGAÆŠI BANYAR WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.

_*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_

_SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._

*Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.*

47&48
Chapter 24 · 0% Book details