← Book details Indo Sarƙa Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 76

Sashe 60

Indo Sarƙa Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su Lubna da sauran Ƴaƴan Alhaji Haruna gabaɗaya basu ji daɗin abinda mahaifiyarsu ta aikata ba, Lubna sai yanzu take jin wata irin kunyar Indo, babban tashin hankalinta Yaseer ne, tunda ta san tunda cen ma Yaseer ba santa yake ba ta Indo yake bare yanzu da haka ta faru. Cikin lokaci ƙalilan duk ta rame ta bushe ta lalace kamar wacce tayi laifi, sai abu na gaba da idan ta tuna yake hana ta bacci shine hukuncin da za'a yankewa mahaifiyarsu, gashi tun ba'aje ko'ina ba mahaifinsu ya sauwaƙewa mahaifiyarsu. Waɗannan tunane-tunane ne suka haɗu suke dagula lissafin Lubna, wanda bacci ma ya ƙauracewa idanunta.

Wata ranar Laraba ce aka zauna aka fara sauraron ƙarar su Indo, kotun cike take da mutane aka aka shigo dasu suka tsaya gurin mazaunin masu laifi, magatakarda ne ya karanta ƙunshin tuhumar sannan Alƙali ya kalli su Hadari ya ce, "Kai meye sunan ka?"

Hadari ya ce, "Sunana Salihu amma anfi sanina da Hadari" Alƙali ya ce, "Shin kaji ƙunshin tuhumar da ake muku" Hadari ya ce, "Naji ya me shari amma a taimaka ayi mana afuwa wallahi sharrin sheɗan ne" ɓangaren Hajiya Safiya Alƙali ya koma ya tambayi sunan ta ta ce, "Sunana Safiya Alhasan" Alƙali ya ce, "Shin ko akwai dalilin da ya sa kika aika a kashe ƴar mutane? Idan akwai kotu tana sauraren ki"

Hajiya Safiya ta kalli Indo dake cen a zaune kusa da mahaifiyarta ta ce, "Ya me shari'a bani da wani dalili face ƙyashi, hassada da baƙin ciki da suka ruɗeni. Kasancewar mun taso gari ɗaya kuma unguwa ɗaya da Safna, sai ya kasance makarantarmu ɗaya kuma ajinmu ɗaya da ita. Safna tana da ƙwazo da ƙoƙari yadda har makarantar mu ya kasance ansan da ita, kafin zuwanta duk ajinmu dama na girmesu dan haka gabaɗaya sai suke tsorona, duk abinda na faɗa basa iya ƙetarewa kuma duk abinda na gani agunka nace ina so zan karɓa baka isa ka tanka ba. Kwatsam sai aka kawo Safna ajinmu, tun daga zuwanta na fara nuna halina akanta amma sai taƙi amince da shi, saboda bata da tsoro ko kaɗan kuma girmana baisa ta ji shakkuna ba. Ganin haka yasa sauran ƴan ajinmu suka fara daina tsorona, daga baya ma sai gabaɗaya ƴan ajinmu suka rainani, tun daga lokacin tsanarta ta ɗarsu a zuciyata. Sai kuma ƙoƙarin da take da shi duk lokacin da akayi jarrabawa ita take zuwa ta ɗaya, ni kuma kusan nice ta ƙarshe ta biyun ƙarshen aji. Wata rana munyi faɗa da ita, dan kuwa ni na takali faɗan kawai sai ta mun gorin ƙoƙari nikuwa na lakaɗa mata duka, aikuwa tana guduwa ta samu ƴan ajinmu suka fara yi minj waƙar Safiyya ganɗama daƙiƙiya, tun daga ranar sunana yayi fice a makarantarmu, har ta kai ta kawo idan bakace Ganɗama babu wanda zai ganeni. Sai na koma mujiya a cikin makarantar kowa tsokanata yake yi, ana haka har Yayana ya zo ya sanar da shugan makarantar, daga ranar ne na ɗan samu sasaauci. Ana cikin haka sai su Safna suka dawo nan layinmu gida biyu ne kawai ya rabamu da su, a lokacin kuma muna shekarar mu ta ƙarshe a sakandire. A lokacin ina tare da saurayina Sulaiman yana ƙyalla ido da ya ganta, ya daina zuwa gurina dana matsa masa da tambaya ya kwatanta mun ita, tare da cewa ya faɗa tarkon ƙaunarta. Ba ƙaramin tashin hankali na shiga a lokacin ba, amma sai mahaifiya ta tausheni tare da nusar dani wataƙila dama ba mijin aurena bane.

Wata rana da yamma na fita naci karo da Safna tana zance da Khalil, tunda na ƙyalla ido akanshi naji duk duniya babu wanda nake ƙauna kamar shi, a ranar dashi na kwana a raina ko baccin kirki banyi ba, tunani na dinga yi yadda zan samu na samu koda lambarsa ce amma na kasa. Sai dabara ta faɗo mun akan na ƙulla ƙwawance da Safna ko na samu ta saki jiki dani na samu lambarsa a gurinta. Shiryawa nayi naje gidansu na sameta muka gaisa fuskarta ba walwala, kasancewar kowa yasan ba shiri muke da Safna, sunkuyar da kai ƙasa nayi na nemi alfarma da mu aje wannan rashin jituwar da muke gefe ɗaya mu cigaba da rayuwa kamar kowa, amsa mun tayi daga haka na fara nuna soyayyata ga Safna a fili wanda a zuciyata ba haka bane, ita kanta Safna da farko ƙin sakin jiki tayi da ni, sai daga baya ta saki jikinta muka cigaba da ƙawancenmu gwanin sha'awa..." Alƙali ne ya ƙatse Hajiya Safiya sannan lauyoyi suka cigaba da fafatawa, daga ƙarshe Alƙali ya ɗaga shari'ar zuwa goma ga watan gaba, sati biyar kafin komawarsu.Hajiya Safiya da su Hadari aka tasa ƙeyarsu gidan yari, haka kotun ta tashi mutane na Allah wadai da hali irin na Hajiya Safiya.

BAYAN SATI BIYU

A yau ne su Indo suka zana jarrabawarsu ta ƙarshe, murna gurinta tare da sauran ɗalibai ba'a magana. Kuma tun safiyar ranar Yaseer ya tura mata saƙwanni kala-kala na soyyaya, kuma a ranar ne ya da Daddynsa abinda ke tsakaninsa da Indo, Daddy ba ƙaramin farinciki yayi ba, a take kuma ya kira ƴan Mahaifin Indo ya sanar dashi, shima ba ƙaramin daɗi yaji ba nan take ya kira sauran ƴan uwansa ya sanar dasu.

_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
[02/10, 19:30] Omu Aslam Bint Adam✍🏼: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share
*INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️
*BY*
*AMEERA ADAM*

*FOLLOW ME @WATTPAD*
_*AmeeraAdam60*_

GARGAÆŠI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.

_*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_

_SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._

*Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.*

91&92

Murna sosai suka yi da jin wannan maganar kowannensu sa albarka ya dinga yi da Allah san barka, Lokacin da Indo taci karo da saƙon Yaseer wani irin daɗi taji a ranta, bayan ta gama karantawa lumshe idonta tayi tana ƙara maimaita saƙon nasa a zuciyarta. Tana cikin wannan yanayin kiran Yaseer ya shigo wayarta, zaro idanu tayi kamar tana gabansa sai kuma taji wata irin kunyarsa ta kama ta, kamar bazata ɗauka ba har kiran ya kusa katsewa ta ɗaga ta kara a kunnenta, cikin sanyin murya ta ce, "Hello Ya Yaseer" daga cen ɓangaren ya amsa da, "Hi ƙalbi" runtse idonta tayi tana murmushi, sannan ya cigaba da cewa.

"Yau na sauke dakwon da na daɗe ina yi na tsawon shekaru, a duk lokacin dana tuna bakya tare dani zuciya da ruhi kan shiga firgici, akan kar wani yayi mun shigar sauri sai gashi yau Allah ya bani ikon gabatar da soyayyar da na jima inayi miki, Humaira bantaɓa ƙaunar wata a duniya kamar yadda nake ƙaunarki ba, a kullin zuciya ta azalzalata take akan na gabatar miki da soyayya ta, da ƙyar nake iya lallashinta har muka kawo tsawon wannan shekarun tare, ki taimaka ki amshi soyayya ta ko na samu sauƙin abinda yake mun yawo a cikin zuciyata, karki hukunta ni da abinda bazan iya ɗauka ba domin tabon bazai taɓa gogewa a zuciyata ba." maganganun Yaseer ba ƙaramin nutsar da zuciyarta yayi ba, haka kawai ta samu kanta cikin farinciki. Wasu tsuntsaye ta ƙurawa kallo dake cikin garden ɗin amma sam hankalinta na wani guri daban, jin tayi shiru yasa Yaseer ya ce, "Humaira! Zaki iya hukuntani ta inda kika ga dama, amma dan Allah ki furta mun kalmar kina sona" ya ƙarasa faɗa a raunane kamar me shirin yin kuka. Firgigit Indo ta dawo da hankalinta kanshi, murmushi tayi tana jin ƙaunarsa na fisgar zuciyarta cikin wata irin murya ta ce, "I love you too Ya Yaseer" sai kuma tayi ɗif saboda tunowar da tayi da alƙawarin da ta yiwa Jamilu, ihun murnarsa ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin da ta faɗa, a gaggauce ta ce, "Ya Yaseer ina zuwa" bata jira cewarsa ba ta katse wayar da niyyar kiran Jamilu ta sanar da shi abinda ke faruwa, saboda Allah ya sani zuciyarta tayi nisa a soyayyar Yaseer, bazata iya ƙin furta masa kalmar so ba.

Kamar almara tana katsewa kiran Jamilu ya shigo wayarta, fuskarsa da yanayin damuwa ya ce, "Ayusher da wa kike waya tun É—azu ina kira busy" da kamar ta ce masa Yaseer ne, sai ta tuna yadda yake nuna bayajin daÉ—in yawan wayar da takeyi da shi, basarwa tayi ta ce, "Ya Jamil masu yi mun Congratulations ne fa" sai a lokacin ya saki muryarsa bayan sun gaisa yayi mata congrats sannan yace.

"Ayusher!" yanayin yadda ya ambaci sunanta ne ya faɗar mata da gaba, tare da jin wani yar tun daga tafin ƙafarta har tsakiyar kanta. Jamilu ya cigaba da cewa.

"Na shafe tsawon shekaru ina dako tare da ɗaukar nauyin abinda zuciyata ce kawai zata iya ɗaukansa, ba dare ba rana koyaushe addu'ar zaɓin Allah nake tare da fatan Allah ya cika mun burina, kunnuwana sun kurumce ta yadda banajin daɗin sautin muryar kowacce mace sai ke" a zabure Indo ta zaro idanu haɗe da dafe ƙirji amma bata ce komai ba, ya ci gaba da cewa.
Chapter 60 · 0% Book details