← Book details Indo Sarƙa Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 76

Sashe 58

Indo Sarƙa Complete Hausa Novel · about 7 min read

Lokacin da Daddy yaje asibiti Musty bacci yake saboda Alluran da akeyi masa, ansamu nasarar ciro harsashin kuma har angyara ƙafar annaɗe da bandeji. Duk abinda ya kamata Alhaji Khalil ya biya sannan ya kira Ƙanin Mahaifin Musty ya sanar dashi, kasancewar Musty maraya ne. kafin wani lokaci ƴan uwan Musty sun cika asibitin.

Bayan kwana biyu jikin Musty yana ƙara samun sauƙi sosai, Da farko Mahaifiyar Indo cewa tayi sai dai Indo ta haƙura da zuwa makarantar, bayan da Daddyn Indo ya gaya mata abinda ya faru. Sai dai Daddy yayi mata nasiha mai ratsa jiki sannan ta ɗan samu nutsuwa, duk ranar da Indo take da Jarrabawa Fahad ne yake kaita, ya jira ta gama ya dawo da ita gida.

Su Hadari fir suka ƙi faɗar wanda ya saka su Kashe Indo sai da suka ji wahala tukunna suka faɗa, a lokacin Alhaji Khalil na gida Kwamishina ya kirashi zuwa cen Headquarter. Bayan yaje ya saurari abinda su Hadari suka faɗa a razane ya ce, "Hajiya Safiya fa? Hajiya Safiya dai matar ɗan uwana?" ana cikin haka Ɗan uwansa Yaya Haruna tare Ɗansa Muhsin suka zo, Ɗan uwan nasa na zuwa ya ce, "Khalil kace mun sun faɗi wanda ya tura su waye dan Allah? Wanne azzalumin ne?" Alhaji Khalil kunyar Yayansa yake yace matarsa ce, Kwamishina ne ya karɓi zancen da, Sunce Hajiya Safiya ce ta sasu kuma har Video lokacin da take basu kwangilar suka nuna mana, tare da kwanan watan ranar da taje ta same su a mazauninsu, Kwamishina ya ƙarasa faɗa yana nuna masa bidiyon wayar Hadari. A razabe Mahaifin Lubna ya ce, "Safiya tawa kai ƙarya ne, a rasa wa za'ayiwa sharri sai Iyalina? Gaskiya da sake bazai yuwu ba."

_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
[02/10, 19:30] Omu Aslam Bint Adam✍🏼: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share
*INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️
*BY*
*AMEERA ADAM*

*FOLLOW ME @WATTPAD*
_*AmeeraAdam60*_

GARGAÆŠI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.

_*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_

_SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._

*Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.*

89&90

Kwamishina gyaran murya ya yi ya ce, "Alhaji dan Allah ka saurareni ka bamu haɗin kai, dan sun faɗi haka bashi zai nuna cewar da gasken hakan bane. Bincike shi zaiyi aikinsa mu tabbatar da me gaskiya, mara gaskiya mu miƙashi Kotu..." a hassale Yaya Haruna ya ce, "Kana zargin Iyalina a matsayin mai laifi kuma ka ce na kwantar da hankalina, sam ni ban yadda da wannan maganar ba. Kai Mhusin tashi mu tafi." Muhsin da tun da yaji sunan mahaifiyarsa a ciki yake muzurai, yana harare-harare ya miƙe ya bi bayan mahaifinsa. Har ya kusa zuwa ƙofa Kwamishina ya ce, "Alhaji karka manta ita hukuma tana amfani da hujja ne, zan turo yara su binciki matarka, ba ma ita ba ko da kai ne bincike ya biyo ta ka kanka ina fatan zaku bamu haɗin kai." Yaya Haruna ji yayi kamar anwatsa masa ruwan zafi, saboda masifa jikinsa har rawa yake ya juyo ya ce, "Na amince idan kuka same ni ko iyalina da laifi duk hukuncin da ya dace kuyi mun, idan kuma yaran nan ƙazafi sukayi mata wallahi sai ɗauki mataki." ya juya fuuu ya bar ofis ɗin Alhaji Khalil na ƙwala masa kira, amma ko waige baiyi ba.

Kwamishina murnushi ya yi ya ce, "Alhaji karka damu, idan da sabo mun saba da ganin irin haka harma fiye da haka. Ka ƙyaleshi na ɗan lokaci zai sakko kasan ko waye aka gaya masa irin haka, zai shiga irin wannan yanayi amma ka bari bincike shi zai fayyace mana komai." Alhaji Khalil ya ce, "Yallaɓai ina tsoron kar wannan dalilin ya wargaza farincikin dangina, wallahi ina matuƙar ƙaunar ƴan uwana banasan zumuncinmu ya ruguje." Kwamishina ya ce, "Abokina sai fa ankauda ƴan uwantaka da sanayya, idan ba haka ba za'ayi kitso da kwarkwata." ajiyar zuciya Alhaji Khalil ya yi ya ce, "Haka ne Abokina, Allah ya iya mana" Kwamishina ya ce, "Amin, zan tura yarana su gayyato mana Hajiya Safiya, kuma zamu tsaurara bincike akai" tattaunawa suka ƙarayi sannan suka yi sallama da Kwamishina ya wuce gida.

Lokacin da yaje gida ya sanarwa da Aunty Safna maganar da su Hadari suka faɗa, jikinta ne ya yi sanyi cikin kuka ta ce, "Ni kuwa me nayi wa Safiya da zata aika haka agareni? Me na tsare mata a rayuwa?" Lallashinta ya dinga yi har ya samu ya lallasheta, ta daina kuka sannan ya kira sauran ƴan uwansa ya sanar da su halin da ake ciki. A cen gidan Alhaji Haruna ƴan sanda tuni sukayi dirar ɗango, da gaske suke yasa Alhaji Haruna ya ce zai ɗauki matarsa ya kai ta da kansa. Hajiya Safiya banda muzurai babu abin da take yi. Hankalinta bai ƙara tashi ba sai da suka ƙarasa tayi tozali da su Hadari, ana tambayar Hadari ya tabbatar da ita, har da lambar wayarta ya shaida musu a wayarta da kwangilar da ta basu, daga ƙarshe ya nuna musu alert ɗin kuɗin da tayi musu wanda ga sunanta nan, ɓaro-ɓaro da lambar bankinta. Lokacin da abin yake faruwa Fahad da Alhaji Khalil sun koma headquater, a gabansu duk yake faruwa.

Alhaji Haruna ne ya buga mata tsawa jin antamabaye tayi shiru. kamar munafuka haka ta fara raba idanu tana motsa baki amma ta kasa magana, a hassale ya miƙe kamar zai doke ya ce, "Wai ba magana nake miki ba? Kece kika basu umarnin kashe Humaira?" girgiza kai tayi ta ce, "A'a ƙarya suke mini" Hadari yayi karaf ya ce, "Ke lallai matar nan ni zakiyiwa latsi, wallahi ko kwalba haka ta ganni ta ƙyale a iya sharri" Kwamishina ya ce, "Idan ba ke bace, ya akayi kikayi musu alert?" tsugunnawa Hajiya Safiya tayi ta ce, "Dan Allah Alhaji ku gafarceni wallahi sharrin sheɗan ne..." kafin ta rufe baki Alhaji Haruna ya ɗauke ta da mari ya ce, "Keda Sheɗan ɗin na ɗura muku ashar, kisa akashe mun ƴar ƙanina ki ce sharrin sheɗan ne?" da sauri Alhaji Khalil ya riƙe ɗan uwansa yana bashi haƙuri, Yaya Haruna banda huci babu abinda yake yi, cikin huci ya ce. "Wallahi sai an hukuntaki annamimiya makira" Muhsin da ke gefe haushin mahaifiyarsa ne yaji ya kamashi, wani irin kallo yake jifanta da shi mai wuyar musaltuwa.

Da ƙyar Kwamishina ya sallami Alhaji Khalil tare da ƴan uwansa, lokacin da zai tafi ya kalli Mahaifiyar su Lubna ya ce, "Kuma wallahi ni da ke har abada kije na sake ki saki uku" Hajiya Safiya rushewa tayi da kuka amma ko waigenta baiyi ba, Fahad banda harara babu abinda yake wurga mata.

Daga nan Headquater kai tsaye kotun Addinin musulunci aka miƙa su Hadari da Hajiya Safiya, Yaya Haruna da kanshi ya ɗauki lauyan masu ƙara. ya yinda Hajiya Safiya ta ɗauki lauyanta, su kuwa su Hadari basu da lauya dan haka Alƙali yace sai dai su kare kansu.

Su Lubna da sauran Ƴaƴan Alhaji Haruna gabaɗaya basu ji daɗin abinda mahaifiyarsu ta aikata ba, Lubna sai yanzu take jin wata irin kunyar Indo, babban tashin hankalinta Yaseer ne, tunda ta san tunda cen ma Yaseer ba santa yake ba ta Indo yake bare yanzu da haka ta faru. Cikin lokaci ƙalilan duk ta rame ta bushe ta lalace kamar wacce tayi laifi, sai abu na gaba da idan ta tuna yake hana ta bacci shine hukuncin da za'a yankewa mahaifiyarsu, gashi tun ba'aje ko'ina ba mahaifinsu ya sauwaƙewa mahaifiyarsu. Waɗannan tunane-tunane ne suka haɗu suke dagula lissafin Lubna, wanda bacci ma ya ƙauracewa idanunta.

Wata ranar Laraba ce aka zauna aka fara sauraron ƙarar su Indo, kotun cike take da mutane aka aka shigo dasu suka tsaya gurin mazaunin masu laifi, magatakarda ne ya karanta ƙunshin tuhumar sannan Alƙali ya kalli su Hadari ya ce, "Kai meye sunan ka?"

Hadari ya ce, "Sunana Salihu amma anfi sanina da Hadari" Alƙali ya ce, "Shin kaji ƙunshin tuhumar da ake muku" Hadari ya ce, "Naji ya me shari amma a taimaka ayi mana afuwa wallahi sharrin sheɗan ne" ɓangaren Hajiya Safiya Alƙali ya koma ya tambayi sunan ta ta ce, "Sunana Safiya Alhasan" Alƙali ya ce, "Shin ko akwai dalilin da ya sa kika aika a kashe ƴar mutane? Idan akwai kotu tana sauraren ki"
Chapter 58 · 0% Book details