Sashe 22
Indo Sarƙa Complete Hausa Novel · about 8 min read
Aunty gida ta koma ya ɗaga kuɗin tana shinshina su cikin shewa sa jindaɗi ta ce, " ALLAH ya kawo mun fara mai farar aniya wannan yarinya da goshi take tashin farko dubu ɗari biyu inaga sunje Abuja sun dawo wayasan alherin da zata samo mana, haka kawai da yarinya zatayi mana baƙin ciki " tana gama magana ta faɗa ɗaki domin ɓoye kuɗin gurin Honourable.
Tun da Indo ta shiga motar Honourable tayi kicin-kicin ta haɗe fuska, ya lura sarai da yanayin Indo cikin zuciyarsa yake faɗin, " Yarinya zama ki ware ne munyi tarayya da irinki ba a dadi kuma tuni sun bada kai bori ya hau, nasan ta inda zan ɓullo miki hmmmm yaro man kaza " da wannan tunane-tunanen suka ƙarasa cen gidansa dake Unguwar Nasarawa GRA, tun bayan fitowarsu daga gidan Aunty sukayi sallama da abokin tafiyarsa ya aikeshi kai wani sako acen unguwar Kabuga,shi kuma ya wuce da Indo gidansa, katafaren gida ne na alfarma mai ɗauke da ƙawatattun furanni masu ban sha'awa, a harabar gidan ya yi parking ɗin motarsa cikin takunsa na ƙasaita ya taka ya fito, zagayowa yayi ya buɗewa Indo ƙofa yana faɗin, " Cutie na fito mu watsa ruwa kafin zuwa anjima mu wuce " Indo watsa masa harara tayi ta ce, " Amma wallahi kaidai anyi ƙaton banza, angaya maka ƴar iska ce da har zan bika cikin gida " Tun da Indo ta fara magana ya kafeta da kallo, tunda yake mu'amala da mata babu macen da komai nata yake burgeshi kamar Indo, sam maganganunta basu ɓata masa rai ba sai ma bin bakinta da ya dingayi da kallo harta dire maganar da takeyi " yawu ya haɗiya sannan ya tako kusa da ita, hannunsa ya kai ya shafi fuskarta da sauri ta matsa tana janye jikinta, lumshe ido yayi na ɗan sakanni ya buɗe sannan ya ce, " Haɗuwata dake na ƴan wasu mintuna yasa na tsinci kaina cikin wani irin baƙon yanayi, tabbas ke ɗin ta daban ce acikin mata,dan Allah karki aikata abinda kike shirin aikatawa domin na lura kina ƙoƙarin bijiremun,idan kika aikata hakan ba ƙaramin illa zaiyi mun ba domin bazan iya jure rashinki ba " duk wannan maganganun da Honourable yakeyi Indi zuba masa ido tayi tana ƙare masa kallo har ya gama, sannan ta ɗora da cewa, " Cab ashe dama alhazawan birni haka kuke ƴan iska ne? Wallahi ko ka mayar dani ko nayi maka ihun kwarto " murmushin gefen baki yayi ya ce, " Haba Humcy kar mu fara ja'inja dake tun bamuje ko'ina ba, karfa ki manta Abuja fa zamu " taɓe bakin Indo tayi ta ce, " Kai ka jiyo ko uwar Abuja ne bazani ba " mamaki yake sosai bai taɓa zaton Indo na doguwar magana haka ba, wani tunani yayi yaga idan ba dabara yayiwa Indo ba babu yanda za'ayi suyi tafiyar nan lafiya ƙalau ba tare da asirinsa ya tonu ba, kallan Indo yayi ya ce, " Duk naji abinda kika faɗa gaya mun yanzu me kike so inyi miki? " Indo daɗi taji har cikin ranta zuciyarta ɗaya ta ce, " Ka mayar dani gidan Aunty " Honourable ya ce, " Ki dai ƙara tunowa bayan nan bakyasan komai? Kuma kin tabbata idan na mayar da ke ba abinda zatayi miki? " Take gaban Indo ya faɗi idanunta ne suka ciko da ƙwallah, sunkuyar da kanta ƙasa tayi ta ce, " Ka buɗe mun gida kawai na tafi ko na haɗu da dangina tunda ta sanadin haka na baro gidanmu " Baba Huwaila ce ta faɗo mata a rai take taji wani kuka yazo mata, sai da tayi mai isarta sannan ta goge hawayenta, Honourable ya fahimci tana cikin damuwa fuskar tausayi ya sauya ya ce, " A ina zaki nemi dangin naki? Dama ba'a gurunsu kike ba " Indo share hawayenta tayi ta gaya masa wacece ita da dalilin zuwanta gidan Aunty da abinda ya fito da ita, cikin zuciyarsa yake faɗin, " Wannan shi ne tsuntsu daga sama gasashshe " amma a fili sai yace, " Ayya karki damu na fasa mayar da ke gurin Hajiya zan taimaka miki har ki nemo danginki, zanje gidajen rediyo da kafafen yaɗa labarai na kai cigiya kinji " Abinka da wanda ya fika shekaru ba'a ɗauki lokaci ba Honourable ya yiwa Indo dabara,tuni ta aminta da zancensa.
Honourable ya fahimci Indo ba abinda ta sani a harkar ilimin boko na addinma bai gama tabbatarwa ba, kallanta yayi ya ƙara ƙasa da murya ya ce, " Daga yanzu ki ɗaukeni tamkar mahaifinki bazan cutar da ke ba, idan zaki dinga kirana kice Honey shi Honey yana nufin Babana da turanci " Indo gyaɗa kai tayi tace, " Nagode Honey " Honourable har cikin zuciyarsa daɗi yaji ya ce, " Cutie muje ciki ki zauna na shirya sai mu tafi amma sai munje Abuja akwai aikin da zai kaini cen mai muhimmanci " Zuciya ɗaya Indo ta taso tabi bayan Honourable har suka shiga cikin falon.Ƙayataccen falo ne na alfarma mai ɗauke da manyan kujeru na alfarma,duk inda Indo ta sanya ƙafarta akan carpet nitsewa takeyi sakin baki tayi tana ƙarewa falon kallo, ita daina iya saninta tunda take a duniya bata taɓa koda mafarkin irin wannan falon ba, sai gashi yau ta ganshi a zahiri ajiyar zuciya ta sauke tana shaƙar iska mai daɗin shaƙa, kujera ya nuna mata da hannu ya ce, " Zauna Cutie na bari na hau sama na sauko " Indo a ɗan tsorace ta dafa kujerar ta hau ta zauna tana ƙara ƙarewa falon kallo.
MU KOMA KURA
Jamilu da su Ado haka suka karaɗe ciki da wajen ƙauyen amma babu Indo babu alamarta, Tun Jamilu yana ganin kamar wasa ne abun har ya fara bashi tsoro,kafin wani lokaci tuni labarin ɓatan Indo ya zagaya ko'ina na cikin garin, masu murna nayi saboda gajiya da halin Indo masu jimami nayi, Baba Huwaila banda kuka babu abinda takeyi musamman da labari ya risketa na cewar anduba ko'ina babu Indo babu alamarta,shi kansa Jamilu ya shiga damuwa da kansa ya je cikin gari yakai report gurin ƴansan saboda lamarin ba ƙaramin tsoro ya basu ba.
Washegari haka fadar Maigari ta haɗu ana jajintawa Lauwali ne ya ƙaraso gurin bayan ya gaida Maigari,Laminu ne yace, " Lauwali ya mukaji da abinda ya faru " Lauwali gyara zaman jakarsa yayi ya ce, " Wani abu ne ya faru bayan tafiyata jiya-jiya fa na tafi Kano " Maigari ya ce, " Yarinyar nan Indo ce ta ɓata annemeta sama ko ƙasa babu ita ko labarinta babu wanda ya samu " Lauwali yace, " Dawowa ta fa kenan zan wuce nace bari na ƙaraso mu gaisa da ranka shi daɗai, amma ban fahimci wace Indo ce baku gani ba? " Laminu ya ce, " Sarƙa fa ta wajen Baba Huwaila tun jiya da ta fita ba wanda yaji ko da labarinta " Lauwali jim yayi sannan ya ce, " Sarƙa fa jiya tare da ita muka tafi motarmu ɗaya da ita, tace mana Baba Huwaila ce ta aiketa garin Kano " gaba ɗaya gurin salati suka ɗauka Maigari ne ya ƙara tsuke fuska ya ce, " Kai Lauwali bama san maganar banza Indon ka gani a motar Kano? " cikin tabbatarwa ya ce, " Ƙwarai kuwa nida Malam Bala muka ganta yanzu haka yana cen Kano zai yo sarin robobi amma xuwa yamma zai dawo, idan kuna tantama bari na kirashi a waya kuji " Lauwali ya ƙarasa magana yana zaro waya daga Aljihunsa, Lambar Malam Bala ya kira yasa a speaker bayan ya ɗauka sun gaisa ya ce, " Malam Bala jiya wa muka gani a mota da zamu tafi Kano? " daga cen ɓangaren Malam Bala yace, " Sarƙa mana ko yau ma kun haɗu da ita a mota? " Lauwali yace, " Ka ga nan Ƙauye hankalinsu duk a tashe yake wai Indo ta ɓata " da sauri Malam Bala yace, " Au Baba Huwaila batasan ta tafi kano bane? " Lauwali ya ce, " Wallahi basu sani ba " daga haka katse wayar yayi ba tare da ya ƙara ji daga bakin Malam Bala ba.
Maigari Ajiyar zuciya ya sauke ya ce, " Amma yarinyar nan anyi shakiyiya haka kawai ta tashi hankulanmu muna zaune ƙalau, kai Ado maza jeka ka kiramun Baba Huwaila " Maigari na rufe baki Ado ya tashi ya nufi gidansu Indo, lokacin da saƙon kiran Maigari ya isa kunnen Baba Huwaila da sauri suka fito ita da Jamilu a tunaninsu ko labarin Indo aka samu, suna ƙarasawa zama sukayi suna jiran ji daga gurin Maigari.
Maigari kallan Baba Huwaila yayi ya ce, " Ansamu Labarin Indo a..." da sauri ta katseshi, " Alhamdulillahi Ranka shi daɗe a ina" Maigari ya cigaba da cewa, " Lauwali ya sanar damu jiya da zashi Kano mota ɗaya suka hau da Indo " Cikin tashin Hankali Baba Huwaila ta ce, " Kano fa Lauwali? Indon tawa ce ta tafi Kano? " Lauwali ya ce, " Ya wuce wai Baba Huwaila tunda da idona ga Indo kuma mun riga ta sauka ma " Baba Huwaila bata ƙarasa jin maganar Lauwali ba ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya,Jamilu wani iri yaji har cikin zuciyarsa dafa Baba Huwaila yayi cikin sigar lallashi ya fara bata baki yana tausarta, ganin ta ƙasa daina kukan yasa Jamilu ya tasheta suka wuce gida tana tafe tana hawaye,Baba Huwaila ba ƙaramin tausayi ta bawa su Maigari ba.