Sashe 76
Indo Sarƙa Complete Hausa Novel · about 5 min read
Zuwan su asibiti da awa guda Allah ya sauki Nusaiba lafiya ta haifo ɗanta namiji kyakkyawa da shi, Nurse ɗin data karɓi haihuwarce ta fara goge jaririn amma wani abu daya ɗaure mata kai, yadda jaririn ya ƙura mata idanu ba kiftawa har hannu tasa ta rufe masa ido amma ƙir idanunsa a kanta. A haka ta samu ta gama gyarashi da gurin aka sa masa kaya Nusaiba ta rungume abinta suka koma bacci, kafin wani lokaci tuni ƴan uwa sun cika asibitin kowa xai zo hannunsa ɗauke da kullar abinci yake shigowa, gudun hayaniyarsu yasa nurses suka hanasu shiga ɗakin da Nusaiba take saboda karsu hanata bacci.
Bayan wani lokaci, Nusaiba ce ta tashi gabaɗaya yunwa takeji cikinta kamar anmata yasa, batasan da kawo abincin da akayi tana bacci ba dan haka ta ƙwalawa Nurse kira, tana zuwa tace ta kira mata su Inno da sauri ta fita ta sanar musu da saƙon Nusaiba, su Inno tare da sauron ƴan uwa ne suka shigo ɗakin fuskarsu ɗauke da farinciki, wasu daga ciki ne suka ɗau jaririn, Nusaiba a shagwaɓe ta ce, "Inno yunwa fa nake ji ku haɗa mun ruwan tea" Inno ita goggo da ƙarfinsu suka nufi wajen kullar amma tunkafin su buɗe sukaci karo da tsottsatssen ƙashi da wanda aka taune, suna buɗe ƙatuwar kular abinci yace ɗaukeni inda kuka ajiye.
Ledar ƙaton buredin ma cen ƙarƙashin gado suka hangota, da alama anciye biredin iskar fanka ce ta tura shi cen ƙasan gadon, mamaki ne ya kamasu amma babu wanda ya magantu a cikinsu, Inno ce ta ɗakko flask ɗin shayi shima ta jishi shafal ba komai a ciki, a hassale ta fara magana. "Yau naga rashin ɗa'a ido biyu, ni za'a gwadawa ɗiban albarka. Waye ya cinye abincin da shayin gurin nan?" Goggo ta ce, "Gane mun hanya yarinya ta haihu madadin taci ta ƙoshi wasu sun cinye"
Da mamaki Mahaifiyar Nusaiba ta ce, "Inno duka abincin aka cinye? To Nusaiba ko kinci abinci ɗazu?" Nusaiba ta girgiza kai, Inno ta ce, "Banda rashin ɗa'a Nusaiba duk cinta ai bazata iya cinye cooler uku ta abinci ba, maza kiramun masu fararen kayan cen gabaɗaya sai na kwashe musu albarka, yara sai rashin ɗa'a da ɗiban albarka." Mami mahaifiya Nusaiba ta nufi mazaunin Nurses ɗin ta kira suka taho tare dan su a tunaninsu wani abun ne ya samu Nusaiba, suna zuwa Inno ta kalle su ɗaya bayan ɗaya ta ce, "Ina kuka kai abincin gurin nan saboda ɗiban albarka yarinyar nan ko loma ɗaya batayi ba, idan sha'awa ya baku basai ku tambaya a baku ba amma zaku nuna mana halin rashin ɗa'a?" kallan juna suka farayi kamar haɗin baki suka ce, "Wane irin abinci ana zaune ƙalau kamar wasu mayunwata" Goggo kulolin ta janyo tana cewa, "Gasu naga ɗazu ke kika taya ni shigo da wata" ɗan zaro Ido sukayi suka ce, "Duka abincin cikin kular aka cinye" Inno ta ce, "Kiji mun shakiyyan yara marasa ɗa'a tambayarmu ma kuke yi, wallahi ko ku fito dashi ko na ɗebe muku albarka"
Ɗayar nurse ɗin ce ta ɗan fara ɗaukan zafi ta ce, "Iya wai me kuka ɗauke mu ne saboda kuma muna ma'aikatan jinya duk wata ƙura aka ɗebo sai a watsa mana..." Inna a hassale ta katseta. "Amma kedai wannan yarinyar anyi maras ɗa'a wallahi idan baki rufen baki ba zan kwashe miki albarka" ganin abun na nema zama faɗa Mami ta sasanta tare da yin waya gida akan a ƙara kawo musu wani abincin.
A yammacin ranar aka sallami Nusaiba ita da Jaririnta, tun a asibiti ake taƙaddama akan zaman Nusaiba a gidan ita Mami ma shiru tayi saboda yadda su Goggo suka ja'ina da Halifa amma fir yaƙi yarda. A hassale Goggo ta ce, "Rakiya wai dole sai mun bi ta yaron nan ne? Shi da ita duk jikokinmu ne me zamu zauna muna bi ta tasu, ni idan ya bari idanma bai bari ba zan ɗauke ta na wuce gurina da ita." Inno sheƙeƙe ta ce, "Hansai au ke zaki tafi da Nusaiba? Wallahi bazan yarda da wannan ɗiban albarkar ba nice na haifi Uban Nusaiba nafiki iko da ita" Goggo ta ce, "Rakiya wallahi baki isa ba nina haifi uwarta kuma ance uwa mafi uba koda uban sarki ne" Inna ta ce, "Ahayye Allah na dawo inji kishiyar me yaji, wallahi baki isa kizo mun da wannan rashin ɗa'ar ba, ninan gurina zan wuce da ita." Halifa ne ya shigo yaji yadda suka fara hawa sama a tsakaninsu dukda sun kasance ƴan uwa kuma aminan juna, Halifa ya fahimci sarai inda maganarsu ta dosa yace,"Nifa gaskiya babu wanda zai ɗaukarmun mata wai magana ɗaya ayita yinta har a asibiti ina dalili" nan da nan sukayo caaa akansa Mami ce ta raba musu gaddama ta ce, "Inno dan Allah kuyi haƙuri ku bar masa matarsa tunda har yace bayasan taje gida wanka, shawara ɗaya zan bayar gabaɗaya kuje ki zauna mata ai ina ga hakan yayi?" gabaɗaya sun aminta da shawarar Mami, Inno ta ce. "Hansai kinga gwara da akayi hakan dan kinsan ni yanzu bana iya aiki a bakin wuta, na dinga kula da aikin cikin gidan kina ɗora garwan wankan, wankan mejego da jaririnta idan ba haka ba kar naxo na aikata rashin ɗa'a" Goggo ta ce, "Eh kuma fa hakane Rakiya kinga zamanmu bibbiyunma zaifi."
Da wannan shawarar suka tarkata zuwa gida tare da Æ´an uwa da abokan arziki.
A daren ranar da suka koma da daddare kimanin karfe biyun dare Inno ce ta fito fitsari ahanyarta ta dawowa, ta hango ƙaƙanin abu na tafiya idan yayi gaba sai ya dawo baya rangwaɗa kai gefe. A ɗan tsoroce Inno ta ce, "Toooo yau wacce irin ɗiban albarka nake gani da daren nan" ta ƙarasa magana tana haskashi da ƴar fitilarta.
A zabure ta ja baya ganin jaririn Nusaiba ne tumɓur ko wando babu, washe mata baki yayi ya dafe ƙeya yana wani irin layi kamar wanda yasha ya maku, cikin wata irin murya ya cafe irin maganar Inno yace, "Tooo yau wacce irin ɗiban albarka nake gani a daren nan" tana faɗa yana wani irin tsalle kamar zai faɗo kan Inno, wurgar da butar tayi saboda tsoro ta fara gudu. Tsalle yayi ya caɓe zanin Inno har ya taɗe ta ta faɗi da rarrafe ta dingan rarrafawa tana ƙwala ihu, lokacin da ta ƙarasa ɗakinsu tuni ta daɗe da wurgar da zani daga ita sai ɗan fatarinta.
_OUM ASLMA BINT ADAM_😉