Sashe 6
Indo Sarƙa Complete Hausa Novel · about 7 min read
Indo ce ta leƙa ɗakin Magajiya bayan sun gaisa suka ce, " oh magajiya ya haƙurin Mlm Haruna naji ance ya rasu mukace bari muxo mu miki gaisuwa tunda ance tsohon mijin ƙanwarki ce Rabi " nan suka jajanta wa juya Indo ta kalli baraka ta ce, " yooo ni jiya ko da so akayi a tafi da Baba Huwaila nifa a tsakar gida na dinga jin muryar fatalwu suna yawo wai sun fara ɗauki ɗai-ɗai ne duk wanda suka je masa ido da ido ya gansu to shi ne sahu na gaba "
_KUYI HAKURI DA WNN BA YAWA_
_FATAN AKHERI GAREKU MASOYA NAGA COMMENTS ÆŠUNKU INA GDY._
_Ummou Aslam Bint Adam_😉
*FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀ï¸
*INDO SARƘA*🤸ðŸ¼â€â™€ï¸
*BY*
*AMEERA ADAM*
*FOLLOW ME @WATTPAD*
_*AmeeraAdam60*_
GARGAÆŠI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.
_*WANNAN LITTAFIN GABA ÆŠAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE UðŸ¤*_
11&12
Hantar cikin Mai gari ce ta kaɗa take yaji wani azababben gumi ya keto masa cikin zuciyarsa yake faɗin, " Au watalwoyin nan ba gidan nan kaɗai suka xo ba? " Indo kamar tasan mai yake zuciyar Mai gari ta cigaba da cewa, " Gashi nan dake Allah yayi Mlm Haruna yana hanya sun tafi dashi " Magajiya ce tai murmushi tace, " Ke Indo daɗina dake shirme wa yace miki fatalwa tana ɗaukan ran mutum kowa kikaga ya mutu lokacinsa ne yayi " Baraka zaburowa tayi tace, " Barta mana Yaya ay kinsan Sarƙa da mugun baki mu da ke suka ɗauka ma da kowa ya huta da sheɗancin ki " ta ƙarasa faɗa ta watsawa Indo harara.
Indo wata shewa tayi ta ce, " Ahayye sai kuma basu tafi dani ba, to ay naji Laure ƴar gidan Mlm Haruna ta ce ta leƙa ta windo ta ga fatalwa ɗaya da fararen kaya a cikin tsakiyar dare " Baraka tsai tayi da tunani tana nazari tunowa tayi da gamon da tayi sai kuma tsoro ya fara kamata, ƙasa tayi da murya tace, " Sarƙa nifa makircinki tsoro yake bani dan Allah da gaske kike Laure ma ta ga fatalwar " tsuke fuska Indo tayi tace, " Au kina nufin ƙarya zan miki Saude ba tare aka bamu labari ba? " Saude tai sauri tace, " Eh man kin tuna ta ce fatalwar ma kamar ta matattun layin nan ce " ba Baraka ba hatta Maigari tsumu yayi a ɗaki, Indo gaba tayi cen ƙofar ɗakin Mai gari ta ce, " Allah ya baka nasara barka da hutawa, dama daga ƙofar gida ne ake sallama da kai za'a sallaci Mlm Haruna "
Da ƙyar ya yunƙura ya tashi saboda gaba ɗaya jikinsa ba ƙwari, murya ba kuzari ya cewa Indo, " barka dai, kije ki ce masa muna zuwa " Indo tashi tayi tana ƙarewa Ƙeyar Maigari da goshinsa yanda yake ta ƙyalli, Baraka tunda taji batun Fatalwa ta shiga taitayinta gaba ɗaya jikinta yayi sanyi.
Su Indo bokitan ruwa su suka É—auka suka fice suna gimtse dariyar da ke cin su.
Mai gari ta maza yayi ya yunƙura ya fita kai tsaye cen ƙofar gidan Mlm Haruna suka wuce zuwansu keda wuya aka fito dashi, Mai gari haka ya ɗinga nesa-nesa da Makara lokacin sa aka zo tafiya da ita maƙabarta zame jikinsa yayi fiiiit ya gudu gida.
Bayan kwana biyu bayan sallar la'asar Su Zulai ne zaune a ɗakin indo suke hira ƙasa da murya Indo tayi ta ce, " Ke Karime leƙa mana tsakar gida kiga Baba Huwaila da Jamilu basa nan? " Karime leƙawa tayi ta dawo ta ce, " Babu kowa " Indo ce ta fara magana, " Yauwa kuna ji na yau da daddare ku shirya zan biyo muku tunda wajen kwana huɗu kenan Mai gari na hutawa, amma wallahi duk wacce ta ɓatamun shiri sai ranta ya ɓaci, kuma kowannen ku ya nemi kayan yayansa namiji ko na babansa ya saka kuma ku baɗe fuskokinku da farar hoda " Saude cikin damuwa ta ce, " Nidai gaskiya Indo banda farar hoda sai ja " Saude ma ta ce, "Wallahi nima haka " Indo janyo kayan kwalliyarta tayi ta yagi leda ta shiga zazzaga musu ta ɗaure ta miƙa musu ta cigaba da cewa, " Kuma kowanne ya taho da ludayin Innarsa " da kallan mamaki suka kalleta ta gyaɗa kai ta ce, " ƙwarai kuwa yanxu dai idan mukaje duk abinda kuka ga nayi kuma kuyi, Ke Karima ay nasan zaki iya kwaikwayon muryar marigayya Mai waina babar mai gari " gyada kai karime tayi Indo ta cigaba da cewa, " Ku kuma duk abinda nace kuyi a lokacin sai kuyi " amsa mata sukayi sannan suka cigaba da tsara yanda zasuyi.
Bayan tafiyar su Karime Indo ce ta faki idon Baba Huwaila ta faɗa ɗakin Jamilu cen ƙasan kayansa ta zaluƙo wata Jallabiyyarsa, sum sum sum ta fice tayi nata ɗakin zuciyarta fal farin ciki.
A ɓangaren Maigari kuwa a ranar da ya wayi gari da tashin hankalin fatalwa da dare yayi fir ƙin kwana yayi a ɗakinsa ya koma bin ɗakuna, ganin babu abinda ya kuma faruwa ya tattara ya koma cen ɗakinsa da kwana.
Cikin dare Indo ce sanye da jallabiyar Jamilu da tayi mata yawa sai jan ƙasa take, hannuwa ma duk sun zazzago saboda tayi mata yawa, wannan karan farin hijabinta ta nannaɗe tayi rawani dashi, a hankali ta tura ƙofa ta dafa katangar gidansu Saude ta dire, ɗakin kwanansu ta leƙa ta lallaɓa ta taso ta, Saude kamar jira take zumbur ta tashi ta shirya suka fice haka suka dinga kama katangu suna biyawa sauran ƙawayen su, daga ƙarshshe suka dangana da gidan Mai Gari.
Lokacin da suka shiga É—akinsa yana kwance bacci yake harda munshari, zagaye shi sukayi Indo ce ta zaro ludayinta daga Aljihu suma sauran cirowa sukayi, kusan lokacin guda suka saita kan Mai gari suna bashi Raaaaaallll.

13&14
Mai gari jin yayi kansa ya ɗaure lokaci guda ga wani irin raɗaɗi da azabar zugi da ya dabaibaye shi, a zabure ya miƙe tsaye saboda ruɗewa da gudu ya ɗane gadon ƙarfen shi yana salati da salallami bisa tozalin da yayi da mugun gamo, Karime hannu biyu tasa ta toshe bakinta saboda yanda dariya ta taho mata Indo ce akan gaba ta fara takowa tana tafe tana zaro harshe tana karkata kai tana wani irin far da idanu, kamar yanda suka ga Indo nayi suma haka suka mara mata baya suna yin irin abinda take yi, Mai gari ilahirin jikinsa rawa yake gumi ne ta ko ina yake keto masa cikin tashin hankali ya ƙara matsawa cen ƙarshen gado yana hakki, Indo wata irin dariyar basawa tayi sannan ta canja murya zuwa ƙatuwar murya irin ta maza ta fara magana.
" Mu jinsin Fatalwa muna maraba da zuwanka cikin mu domin a daren nan zaka ƙarasa rayuwarka acikin mu " ta ƙarasa faɗa tana wani irin jijjiga kai.
Mai gari baisan lokacin da ya fashe da wani irin kuka ba yana roƙonsu, " Dan Allah kumun rai ku agaza mun ku gayamun duk abinda kuke buƙata zanyi muku, wallahi ko dukiyata kuka ce zan iya kwashewa duka na baku, nidai ku agaza mun ku daina wahal dani dukan rannan ma da kuka mun har yanxu ban warware ba " ya gama maganar yana goge majinar da take ta tsiyaya tun fara kukansa.
Saude ce tayi karaf ta ce, " Ay yanda muka fara azabtar fa kai akanka har sai kan ya ruɓe ya faɗi da kansa sai awayi gari ka mutu " Indo daɗin maganar Saude taji har cikin ranta ta karɓe maganar Saude da, " Ay yanda muka cinyewa Malam Haruna kayan ciki ya dinga amai da gudawa kaima haka zamu fara cin ƙwaƙwalwarka har sai idanunka sun daina gani wuuuuuuuu garaaaraaaaraaaaa " Indo kamar wata ƴar bori haka ta fara wasu irin surutai tana bige-bige, suma su karime haka suka fara yi basu jima ba suka daina yi Indo ta bugawa Maigari tsawa ta fara magana, " Kaaaaaaaai sauko ƙasa ko mu rufta ka ƙarƙashin ƙasa kaida gadon da kake kai "
Indo tana rufe baki Maigari ya duro ƙasa ya durƙushe a gabansu, tsakiyar kansa ta kuma daidaita ta bashi ƙwal da ludayi, cikin tsananin azaba Mai gari ya kwarara ihu yana cewa, " Magajiyaaaaaa Barakaaaaaa ku taimaka zasu kashe ni " daga cen ɗakunan su suna bacci suka jiyo ihun Maigidan nasu azabure suka fito kusan lokaci guda suka fito tsakar gida, sai dai daga nesa suka fara hango mutane da fararen kaya, Jin motsin fitowarsu yasa Indo ta ce, " Ku miƙomin Likafanin infara ɗaura masa inmuka gama dashi sai mu koma gun matansa, dama Baraka munyi arba da ita tun zuwanmu na farko " Su Magajiya har gware suke wajen shiga ɗaki da ƙarfin gaske kowacce ta banko ƙofar ɗakinta.