← Book details Indo Sarƙa Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 76

Sashe 7

Indo Sarƙa Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maigari cikinsa ne ya karta jin abinda suka ambata ko alamun gudawar baiji ba sai jin ɗumi yayi yana bin wondonsa, wannan karan kasa magana yayi sai hannuwa biyu da ya haɗa guri ɗaya yana roƙonsu, Zulai ce ta fara magana, " Alfarma ɗaya ce zamu yi maka duk wani kayan marayu da suke hannunka ka tarkata ka mayar musu da abinsu inba haka ba kullin zamu dinga azabtar da kai kafin mutuwarka " Bakin Mai gari har rawa yake ya ce, " Ko yanzu kuka ce a shirye nake na kai musu kayansu nidai kumun rai ku daina azabtar dani " lokaci ɗaya suka fara wata irin dariyar basawa kamar haɗin baki lokaci ɗaya suka kuma bashi ƙwal ƙwaƙwaaaal da ludaya akai, sannan Indo ta ce, " Kuma a sharaɗinmu duk marayun da ka mayarwa suka ƙi karɓa to wanda suka rasa zamu turo cikin dare ya karɓi abunsa, misali idan babansu ne ya mutu ka kaiwa iyalansa suka ƙi amsa shi mammacin ne zai taso cikin dare ya karɓi abunsa. " banda gyaɗa kai ba abinda Mai gari yake yi gefe ɗaya kuma yasa hannuwa biyu ya dafe kansa yana tsoron jin wani dukan.

Indo ce ta buga mai tsawa ta ce, " Tashi ka shige ƙarƙashin gado karmu ganka a waje har assalatu " da rarrafe ya tashi zai shige Indo ta kuma cewa, " Au bayan gari kayi a wando aykuwa zamu sakar maka shi nan gaba ka dinga sakinsa kamar yanda tumaki suke yi " Mai gari juyowa yayi zaiyi magana ta buga masa tsawa da sauri ya shige ƙarƙashin gado yana haki.

Kamar yanda Indo tayi a ranar zuwanta na farko yanxu ma haka suka fara tafiya da rarrafe, suna zuwa bakin ƙofar Baraka Indo ta sa hannu ta buga da ƙarfin gaske tana cewa, " Itama ta nan ɗakin wa'adinta ya kusa zuwa na gaba da ita zamu tafi " wucewa sukayi suka je suka kama katangu suka ɗane suka fice daga gidan.

Suna fita suka fara tuntsirewa da dariya harda riƙe ciki, daga cen nesa suka ga hasken fitila ƴan ƙwamiti na buga musu tsawa, da gudu wacce ta tafi ta faɗa gidajensu.

Washe gari gaba ɗaya jikin Mai gari ya rikice ko motsin kirki ya kasa yi sai sauke wahalallan numfashi yake yi gudawa na fita ba ƙaƙƙautawa, a ɓangaren su Magajiya gaba ɗayansu rasa wanda zai fito sallar asuba akayi sai da gari ya waye sosai har masu tallan Ƴar tsala sun fara kawo musu sannan Magajiya tayi ra maza ta fito tayi alwala Baraka ma lokacin ta samu ta fito tayi alwala amma gaba ɗayansu kowa a tsorace yake, sai da sukayi Sallah sannan suka koma ɗakin Maigari don su ga halin da yake ciki, tun daga tsakar ɗakin suka fara hango Ƙudaje yamama har zuwa ƙarƙashin gado, leƙawa sukayi tsoro ne ya kamasu haɗe da tashin hankali ganin halin da Mai gari yake ciki, janyo shi sukayi suka fito dashi suna zaunar dashi ya tafi ya faɗi yaraaaaf, kuka suka fasa alokaci guda musamman da suka ga idanunsa na tafiya luuuuuuuuuuu kamar yana suma, da sauri suka cire masa kayan jikinsa suka gyara shi, Magajiya ce ta fita ta sanarwa da fadawan Mai gari, da sauri suka bazamo suka xo cikin gidan alokacin Mai gari banda sumbatu ba abinda yakeyi, kurar ruwa aka samo aka shimfiɗa tabarma da filo aka sanya mai gari aciki, kai tsaye aka tura shi aka wuce Asibitin gangare dashi.

*MY LVLY SIS INA JIN DAƊIN COMMENTS ƊINKU DAN ALLAH DUK WANDA YAYI COMMENTS RANNAN ZUWA YAU INBANYI REPLAY BA AMUN AFUWA NAYI BUSY NE TYPING ƊINMA KAWAI INA DAGEWA NE, IYA WUYA ANA TARE.*🤸🏼‍♀️🤸🏼‍♀️

_ASEELA FANS HOW MARKET?_🤭😛😛😛

_Ummou Aslam Bint Adam_😉

[17/06, 03:31] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

*INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️
*BY*
*AMEERA ADAM*

*FOLLOW ME @WATTPAD*
_*AmeeraAdam60*_

GARGAÆŠI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.

_*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_

15&16

_KUYI HAƘURI BAN TACE SHI BA_🤭

Lokacin da suka ƙarasa Asibitin gangare Mai gari ya daɗe da daina gane mutane, duk inda tashin hankali yaje su Baraka sun kai cen, Magajiya ce ma take ɗan tausarta tana bata bacci, cikin jin haushin maganar Magajiya ta ce, " Eh ay dama ce Yaya bakida matsala koda Malam mutuwa yayi saboda ƴan matanki biyu duk kin aurar dasu babu ke babu ɗawainiyar marayu, nikuwa fa kina gani Hasiya ko shekara biyar cika ba ga Ɗahiru mai shekara biyu ay dole nayi kuka " ta ƙarasa faɗa tana rushewa da wani kukan, Magajiya maganarce ta bata haushi aykuwa cikin hassala ta cewa Baraka, " Yoooo Allah na tuba ɗa ay baifi ɗa ba yanda kike taƙamar Malam ubansu ne suma su Sadiya ay ubansu ne kuma nida su sai munfi ki jin rashinsa tunda ni da kika ganni tunda jajayen sawu na muke tare da shi sai ke mai shekara shida dashi zaki nunamun san iyawa, gwana ta gwanaye kinfini shaƙuwa da shi ne? " Gama maganar Magajiya kamar ta watsawa Baraka wuta aykuwa atake suka fara cacar baki kowaccensu zuciyarta a wuya, Sai da au Ado suka sasanta sy tukunna, Lokacin da suka isa Asibitin Nurses biyu kawai suka samu aciki Amma likita bai ƙaraso ba kasancewar dama likita guda ɗaya ne acikin asitin sai Nurses da suke taimaka masa, Gado aka bashi su Ado ne sukayi ƙoƙari suka ɗorashi akai Mai gari banda idanu da yake binsu dashi ba abinda yake iya taɓukawa.

Dudduba shi suka fara yi sannan suka sa masa ruwa da Allura kafin babban likitan ya ƙaraso yayi masa duk abinda ya dace, cikin Alluran da akayiwa Mai gari harda na bacci domin ya samu hutu dan yanda suka lura kamar gaba ɗaya jikinsa babu ƙwari.

A cen ɓangaren Indo bayan da gari ya waye Baba Huwaila shirun Indo taji yayi yawa, ɗakin nata ta bankaɗa tana ƙwala mata kira, Indo cen cikin bacci ta fara jiyo muryar Baba Huwaila tana mata magana, juyi tayi ta ƙara gyara kwanciya tana cewa, " Baba Huwaila dan Allah ki barni na matse kaina har ya fara sarawa tashin da kika mun " Baba Huwaila sakin labulen tayi tana faɗin, " Indo koea rai yayiwa daɗi baya mai shi ba dama tashinki nayi naga hantsi har yayi baki karya ba, idan taki ta kawoki ina zaune zaki neme ni " Jamilu ne ya shigo da sallama jikinsa a sanyaye, ganin yanayinsa yasa Baba Huwaila ta fara tambayarsa, " Kai Jamilu lafiya naga ka shigo mun a saluɓe kamar ɗan autan kunkuru? " Zama yayi akan turmi yace, " Inna Inafa lafiya naje Shagon Iro ina hanyar dawowa naga anwuce da Maigari acikin kurar ruwa ba lafiya da alama ma baya cikin hayyacinsa dan banda sumbatu ba abinda yakeyi, lokacin da su Ado sukemun bayani sai barin wasiyya yake, kai gaskiya jikin Maigari fa sai Allah kawai Inna " Salati Baba Huwail ta rafka tana faɗin, " To Allah gamu gareka rannan munyi rashin Malam Haruna ga kuma Maigari amma kuma cuta ba mutuwa ba " Indo dake kwance tana jinsu cikinta ne ya karta gabanta yau faɗuwa, zumbur ta miƙe tsaye tana mutstsika idanu lokaci guda duk tayi fiƙi-fiƙi, farat sai gata a tsakar gida ba tsammani ta jefowa Jamilu tambaya, " Yaya Jamilu amma dai kaga yana numfashi ko? " hararara ya watsa mata sannan yace, " Idan baya numfashin wani zaki busa masa? " murguɗa baki gefe tayi ta ɗauke kai gefe tana ƙunƙuni ƙasa-ƙasa duk kuwa da har lokacin gabanta bai daina faɗuwa ba.

Suna nan tsakar gida suka ji sallamar Karime da Zulai, Indo na ganinsu ta fara ƙifta musu idanu, gaida Baba Huwaila sukayi da Jamilu sannan suka cewa Indo, " Indo zaki ɗiban ruwa? " karaf Baba Huwaila ta karɓe da, " A'a gaskiya tashinta kenan daga bacci ko karyawa batayi ba..." Indo katse Baba Huwaila tayi, " Baba Huwaila bari naje idan na ɗebo naci abincin " tana gama faɗa ta wuce cen bakin randa ta ɗau bokitinta, hijabinta dake kan ƙaure ta zara ta ɗora akan kafaɗarta suka nufi hanyar fita, Jamilu da tun ɗaukan hijabinta ya bita da kallo yaga iya gudun ruwanta ne ya buga mata tsawa yana faɗin, " Ke rasa kunya haka zaki fita babu mayafi kina tafe da kafa kamar ta balbela " bata jiyo ta kalleshi ba ta tsaya tana gyara hijabinta ƙasa-ƙasa ta ce, " Eh anji tubarkallah maye yaci kansa " tana gama faɗa ta ƙara gaba.

Suna fita daga gidan da sauri Indo ta riƙe hannun su Zulai suka zagaya bakin wata bishiyar dalbejiya, sai da ta kalli gefe da gefe cikin ƙasa da murya Indo tace, " Ke Karime kinji me ya faru da Mai gari kuwa? " cikin yanayin jimami tace, " wallahi abinda ya kawo gidanku kenan dan mu samu mu keɓe mu jajantawa juna ni wallahi tsorona ɗaya karya mutu ya rataya a wuyanmu " jikin Indo sanyi ya ƙarayi tsoro ya kuma kamata ta ce, " Wallahi nima haka amma fa gani nake jawai tsurewa ce yayi " Zulai dake gefe ta ce, " Sarƙa ko ludayan da muka dinga ranƙwala masa sun isa su kai Maigari lahira " dariya ce ta taso musu lokaci guda suka dinga ƙyaƙyatawa, suna cikin haka sai ga Saude ta ƙaraso, ɗan tsuke fuska tayi ta ce, " Au wato abunma wulaƙanci ne ko a biyo mun ko ay zan rama " Karime ta galla mata harara tace, " Innarku bata gaya miki munzo akace kinje ansar Nika, shi ne muka biyowa Sarƙa inyaso sai mu biyo ta gidanku " Indo kallansu tayi ta ce, " Kai ni ba wannan ba, ance Mai gari na Asibitin gangare abinda zamuyi kawai muje muga halin da yake ciki sai muce dubiyarsa muka xo, amma wallahi Naji Yaya Jamilu yace baisan fa wanda yake kansa ba " da wannan shawarar ta Indo suka tsaya kai tsaye suka wuce cen Asibiti gurin Mai gari.
Chapter 7 · 0% Book details