Sashe 63
Indo Sarƙa Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gabaɗaya falon shiru ya ɗauka banda shassheƙar kukan Yaseer babu abinda yake tashi, tausayinsa ne ya kama mahaifansa cikin sigar lallashi Daddynsa ya ce, "My Son! Kayi haƙuri, Allah ya rubuta Humaira ba matarka bace, abin da mukayi ba munyi domin mu baƙanta maka bane, munyi ne domin nuna hallaci ga waɗannan bayin Allahn, na roƙoka dan Allah kayi haƙuri insha Allah shi zai saka maka da mafi alheri agareka." Yaseer ya ce, "Daddy Humaira ce alkairi a gareni meyasa zaku rabani da ita, meyasa tun farko baku ce Jamilu zaku bawa ba kuka zuba ido kuna ganina ina ta dakon soyayyarta, Daddy zuciyata zafi yake mun bazan iya rashin Humaira ba." Daddyn Fahad ne ya ce, "Yaseer bamasan sakarcin banza da wofi, karka mayar da mu sa'anninka mana muna faɗa kana faɗa, sakarcin banza sakarcin wofi wallahi ranka zai..." da sauri Alhaji Khalil ya katse shi, "Haba Alhaji dan Allah ka yi haƙuri yaron nan yana cikin wani yanayi da dole ya kasa fahimtar abinda aka sanar da shi, kar a doke shi a hana shi kuka mana abun da ciwo fa" Daddyn Yaseer ya taso ya dafa Yaseer ya ce, "My Son bazan hana ka kuka ba, amma dan Allah karka sawa kanka matsananciyar damuwa domun danuwarka damuwa ta ce" Yaseer gyaɗa kai yayi amma shi kaɗai yasan ya abinda yake ji cikin zuciyarsa, miƙewa yayi tsaye ya ce, "Daddy zan wuce gida yanzu" da sauri Daddyn shi ya ce, "Yaseer ka bari mu wuce tare banasan ka fita a wannan yanayin da kake ciki, Alhaji Haruna ya ce, "Ɗana Yaseer abu na ƙarshe da zan roƙi alfarmarka ita ce, karka riƙi yaron nan Jamilu a zuciyarka domin shi a yanzu ma baya cikin hayyacinsa, yana kwance a asibiti baisan abinda yake faruwa ba." Yaseer gyaɗa kai kawai yayi ya fice daga ɗakin Daddynsa na rufa masa baya.
A lokacin da ake tsaka da shagali Indo ba ƙaramin kyau tayi ba cikin tsadajjen leshinta baƙi, kowa ya kalli fuskarta zai tabbatar da irin farin cikin da take ciki, sai walƙiya take tasha ado ta ko'ina. Daga wajen harabar gidan maroƙa da makaɗa ne kala-kala suka shigo gidan suna busa tare da shelar ɗaurin aurenta.
"Allah ya kawo mu, bikin ƴar gata kuma ƴar dangi, fara mai farar aniya tauraruwa acikin taurari, Aishatu Indo uwar muminai tare da angonta sukari bakai farin banza ba, Ango Jamilu kayi dacen mata Allah ya tsaga da rabonka, babban goro sai magogin ƙarfe Allah ya sanya alheri ya bada zaman lafiya Aishatu tare da Angonta Jamilu, ina iyayen Aisha ku fito ku nuna farincikin ƴar dangi, ku nuna mun ƙauna tabbas wannan bikin na ƴar gata ne bantaɓa zuwa bikin ƴar dangi irin wannan ba..." Haka maroƙa da makiɗan nan suka dinga banbaɗanci Abokan mahaifin Indo sai zuwa suke suna zuba musu kuɗi.
Kafin wani lokaci take maganar auren Indo da Jamilu ta karaɗa kunnuwa kowa dake gidan, ciki kuwa harda mai gayya mai aiki wato Amarya Sarƙa, lokacin ne Momma ta ja Hannun Indo ɗaki take lallashinta, Indo fashewa tayi da kuka ta faɗa jikin Momma gwanin tausayi, Momma bubbuga bayanta tayi tana lallashinta amma indo banda ajiyar zuciya babu abinda take yi, A hankali ta ɗago ta kalli Momma ta ce, "Momma zuciyata da ruhina Ya Yaseer take so, Momma anya zan iya jure rashinsa kuwa? Me yasa tuntuni Jamilu bai koyar dani sanshi ba sai da ya bari nayi nisa a soyyayar Ya Yaseer zai tarwatsa mun farincikina, Momma ni bana sanshi wallahi bazan iya rayuwar aure da shi ba..." da sauri Momma ta toshe mata baki ta ce, "Kul karna ƙara jin waɗannan kalmomin daga bakinki, kar kuma ki sake ki ƙara furta wata magana mara daɗi akan mijinki, Jamilu ya zama mijinki ba yanda zakiyi haka Allah ya tsara, babu yadda zamuyi dama tun cen Allah ya ƙaddara ke matarsa ce."
Jin waɗannan kalaman ba ƙaramin ƙara ɗaga hankalin Indo yayi ba, zuciyarta har zugi take soyayyar Yaseer na ƙara nuƙurƙusarta, jiki a sake ta dafa gado ta zauna Momma lallashinta ta cigaba da yi, sannan ta fice daga ɗakin ta bar Indo a kwance.
Wani tunani Indo tayi kamar wacce aka zabureta da sauri ta miƙe zaune ta lalubo wayarta, number Yaseer ta kira amma shiru bai ɗauka ba, ta kira ba adadi amma shiru bai ɗaga ba daga ƙarshe ma da ta kira sai ji tayi wayar a kashe. Tana jin haka ta rushe da wani irin kuka mai tsuma zuciya, tana cikin haka Mahaifiyarta ta shigo ta sameta a wannan halin, har cikin zuciyarta taji kukan da ƴarta ta takeyi, jiki a sanyaye ta ƙarasa bakin gadon ta zauna tana fuskantarta.
Indo faɗawa tayi jikin Mahaifiyarta ta ce, "Ammi wai Jamilu ne mijina wallahi banasan sa Ammi..." da sauri Aunty Safna ta rufe mata baki ta ce, "Kul Humaira banasan jin haka daga gareki, Ki buɗe kunne kiji abinda zan gaya miki Humaira, kinsan dai mu iyayenki ne bazamu zaɓa miki abinda zai cutar da ke ba. Kinfi kowa sanin su waye Baba Huwaila kinsan irin hallaci da nuna ƙaunar da suka nuna miki, Jamilu ba shi yasa muka aura miki shi ba, hasalima yana cen kwance ba lafiya, Baba Huwaila ita ta kira mahaifinki da safen nan tana kuka wai Jamilu ba lafiya, yana kwance rai a hannun Allah likitoci sunce zuciyarsa ta buga, Mu dama bamusan Jamilu yana sanki ba da mun sani da tuni mu ɗauki matakin da ya dace, a lokacin ta sanar da mu cewar indai ba'a bashi abinda yake so ba zai iya rasa rayuwarsa. Da farko Baba Huwaila cewa tayi bazata sanar da mu ba, amma ganin yana cikin wani hali yasa ta nemi wannan alfarmar a gurinmu, Humaira yanzu kina ganin ko ba ke ba, da ace muna da wata ƴar bayan ke Baba Huwaila ta nemi alfarmar aurawa Jamilu zamu hanata ne? Humaira ki zama ƴar halak ance ɗan halak shi yake rama hallaci, a yanzu magana nake miki ta ƴa da mahaifiya, umarni ne nake baki da karki bamu kunya karki je gidan mijinki kiyi abinda zaki ɓata rawarki da tsalle. Kinsan dai irin ƙaunar da Baba Huwaila ta nuna miki, tunda ke da bakinki kike faɗa mana. Kinga lalurar da ke damun mijinki, ki rungumi mijinki hannu bibbiyu kiyi masa biyayya yi nayi bari na bari, nasan dai a iya zamanku kinsan halin Jamilu wanda yake so da waɗanda baya so. Ki kiyaye abunda zai ɓata masa rai kuma yadda kike wa Baba Huwaila ki cigaba karki fasa ke harda sauran ƴan uwansa baki ɗaya." tunda Mahaifiyarta ta fara magana Indo take ruwan hawaye, ita kanta tasan duk abubuwan da Mahaifiyarta ta faɗa haka ne, amma shin babu wanda zai fahimci yadda zuciyarta take mata zugi da raɗaɗi ne? Me yasa bazasu fahimci halin da zuciyarta take ciki ba, kaf cikinsu tasan babu wanda yasan zafin rabuwa da masoyi, cikin hawaye ta kalli mahaifiyarta ta ce, "Amma Ammi meyasa..." Aunty Safna cikin dakiya ta katse Indo ta ce, "Banasan jin komai Humaira, so nake ki zama yarinya ta gari wacce zamuyi alfahari da ke, banasan ko kaɗan a samu matsala daga gurinki. Allah ya albarkaci aurenku ya bada zuri'a ɗayyiba." Auntya safna na gama faɗa ta tashi ta fice daga ɗakin, tana fita Indo ta koma gado tayi lamo hawaye na bin idanuwanta.
Likitoci cikin gaggauwa suka amshi Fahad suka shiga bashi kulawar data kamata, gwajin farko da likitoci sukayi masa suka tabbatar da zuciyarsa ce take neman bugawa, tashin hankali iyayensa suka shiga nan da nan suka shiga zarya da mamakin yadda akayi har damuwa tayi masa yawa, batare da sun fahimci halin da yake ciki ba.
Babu jimawa Likitoci suka shawo kan matsalar ta hanyar allurai da magunguna da suka bawa Fahad, abu ɗaya likitan ya cewa su Daddy shine akwai abinda yake buƙata, matuƙar ba'a bashi ba baza'a samu a shawo kan matsalar ba, idan kuma wani abu ne yake damumsa ayi ƙoƙarin kawar masa da damuwar domin samun sauƙin ciwon nashi.
Ranar wunin Indo da daddare Alhaji Haruna ya tara Æ´an uwansa, akan su tattauna lokacin da za'a kai Indo É—akin mijinta, tattaunawa sukayi gabaÉ—aya suka yanke shawarar nan da kwana uku, za'a je a kwaso kayanta na gidan Yaseer dake Abuja, aje a jera mata a gidan da Mahaifinta ya bawa Jamilu dake Unguwar Tukuntawa a garin Kano. Da wannan shawarar suka tashi daga zaman.
Jikin Fahda ba laifi yana samun sauƙi sai dai gabaɗaya ya rame ya lalace, kamar wanda ya shekara yana jinya. A ɓangaren Yaseer duk wanda ya ganshi zai fahimci irin matsananciyar damuwar da yake ciki, danma Momma da Daddyn sa suna matuƙar ƙoƙari, wajen ganin sun jashi a jiki da kawar masa da damuwa. Ya rame sosai yayi fari idanuwansa duk sun faɗa har wata ƙasumba ya tara a fuska, duk dare sai yayi sallah ya kai kukan gurin Ubangiji, akan ya yaye masa damuwar da yake ciki tare da sawa zuciyarsa dangana, tunda yasan a duniya gabaɗaya ya riga da ya rasa Humaira, babu inda yake zuwa daga zaman ɗaki sai ɗaki.
BAYAN KWANA UKU
Duk wasu shirye-shirye na tarewar Indo ankammala su, angama jera mata komai a gidanta, gidan madaidaici ne mai ɗaki huɗu, kitchen da banɗaki. Gidan dukda ba wani babba bane amma ya tsaru duk wanda ya gani sai ya birgeshi, anzuba mata kaya dai-dai misali haka daga ɓangaren kayan kitchen abin ba'a magana. Ranar laraba su Mommy ne suka taho da Indo garin Kano, lokacin da za'a taho da ita ba ƙaramin Nasiha mahaifi da mahaifiyarta suka yi mata ba, banda kuka babu abin da Indo take yi. Ita kanta Aunty Safna wannan karan sai da ta goge hawaye, ɗan zaman shekara uku zuwa huɗu da tayi da ƴar tata yasa sun shaƙu sosai, sai dai ya ta iya dama dole tasan haka zata faru tunda ƴa mace ƴar gidan wani ce.