← Book details Indo Sarƙa Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 76

Sashe 46

Indo Sarƙa Complete Hausa Novel · about 8 min read

Koda ta je kanta tsaye ta buɗe ƙofar ta shiga tana cewa, "Ya Fahad wai dama haka kake da tsoro kana ina?" mamaki ne ya kama Indo da taga ba Fahad ba alamunsa, dariya tayi a fili ta ce, "Dama duk basarwar da hura hancin da yake na banza ne, wai mage ita ƙaton gardi yake wa gudu" tana shirin fita ta ji motsinsa ya fito daga drower kayanta, fuska a murtuke ya ce, "Ke wa kike gayawa haka?" Indo ƙare masa kallo tayi wannan karan ya sa jallabiyarsa sai dai a juye ya sa ta gaba a baya, dariya ta farayi ganin yadda duk yayi wani fiƙi-fiƙi da shi, takaici ne ya kamashi kamar zaiyi mata magana sai kuma ya ƙyaleta, Indo shiru tayi ita ta tsuke fuska ita nan a dole batasan raini ta ce, "Wallahi sai dai ka tsukewa wasu fuska badai ni ba, sai kace bakai ka bangajeni ka zuba a guje ba, shine kazo mun ɗaki ka wani ɗafe drower kamar wani biri ay..." hannu ya sa ya bige mata baki ya riƙe kunnenta da ƙarfi yana murzawa ya ce, "Ki dinga iya bakinki akan rashin kunyar nan taki sai na basa bakinki" Indo duk yadda taso fusgewa ta kasa, sai da ya ga dama dam kanshi ya saketa yana sakinta ta watsa masa harara ta ce, "Chab wallahi ka fasa mun baki dan kuwa ka gane wace Sarƙa, kuma wallahi bazan fitar maka da magen ba kaje ka nemi me fitar maka, kuma Malam ka fice mun daga ɗaki." Ta sauri ya kai hannu da niyyar ya wanketa da mari, amma sai ya fasa ya damƙi gashin kanta har sai da ta saki ƴar ƙara, ƙirjinta sai bugawa yake saboda tsoro amma sai ta dake ta ce, "Ka sakarmun kaina idan ba haka ba wallahi na tada aljanu na kowa a gidan nan bazaiji daɗi ba." Dukda Fahad na cikin fushi bai hanashi yin murmushin gefen baki ba, wani uban ranƙwashi ya sakarwa Indo a tsakiyar ka wanda bata taɓa tsammani ba, sannan ya ce, "Taƙama kike da aljanu ko?" to ki tayar da su bisimillah" Bai ƙarasa faɗa ba yaji jikin Indo ya saki, wata uwar ƙara ta ƙwallah ta yanke jiki ta faɗi.

Fahad gaba yayi yana cewa, "Lallai yarinya naki wasa ne, makircin mata wanne ne bansani ba zama ki tashi da kanki" yana gama faɗa ya fice daga ɗakin ko ƙofar ɗakin bai tsaya janyowa ba.

Yana zuwa Falo Mommy ta ce, "Fahad zanga ranar da zaka daina tsoron mage, ina ka baro ƙanwar ta ka? Ba ita zata fitar maka da ita ba..." Mommy bata ƙarasa magana ba suka ji ihun Indo tare da jin ƙarar fashewar abu, da sauri suka juya suna kallan ƙofar ɗakin da Indo take ciki, ƙarar fashewar abun yayi dai-dai da fitowar Aunty Safna, tana ƙarasowa ta ce, "Subhanallah ƙarar meye haka?" Kafin su bata amsa suka kuma jin wata ƙarar, da gudu suka nufi hanyar ɗakin dan ganin abin da yake faruwa.

Suna zuwa da tsananin mamaki suka fara kallan Indo wacce take ta fashe-fashen abubuwa, hannunta jini ne kaÉ—an yake zuba, jin motsin mutane ne yasa ta juyo idanunta a juye ta nuna su tana cewa.

"Ku fice mana daga ɗakin nan bama buƙatar ganin kowa tun bamu illata ku, ko mun salwantar da rayuwarku ba" Sosai suka tsorata da ganin yanayin da Indo take ciki, Fahad ne yayi ƙarfin halin cewa. "Ke wai baki da hankali ne me yake damunki, dama aljanin ƙaryar da kika ce zakiyi dama ɓarna zakiyi? Bakya ganin yadda kike jiwa kanki ciwo kina hauka ne...?" Cikin tsawa Indo ta ce, "Rufe mana baki, bama buƙatar shirmenka a gurin nan" Fahad da sauri ya ƙarasa gurinta ya fisgo hannunta da niyyar ya janyo ta, daga gurin saboda ƙwalaben da ke zube a gurin. Fahad bai ankara ba yaji Indo ta fuske hannunta haɗe da hankaɗashi jikin bango, cikin jin zafi ya ce, "Auch" Aunty Safna ce ta ƙarasa ta riƙeshi, kallan Indo tayi ta ce, "Ke me yake damunki ne?" da wata irin murya Indo ta ce, "Na gaya muku ku fice ku bamu guri, tun bamu sauke fushinmu akanku ba" Mommy ce ta sha jinin jikinta, dafa Aunty Safna tayi ta ce, "Safna yarinyar nan fa da alama ba ita bace kamar shafar jinnu ne a jikinta." Aunty Safna zatayi magana Fahad ya ce, "Ina zuwa" Toilet ya faɗa ya ɗauro alwala sannan ya ce Mommy ta miƙo masa ruwa a kofi, babu jimawa Mommy ta kawo masa ya ƙarɓa ya fara karanta ayoyin tsari daga cikin ayoyin Alƙur'ani.

Ganin ya fara tunkarota yasa Indo ta fara ja da baya dariya na niyyar kubce mata, yana zuwa yayi bismilla yana mata tofi tare da yayyafa mata ruwan Addu'a, da ƙarfinta Indo ta fara kaiwa Fahad duka sannan ta ƙwallah wata irin ƙara ta durƙushe a gurin babu jimawa jikinta ya saki ta faɗi gefe tana numfashi.

Bayan wani lokaci ɗagowa tayi a hankali ta tashi tana dafa kanta, kamar wacce tayi aljanun gaske. Ganin jini a hannunta yasa ta juya tana ƙarewa ɗakin kallo, hango Fahad tayi a gefe ta watsa masa harara a fili ta ce, "Dama rashin imanin naka har ya kai ka fitar mun da jini a jiki, wallahi Ya Fahad ka kiyaye ni tun kafin..." Aunty Safna ce ta katse ta tana mata faɗa, Mommy riƙo hannun Indo tayi suka wuce Falo, fitar su tayi dai-dai da zuwan Family Doctor ɗinsu, ciwukan jikin Indo ya shiga gyarawa haɗe da sa mata magunguna, ita kuwa sai wani basarwa take tana cije baki.

Fahad da kansa ya fita ya kira Baba me gadi dasu Badaru, ɗakinsa suka shiga suka fara dubawa sai da suka yiwa komai filla-filla, amma babu mage babu alamarta har cikin toilet suka duba. Share ɗakin sukayi har zuwa falo da duk guraren da Indo ta barbaɗa kifin suka goge, Mommy ce ta fesa turaren ƙamshi ta koma cen gefen Indo ta zaune, Fahad jiki a sanyaye ya shigo falon ya zauna.

Shi ba abin da Indo tayi ne yake bashi mamaki ba, tsoronsa ɗaya da su Baba megadi suka duba ɗakinsa da sauran gurare amma ba mage ba alamarta. Mommy ce ta ce, "Habibi lafiya kuwa? Indai jikin Humaira ne da sauƙi sosai, dan munyi waya da Daddynku insha Allah gobe zamu gurin masu magani." Indo gabanta ne ya faɗi, a zuciyarta ta ce, "Na shiga uku karfa su kaini gurin masu riƙiyya asirina ya tonu" amma a fili sa ta ɗan yamutsa fuska ta ce, "Mommy nikam na warke dan wallahi bana ƙaunar shan magani daga na bature har na gida" Fahad taɓe baki yayi ya ce, "Mommy nifa ba wannan ne damuwata ba, babban tashin hankali na da aka duba ba'a ga magen nan ba."

Indo murmushi tayi a fakaice da sauri ta ce, "Cab Allah sa ba aljana ka haɗu da ita ba, dan haka ya taɓa faruwa lokacin da ina Kura. Aljanar mage ta shiga gidan su Harisu, shu'umar aljanar magen nan har ƴaƴan gidan ta fara taɓawa" Fahad cikinsa ne ya karta take gumi ya tsatstsafo masa, ita kanta Mommy sai da gabanta ya yanke ya faɗi jin abinda Indo ta faɗa.

FATAN ALHERI❤️😘

_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
[21/09, 12:43] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp

*INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️
*BY*
*AMEERA ADAM*

*FOLLOW ME @WATTPAD*
_*AmeeraAdam60*_

GARGAÆŠI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.

_*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_

_SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._

*Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.*

83&84

Fahad sosai ya zuba mata ido dan gano gaskiyar abinda ta da faɗa, amma sai ya gagara fahimtar haka a ɗan tsorace ya ce, "Habeebty wai Aljanu na irin haka?" Mommy da har lokacin a tsorace take ta ce, ,"Eh to kasan komai akace aljani lamarin sai Addu'a" Fahad ya ce, "To kuwa zanje inkira Malam Khalid ai basufi ƙarfin ayar Allah ba" Indo ba haka ta so ba, amma dan karsu gano ta sai ta basar. Mommy ta ce,"To Allah ya tsaremu daga sharrinsu" daga haka Fahad tashi yayi ya fice daga falon.

Yamma liƙis Fahad ya shigo shi da Malam Khalid, ɗakinsa suka shiga Malam ya zauna ya fara karatu ya jima yanayi, amma babu wani abu da yaji ko ya gani da zai baka shaidar da shafar aljanu a ɗakin, bayani yayi wa Fahad kuma ya gamsu sannan ya sanar da shi zai yiwa Indo ruƙiya. Kai tsaye Fahad ɗakin Indo ya wuce sau biyu kawai ya ƙwanƙwansa, yana shiga ya sameta kwance a kan katifa sanye da wata doguwar rigar, rigar roba ce dan ta ɗan kamata, kanta ko ɗan kwali babu.

Fahad wani abu ne ya tsarga masa baisan lokacin da ya shagala da kallonta ba, sai ji yayi ta ce, "Ya Fahad yanzu kuma me ya kawo ka ɗakina? Ko yanzu ma zuwa zakayi ka dake ni" sai ta nutsuwarsa yayi ya ce, "Ki fito akwai mai ruƙƙiya a falo" Indo ɗan tsorota tayi, da sauri ta ce, "Me ya haɗani da me ruƙiyya ko nice na koma maka magen?" maganar Indo taso bashi dariya amma sai ya kanne ya ce, "Ai da zaki koma magen ma da nafi kowa murna, inɗaukeki inkaiki cen waje na yar ko na huta" yana kaiwa nan ya fice daga ɗakin.
Chapter 46 · 0% Book details