Sashe 14
Indo Sarƙa Complete Hausa Novel · about 8 min read
" Baba Huwaila ba komai amma bari naje gidansu Zulai na dawo " Indo bata jira cewar Baba Huwaila ba ta shuri takalmanta zata fita, É—akinta ta faÉ—a cen cikin fanteka ta buÉ—e ta É—auko wani É—an mukulli ta É“oyeshi ta fice, wani É—an É—aki dake jikin Æ™ofar shiga gidan Baba Huwaila ta buÉ—e banda Æeraye da gafiya babu komai a É—akin sai wasu Æ™ananan buhunhunan gero da sauran kayan amfanin gona, Indo na shiga É“erayen suka fara guduwa ramukansu.
Cikin sa'a ta sa dutse ta buga wata ƙatuwar gafiya take ta mutu, fita tayi da sauri taje ta ɗauko magen Baba Huwaila a soro ta ajiyeta ta samu wani tsohon zanin Baba Huwaila ta yayyaga shi ta ɗaure ƙugun magen kamar wani ɗan biri, sauran igiyar ta ɗaure a jikin kofa ta fita taje ta ɗaure jelar Gafiyar da sauran tsumman sannan ta koma ta kunto magen, acikin wani tsohon buhun ta jefa gafiyar ita kuma magen ta sata a cikin hijabinta, idan kaga Indo zaka rantse aikenta akayi.
Janyo É—akin tayi ta rufe mukullin taje soron gidansu ta É—aga dutse ta ajiye tana gudun kar ta shiga gida asirinta ya tonu, lokacin da indo ta wuce Jamilu na zaune da Abokinsa Hassan kamar mutuniyar kirki haka ta wuce su, Jamilu mamaki ne ya kamashi ganin irin tafiyar nutsuwar da Indo take yi, sai dai acikin zuciyarsa daÉ—i yaji a tunaninsa faÉ—an da yayi mata ne yasa ta fara nutsuwa.
Kai tsaye Indo gidan Mai gari ta nufa taci sa'a babu mutane sosai yawanci masu wucewa ne, sai da ta faki ido sannan ta ɗane bishiyar kofar gidan Mai gari, murmush tayi musamman da taga motar su Fahad na ƙofar gidan.
Ta hau bishiyar babu jimawa taga Fahad ya fito da waya akunne da alama waya yakeyi, jikin motar ya jingina ya bawa bishiyar da Indo take kai baya, a hankali indo ta fito da gifiyar cikin Buhu ta fara zurota tana riƙe da igiyar, sai da ta kawota kusa da dai-dai ƙeyar Fahad sannan ta fito da magen nan itama ta fara zurota, Magen nan na hango gafiya tayi wani kukan kura ta kai mata cafka a dai-dai lokacin Indo ra saki Gafiyar da magen hannunta ta faɗa kan kafaɗar Fahad, kusan tare suka sauka kan Fahad gafiyar da magen, take magen ta fara yagar gafiyar da faratanta tana haɗawa da wuyan Fahad.
Banda ihu ba abinda Fahad yake yana faɗin, " Help ! Help " ihun Fahad yayi dai-dai da fitowar su Momy, Indo dake saman bishiya banda dariyar ƙeta ba abinda takeyi, tana tsaka da dariya taga Fahad ya faɗa gidan Mao gari da gudu, a hankali ta furta.
" To idonsa ya rufe baida Mommyn bane? " tana gama faɗa ta kuma ƙyaƙyatawa da dariya.
_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
[06/07, 18:06] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀ï¸
*INDO SARƘA*🤸ðŸ¼â€â™€ï¸
*BY*
*AMEERA ADAM*
*FOLLOW ME @WATTPAD*
_*AmeeraAdam60*_
GARGAÆŠI BANYAR WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.
_*WANNAN LITTAFIN GABA ÆŠAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE UðŸ¤*_
33&34
A tsorace duk suka bi bayan fahad da kallo ko zasu ga wani abinda ya sashi gudu amma basu ga komai ba, Mommy hankali tashe ta juya tana ƙwalawa Fahad kira, Mai gari ma rufa mata baya yayi suna kiran Fahad amma ko ƙurarsa basu gani ba, suna shiga gidan a cen ƙuryar ɗakin Mai gari suka hango Fahad yana ta karkaɗe-karkaɗen riga, Mommy saurin dafa shi tayi ta ce, " Fahad lafiyarka me yake faruwa ne " Kafin Fahad yayi magana Maigari ya ce, " Wallahi ni dama nasan tunda ya taɓosu bazasu ƙyaleshi haka ba, Haba Malam fatalwa wasa ce? Ba yan da banyi ba dan inja kunnenka kaƙi ita fa fatalwa ba ruwanta da ɗan birni ko ƙauye " Jiki a sanyaye Mommy ta ce, " Yaya kana nufin fatalwa ce tasa Fahad wannan abun? "
Fahad da baƙin ciki ya kamashi kamar zaiyi kuka yace, " Mommy wallahi bazan ƙara dawowa garin nan ba, mage ce fa ta kama ɓera akaina Mommy..." saboda takaici kasa ƙarasa maganar yayi Mommy mamaki ne ya kamata ta ce, " Mage ta kama ɓera akanka Fahad? Shi ɓeran ya akayi ya hau kanka? " Fahad jin maganar Mommy yayi kamar anwatsa masa ruwan zafi, furzar da iska yayi ya nunawa Mommy wuyansa, Hannunta Mommy ta kai gurin ta ga yanda shatin yaƙushin mage ya fito a wuyansa gurin har yayi ja, Sannu Mommy ta fara jera masa yana amsawa da ƙyar, Mai Unguwa kallan Fahad yayi yace, " Kai Fahad ka tabbata mage ce tayi maka haka ba fatalwa ba? " Cikin jin haushi Fahad ya ce.
" Dan Allah ka daina mun maganar wata fatalwa, naga jiya-jiya nace maka wata yarinya ce zaka take zuwa tana raina muku hankali " Maigari shiru yayi kamar bazai yi magana ba sai kuma ya ce, " Amma wallahi ka bani kunya Fahad magence kake yiwa wannan ihun da tsalle kamar zaka suma, kudai yaran birni sakalci yayi muku yawa " Fahad ƙara tsuke fuska yayi ya ce, " Muje Mommy muyi mu bar garin nan " Mommy gaba tayi Fahad na biye da ita a baya.
Lokacin da su Mommy suka shiga gidan Maigari Indo sakkowa tayi tana dariya, wajen motarsu taje ta fara leƙawa tana duddubata,gurin morrior taje ta tsaya tana ƙarewa fuskarta kallo, muryar Mommy ta jiyo tana cewa, " Ai dama Fahad tun yana ƙarami babu abinda yafi tsoro kamar magane shiyasa inasan kiwonta akan dole na haƙura " Indo acikin zuciyarta ta ce, " Alƙur'an da nasan haka ne acikin motar na zura masa magen naga abinda zaiyi mutum sai shegen iyayin tsiya "
Fahad na ƙarasawa ko magana bai yiwa Indo ba yasa hannu ya ja hijabinta ya janye ta gefe saboda gabaɗaya ransa a ɓace yake, Mommy ce ta kalleta ta ce, " Ƴan mata kwalliya ake kallo a mudubi? "Indo washe baki tayi ta ce, " Ai banmayi kwalliyar ba sai zani dandali anjima " Mommy tsai tayi ta kafe Indo da kallo tana ƙarewa fuskarta kallo, hatta muryarta jinta tayi kamar tasan mai irinta Fahad ne ya katse mata tunani da, " Mommy ki shigo mu tafi "
Mommy jakarta ta zuge ta ɗauko dubu ɗaya ta miƙawa Indo ta ce, " Ƴan mata ya sunanki? " Indo daɗi ne ya kasheta tayi farat ta ce, " Sunana Indo " Murmushi Mommy tayi ta ce, " To maza ki tafi gida ki gaida Innarki a daina wasa a hanya"
Indo hannu biyu ta sa ta karɓi kuɗin tana zabga godiya,Maigari ne ya ce, " Maza Sarƙa a wuce gida " Indo gefe ta ja Mommy ta buɗe mota ta shiga tana yiwa Maigari sallama amma har lokacin waigen Indo take da zubin tafiyarta "
Indo na hango motarsu Fahad ta fara tafiya ta tsaya tana ƙare musu kallo har suka ɓacewa ganinta, A guje ta sheƙa gida tana karya kwana sukayi karo da Jafaru Ɗan gidan Malam Isa ya karɓo markaɗen gasarar koko da mahaifiyarsa take na siyarwa, gaba ɗaya gasar ta ɓata musu jiki shi da Indo, cikin fargaba da tsoro ya ɗora hannun aka yana cewa, " Yau na shiga uku Indo kinja mun wallahi bazan yarda ba sai kin biyani "
Wani Uban ashar Indo ta ƙunduma ta ce, " Wallahi Jafaru idan duk ƙauyen nan gatanka ne bazan biya ba tunda ai gware mukayi ba da sani na na bige ka ba, meyasa da kaga na taho baka matsa ba? Ji yanda ka ɓatamun jiki wallahi sai anwankemun hijabi na "
Isa da takaici ya kamashi ya shaƙo wuyan Indo ya ce, " Sarƙa wallahi bazaki rainamun hankali ba dole Baba Huwaila ta biya ni, yarinya sai tashen rashin ji kamar jikar sheɗanu " Indo fisge hijabinta tayi ta ce, " Wallahi Isa ka iya bakinka idan ba haka zan shuka maka tsiya " Cikin jin haushi Isa ya kife Indo da mari ya ce, " Ni zaki kawowa iskanci Sarƙa duk abinda nayi miki aike kika ja " Indo bokitin ƙullin ta sura da sauri ta juyewa Isa sauran ƙullin akai ta kifa masa bokitin acikin kansa sannan ta zura aguje, Isa banda lalube ba abinda yakeyi yana tafe yana kurma ihu ga ƙulli ya shigar masa idanu, yana tafe Audi ya taho akan mashin yayi ciki da Isa.
Audu da Isa cen gefe suka faɗi kowa na maisa ajiyar zuciya, Audu salansa ce ta danne masa ƙafa cikin azama ya ture mashin ɗin gefe, Isa kuma kurjewa yayi a cinya da hannuwansa sai kansa da ya dinga buguwa da bokiti, mutane ne suka taru agurin suka fara ƙoƙarin kai musu agaji.
Indo gida ta faɗa da gudu tana haki acen ƙofar ɗakin Baba Huwaila ta zauna tana sauke ajiyar zuciya, Baba Huwaila dake tuƙa tuwo ɗagowa tayi ta ce, " Indo wata maganar kika ƙara ɗaukomun ko? " Indo har lokacin bata daina sauke numfashi ba ta ce, " Baba Huwaila wallahi ba abinda nayi kawai gware mukayi da Isa " gyaɗa kai Baba Huwaila tayi ta ce, " Nasan za'a rina tunda ga jikinki nan ya nuna, ki tashi kije kiyi wanka ki gyara jikinki " Indo zumɓurar baki tayi ta ce, " Gaskiya sai dai na wanke ido na, yamma fa tayi sanyin magariba ya fara sauka " Baba Huwaila riƙe haɓa tayi tace, " Indo yanzu Allah rayuwa zata yiwu haka rabonki da wanka yau kwana nawa? Idan ba mantawa nayi ba kusan kwana huɗu kenan kullin sai dai ki wanke ido a haka zaki samu saurayi? Kibar ganin ina kareki agurin Jamilu dan kar ya samu lagonki ne yasa bana goyon bayanki, wallahi idan baki tashi kin tafi bayi kinyi wanka ba ina gama kwashe tuwon nan da kaina zan kamaki inwanke ki tass"