← Book details Indo Sarƙa Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 76

Sashe 27

Indo Sarƙa Complete Hausa Novel · about 8 min read

GARGAÆŠI BANYAR WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.

_*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_

_SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._

*Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.*

51&52

Momma kallan Yaseer tayi ta ce, "Haba Yaseer waɗannan tambayoyin ai ka bari mu shiga gida mu huta" murmushi ya yi yana sosa ƙeya amma har lokacin satar kallon Indo yake, ita kuwa sai sunne kai take kamar mutuniyar kirki. Cikin gida suka shiga kai tsaye ta wani ƙaton falo suka shiga, Indo kanta ne ya juye saboda yadda ta ga falon ya ƙayatu. Wani irin sanyi ne yake ratsa ta gashi duk inda ta jefa ƙafarta jinsu take cikin lintsumammun carfet.

Wani tunani Indo tayi cikin zuciyarta take ayyana anya ba gidan ƴan yankan kai ta zo ba kuwa, tana tsaka da tunani Momma ta kalleta ta ce, "Daughter ga guri zauna" Indo sam bata fahimci me akace ba tun da taji kalmar zama ta san tayi guri akayi mata, banda kalle-kalle babu binda take yi. Suna nan zaune mai gadi ya shigo da manyan akwatunan yana dire su ya juya, a cen gefe Indo ta rakuɓe ta zauna Alhaji ya zauna a kujera ya kalli Indo ya ce, "Yarinya meye sunanki?"

Indo ta samu kanta da cewa,"Suna na Humaira"

Momma ta ce, "Masha Allah suna me daɗi ashe mamana ce" Indo murmushi tayi tana sunne kai ƙasa.

Daddy ya ce, "Ke kuwa me ya fito da ke a tsohon dare nan bakya tsoron hanya?" Indo ras gabanta ya faɗi tanasan ta sanar da su gaskiya, amma tana tsoron karsu mayar da ita kura saboda taci alwashin bazata koma ba sai ta nemo inda iyayenta suke. satar kallon Yaseer tayi cikin zuciyarta ta ce, "Idan kuma ya gaya musu gaskiya fa?" ɗayar zuciyar ta ce,"Ke wannan fa ba shi bane baki ga wannan yafi haske ba? Kuma wannan yafi ruwan mutumci. Cikin suɓutar baki ta ce, "To kodai ƴan biyu ne? Amma jiya ba a kano kika ga Fahad ba?" Ji sukayi Indo tayi shiru Momma ta ce, "Mamana muna so muji me ya fitar da ke da kina mace gaki da ƙarancin shekaru"

Indo sunkuyar da kai ƙasa tayi ta ce, "Ni ƴar gudun hijira ce, antarwatsamu nida iyaye na kowa ya kama gabansa, ni da wasu ƴanmata muna zaune a gidan wata mata tana taimaka mana da abinci ashe ba dan Allah take yi ba, kwatsam rannan sai tayi mana sababbun ɗinkuna ashe haɗamu zatayi da wasu alhazawan birni, wasu daga cikinmu sun karɓi tayin da aka musu mu kuma shine muka gudu" tsoro ne ƙarara ya bayyana a fuskar Momma da sauri ta ce, "Ina ne gidan matar?"

Tsoro ne ya kama Indo take ganin kamar asirinta zai tonu, saboda muddin aka je gidan Aunty zata ce basu daÉ—e da haÉ—uwa ba, ita kuwa ta fito da alwashin nemo inda iyayenta suke, dabara ce ta faÉ—o mata ta ce, "Ai matar a kano take, kuma dama gidan da take na haya ne, a ranar da muka taho nan a ranar ta tashi shine ta cewa shi Honey idan mun koma ya kirata zata bashi address É—in inda ta koma."

Kallan juna suka yi cikin haɗin baki suka ce, "Waye Honey kuma?" Indo ɗan tsorata tayi musamman yadda taga tsoro ƙarara a fuskarsu, dake wa tayi ta basu labari tiryen-tiryen har zuwan ta gurin mai abinci, tausayinta ne ya kamasu a lokacin suka fahimci a rashin ilimi a tattare da ita.
Daddy ne ya ce, "Yanzu dare ya yi haka mu barwa zuwa safiya idan Allah ya kaimu, idan mun fita zaki gane hotel ɗin?" Indo ta ce, "Gaskiya bazan gane ba, kaina duk ya juye" Yaseer ya ce, "Amma Daddy..." Daddy ya katse shi da, "A'a Son Mommynka na buƙatar hutu mu barwa zuwa safiya" Yaseer ne ya bi wata hanya ya fara ƙwalawa Baba Mariya kira amma shiru ko motsinta babu, Mommy ce da kanta ta riƙe hannun Indo tabi hanyar da ita suka fara ƙwanƙwasa ƙofa, basu daɗe ba Baba Mariya ta fara tambaya, daga cen ɓangaren Momma ta ce, "Baba Mariya buɗe nice, baƙuwa na kawo miki" da sauri ta buɗe ƙofar tana murje idanu, ganin Momma a katse ya sa ta washe baki tana faɗin, "Hajiya barka da zuwa saukar yaushe" Murmushi Momma tayi ta ce, "Da daren nan muka sauka Baba Mariya, ga yarinya na kawo miki" Baba Mariya ta ce, "To shikenan Hajiya, ƴanma shigo muje" Indo kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki haka ta fara takawa ta wuce ciki" tana shiga Momma tayi musu sallama ta koma falo lokacin Yaseer baya nan, kai katsaye ɗakinta ta wuce a gajiye.

Indo na shiga ta nemi guri ta rakuɓe a gefe sai raba idanu take, tana bin ɗakin da kallo. Baba Mariya ce ta katse ta da faɗin, "Ƴanmata ya sunanki ne?" Indo ta ce, "Suna na Humaira" Baba Mariya ta ce, "Wai ashe tsohuwa ce, shiyasa ina arba dake na fara jin yunwa" Indo murmushi tayi kawai ta ƙarewa bangom ɗakin kallo da ya ke ta walwali, Baba Mariya ta cigaba da cewa, "Ga katifa nan ki kwanta mana tsohuwa" Indo cire mayafinta tayi ta haye kan katifa ta kwanta.

WASHEGARI

Baba Mariya duk ta gama aikace-aikacen da ta saba, har wanka sunyi ita Indo sannan ta haɗa musu kayan breakfast ta kawo musu ɗaki, sai da suka ci suka yi ƙat har sun fara taɓa hira suka ji Momma na ƙwala musu kira, da sauri suka fita cikin girmamawa suka gaishe ta.
Zuwan su falo ke da wuya sai ga Yaseer ya shigo sai zabga ƙamshi yake sanye yake da Ash ɗin shadda mai ɗauke da aikin baƙin zare, kansa sanye yake da baƙar hular hannunsa da ɗaure da wani tsadadden agogo. Indo na ɗago kai suka haɗa ido take gabanta ya yi wani irin mummunan faɗuwa, Yaseer kallanta yayi yana murmushi yana shirin magana Indo ta ce, "Ina kwana?" muryarta wani irin amo tayi masa mai ratsa kunnuwa wanda yayi dai-dai da bugun ƙirjinsa, ƙaƙalo murmushi ya yi ya ce, "Lafiya ƙalau Humaira ya gajiya" wani tsautsayi ne ya kwasheta ta ƙara ɗago idanunta zata amsa karaf suka ƙara haɗa ido, ba ƙaramin kyau yayi mata ba musamman murmushin sa da yake ƙarawa fuskarsa kyau, cikin sanyin murya ta ce, "Ba gajiya"

Ƙarasawa yayi ya rungumo Momma yana faɗin, "Morning my Habeebty ya gajiyar hanya" Cikin jindaɗi Momma ta ce, "Lafiya ƙalau Habeebee har anshirya?" ɗagowa ya yayi ya ɓata fuska kamar zaiyi kuka cikin marairaicewar murya ya ce, "Momma ya na iya zan tafi Office, da su wasu ne da sun ɗaga mun ƙafa na yau kaɗai amma ina" Momma ta ce, "Haba Yasee idan ka fita gabaɗaya awa nawa zakayi indai nice har sai ka gaji da gani na" ɗan jinjina kai yayi yana kwaɓe baki kamar ƙaramin yaro sannan ya ce, "Shikenan Momma sai na dawo" Yaseer har yayi gaba Momma ta ce, "Yaseer Idan ka samu lokaci zan aikeka akwai siyayyar da zaka yiwa Humaira" da sauri ya juya yakai kallonsa gurin Indo ya ce, "Ok Momma babu damuwa" yana gama faɗa ya fice daga falon, Ajiyar zuciya Indo ta sauke, ga wanda ya lura da ita zai fahimci rashin nutsuwar da take ciki.

Momma ce ta kalli Indo ta ce, "Humaira ni da Alhaji mun tattauna akan zamu riƙe ki tsakani da Allah, kuma zamu taimaka miki wajen nemo iyayenki indai suna raye, ina fatan kema zaki zauna da mu zuciya ɗaya kamar yadda muka ɗaukeki ki ɗaukemu kamar iyayen da suka haifeki shi kuma Yaseer ki ɗauke kamar yayanki, wannan Baba Mariya ce tana da jikoki biyu amma sunje gida mai aikinmu ce, ki girmamata ki bata girmata dan banasan raini" Indo gyaɗa kai tayi cikin farin ciki ta ce, "Nagode Hajiya Allah saka da alheri, Allah jiƙan mahaifa" Momma taji daɗin addu'ar taji ta ce, "Daga yau karki ƙara kirana da Hajiya yadda Yaseer kikaji Yaseer na kira da Momma kema haka zaki dinga faɗa" Indo a kunyace ta ce, "To Momma" shiru ne ya biyo baya Indo ta faɗa nazari, kamannin Yaseer ne suke ƙara dawo mata kan ƙwayar idonta. A gefe ɗaya Ayyano Fahad tayi cikin zuciyarta take faɗin, "Kai wannan lamari akwai ɗaurewar kai, gaskiya baxai yuwu ace mutum ɗaya bane tunda halinsu ma ba ɗaya ba, Fahad bashi da mutumci ga shegen iya yi. Shikuwa Yaseer da ganin kalarsa ta masu mutumci ce?" cikin suɓutar baki a hankali ta ce, "To ko ƴan biyu ne?" karaf taji Momma ta ce, "Humaira magana kike ko akwai abinda kike so? Karfa kiji kunya ta ni ƴa na ɗaukeki" Indo murmushi ta ƙirƙo ta ce, "Ba komai Momma dama cewa nayi a miƙa godiyata gurin Alhaji" Momma ta ce, "Zaiji insha Allah, ni bari na ƙarasa ciki" tana gama faɗa ta tashi ta nufi hanyar sashenta. Baba Mariya ce ta cewa Indo, "Tsohuwa ki saki jikinki mutanen gidan nan fa basu da matsala, nima dai kinganni mai aiki ce amma warkan da ni" Indo dariya tayi ta ce "To shikenan Baba Mariya".

A ƁANGAREN SU JAMILU

Tun yana zaman jiran kira daga gidajen radiyo har zaman ya fara damunsa, kullin sai dai suyi waya da Baba Huwaila yayi ta kwantar mata da hankali. Ana cikin haka har sai da suka shafe kwanaki babu alamun Indo daga gurin aiki tun suna ɗaga masa ƙafa har suka fara masa magana, yana shirin tafiya ya samu transfer daga hukumar aikata, anyi masa canjin aiki zuwa makarantar sakandire ta maza dake cikin Sa'adatu rimi dake dake cikin garin Kano, ba shiri ya haɗa kayansa ya koma Kura.
Chapter 27 · 0% Book details