← Book details Indo Sarƙa Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 76

Sashe 43

Indo Sarƙa Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baba Huwaila ce ta ɗago fuska da ƴar damuwa ta ce, "Ƴata Safna banji daɗin abinda kika faɗa ba, na cewar babu dangin Iya bare na Baba game da Indo. Wallahi tunda nake da Indo bantaɓa jin cewar ita ba jinina bace" Aunty Safna kunya ta ɗan kamata ta ce, "Baba Huwaila ban faɗa da wata manufa amma kowa ya sani Indo takice da Jamilu, Amun afuwa tuba nake" ta ƙarasa faɗa cikin sigar wasa, gabaɗaya dariya aka sa banda Fahad, Lubna da Yaseer da kowa ya sha toka yana muzurai, musamman Fahad da sai furzar da huci yake. Baba Huwaila murmushi tayi ta ce, "To shikenan kin fanshi kanki"

Mommyn Fahad ce ta numfasa ta kalli Indo ta ce.

"Aisha bari nayi miki bayaninmu dalla-dalla yanda zaki san matsayin kowa a gurinki" Indo gyaɗa kai tayi tana binsu da kallo, suna haɗa ido da Fahad ya watsa mata harara taɓe baki Indo tayi tana murguɗa masa baki a fakaice.

Mommyn Fahad ta ce, "Kinga wannna da kike gani Fahad ɗan uwanki ne, nina haifeshi kuma shi kaɗai ne ɗana" Wani ƙululun baƙin ciki ne ya cika Fahad, gani yake kamar zata rainashi wai har sai anwani gabatar mata da shi kamar uwar mutane, Indo ta lura da yanayinsa har Mommy zata cigaba da magana ta ce, "Amma Mommy gaskiga kamar bake kika haifeshi ba, dan wallahi bashi da kirki sai yayi ta hararar mutane" Da sauri Aunty Safna ta ce, "Aisha gidanku Yayan naki kike gayawa haka" Indo shiru tayi shikuwa sai wani ƙaracin mazu yake.

Mommy ta cigaba da cewa, "Yaseer kuma ɗan uwansa ne abokin tagwaitakarsa ne" da sauri Indo ta ce, "Shima ke kika haifeshi" Mommy ta ce, "A'a ga mamansa cen Momman yara" kan Indo ne ya ɗaure Baba Huwaila ta ce, "Amma hajiya dan Allah karkiga na muku shishshigi, naji kince tagwaye ne amma kuma kowa mahaifiyarsa daban, ya abun yake?" Mommy zatayi magana karaf Momman yara ta ce, "Baba Huwaila Yaseer da Fahad tagwaye ne, Fahad ne Hasan Yaseer Usaini, Mommyn yara ita da mijinta Abi suka mun kyautar Yaseer tun lokacin da ta haifesu a asibiti saboda mu Allah bai azurta mu da haihuwa ba, kuma ba yadda banyi da Daddyn yara akan ya ƙara aure amma yaƙi sai da kyar ya auro wata bazawara, shekara biyu da aure suka rabu, kuma itama bata haihu ba. Daga kanta bai ƙara auren wata matar ba, kuma tunda muka samu Yaseer sai damuwar rashin haihuwa da kau daga zuciyoyinmu. Abinda ya sa ma ba'a kiransu da Hassan da Hussaini saboda karsu fahimci cewar ciki ɗaya suka fito, kuma daga ɓangaren mahaifinsu har na mahaifiyarsu, dogon meeting akayi akan duk wanda ya sanar dasu cewar ciki ɗaya suka fito basu yafe ba. Mommyn yara ƙanwar mijina ce wato ƙanwar mahaifin Indo amma wallahi ta zama kamar ƴar uwata ta jini." Fahad da Yaseer kallan juna suka fara yi lokaci ɗaya sukaji Indo ta bushe da wata irin dariya.

FATAN ALHERI❤️🥰

_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
[17/09, 19:47] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp

*INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️
*BY*
*AMEERA ADAM*

*FOLLOW ME @WATTPAD*
_*AmeeraAdam60*_

GARGAÆŠI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.

_*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_

_SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._

*Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.*

77&78

Da mamaki gabaɗaya juyawa sukayi suna kallanta da mamaki, Fahad ne ya ƙara tsuke fuska ya ce, "Ke meyake damunki ne?" Indo ba kunya ta watsa masa harara ta ce, "Nace maka akwai abinda yake damuna ne? Ina da baki za'a hanani dariya ne..." da sauri Aunty ta katse ta tana bige bakinta ta ce, "Aisha wai yaushe kika raina yayanki haka?" tura baki gaba Indo tayi Fahad yayi gutun tsaki ya ce, "Aunty ki barta dani akan rashin kunya zata mun bayani" Mommyn Fahad ta ce, "Aisha banasan tsiwa kinga Fahad yayanki ne" Yaseer jin ana tayiwa Indo faɗa yasa ya ce, "Brother kaima ka fiya shiga sangar Humaira meyasa ni bata mun haka" Indo dukda fushi take da Yaseer amma taji daɗin yadda Yaseer ya gayawa Fahad, ita kanta ta rasa dalilin da yasa sam basa jituwa da Fahad, ita ta rasaa meyasa yake yawan shiga sabgarta, tana tsaka da wannan tunanin taji Fahad ya ce, "Karka ɓatamun rai Yaseer kasan banasan raini" Alhaji Khaleel ne ya kalli Indo da take cika tana batsewa, sannan ya kalli Fahad ya ce, "My Son ka hukunta ta dan na lura kunnenta baya ji" Maigari wata irin dariya yayi mai ɗauke da manufar har yanzu bakusan wacece Sarƙa ba, sannan ya ce.

"Kai Fahadu wallahi karma ka fara tarkarwa kanka dan wallahi duka baya yiwa Sarƙa, idan kuwa ka biye mata wallahi har fitsari a wando sai ta saka ka" Aikuwa lokaci ɗaya mutanen falon suka fashe da dariya, Yaseer dariya yake harda riƙe ciki. Kallan Fahad yayi yana dariya ya ce, "Wa yaga Brother na sakin amalala" Duk inda ɓacin rai yakai Fahad yaje gurin, iya ƙuluwa ya ƙulu kansa ya sunkuyar ƙasa yana furzar da iska mai zafi, ganin zaman bazai kawo masa mafita ba yasa ya miƙe batare da ya tankawa kowa ba ya fice.

Sai bayan da suka tsagaita da dariya sannan Mommy ta cigaba da cewa, "Humaira kina da ƴan uwa masu yawa, waɗanda sai a hankali zaki gane kowannensu, ga wata ƴar uwar taki cen wato Lubna, ita ma ƴar yayan mahaifinki ce. Sannu a hankali daga dangin mahaifinki har na mahaifiyarki zaki gane su" Indo murmushi tayi, ita ba bayanin da Mommy tayi ne ya sa ta murmushi ba, yadda ta ga Fahad ya shaƙa ne ya bata matuƙar dariya, suna nan zaune su Aseel suka shigo sanye da uniform ɗin makaranta, suna shigo Aseem ya faɗa kan Momma yana dariya, Indo bin yaran tayi da kallo tana kallon yanayinsu, a fuska ta ɗan lura da yanayin kamar da suke amma bawai kana ganinsu zaka fahimci kamanninsu ba, harsai ka zuba musu idanu. Kallansu ta ƙarayi a karo na biyu tayi murmushi, tana ƙara kallan tabon gefen kansu irin nata da kuma su Yaseer.

Gaida mutanen falon sukayi sannan Aunty Safna ta gabatar musu da Indo, maƙaleta sukayi suna dariya daga baya suka ɗagata, suka haye sama domin cire uniform ɗinsu. Domin sai wani murmushi take ita gata babba, idan ka ganta zaka rantse haka take gabaɗaya da nutsuwa.

Abinci da abinsha aka gabatar musu suka zauna suka fara ci ana ci gaba da hira, sai da sukaci suka yi ƙat sannan Alhaji ɗan Baba Huwaila, ya sanar musu da komawarsu gida saboda kar dare yayi musu, Alhaji Khaleel ne ya nemi izinin su kwana, amma ya ce sam haka bai dace ba. Aunty Safna da kanta ta nemi izini da a bar mata Baba Huwaila ta kwana biyu a gurinsu, Alhaji bai musa ba kuma da su Momma su kansu ba ƙaramin daɗi suka ji ba. Su Momma da su Mommy suma tashi sukayi kowa zai koma garinsu, Su Mommy, Alhaji, Mai Unguwa da Jamilu sune suka wuce Kano. Yaseer da su Momma suka wuce garin Abuja, Yaseer yaso ya ɗan keɓance da Indo amma kunyar Iyayensa yasa ya kasa yi mata magana. Jamilu ma haka ya tafi zuciyarsa fal tunanin Indo. Fahad anan ya zauna saboda dama rabi zamansa a Kano yakeyi rabi kuma a Kaduna, saboda wani kamfani da yake kula da dashi na sarrafa takalma da robobi. Baba Huwaila ba ƙaramin kulawa take samu ba ita da Indo, babu abinda sukeyi sai dai su ci abinci suyi wanka su kwanta, Aunty Safna mace ce mai faram-faram da sakin fuska bata da matsala ko kaɗan. Fahad tun bayan tafiyarsu Mommy ya koma cen ɗakinsa, bai cika fitowa ba dan haka ma basa haɗuwa da Indo.

Baba Huwaila Satinta biyu ta matsa sai anmayar da ita gida, ba yanda basuyi da ita ba akan ta haƙura ta ƙara ko sati guda ne amma taƙi, kaya suka haɗa mata sha tara ta arziƙi da kayan abinci kala-kala. Ranar da zata tafi gabaɗaya suka ɗunguma zuwa garin Kano, Banda Fahad da ya ce musu sai washegari zai tafi saboda bai gama wani uzurinsa ba. Ya yi haka ne saboda haɗa tafiya da Indo dan lura yarinya na nema fara bashi matsala. Lokacin da suka je Kano tarba akayi musu ta karamci da mutumci, Jamilu bakinsa wasai kamar gonar auduga, sai zanga fara'a yake. Bayan sallar la'asar suka ɗunguma Unguwar Tudun Yola, gabaɗaya har su Baba Huwaila dan su gano gidansu Mommy acigaba da sada zumunci.

Mommy ba ƙaramin daɗi taji ba nan ma hira suka baje suna yi, Su Baba Huwaila basu suka koma gida ba sai bayan magriba. Lokacin da zasu tafi Indo da Baba Huwaila rungume juna sukayi suna kuka, sai da sukayi mai isarsu sannan suka saki juna Driver ya ɗauke su ya kaisu gida. Su Indo anan zasu kwana biyu sai ranar Lahadi zasu koma gida kasancewar ranar Juma'a suka zo.
Chapter 43 · 0% Book details