Sashe 42
Indo Sarƙa Complete Hausa Novel · about 8 min read
A firgice kowa ya kalli Alhaji Khaleel a lokacin daya zo nan a zancensa, murmushi ya yi saboda yadda yaga firjici a idanunsu sannan ya ci gaba da cewa. "Da sauri Safna ta ja da baya tana kare jikinta da hannuwanta, matsawa ya yi kusa da ita yana wani murmushi. A firgice na ɗago na ce, "Ka dubi girman Allah karka taɓa min matata" ko kallona baiyi ba ya fara takawa zuwa gurinta. Cikin tsawa ogansu ya buga masa tsawa yana faɗin, "Kai Ƙusa wane irin kidahumi ne kai? Dama a bajat ɗinmu munyi da wannan harƙallar ne? Wallahi idan ka ɓata mun shiri sai dai wani ba kai ba. Aikin sa kaine kawai nake yadda naga dama, amma aiki ture ina tsayawa akan ƙa'idata" yana gama faɗa ya juya ya fice, sauranma suka rufa masa baya.
Suna Fita Safna ta durƙushe a gurin tana wani irin gursheƙen kuka, mai tsuma zuciyar me sauraro. Duk wanda yayi tozali da Safna sai ya tausaya mata, jiki ba ƙwari na janyo jiki dukda har lokacin jini na zuba a jikina na rungumota jikina. Bani da wata mafita ko dabara nima fashewa nayi da kukan, saboda yadda zuciyata take azalzalata akan ƴarmu ƙwaya ɗaya tilo, muna cikin haka muka jiyo jiniyar ƴan sanda a ƙofar gidanmu. Ɗagowa nayi da raunanan idanuna na ce mata, "Why Safna? Meyasa zaki basu ƴarmu kikasan halin da zata shiga?" kafeni tayi da ido kamar wacce bata cikin hankalinta zuwa wani lokacin ta kuma rumgumeni tana rushewa sa wani irin kuka, ban hanata ba saboda nasan yadda tsananin soyayya take tsakanin Ɗa da uwa, kallanta nake ina daɗa jinjina irin zallar soyayyar da Safna take mini, dagowa tayi cikin dakusashshiyar murya ta ce, "Me muka yi musu? Me yasa basasan su ga muna mallaki ɗa ko ƴa a rayuwarmu? Me muka tsare musu? Kuma su waye suke aikata munanan abubuwan nan haka a kanmu?" Murya a naunane na ce, "Har yanxu amsar dana gagara bawa kaina kenan. Gabaɗaya kaina ya kulle bansan wanda zan zarga akan wannan lamarin ba, abu ɗaya na riƙe Allah baya zalinci. Tunda bamu da haƙƙi kuma bamu zalinci kowa ba shi zai saka mana, amma meyasa kika bada Aisha bakya tunanin irin cutarwar zasuyi mata?" hawayen Idonta ta goge ta ce, "Na sanka na tsawon shekaru kuma nayi sabo da kai na tsawon shekaru, mutuwa ita kaɗai zata iya rabani da kai. Kai nagartaccen mutum ne taya zan fifita wacce ko wata uku banyi da ita ba akanka? Kana ganin idan nayi haka na maka adalci? A yadda na fahimta zasu iya kasheka muddin ban basu Aisha ba. Ni kuma ban shirya rabuwa da kai ba, kuma nasan muddin muna tare Allahn da ya bamu ita zai iya ƙara mana wasu masu albarka" tana zuwa nan kuka yaci ƙarfinta, rungumeta nayi a jikinta ina jin wata irin soyayyarta a zuciyata, cikin kuka ta ci gaba da cewa, "Na rubutua lambar wayarmu da taƙaitacen bayani, haɗe da hoto na sa a cikin pampars ɗinta. Nasan ko kasheta sukayi duk wanda ya tsinci gawarta zaiga lambarmu zai neme mu." hawaye ta cigaba da yi sannan ta ɗaga hannu sama ta ce, "Ya Allah kana gani bamu cutar da kowa ba bamu zalinci kowa ba, Allah mun ɗauki wannan lamarin a matsayin ƙaddararmu, Allah ka bamu ikon cinye waɗannan ƙaddarorin da kake jarabtar mu da su. Ya Allah mun dogara da kai ka tsare mana yarinyar mu a duk inda take da tsarewarka, idan ba me tsawon kwana bace Ubangiji ka karɓi rayuwarta cikin sauƙi." tana gama addu'ar mukaji shigowar ƴan sandan, da sauri suka ƙaraso gurunmu suna tambayar yadda abun ya faru, taimaka mun sukayi suka fita dani kai tsaye suka wuce asibiti da gabaɗaya, sai da basu samu nasarar kama ko mutum ɗaya daga cikin ƴan fashin ba.
Muna zuwa asibiti suka shiga bamu kulawar gaggawa, zuwan mu babu wuya ɗan uwana suka ƙaraso shida matarsa. Satinmu biyu a asibiti aka sallamomu kuma har wannan lokacin babu labarin Aisha, ƴan uwa sun yi jimami kowa yaji ɓatanta. Safna kullin cikin kuka take da damuwa a lokacin har hawan jini sai da ya kamata, sai a hankali ta fara cire damuwa muka fauwalawa Allah lamuranmu, tun muna sa ran jin labarin Aisha har tafiya ta miƙa muka daina tunanin sake jin labarinta ganinta.
Bayan wasu shekaru sai Allah ya azurtamun da samun ƴan biyu duka maza Aseel da Aseem. Ba mu ɗora soyayyarmu akansu ba, saboda suma gani muke a kowanne lokaci zamu iya rasasu. Kuma cikin ikon Allah sai gashi Allah ya raya manasu yanxu haka suna da shekara goma bibbiyu a duniya, tun daga kansu haihuwa ta tsaya mana. Allah da ikonsa sai gashi yau Allah ya nuna buwayarsa, ya dawo mana da ƴarmu a lokacin da muka riga da mun cire rai akanta." Alhaji Khaleel ya ƙarasa faɗa cikin nuna godiyarsa ga Allah subhanahu wata'ala.
Gabaɗaya mutanen falon jikinsu ne yayi sanyi, tausayin waɗannan bayin Allahn na ratsa zuciyoyinsu. Ita Kanta Indo tausayin Iyayenta ne ya kamata, Safna da ke goge hawayen ta ce, "Tabbas lamarin Ubangiji da girma yake Allah mun gode maka" Fahad ji yayi ɗan tausayin Indo ya ɗan tsarga masa, tunaninsa ɗaya ya aka ƙare bayan da ƴan fashin suka tafi da ita kuma ya akayi ita da suke Kaduna amma tayi rayuwa a garin Kano, cikin Kanon ma a wani ƙauye da ke garin Kura, Aunty Safna ce ta gyara zama ta ce.
Fatan alheri masu comments ina gdyâ¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸ðŸ¥°ðŸ¥° whatsapp da wattapad har facebook É—inma ina fatan alheri🥰🥰🥰
_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
[14/09, 20:00] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀ï¸
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*INDO SARƘA*🤸ðŸ¼â€â™€ï¸
*BY*
*AMEERA ADAM*
*FOLLOW ME @WATTPAD*
_*AmeeraAdam60*_
GARGAÆŠI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.
_*WANNAN LITTAFIN GABA ÆŠAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE UðŸ¤*_
_SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._
*Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.*
75&56
Aunty Safna gyara zama tayi ta ce, "Da farko suna na Safna Yusuf Bature, asalinmu ƴan garin Zaria ne. Mu biyu ne kawai agurin iyayenmu nida yayata Momman yara, kafin ni sun haifi yara da yawa suna rasuwa sannan ni, iyayenmu sun rasu bayan bikin Momman yara da shekara biyu, sanadin rasuwarsu hatsarin mota sukayi. Nikuma a lokacin ina da shekara goma sha biyu a duniya, rasuwar iyayena yasa na dawo hannun yayata da zama, kuma mijinta ya riƙeni da gaskiya kamar ƙanwarsa.
Ina nan ina karatu na har ƙaninsa ya dawo gurinsa da zama, wata shaƙuwa ce ta shaƙuwa mai ƙarfi ce ta shiga tsakaninmu, daga baya kuma ta riƙiɗe zuwa soyayya, tun yayyanmu basu fahimata ba har suka fahimce mu, bayan na kamalla karatuna na sakandire sai manya suka shiga maganarmu aka tsaida rana. Lokaci na zuwa aka ɗaura mana aure." Aunty Safna ɗagowa tayi ta kalli mutanen falon da sukayi zuru suna sauraronta ta cigaba da cewa. "Basai na ja ku da nisa ba tunda duk abinda zan faɗa Hubby ya riga da ya faɗa, sai dai abinda ya manta bai sanar da ku ba shine. A ranar da za'a tafi da Aisha ranar Momman yara ta kawo mana ziyara, kuma ta kawowa Aisha Sha tara ta arziki wanda wannan ba baƙonta bane. Saboda duk zuwan da zamuyi gidansu sai ta bani wani abun wanda ta saiwa Aisha, saboda tsananin ƙaunar da take mata. a ranar ne ta zo mata da kaya acikinsu harda zobe da azurfa na jarirai da ta saya mata, tare da wasu riga da siket masu kyawun gaske. Da kanta ta sawa Aisha kayan nan da awarwaron azurfar da ta kawo mata, kuma ba ƙaramin kyau sukayi mata ba. Daddare lokacin da ƴan fashin nan suka zo mana bayan na shiga ɗaki, lokacin da naji sun harbi Hubby wani tunani yazo mun, takarda na samu da biro na rubuta lambar wayarmu da bayanin tursasawar da ƴan fashin sukayi mana, sai hotonmu dake drower mudubi na ciro kati ɗaya na ninkeshi da takardar, na tura mata acikin pampers ɗinta. kafin fitata nayi kuka kamar raina zai fita saboda kowa yasan soyayya irin ta ɗa da mahaifiya" Aunty Safna na zuwa nan hawayenta ya tsananta, sai da ta goge hawaye ta cigaba da cewa.
"Ina ji ina gani haka na fita na basu Aisha saboda ceton rayuwar maigidana, zancen da nake muku har yanzu bamusan waye ya aikata mana wannan mugun ƙudurin ba, sai dai abu guda na bawarwa raina koma waye tabbas wannan ba masoyinmu bane, babban maƙiyinmu ne da bayasan farincikinmu. Allah da nashi ikon sai gashi ya dawo mana da ƴarmu cikin ruwan sanyi, tabbas wannan baiwar Allah da ta tsince da ke Baba Huwaila bamu da abinda zamu ce muku, baki bazai iya furta kalmomin godiya ba saboda ɗubin alkairin da kukayi mana. Na jima banga mutane masu karamci kamar ku ba, kuma na jima banga mace mai riƙon Alƙawari kamar ke ba Baba Huwaila, anbaki amanar Aisha dukda ba ran uwar goyonta hakan baisa kin wofantar da ita ko kin azabtar da ita ba, wannan shi ne abinda yayi mana ƙaranci wato riƙon Alƙawari ga dai Aisha a gurinki ba dangin iya bare na Baba amma kinmata riƙo kamar jikarki ta jikinki, tabbas wannan abun a jinjina miki ne Allah ya saka miki da mafificin alheri Ameen" gabaɗaya Falon suka amsa da Ameen.