Sashe 72
Indo Sarƙa Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da safe Jamilu ne ya haɗa musu komai na breakfast bakin Jamilu yaƙi rufuwa sai wani nan yake da indo, ita kuwa dama yaya lafiyar kura sai zuba iya shegenta take san ranta. Jamilu sabon hutu ya ɗauka agurin aiki sai da yayi sati biyu a gida ana shan amarci sannan ya koma badan san ranshi ba, Indo har wata ƴar ƙiba tayi ta kwanciyar hankali cikin ƴan kwanakin Jamilu ya ƙara mantar da ita duk wasu abubuwa da suke damunta, haka itama ta rungumi mijinta da farko ne take jin kunyarsa musamman da ta ga wasu zafafan baƙin abubuwa da yake mata, a ranta har take mamakin ashe shima ɗan gari ne amma a haka idan ka ganshi zaka ɗauka da zaka sa hannuka a bakinsa bazai tauna ba a fannin soyayya, ashe abun ba haka bane.
Yaseer da Lubna sun ƙara haɗa kansu har iyaye sun shiga maganarsu, haka shima Fahad Mommy nayi masa magana ba'a ɗau lokaci ba ya samu Fahima da maganar dama kuma ko Mommy batayi masa magana ba, yana da niyyar tunkararta ya sanar mata da saƙon dake cikin zuciyarsa dan yayi sake a baya baiji da daɗi ba. Gabaɗaya lokaci ɗaya aka tsayar da ranar biki akan wata bakwai saboda wani course da Fahima zatayi, da wata huɗu akayi niyyar sawa wannan dalilin yasa aka kaishi watanni bakwai.
BAYAN WATA BIYU
Indo ce ke fama da ciwon ƙirji komai taci sai zafin ƙirji da yake damunta, tun ciwon baya damunta har ya kai ko abinci zata ci ta dinga fargaba. Wannan dalilin yasa Jamilu ya ɗauketa zuwa asibiti saboda zarginta yake da samun tagomashin alheri, suna zuwa gwajin farko aka tabbatar da Indo na ɗauke da ciki na sati bakwai, murna gurin Jamilu bakinsa har baya rufuwa ita kuwa gani take kamar ba haka ba, suna kan hanya zasu wuce gidan Baba Huwaila ta kalleshi tace, "Ya Jamil wai cikin haihuwa irin mutane nake dashi" dariya yayi saboda har gobe idan sakarcinta ya motsa sai ta nuna hali, kallanta yayi ya ce, "In tambayeki mana" ta ce "Ina jinka" ya ce, "Mijinki irin na mutane ne ko babyn roba" ta gane sarai inda maganarsa ta dosa dukan wasa ta kai masa ta ce, "To gani nan dai dan gani nake kamar baida wani ƙwazo" da sauri ya taka birki ya ce," Mun fasa zuwa gidan Baba Huwaila muje gida na nuna miki ƙwazon nawa" dariya ta kwashe dashi ta ce, "A'a wallahi da wasa nake" a haka suka ƙarasa suna hira har suka je gidan.
Suna zuwa Indo ta É—afe Baba Huwaila da sauri Jamilu ya ce, "Keeeee wai meyake damunki ne? Bakisan yanayin da kike ciki yanzu ba?" shewa Baba Huwaila tayi ta ce, "Ahayye! Allah na gode maka Jamilu wai yau kai ne baka san motsin Indo, duniya yayi ke muje ciki karya isheni da kitifi sai kace akan matarka aka fara samun ciki" Indo turo baki gaba tayi ta ce, "Ni ce miki nayi ciki gareni" kiran wayar Jamilu akayi yana É—auka da sallama Malam Isa yace, "Malam Jamilu lafiya yau baka shigo makaranta ba" Jamilu yace, "Wallahi Madam ce ba lafiya na kaita asibiti" Malam Isa yace, "Ayya Allah bata lafiya amma fa da alama shawarata tayi aiki to idan Allah ya raba lafiya ayi mun takwara" Jamilu dariya yayi yace, "Shegen kaya baka da dama sai Allah ya kaimu gobe idan na shigo" daga haka sukayi sallama.
Wata kulawa ta musamman Indo take samu agurin Jamilu, Baba Huwaila tunda ta fahimci Indo nada ciki farinciki ya kamata bakinta har kunne a haka har cikinta yakai wata takwas shida, wanda hakan ne yayi dai-dai da lokacin bikin Yaseer dan anƙara na Fahad da wata biyu saboda karatun Fahima.
Da farko Jamilu yaso hanata zuwa amma Baba Huwaila ta nuna sam bazai yuwu ba, saboda tunda aka kawo Indo bataje gida ba sai dai iyayenta su kawo mata ziyar, badan ya so ba haka ya sai musu ticket ɗin jirgi suka wuce garin Abuja acewarsa bazai iya barinta ta tafi ita kaɗai ba, tafiyar ma basu tafi ba sai ranar da za'a yi kamun amarya da Ango. Lokacin da suka je kowa kallon Indo yake yadda suka ga tayi ƙiba tayi kyau cikin jikinta ya fito sosai, Lokacin da suka haɗu da Yaseer gaisawa sukayi kamar wani abu bai taɓa shiga tsakaninsu ba, haka Jamilu dasu Fahad faram-faram suka gaisa suka shiga hada-hadar biki, kwanasu uku suka tarkato suka dawo garin Kano.
BAYAN WASU WATANNI
Cikin ikon Allah, Allah ya sauki Indo lafiya ta haifo Ɗanta namiji mai kama da Jamlu sak sai dai hasken farta da ya ɗauko, wani ikon Allah sai ga gefen kansa ɗauke da tambari irin na kan Indo. Murna gurin ƴan uwa da Abokan arziƙi baya musaltuwa daga asibiti gurin Baba Huwaila aka wuce da ita, dan tace babu inda Indo zata agurunta zata zauna, hakan ba ƙaramin daɗi yayiwa iyayen indo ba. Ranar suna jariri yaci sunan marigayi mahaifin Jamilu wato, Muhammad suna kiranshi da Abulkhairi anyi taro gwanin birgewa daga cikin waɗanda suka zo suna harda Maigari dasu Zulai, a lokacin Zulai ƴaƴanta biyar Saude kuma ƴaƴanta uku biyu sun rasu, anci ansha a taron sunan daga nan kowa ya kama gabansa. Kafin Indo tayi arba'in aka fara bikin Fahad da Fahima ranar da aka ɗaura auren Fahad Indo sukayi arba'a a washegarin ranar Indo ta wuce garin Kaduna gurin iyayenta yawon arba'in.
BAYAN SHEKARA BIYAR
Indo ce laɓe a jikin labule ta ga wucewar Jamilu cikin toilet, da sauri ta fito tana dariya ƙasa-ƙasa dan tasan muguntar data shirya masa mukulli tasa ta rufe ƙofar, Jamilu na shiga banɗaki bayan ya cire kayansa har ya fara saɓa sabulu yaji wani kuka daga sama, ɗaga kan da zai yi sama ya hango macizai biyu a saitin kansa, wata uwar ƙara ya ƙwalla ya fara fusgar ƙofa dan ya buɗe amma ya kasa ga macizan sai zaro harshe suke, dariya Indo take harda riƙe ciki sai da tayi mai isarta sannan ta miƙe a hankali ta buɗe ƙofar ta koma kan gado da gudu ta zauna. Da sauri taje ya buɗe ƙofar ya fito fuskarsa duk kumfa wannan karan Indo dariya take harda hawaye, yana murje ido yace, " Hala ke kika ƙullamun?" cikin dariya ta ce, "Wallahi ramawa nayi ka tuna abinda kuka mun rannan kaida su Abulkair, Lah kalleka fa yadda ka fito namiji da kai wai kake tsoron macizai" girgiza kai yayi ya juya yace, "Allah ya shiryeki Sarƙa haihuwa biyu amma har yanzu halinki na nan" yana shiga ya fisgo macizan robar ya watso waje. Indo kwasarsu tayi ta tafi falo acen ta samu Hanan ƴar shekara ɗaya da Abulkairi mai shekara biyar suna wasa, ta zube musu kayan wasansu.
Rayuwa mai daɗi aka cigaba da gudanarwa a gidan Indo da Jamilu haka gidajen su Yaseer, matar Fahad ta haifi Ƴa mace me sunan Momma ana ce mata Ilham matar Yaseer kuma namiji ta haifa aka sa sunan Dadddyn Lubna suke kiransa da Aslam, haka suka cigaba da rayuwa gwanin sha'awa.
TAMMAT BIHAMDULILLAH🥰
ANAN NA KAWO ƘARSHEN LITTAFIN INDO SARƘA DARASIN DAKE CIKI ALLAH YA BAMU IKON ÆŠAUKA, KUSKUREN DAKE CIKI ALLAH YA YAFE MANA BAKIÆŠAYA.ðŸ‘ðŸ»ðŸ‘ðŸ»ðŸ‘ðŸ»
INA MATUƘAR GODIYA GAREKU MASOYA BISA YADDA KUKA JURE BIBIYAR LITTAFIN NAN NA TSAWON WATANNI BABU ABINDA ZANCE MUKU SAI ALLAH YA BAR ƘAUNA, WATTPAD, WHATSAPP DA FACEBOOK INA MATUƘAR GODIYA FANS NAJI DAƊI SOSAI YADDA KUKA JURE ASHA RUWAN TSUNTSUYE NA, NA YAU DA UPDATE GOBE BABU🤣🤣🤣 MUTANENA NA WATTAPAD MUSAMMAN MASU CEWA" UPDATE SOOOOOOON PLS SIS" IYA WUYA ANA TARE ZANYI MISSING ƊINKU WALLAHI😥😥😥
SAI NA WHATSAPP MASU CIJIYAR "YAU BA SARƘA NE SIS AMEERA INA KIKA SHIGA🗣ï¸" KU DAMA ANA TARE KO BA SARƘA🥰🥰
*FATAN ALKAIRI GA ƘUNGIYATA TA FIRST CLASS WRITER'S☀ï¸*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
AKWAI MARUBUTU DA DAMA DA SUKA BANI GUDUNMAWA BA LOKACI BAZAI BARI NA LISSAFAKU AMMA KUMUN AFUWA, KUNSAN YANAYIN TYPING SAI A HNKL AMMA ZAN MIƘA SAKON GODIYA GA *MARYAM MUHAMMAD SANI (MUM AMNASH)* ALKAIRIN ALLAH YA JE MIKI HAR GADON BARCINKI😘😘😘
KU TARA DANI A SABON LITTAFINA NA JARIRINA👹 LABARI ME TAFE DA BARKWANCI HAƊE DA BANTSORO FREE NE SAI COMMENTS KAWAI NAKE BUƘATA, ZAI FARA ZUWAR MUKU 15/10/2021.
SAI LITTAFINA NA *ANYA BAIWA CE* SHIKUMA 200 NE GAME BUƘATA.
GABAÆŠAYA GA ÆŠANÆŠANONSU NAN 👇ðŸ»ðŸ‘‡ðŸ»
[26/09, 00:43] Ameera Adam🌚: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀ï¸
*ANYA BAIWA CE?*
Na
*AMEERA ADAM*
_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, GAME BUƘATAR VIP POSTING SAU BIYU A RANA ZAI BIYA 400, GABAƊAYA ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 0706 206 2624,DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
FREE PAGE 1
Tafe take tana ɗan waige dan gudun kar wani ya ganta ko taci karo da wani a hanya, saboda abin da ta gano take san zuwa ta isar da shi ko ta samu ɗan alheri, aikuwa batayi aune ba tana shiga soron tsakiya suka yi gware da mutum a zabure ta ja da baya tana sauke ajiyar zuciya kamar wacce tayi tseren gudu, kallan tsaf yayi mata yana karantar yanayinta yasan tabbas akwai abinda ke ƙunshe cikin bakin ta, aɗan diriri ce ta kalle shi ta ce.
"Yautai mugun tsuntsu masha miyarka sai yayi dare"
Kallanta yayi sai da yayi murmushin gefen baki yana ƙara karantar yanayin ta sannan ya ce, " Tauraruwa mai wutsiya..., Kura kike ga tsoro ga ban tsoro. Ina zaki kike sauri kina ta juye-juye haka? " Sai da ta juya hagu da dama ta kuma leƙa soron ƙarshe tana mai miƙa wuya cikin ƙasa da murya ta ce, " Gobara daga teku maganin ta sai Allah, wata ƙura ce take ƙoƙarin kunno kai a cikin gidan nan amma karka ce kaji daga baki na " ta ƙarasa magana tana kuma duba gabanta da bayanta.
"Jakadiya Kubura kenan, ay harbi ga É—an jaki gado ne, kuma iya ruwa fidda kai gayamun ina sauraron ki kowa ya biya allon sa ya wanke " ya faÉ—a cikin son jin labarin.