Sashe 40
Indo Sarƙa Complete Hausa Novel · about 8 min read
Alhaji Khaleel gyara zama ya yi ya fara cewa, "Kamar yadda kuka ji daga bakin ɗan uwa na suna na Ibrahim Khaleel. Asalin iyayenmu fulanin shanono ne, sunan mahaifinmu Baffa Inusa sai ɗan uwansa Baffa Musa amma duka muna kiransu da Baffa, su biyar ne agun mahaifinsu amma su biyu ne agurin mahaifiyarsu da suke Uwa ɗaya uba ɗaya. Mahaifinmu ƴan biyu ne shi da ɗan uwansa kamarsu tayi tsanani har ba'a cika gane su ba sai da tabon gefen kan mahaifinmu wanda muka gada daga gurinsa gashi kuma har kan jikokinsa, Baffa Musa shi ne Hassan sai Baffanmu shi ne Usaini. kasuwanci ne ya kawo mahaifinmu garin Kano tare da sauran ƴan uwansa. A hankali tun yana zuwa ya koma, har ya fara tunanin dawo da mahaifiyarmu garin nan. Da farko ƴan uwanta ƙin amincewa sukayi da kyar suka bari ya dawo da ita, daga haka sai ya koma sai bayan wasu lokatu yake kaiwa ƙauyensu ziyara yaje ya gano ƴan uwansa da Ƴan uwan mahaifi dana mahaifiyarsa, saboda tun kafin mahaifinmu yayi aure Allah ya yi wa iyayensa rasuwa. Haka suka ci gaba da gudanar da kasuwanci har Allah ya sa musu albarka.
Mahaifiyar mu sunanta Raliya amma muna kiranta da Goggo, su goma sha biyu agurin mahaifinsu. A gurin mahaifiyarsu kuma ita ce ta fari tana da ƙanne biyar, mahaifinsu yana da mata uku kuma shima ainahinsa ɗan garin shanono ne. Mu biyar iyayenmu suka haifa huɗu maza ɗaya mace. Yaya Sani, Yaya Mubarak, Yaya Haruna, Yaya Halima sai ni. Dukkanmu mun samu ilimin boko da na addini dai-dai misali, kuma har yau har kwanan gobe bamu bar harkar kasuwancin da mahaifinmu ya gina mu akai ba. Dukda mahaifanmu sun tsufa amma har yanzu suna alfahari da haɗin kanmu, kuma muma muna fatan wannan haɗin kai namu ya tafi har ƴaƴa da jikokinmu.
Ɗagowa Alhaji Khaleel ya yi yana kallon mutanen falon da kowa ya yi shiru yana sauraronsa sannan ya cigaba da cewa, "Na taso a hannun ɗan uwana Yaya Mubarak shi ya kula da karatuna tun daga farko har ƙarshe, lokacin da na kusa kammala karatuna sai suka janyoni cikin harkar kasuwancin fata da robabin da sukeyi, dukda a lokacin inada sha'awar aikin gwamnati, amma sai na kauda kaina sabida karna saɓawa ƴan uwana, tunda banida kamar su sun ɗaukeni kamar ɗan da suka haifa na cikin su. Kuma a wannan shekarar ne suka buɗe wani babban kamfani na sarrafa maganin sauro, a hankali sai Allah ya albarkaci abun bayan buɗe wannan kamfanin da shekara uku sai suka ƙara tunanin buɗe wani kamfanin tare da gidajen mai guɗa biyu, kuma a wannan shekarar ne Allah ya karɓi rayuwar mahaifiyarmu. Mutuwar Goggo ba ƙaramin ɗaga mana hankali ba tare da mahaifinmu dan ta sanadin haka ne ya jininsa ya hau, tun daga wannan lokacin sai Yaya Haruna ya ɗauki Mahaifinmu ya koma gidansa da zama, komawarsa gidan Yaya Haruna sai suka haɗu da Inna Hafshe wacce ta kasance me aiki ce a gidan. Ba'a ɗauki lokaci ba aka sanarwa da danginka aka ɗaura musu aure, Yaya Haruna ya basu gidansa da yake Unguwar Hausawa. Mahaifinmu yayi aure da shekara guda aka fara maganar aure na da Safna, wacce ta kasance ƙanwa ce a gurin matar Yaya Mubarak, ba'a ɗauki lokaci ba aka tsaida wata bakwai lokaci na zuwa aka ɗaura aurenmu muka tare a nan garin Kano unguwar Gyaɗi-gyaɗi." wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke sannan ya kalli Safna ya ce, "Ummu Banat na gaji fa ko zaki ci gaba da basu labarin?" hararar watsa ta jefa masa ta ce, "Aikuwa idan ka yarda sai dai idan nima na fara basu labarin daga farkon nawa" ta ƙarasa faɗa tana kashe masa ido ɗaya.
Martanin hararar wasa ya mayar mata ya ce, "Wallahi bazai yuwu ba sai dai ki bari na gama kya ɗora" Fahad murmushi ya yi ba ƙaramin birgeshi su Uncle Khaleel suke ba, sun fara girma amma har zuwa wannan lokacin suna bawa junansu kulawa, lumshe idanu yayi yana ƙissima wasu abubuwa a zuciyarsa.
Uncle Khaleel ya cigaba da cewa, "Shekarar mu Biyar a Kano muka dawo nan garin Kaduna, sakamakon buɗe sabon Kamfinmu da akayi a cikin garin, kuma ni da Yaya Haruna ne muka dawo sauran ƴan uwana suka ɗora mana alhakin kula da duk wani shige da ficen sa. Har zuwa wannan lokacin Allah bai azurtanmu da samun haihuwa ba, tun Safna bata damuwa har abin ya fara damunta. Haka muka fara shige da ficen neman magani mune daga wannan asibitin zuwan wancen, amma duk inda muka je abu ɗaya ne zasu dubamu suce lafiyar mu ƙalau kawai lokaci ne baiyi ba. Wata matsala da muka fara fuskanta ta yawan ɓarin da Safna takeyi, amma muna zuwa asibiti da aka dubata suka sanar da ni, maganin zubar da ciki take amfani da shi shiyasa cikin jikinta baya zama" A dai-dai lokacin da yazo wannan gaɓar Hawayen da Safna take ɓoyewa ne ya gangaro mata, a hankali ta sa hannu ta fara gogewa. Ɗagowa ya yi ya miƙa mata wani farin kyalle a hankali ya furta, "Kefa kika mun alƙwarin kin daina wannan kukan, a duk sanda muke tada wannan maganar" Kukan ne yake niyyar cin ƙarfin ta sannan ta, "Amma kasan ancutar dani matuƙa" Momma dake cen gefe ta ce, "Haba Safna Allah ma muna masa laifi ya yafe manan bare kuma ɗan Adam, wannan maganar ta riga da ta wuce kuma duk wanda ya cutar da ke Allah zai saka miki" Safna gyaɗa kai tayi tana goge hawayen Idonta.
Alhaji Khaleel ya ci gaba da cewa, "A wannan lokacin na shiga tashin hankali mara musaltuwa, kuma abubuwa da dama sun faru idan Safna tazo baku labari zakuji daga gareta, bayan mun samu mun kawar da wannan matsalar da shekara guda, sai Allah ya taimakemu muka ƙara samun wani rabon, har Allah ya sauki Safna lafiya ta haifi ɗanta namiji. Sai dai kash Allah ya yi bame tsawon rai bane,, ranar suna aka sameshi kan gado baya numfashi" Wannan karan ma kukan Safna ne ya tsananta har tana ƴar shasheka, bai ce mata komai ba, sai dai yana jin kukan nata har cikin zuciyarsa. Ya ci gaba da cewa, "Mun ji mutuwar Muhammad sosai kasancewar yaro lafiyayye, amma ita mutuwa babu ruwanta da me lafiya. Haka gidan suna ya juya zuwa gidan mutuwa akayi ta jimami, haka muka fauwalawa Allah lamuranmu. Bayan faruwar haka da ƴan watanni Safna ta kuma samun ciki shima kuma ta haifeshi lafiya ƙalau, amma wani ikon Allah shima kamar wancen ranar suna ya mutu."
Wata nannauyar ajiyar zuciya Alhaji Khaleel ya sauke sannan ya ci gaba da cewa, "A wannan haihuwar da tayi dama likitoci sun sanar damu, hutun da Safna zata ɗauka kafin ta kuma ɗaukan wani cikin, a ƙalla zata yi shekara uku kafin ta kuma ɗaukan wani cikin saboda mahaifarta ta samu hutu. Haka muka barwa Allah lamuransa muka zauna har zaman jiran adadin shekarun da likitoci suka ɗaukar mana, a lokacin ba shawarar da ba'a kawo mini ba akan na ƙara aure amma ban amince ba, amma ban sani ba ko Safna kan Ungulu ta binne mini oho" ya ƙara faɗa cikin sigar zolayawa yana kallonta, gabaɗaya falon ba wanda bai dara ba, Daddy ya ce, "To gasu nan ai ƙila bakinsu ɗaya, inajin Mommyn yara ita ta nuna musu hanya tun da aka ce daga na gaba ake gane zurfin ruwa, kana gani ta kanainaye ta hana bawan Allah ƙara aure, nima kuma gani da Momman yara shiru" dariya suke sosai Mommy ta ce, "Eh mun ji ba komai, haka kawai muna zaune za'a ƙwace mana mazaje ne" Alhaji Khaleel ya numfasa ya ci gaba da cewa.
"Bayan shekara Uku sai Allah ya ƙara azurta mu da samun haihuwar ƴa mace, da farko hana taron sunan nayi amma sai nayi tunanin duk abin da Allah ya ƙaddara babu mai iya canza shi, ranar suna yarinya taci suna Aisha haka Momman Yara ta dinga kaffa-kaffa da jarira dan ba kowa ake bawa ita ba, kuma ba'a barinta ita kaɗai a ɗaki.
Bisa arashi Safna na falon ƙasa gurin wasu baƙi suna gaisawa, itama Momman yara ta sauka ƙasa wani uzuri, tana dawowa ta nemi jaririya sama da ƙasa ta rasa, cikin tashin hankali ta fito tana sanar da abinda yake faruwa, nan da nan aka rufe gidan aka hana kowa fita, kuma aka ci gaba da dube-dube amma ba jaririya babu alamunta. Sai da aka koma ana duba cikin ɗakin aka fara jiyo motsi a cikin drowa, lokacin Momman yara ce da Safna a ɗakin sai sauran ƙawayenta. Da sauri aka buɗe ga mamaki sai ga yarinya ta faɗo ta sauri Safna ta riƙe ta, wani babban tashin hankali gani sukayi an naɗe kan jaririyar da ɗankwalin Mommyn Yara. a razane Safna ta furta, "Dankwalin Mommyn yara? aka naɗe wuyan ƴa ta za'a kashe ta? Lallai akwai lauje cikin naɗi" da sauri Momma ta karɓi jaririyar sai dai har lokacin numfashinta sama-sama yake fita.
*ALHAMDULILLAH AM BACK, INA GDY DA ADDU'ARKU MUTANENA NA WATTAPAD MUCH-MUCH ƘAUNA BA ADADI NA RISKI SAƘONKU NA ADDU'A HAR ÆŠAZU NAGANSU DA YAWA, MUTANENA NA WHATSAPP MUSAMMAN ƳAN GROUP ÆŠINA WOLLAH BANDA BAKIN GODIYA A GURINKU SAƘONNINKU BAZASU ƘIRGU BA INA GDY SOSAI ALLAH BAR ƘAUNA â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸*
FATAN ALHERI A GAREKU🙋ðŸ¼â€â™€ï¸
PLS SHARE GIDA BIYU KAWAI NA TURA SAI WATTPAD
_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
[13/09, 11:20] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀ï¸
*INDO SARƘA*🤸ðŸ¼â€â™€ï¸
*BY*
*AMEERA ADAM*
*FOLLOW ME @WATTPAD*
_*AmeeraAdam60*_
GARGAÆŠI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.
_*WANNAN LITTAFIN GABA ÆŠAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE UðŸ¤*_
_SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._