Sashe 61
Indo Sarƙa Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Idanuna sun makance! Bana ji bana gani idan ba sauke ƙwayar idanuwa nayi akanki ba, tun kina ƙarama nake lallashin zuciyata akanki saboda kinyi yarintar da bazaki iya ɗaukan kalamaina ba. Nasan duk wanda ya tambayeki halina kalmar mugu, itace kalma ta farko da zaki fara gaya masa daga cikin halayena, saboda gani kike a duk duniya babu wanda ya tsaneki sama da ni. Ko kaɗan ba haka bane! Duk abin da kika ga inayi ina yinsa ne saboda tarbiyyantar da ke akan abinda ya dace, bahaushe ya ce kaza na taka ƴaƴanta badan bata sansu su ba... Ina matuƙar ƙaunarki Humaira dan Allah karki juyomun da martanin da zuciyata bazata iya ɗauka ba, dan Allah karki wargaza saƙar da na daɗe ina saƙawa a zuciya, ki taimaka ki furta kalmar ina sanka ko zuciya ta samu saƙin azalzalar da take mun." tun da Jamilu ya fara magana jikin Indo yayi sanyi ta sandare guri ɗaya tana sauraron maganganunsa, tabbas Jamilu ya nuna mata kulawa ya ƙaunace ta a lokacin da bata da kowa, ya riƙeta kamar ƴar uwarsa a lokacin da batasan kanta ba, Jamilu mutum ne me karamci da nuna kulawa uwa uba kyawawan ɗabi'u da riƙon addini, amma ya zatayi da Yaseer da dakon soyayyarsa da take yi na tsahon shekaru? Ta amsa ta ƙaunar Yaseer anya idan ta amsawa Jamilu bata sa yaudara cikin lamarinta ba? Tun da tasan ko addinin kirista bai amince da auren maza biyu ba, bare kuma a addinin musulunci. Amma ta yaya zata bijirewa Jamilu bayan sun gama mata komai a duniya? Da wanne idon zata kalli Baba Huwaila bayan ta furta bazata iya auren jininta ba, jinin nata ma kamar Jamilu da duk cikin jikoki babu wanda take ƙauna kamar shi, kuma duk ƙaunar da take masa amma ta fifita ta akanshi, da duk abinda take aikatawa Baba Huwaila bata ganin laifinta. Tabbas Jamilu ya tsaya mata da gangar jikinsa da aljihunsa, duk irin ɓarna da ta'asar da takeyi shi yake biya, amma dukda haka ta kasa amincewa da soyayyarsa? Anya tayi hallaci kuwa?
Jamilu jin tayi shiru yace, "Ayusher! Bazan tursasa miki ba saboda duk abinda kike so shi nake so, idan kinga ban dace da ke ba karki cuci kanki ki fito ki gaya mun" ya ƙarasa faɗa muryarsa na rawa.
Idanunta ne suka ciko da ƙwallah, murya na rawa ta ce, "Ya Jamil!" sai kuma ta kasa furta komai, ganin kukan da take ɓoyewa na neman cin ƙarfinta yasa ta kashe wayar gabaɗaya, tana juyawa zata fita daga garden ɗin ta ci karo da Fahad yana tsaye harɗe da hannu a ƙirji, da gudu ta bi ta gefensa ta wuce cikin gida kai tsaye ta wuce ɗakinta, ta faɗa kan gado tana rushewa da matsanancin kuka.
Fahad daskarewa yayi a gurin saboda jin maganganun da Indo ta furtawa Yaseer, saboda tun farkon hirarta da Yaseer ya shigo gurin, da niyyar fara sakarwa Indo Fuska kafin ya sanar mata da ƙudurinsa. Ƙafafuwansa ne suka gaza ɗaukar gangar jikinsa saboda yadda yaji kansa yana sara masa, kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki haka ya taka zuwa ɗakinsa ya haɗa kai da gwiwa. Aunty Safna ba ƙaramin jin daɗin soyayyar Yaseer da Indo taji ba, haka Momma wacce bakinta yaƙi rufuwa. Ganin lamarin na gidane yasa cikin kwana biyu Daddyn Yaseer wato Yayan Mahaifin Indo suka tsayar da maganar auresu, cen gurin Yaya Haruna aka kai kuɗin Indo dubu ɗari da hamsin da sa ranar wata shida. Murna gurin iyayensu abun baya musaltuwa, haka ɓangaren Yaseer ana tabbatar masa da sa ranarsa da Indo ya kira ɗan uwansa, cikin murna ya sanar masa. Lokacin da Yaseer ya sanarwa da Fahad yana kwance wani irin zazzaɓi ya rufeshi, ɗan sakin fuska yayi kamar ba abin da yake damunshi, ya nuna farincikinsa ga ɗan uwan nasa sannan sukayi sallama.
Indo tun da ta shiga ɗaki sai da ta sha kuka me isarta sannan tayi wanka ta koma ta kwanta, tun da ta kashe wayarta bata ƙara kunnawa ba, mahaifiyarta ta lura da ƴar damuwar da take ciki da farko tayi niyyar ta tunkareta domin taji matsalarta, amma sai ta bari zuwa kwana biyu dan taga yadda yanayin nata zai sauya. Indo ko da ta ji sa ranarta da Yaseer tayi farinciki amma sai ta rasa da wane ido zata kalli Jamilu, kuma me zata gaya masa? da wannan tunanin bacci yayi awon gaba da ita.
Baba Huwaila ce zaune tana waya da Aunty Safna, Jamilu ne ya shigo ya nemi gefen Baba Huwaila ya zauna, dariya yaji Baba Huwaila tayi haɗe da guɗa ta ce, "Ayyiriri kai Alhamdulillahi da Allah ya nuna mun wannan ranar, yanzu Indona ce aka sawa ranar aure Safiya? amsa mata akayi daga cen ɓangaren sannan ta kuma cewa.
"Allah ya nuna mana da rai da lafiya ina jikar tawa ne banji motsinta ba?" Aunty Safna ta ce, "Tana É—aki wai kanta ne yake ciwo" Baba Huwaila ta ce, "Ki duba mun ita kafin na kirata a waya" hira suka yi sannan sukayi sallama.
Baba Huwaila da murnarta ta ce, "Kai Jamilu yaudai ansaka ranar Indo, mugun bakinka ya koma kanka yaudai Indo ta kusa zama ta Yaseer. Aikuwa Allah ya kaimu da rai da lafiya ranar auren Indo sai nayi rawa na juya" tunda Baba Huwaila ta fara magana kansa ya sara, fuska ba walwala ya ce, "Allah sanya alheri" Sototo Baba Huwaila tayi ta ce, "Au Jamili baƙin cikin naka haka ya shahara akan yarinyar nan, na gaya maka abun daɗi amma sai haɗe fuska kake kamar wanda yaci kashi." Jamilu da yaje har wuya ya ce, "Wai Baba Huwaila me yasa kike haka ne me zan yiwa baƙin ciki, dama haka Allah ya tsara." yana gama faɗa ya tashi zai fice, Baba Huwaila riƙe baki tayi ta ce, "Jamilu bansan lokacin da ka lalace da hassada ba, hassada ta samu gurbin zama a zuciyarka, Anya Jamilu rayuwa zata yuwu haka?" yana jinta har ta gama magana bai kulata ba ya fice ya nufi ɗakinsa kansa na juyawa.
Indo sai bayan kwana biyu da sa ranarta da Yaseer ta buɗe wayarta, saƙonnin Yaseer har babu adadi daga text msg har zuwa whatsapp. Replay tayi masa ta whatsapp bayan minti goma sai ga kiransa ya shigo wayarta, ɗauka tayi da sallama murya a sanyaye. Amsa mata yayi sannan ya fara jero mata tambayoyi kala-kala, murya ba walwala ta ce, "Wallahi bana jin daɗi ne Ya Yaseer shiyasa na kashe wayata gabaɗaya" sannu yayi mata daga nan ya ɗan fara janta da hira tun tana ɗan ɗari-ɗari, har ta saki jikinta suka sha hira sannan sukayi sallama.
Yamma liƙis Indo na kwance a ɗaki, kiran Jamilu ya shigo wayarta. Wata mummanar faɗuwar gaba taji da ta ga lambar Jamilu, kamar bazata ɗauka ba tayi ta maza ta ɗauka da sallama tayi shiru. Daga cen ɓangaren Jamilu ya amsa ba yabo ba fallasa sannan ya ce, "Ayusher ashe ansa ranarki amma baki gaya mun ba?" Indo shiru tayi ƙirjinta na ci gaba da lugude, Jamilu ya cigaba da cewa. "Ina taya ku murna sosai Allah sanya alkairi Ubangiji ya kaimu lokacin da rai da lafiya, Baba Huwaila ma ta ce ta neme ki bata samu ba" Murya na rawa Indo ta ce, "To zan kira ta" Jamilu ya ce."Maganar da na miki rannan inasan ki binneta tunda bayan ke babu wanda na sanarwa, ina miki fatan alkairi Ayusher a koyaushe". yana gama faɗa ya katse wayar, Indo na jin haka ta cire wayar daga kunne tana rushewa da kuka, ita kam bata san haka cakwakiyar soyayya take ba, meyasa tun tuni Jamilu bai sanar mata ba ko dai zata rabu da Yaseer ne? Wani tsagi na zuciyarta soyayyar Yaseer ce ke cigaba da azalzalar zuciyarta, a zuciyarta take waɗannan kalaman a fili ta furta, "Anya zan iya jingine soyayyar da nake yiwa Ya Yaseer kuwa? Idan na juyawa Jamilu na yiwa kaina adalci kuwa" bata da wannan amsar illa komawa da tayi tai lamo tana shashaheƙar kuka.
"Yanzu Fahad ya kake so nayi? Kasan dai mace bata auren maza biyu ko? Tuntuni kasan kana san nata kayi sake har ta fara soyayya da ɗan uwanka? Babu abinda zan iya maka yanzu illa kayi haƙuri haka Allah ya tsara, kasan matar mutum kabarinsa kuma dan Allah karka bari ɗan uwanka yasan da wannan maganar." Mommy ta ƙarasa faɗa cikin lallashi. Fahad miƙewa yayi ya amsa ciki-ciki yana furzar da isaka mai zafi, ya fice daga falon.
A ranar ya dawo garin Kaduna dan gani yake zamansa a ko'ina zafi yake masa idan ba a Kaduna ba. Washegari Indo na garden a zaune ta zubawa tsuntsaye Ido, a zahiri su take kallo amma hankalinta ya tafi wani guri daban, Fahad ne ya shigo gurin ya janyo kujera ya zauna suna fuskantar juna, Indo miƙewa tayi zata zauna muryarsa a raunane yace.
"Humaira! Dan Allah ki zauna" maganarsa har amsa amo tayi mata a dodon kunnenta, a iya saninta tunda take dashi bai taɓa ambatar sunanta ba, tana tsaka da tunani ya ce.