← Book details Indo Sarƙa Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 76

Sashe 12

Indo Sarƙa Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wannan taron ban tarashi domin komai ba sai dan inbada cigiya, ina buƙatar sannin waye me wannan takalmin daga yanzu zuwa nan da bayan la'asar, zan bawa duk wanda ya gayamun waye mai takalmin nan tukwicin naira dubu ɗari biyu " hayaniya ce ta fara tashi sama-sama kowa da Abinda ake faɗa, Fahad ne yayi gyaran murya ya cigaba da cewa.

Ina buƙatar hujja gamsassa nasan dai takalmin na mace ne kuma akwai hujjar da inna gani zan gane wacce take da mallakin wannan takalmin "

Indo kallan tsaf tayi masa sannan tayi murmushi, daga cen gefe ta É—aga hannu, kallanta yayi cikin mamaki ya gyaÉ—a kai alamar ta fito, da idanu ya bita yana wani nazari domin gani yake kamar yaso yasa fuskarta.

Tana fitowa gaban jama'a ta kalleshi ido cikin ido ta ce, " Nasan Mai takalmin amma dubu É—ari biyu tamun kaÉ—an kuÉ—in tukwici"

Da mamaki kowa ya zurawa Indo ido shi kansa Fahad mamaki ne ya kamashi, jinjina kai yayi ya ce, " Faɗi duk abinda kike buƙata na miki alƙawari zan cika miki "

Indo sunkuyar da kai ƙasa tayi kamar mutuniyar kirki sannan ta ɗago ta ce, " So nake kayi sati biyu acikin garin nan, kuma wannan kuɗin ka maidasu su zama naira dubu ɗari biyar "

_Ummou Aslam Bint Adam_😉
[17/06, 03:31] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

*INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️
*BY*
*AMEERA ADAM*

*FOLLOW ME @WATTPAD*
_*AmeeraAdam60*_

GARGAÆŠI BANYAR WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.

_*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_

BAYAN ƊAN HUTUN DANA ƊAUKA YANZU NA DAWO🌚 BARKANMU DA SALLAH DA FATAN KOWA YAYI SALLAH LAFIYA, INA MUKU FATAN ALHERI.🥰

27&28

Fahad Jim yayi saboda Allah ya sani ba zai iya ƙara koda kwana uku a wannan ƙauyen ba bare kuma sati guda, Indo kamar ta so ta gano lagwan Fahad ta ɗauke kai gefe tana murmushin gefen baki, kallan sa tayi ta tsuke fuska ta ce.

" Naji kayi shiru inbazaka iya ba zan wuce dan ina da Abinyi "

Da sauri Fahad ya ɗago da kansa yana kallon saboda yanda tayi maganar cikin izza da ƙasaita kai ka ɗauka wata isashshiyar budurwa ce take magana, ɗan karka kansa yayi gefe yana jinjina kansa saboda kusan tunda yake a rayuwarsa babu wanda ya taɓa gaya masa haka, guntsun zaki ya ja sannan ya ce.

" Bazan iya sati a cikin baƙin ƙauyen nan naku ba, while zan iya ƙara miki kuɗi akan yanda kika buƙata but karki wuce yau banji wani issue ba, ki tabbatar da kin haɗo da ɗayan warin takalmin "

Indo bakin zaninta ta kunto ta ciro gyaɗarta marau sai da ta ɓare ta watsa ta a baki, tana ci tana tauna kamar ba zata bawa Fahad amsa ba ta, maida ƙullin gyaɗar tayi jikin zaninta ta ɗaure sannan tayi taku biyu ta kalleshi ta ce, " Kamar yanda na gaya maka ina da abinyi idan har bazaka ƙara sati ba to shikenan, kuma ƙauye dai naga asalin kowa ƙauye wanda ma basu da ƙauye ba birgewa sukayi ba " sauran gyaɗar hannunta ta watsa baki ta cigaba da tauna "

Fahad haushi ne ya kamashi saboda irin maganganun da Indo ta gaya masa, basarwa yayi saboda ya lura idan ya biyewa Indo sai ta zubar masa da mutumci a idanun jama'a.

Ɗauke kansa yayi daga kallanta ya ce, " Shikenan ba buƙatar hakan kije na gode "

Indo zuciyarta fes saidai a ɓangare ɗaya ƙirjinta banda lugude ba abinda yake dan gani take kamar fahad zai gano ta.

Wasu tafka-tafkan tsofaffun sifas ɗin Jamilu ne saƙale a ƙugunta da ta ɗaure su da mayafinta, cikin halin ko inkula ta kunce su ta fankama abinta a ƙafa, Fahad haushin Indo ne ya rufe a fili ya ja gudun tsaki ya kuma ɗauke kai gefe.

Gabaɗaya mutanen gurin ido suka zubawa Indo kowa yana mamakin ƙarfin hali irin na Indo, ƴan matan garin kuma suna mamakin yanda Indo ta tsaya take iya gayawa Wannan kyakykyawan Ɗan birnin magana, ta ɓangare guda kuma suna ganin wautar Indo da taki amincewa da buƙatarsa alhalin tasan wannan Mai takalmin ga kuma maƙudan kuɗin da yace zai bayar.

Su Zulai na gefe guda suna ƙus-ƙus da alama zancen Indo sukeyi akan takalmin Lami ce tace wa Zulai.

" Zulai ni takalmincen sai yayi mun kama da naccgff Sarƙa ko dai nata ne take wa Ɗan birni basaja? "

Zulai da tasan halin Indo idan akaji magana daga gurinta ta fito ta ce, " Oho waya sani yanda kika ganshi nima haka na gani "

Lantan abokiyar ƴar tsamar Indo tayi karaf ta ce, " Ke Zulai wallahi kinyi asara yanzu Sarƙa kike tsoro saboda kina gudun karta yankaki ɗanye, ai nasan komai sarai wannan takalmin Sarƙa ne mu za'a rainawa hankali "

Zulai ta watsawa Lantan harara ta ce, " Kanki ake ji keda bakya tsoro ai gaki nan a tabonta a goshinki "

Suna cikin haka Indo ta ƙaraso gurin sai da ta ƙare musu kallo sannan ta tsare su da ido ta ce, " Magana ta akeyi ko " Lantan ɗauke kai gefe tayi Zulai ta ce, "

Indo gaba tayi ta koma bakin bishiya ta zauna tana sauraron abinda Fahad zai ce.

Fahad kallonsu yayi ya ce, " Bayan ita babu wanda yasan mai takalmin nan? So idan babu kowa zai iya tafiya " kamar masu jira haka suka dinga wucewa zugwi-zugwi, wasu daga cikinsu tsaki suke suna ƙananan maganganu.

Fahad na nan zaune wata dabara ta faÉ—o masa, murmushi yayi a fili ya furta, " Dole mu shirya tafiya gida yau hakan ne zai bani damar kama duk wacce take shuka tsiyar nan "

Indo dake cen bakin bishiya a zaune tunanin irin muguntar da zata yiwa Fahad kafin ya tafi dan ta fanshe marinta, tana nan zaune Fahad ya tako cikin nutsuwa kamar bazai tak ƙasa ba, sai da ya wuce ta ta harari bayansa a fili take, " Yana tafe yana ƙwanbare baya kamar Allon Malam Barau mai tsangaya "

BA LALLAI NA DINGA POSTING KULLIN BA SABODA ASEELA FANS MA SU SAKONI GABA🤣 GA WANDA BAIJI BARI BA SO KAWAI SAI YANDA TA KAYA.

_BINT ADAM CE_😉🌚
*FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

*INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️
*BY*
*AMEERA ADAM*

*FOLLOW ME @WATTPAD*
_*AmeeraAdam60*_

GARGAÆŠI BANYAR WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.

_*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_

29&30

Fahad yaji sarai abinda indo ta faɗa har yayi gaba kamar bazai juyo ba sai kuma ya dakata ya jiyo ya kalleta, indo basarwa tayi kamar ba ita tayi maganar ba sai ma ta fara waƙar, " Ahayye sha madarar lilo..." waƙar take yi har ƙarshenta tanayi tana taunar gyaɗarta tana gyaɗa kanta, girgiza kai Fahad yayi ya wuce yana mamakin fitina irin ta wannan yarinyar.

Indo na zaune su Zulai suka ƙaraso gurinta suma zama sukayi a gefenta, Indo na ganinsu ta watsa sauran gyaɗar a baki ta cinye, Zulai ce ta ce, " Sarƙa saboda kin ganmu zaki cinye sauran gyaɗar? " Indo kamar jira take ta ce, " Ni banma ga ƙarasowarku ba sai yanzu, to idanma na cinye ba tawa bace " Saude ta ce, " kedai kawai kice kin cinye amma ba maganar baki ganmu ba "

Indo shiru tayi bata tanka musu ba, tashi sukayi zasu tafi ko me indo ta tuno da sauri ta ruƙo hannun Zulai ta ce, " Yauwa ƙawaye na ina zaku ne? "

Saude ta ce, " Zamu tafi munga kamar bakya buƙatar zaman mu " Tasowa tayi ta shiga tsakiyarsu tana saƙala hannuwanta akan kafaɗarsu ta cigaba da cewa.

" Saude kunsan me nake so? " Kamar masu jiranta suka ce, " A'a sai kin faÉ—a "

" Wallahi tun É—azu nake tunanin irin abunda zanyi wa wannan É—an birnin na fanshe marin da yamun amma na rasa ku kawo wata dabarar " cewar Indo.

Zulai tayi karaf ta ce, " Sarƙa kinsan Lantan taso gane kece me takalmin nan ɗazu har tambayata tayi " cikin halin ko'inkula Indo ta ce, " To ai da kun bata amsa inyaso taje ta faɗa masa wallahi dai-dai nake da zamaninta tasan karnmu da ita baya kyau " Saude ta ce, " Gaskiya Sarƙa tsoro nake ji kinga fa yanda mukayiwa Mai gari baiji da daɗi ba, kawai kiyi haƙuri tsoro nake karmu jawa kanmu ruwa, haka kawai a kamamu a tafi damu birni gurin ƴan sanda "

Tunda Saude ta fara magana Indo ta kafeta da ido cikin masifa ta ce, " Da haƙurin ya mutu sadakar nawa kika bani, dama na lura tun cen ke matsoraciya ce, ki barshi bana gayyarki kuma wallahi idan asirinmu ya tonu ko bake bace kece, aikin banza ni wallahi bana tsoron mutum sai Allah, ba ƴan sanda ba Allah sa gun ƴan itace za'a kaimu " Indo na ƙarasa maganar taja hannun Zulai zasu wuce, Saude jiki a sanyaye tabi bayansu tana bawa Indo haƙuri.

Indo zuciyarta ƙal saboda dama tasan su Zulai bazasu watsa mata ƙasa a ido ba, cen ƙofar gidansu indo suka ƙarasa akan dandamalin ƙofar gidan suka zauna, Zulai ce ta kalli Indo ta ce, " Wai Indo ya akayi kika bar takalminki gidan Mai gari kodai tarko suka ɗana miki? " Indo jim tayi kamar mai nazari sannan ta bawa su Zulai labarin abinda ya faru tsakaninta da Fahad, dariya suke harda riƙe ciki.

Itama dariyar take sosai suna nan zaune Jamilu yazo ya wucesu ya samesu suna wannan dariyar, jikinsa ne ya bashi wannan zaman nasu ba abin arziƙi zasu ƙulla ba, har ya kusa shiga gida ya juya fuska a tsuke ya ce.

" Ke kizo muje zan aike ki "

Biris Indo tayi kamar bataji Mai ya ce ba ta cigaba da ƙyaƙyata dariyarta, Saude ce ta ce, " Sarƙa ana miki magana "

Indo ɗauke kai gefe tayi ta ce, " Waye yake kirana ni banji an ambaci suna na ba ai " Jamilu ƙarasowa yayi ya zuba mata rankwashi yace, " Ni ne nake kiranki "
Chapter 12 · 0% Book details