← Book details Indo Sarƙa Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 76

Sashe 8

Indo Sarƙa Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokacin da suka je tuni Mai gari ya jima da bacci, a farfajiyar asibitin suka ci karo dasu Baraka, Indo gurin Magajiya ta nufa sai sa ta gaisheta sannan tayi mata ya mai jiki, Magajiya cikin dattako ta msa mata Baraka dake gefe ta hayayyaƙowa Indo tana faɗin, " To rasa kunya wato ni ban isa ki gaida ni ba ko? " harara indo ta watsa mata ta ce, " Mutumci ay madara tuni kin riga da kin zubar da naki "

Indo na gama faɗa ta wuce hanyar da zata sadasu da ɗakin mai gari, Nurses ɗin nan suna zaune suka tahowar su Indo da bokitai, da sauri ta dakatar dasu tana tambayrsu, Indo ba tsoro ta shaida musu dubiyar Mai gari, hanasu shiga tayi suka juya jiki ba ƙwari, sai dai fal zuciyarsu a dagule take.

Baraka sai habaici take wa Indo ita kuwa ko a jikinta, har sunbi hanyar fita Indo ta cewa su karime, " kuxo mu zagaya ta bakin window ay bazasu gammu ba " su Indo zagaya sukayi suka je bakin ƙofar da Maigari yake kwance, hangoshi sukayi yayi ɗai-ɗai da alama baccin wahala yake, musu suka farayi a junansu akan cewar Maigari ya mutu wasu kuma suka ce suma bai mutu ba.

Dutse Indo ta ɗauka ta ce, " bari mu raba gardama " tana rufe baki ta saita Maigari ta jefa mai dutsen hannunta aykuwa cikin sa'a ta wurga masa dutsen nan akan wani ƙululu dake goshinsa.

_Ummou Aslam bint Adam_😉
[17/06, 03:31] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

*INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️
*BY*
*AMEERA ADAM*

*FOLLOW ME @WATTPAD*
_*AmeeraAdam60*_

GARGAÆŠI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.

_*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_

17&18

_KUYI HKR BAN TACE SHI BA_👏🏻

Mai gari cikin bacci ya ji wani irin raɗaɗin azaba akan kamar wanda aka zabura haka ya miƙe azabure yana kurma ihu, Nurses ɗin da ke waje ne suka jiyo sautin Maigari da sauri suka shigo ɗakin suma su Baraka rufo musu baya sukayi dan suka mai yake damun mai gidan nasu, lokacin da suka ƙaraso ɗakin tuni Mai gari ya daɗe da shigewa ƙarƙashin gado, yana faɗin, " Dan Allah kuyi haƙuri ku mun rai wallahi duk zan maida musu dukiyoyinsu " da farko rasa gurun da Mai gari yake sai ihun sa da ke tashi, ɗayar Nurse ɗince ta ɗan sunkuya ta bankaɗa ƙasan gadon sakamakon hango pan ƙafafun Maigari da tayi sun leƙo, da sauri Maigari yaja da baya yana kuma kurma ihu, Magajiya ce ta zura kanta ta ce masa, " Malam dan Allah ka dinga ambaton Allah, sannu ko jikin ne? " sai da yaga fuskar Magajiya sannan ya saki ransa ya fara magana, " Dan Allah Magajiya karku ƙara nesa dani wallahi sunce kashe ni zasuyi fatalwa ce take bibiyar rayuwa ta " gaba ɗaya Nurses ɗin dariya abun ya basu sai kawai suka maze ɗaya daga cikinsu ta ce, " Ranka shi daɗe ka fito daga gurin nan dai babu wata fatalwa da zata zo gurinka " Maigari sai da ya kalli hagu da dama ya kuma zuro kansa sosai sannan ya yanƙura ya fito da ƙyar yana yana muzurai, kan gado ya hau ya zauna sannan ya kalli Ado dake gefe ya tsuke fuska ya ce, " Kai Ado ina Rawanunmu aka barmu kai ba hula ba rawani mai yake damunku ne? "

Ado sosai kansa yayi cikin zuciyarsa yake ayyana ƙarfin hali irin na Maigari yana cikin wani hali yana neman wani rawani, amma sai ya ce masa, " Allah ya baka yawan rai lokacin da muka taho asibiti kana cikin wani yanayi ne babu damar neman Rawani " ɗan jim Mai gari yayi yana tunanin halin da ya tsinci kansa aciki, shafa kansa yayi yaji wasu irin manyan ƙululai sai zugi suke masa, runtse idanunsa yayi cikin jin zafi sannan ya buɗe su, Mai gari ko tunanin mai yayi sai gani sukayi ya zabura yana cewa su Baraka su wuce shi gida zai tafi, Babu yanda Nurses ɗin nan basuyi da Maigari akan ya haƙura ba amma fir yaƙi amincewa, babu yanda su Baraka da Magajiya suka iya haka Maigari ya sasu a gaba suna tafe yana binsu abaya, su Ado kuma su aka bari da tura kura.

Indo tun bayan tashin Maigari banda dariya babu abinda sukeyi gudun kar aganosu yasa suka tsutatsuna suna leƙowa da kawunansu, lokacin da sukaji Maigari yace zasu wuce tuni su Indo suka saɗaɗa suka fice daga Asibitin.

Mai gari na komawa gida ya sake shiri da rawani, cen ƙasan akwatin ya buɗe ya ɗebo wasu takardu kala-kala, cen wata jaka a saƙale ya ɗauko itama ya dinga ɗebo takardu sai da ya haɗa duk takardun da yake buƙata sannan ya fito tsakar gida ya ƙwallawa matansa kira, cikin gurmamawa sun zo suka rissuna a gabansa gyara tsayuwarsa yayi ya ce, " Kuyi gaggawar kammala aikin gida anjima kaɗan ku sameni a fada " da mamaki suka ɗago cikin haɗin baki sukace, " Fada " Maigari gaba yayi yana faɗin, " ƙwarai kuwa domin yau ko wanne shege zai karɓi takardun gadonsu nima na huta da masifa " ya na gama faɗa yasa kai ya fice.

Maigari yana zuwa fada ya aika sanƙira yayita shela yana sanarda Maigari nasan ganin kowa a fada babba da yaro, Lokacin sa yaje wucewa ta gidansu Indo tana zaune tana cin abinci, dariya ce ta taso mata cikin suɓutar baki ta ce, " Shege Maigari anji maza " Baba Huwaila zaro ido tayi ta wurgawa Indo daƙuwa sannan ta fara mata faɗa, ɗauke kai gefe Indo tayi sannan ta ce, " Yauwa Baba Huwaila dan Allah kimun alƙawarin komai nace kiyi zakiyi " da kallon mamaki ta bi Indo zuwa cen ta ce, " Ja'ira wani abun kika aikata ko? " marairace fuska Indo tayi ta ce, " Dan Allah nidai kimun alƙawari zan gaya miki " Baba Huwaila ta ce, " To na miki ina jinki idan baifi ƙarfi na ba "

Indo saboda murna tashi tsaye tayi tana rawa harda juyi sannan ta koma ta zauna ta ce, " Baba Huwaila nasan kiran da Maigari yake mana takardun gadona zaije mu karɓa dan girman Allah kice mun yafe yaje ya riƙe, ba dan raina doka ba ma wallahi Baba Huwaila da sai muyi zamanmu " kallon baki da hankalu Baba Huwaila tayi mata sannan ta ce, " Lallai yarinyar nan abunda muke nema amma kuma mun samu dama muce bama so? Har yanxu da sauranki " Indo tsuke fuska tayi ta ce, " Kinsan dai alƙawari kayane kuma kin riga da kin ɗauka, Bba Huwaila kinsan dai ba zanyi abu dan na cutar damu ba " jikin Baba Huwaila ne yayi sanyi ta amincewa Indo, daga nan ta shi sukayi kowacce ta ɗau hijabinta suka kai tsaye suka wuce fadar Maigari da tuni harta fara cika.

KUYI HƘR DA WANNAN.

_Ummou Aslam Bint Adam_
[17/06, 03:31] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

*INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️
*BY*
*AMEERA ADAM*

*FOLLOW ME @WATTPAD*
_*AmeeraAdam60*_

GARGAÆŠI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.

_*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_

19&20

_SHIMA KUMUN AFUWA BAN TACE SHI BA_👏🏻

Mai gari na zaune sai waige yake yana hango mutane yake daga ko'ina suna tahowa zuwa fadarsa, daga cen nesa ya hango Indo da Baba Huwaila suna tahowa ajiyar zuciya ya sauke yana kuma leƙen Musataf ɗan gidan Marigayi Malam Sada kasancewar iyalan gidan ne kaɗai bai hango ba, daga cen Yamma ya hango zugar gidan Malam Sada sun taho a karo na biyu ya ƙara sauke ajiyar zuciya, sunkuyar da kansa ƙasa yayi shi kaɗai yana nazari bayan wani ɗan lokaci ya ɗago da kansa bayan kowa ya hallara agurin.

Ado ne ya ɗaga wata ƴar lasifa irin wacce masu sayen kayan gwangwan suke yawo da ita ya fara magana, " Assalamu alaikum, barkanku da wannan lokaci na tabbata duk gurin nan akwai iyaye ko yayyen waɗannan yaran da suke mana surutu, ya kamata ku ja kunnensu inba haka ba kowa zai biya kuɗin tara kamar yanda aka saba biya aduk wani babban taro irin wannan " Ado na gama magana harabar gurin yayi tsit sai dai ɗan abinda ba'a rasa ba, ƙasa-ƙasa mutane ke ƙus-ƙus kasancewar sun jima ba suji Maigari ya yayi wannan gagarumin taron ba, tun lokacin da aka turo musu da tallafin gidajen sauro daga gwamnati, hakan ne yasa kowa yayi tsit ya ya maida hankalinsa ga Maigari, sai dai ganin baby baƙin fuska yasa suka fara wasi-wasin maƙasuɗin taron.

Ado miƙawa Maigari lasifika yayi sannan ya koma cen gefe ya tsaya, Maigari ƙara miƙa kansa gaba yayi sannan ya waiga gefe da gefe yana ƙarewa mutanen gurin Kallo, Gyaran murya yayi sannan ya fara magana, " Asalamu alaikum warahamatullahi ta'alawabarakatuhu, Nasan da yawa daga cikinku zasuyi mamakin wannan taro na gaggawa ba tare sanarwa daga baya ba kafin wannan rana, Wannan taro mun yi shi ne domin mu dawowa da wasu mutane daga cikinmu waɗanda aka damƙa mana dukiyoyinsu, gonakinsu, da ƴan kadarorin da ba'a rasa ba " ƴar hayaniya ce ta fara kaurewa agurin ƙasa-ƙasa kowa da abinda yake furtawa waɗanda kuwa suka san da dukiyarsu agurin Mai gari jin suke kamar Sallah saboda murna bakunansu sunƙi rufuwa, Maigari ne yayi gyaran murya hatsaniyar ta ɗan tsagaita sannan cigaba da cewa, " Zamu fara kiran sunayen takardun dallah-dallah ɗaya bayan ɗaya, duk wanda yaji sunan Mahaifinsa ko kakansa ga wanda takardunsu ke gurina sai su miƙe tsaye, zamu ware su guri guda idan mu kammala ware su sai mu ƙara dawowa mu maimaita kiransu ɗaya bayan ɗaya domin mu tabbatar da sahihancin wanda ya amsa dan kar mu bawa wanda ba shi ne mai mallakin gadon ba " Akaro na biyu ƴar hayaniya ce ta ƙara tashi wannan karon Ado ne yayi magana sannan suka dakata.
Chapter 8 · 0% Book details