← Book details Indo Sarƙa Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 76

Sashe 26

Indo Sarƙa Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani murmushi mai ɗauke da manufar lallai yarinya bakici nanin ba Hajiya mai abincin tayi sannan ta tsuke fuska kamar bata taɓa dariya ba tace, "Ke dube ni nan ki gani kinga na miki kalar wacce zaki rainawa hankali? To tun muna magana cikin mutumci ki bani kuɗi na idan ba haka ba na haɗaki da ɗaya daga cikin yarana ki kaishi inda Honey yake "Indo zuru-zuru tayi ta rasa abinda yake mata daɗi cikin marairaicewa ta ce.

"Wallahi kinganni Hajiya a garin nan babu wanda na sani Honey kawai na rako daga nan yace zai kaini gidan rediyo cigiyar iyayena shine muka zo cin abinci nan ni kuka bansan guduwa zaiyi ba " Dariya Hajiyar tayi ta ce, "Honeyn Ubanki ne da bazai nuna miki hali irin na maza ba " Indo tayi ta farat tace,"Eh, kamar uba haka na ɗauke shi amma dan Allah kiyi haƙuri ko gurin da zan kwana bani da shi " ƙare mata kallo Hajiya tayi taga irin tsukakkun riga da siket ɗin dake jikin Indo sannan ta ce, " Kai Allah wadaran naka ya lalace, banda lalacewar zamani yanzu wai ƴar ƙanƙanuwar yarinyar kamar ke har kinsan shiga Abuja ki raka ƙasurgumin ƙato wai honey,tunda uba kika ɗaukeshi sai ki kirashi yazo ya biyani kuɗi na,har namijin bariki zaki ce kin ɗaukeshi uba" Indo tsumu tayi babu amsa banda raba idanu babu abinda takeyi, saboda ta ma rasa ta ina zata nemarwa kanta mafita daga gurin wannan mai abincin.

Cen ƙasa Hajiya ta nunawa Indo tace, " Ga guri cen ki zauna har ki nemar mum kuɗina idan Honey yaji shiru ai dole ya biyo sahunki" Indo cikin zuciyarta take tunanin anya kuwa Honourable zai dawo saboda irin dukan da tayi masa,wani murmushi ne ya ƙwace mata da ta tuna sanda ta ɗaurewa Honourable ƙeya da wayar talabijin,rabonda tayiwa wani irin wannan gigitaccen dukan tun zuwan da suke yiwa Maigari,ƙauyensu ne ya faɗo mata da Baba Huwaila tunawa tayi da a gida take da tuni tana cen kwance akan katifarta,hawaye ne ya zubo mata cikin zuciyarta take addu'ar Allah ya cika mata burinta.

A ranar da Jamilu ya shigo cikin garin Kano Unguwar Hotoro ya sauka gidan wani kawunsa Kawu Umaru ɗan Baba Huwaila na biyu ne,duk abinda yake faruwa haka ya sanar da shi da manufarsa ta shigowarsa cikin gari,ba ƙaramin damuwa suka shiga ba jin halin da Baba Huwaila take ciki ta sanadin barin Indo daga gida.
Washegari da safe Kawu Umaru suka shirya kai tsaye gidan rediyon Freedom da Rahama suka je suka bada cigiyar Indo da yanayin kamaninta tare da adireshin gurin da za'a sameta idan anganta da lambar waya,daga nan gidan talabijin na Abubakar rimi (ARTV) suka wuce nan ma aanarwarta suka bayar tare da wani tsohon hotonta,dana nan gida suka wuce Jamilu har lokacin ji yake kamar ya rasa wani abu mai muhimmanci a rayuwarsa ne,bai taɓa zatan Indo zata shiga ransa kamar yanzu ba sai gashi rashinta na neman hargitsa rayuwarsa,a ɓangare ɗaya kuma damuwar Baba Huwaila ba ƙaramin ɗaga hankalinsa take ba.

Honourable tunda ya cilla motarsa a kan titi ya bata wuta, da farko yaso ya canja Hotel,amma sai yayi tunanin sabon da sukayi da ma'aikatan kuma sun san waye shi ga irin ɓarnar da Indo ta tafka musu,yana komawa ɗaki ya sake ya sanar musu da abinda ya faru tare da alƙwarin biyansu kuɗin duk abinda aka lalata musu,yana shiga ɗakin da ya sake faɗawa kan gado yayi cikin gajiya saboda gabaɗaya jikinsa tsami yake da dukan da Indo tayi masa, afili ya furta," Shegiyar yarinya haka kawai zata illatani kai amma fa wannan aljanu nata ƴann azaba ne..." Maganarsa ce ta katse sakamakon kiran wayarsa da ya shigo,Numaber Hajiya Medile ya gani kauda kai yayi da guntun tsaki kamar bazai ɗauka ba sai kuma ya ɗauka murya ƙasa-ƙasa.

"Hello Hajiya ya akayi ne?" daga cen ɓangaren Aunty ta amsa, "Allah ya taimaki Honourable ai tunda naji shiru nace labari yasha bam-bam" a daƙile yace, "Eh labari kam yasha bam-bam Hajiya " daɗi ne ya kama Aunty tace,"To gaskiya Alhaji sai ka ƙaromun toshi,Ni banji motsin ƴar tawa ba ko bata kusa ne? " Fuska a tsuke yace," Ai dama bazaki ƙara jin motsinta a kusa dani ba, ashe mahaukaciya kika haɗani da ita bansani ba?Yarinya ta dinga dukana a ɗaki kamar wani ƙaramin yaro yanzu jikina yayi tsami banda ciwo babu abinda yake mun " salati Aunty ta sa sannan tace, " Duka fa Honourable Au haka Humaira zata yi maka bani ita a wayar zanci ubanta maza bani ita " guntun tsaki Honourable yayi yace, " Na kaita wanu Resturent na baro ta acen bazan iya da ita ba,sai ta ɓatamun suna ta zubar mun da kimata zan miki transfer na 1million ki share zancenta kawai" cikin rawar Murya Aunty tace, " To to bari na turo maka da Account Number yanzun nan " Bai tanka mata ba ya katse wayar afili yake furta, " Lallai wannan mata akwai mahaukaciya babu ruwanta da halin da yarinyar take ciki idan siyar da ita ma nayi shikenan ita dai burinta ka bata kuɗi " yana gama magana ya tashi ta faɗa toilet domin watsa ruwa.

Har kusan ɗaya na dare Indo na zaune tun tana zaune har ta fara gyangyaɗi,lokacin yaran Hajiya sun gama haɗa komai sun fara shirin tashi,Hajiya ce ta ɗakawa Indo duka a cinya tace, " Ke sai ki tashi mun tashi zamu rufe gurin" murje ido Indo tayi tana ɗan dube-dube sannan ta ɗauki ɗan figigin mayafinta,fitowa sukayi daga gurin aka rufe daga haka kowa ya fara kama gabansa yana tafiya makwancinsa,Hajiya ce ta kalli Indo tace, " Tunda na ganki zuciyata ta tsinke da mamaki saboda irin ƙanƙanta shekarunki,kiyiwa kanki faɗa wannan rayuwar da kika ɗaukarwa kanki ba me ɓillewa bace,tun wuri tun lokaci bai ƙure miki ki koma gaban iyayenki,kike na yafe miki kuɗin abincin amma idan halinki ne wata ran sai kinyi dana sanin abinda kike aikatawa " Hajiya na gama magana ta shiga motarta ta bata wuta ta wuce abinta.

Indo ta fahimci sarai inda maganar Hajiya ta dosa wani irin kuka ne ya ƙwace mata,durƙushewa tayi agurin tayi mai isarta sannan ta tashi ta cigaba da tafiya batare da tasan inda take cilla ƙafafuwanta.
Tafiya tayi mai nisa har sai da ta fara gajiya tsirarun mutane kaɗan-kaɗan ne sai motoci kaɗan da suke wucewa wani layi ta shiga ta cigaba da tafiya har ta ƙarasa ƙofar wani gida,Masallaci ta gani a gefensa da fanfo ruwa ta tara hannunta ta sha sannan ta taka ta hau kan interlock ɗin ƙofar gidan ta tsugunna,ta kurewa tayi aguri ɗaya saboda ɗan sanyi-sanyin da ke ratsa jikinta,kanta ta tusa cikin cinyoyinta babu jimawa bacci yayi awon gaba da ita.

Ƙarasowarsu amota ke da wuya fitilar motarsa ta haske bakin gate ɗin,yana shirin danna horn ya hango mutum tsugunne a bakin gate,a hankali ya danna horn wanda shi ya tashi Indo daga wahalallan baccin da take yi badam jin daɗi ba, a zabure ta miƙe ta matsa gefe ƙarasowa yayi da mota daga kusa da mazaunin Driver aka zuge glass ɗin motar aka fara magana, " Ke ƴanmata lafiya me kikeyi anan da tsohon daren nan?" Indo murza ido tayi ta ce wallahi bani da kowa a garin nan wani mugu ne ya gudu ya barni " kawai sai ta rushe da kuka.

Kafin su bata amsa maigadi ya leƙo ta window sa yana musu barka da zuwa,da sauri ya zagayo ya buɗe musu ƙofa matar ce ta kalli Indo tace, " Biyomu ciki " suna shiga mutumin ya ce, " Wannan ba ganganci bane daga ganin yarinya kice ta shigo mana cikin gida?"
" Idan ka lura akwai damuwa tattare da yarinya nan,idan bamu taimaka mata ba dole wasu zasu taimaketa watakila ta faÉ—a hannu na gari ko akasin haka, mu fara jin daga bakinta inyaso zuwa safiya sai musan abinyi " jinina kai yayi ya shiga da motar ciki.

Indo kamar wacce ƙwai ya fashew a ciki haka ta fara takawa ta shiga cikin gidan,dukda ba yau ne karanta na farko shiga cikin gida mai kyau ba amma ko a mafarki bata taɓa tsammanin zata taka guri irin wannan ba " parking ɗin mota sukayi a parking space sannan suka tako gurin da indo take.

Suna shirin yin magana wani matashi ya taho da gudu yana faɗin, " U are highly welcome my Momma "ya ƙarasa faɗa yana rungume matar da ke tsaye,Indo mamaki ne ya kamata ta kafeshi da kallo gabanta har faɗuwa yake take jikinta ya hau rawa,dukan bayansa matar tayi ta ce," Yaseer wai meyasa kullin baka girma ne ko sai nayi sirika tukunna " cikin murmushi yace, " Momma almost two months kenan fa rabonda na saki a idona kuma Daddy bai gayamun zai je ɗauko ki ba,kawai yace yau kar nai bacci idan ya dawo zaimun suprise " tunda ya fara magana Indo ta kafeshi da kallo tana mamakin zuwansa Abuja,cikin zuciyarta take maimaita sunan Yaseer da taji Momma ta faɗa har take tunanin ya akayi Fahad ya koma Yaseer?, Momma ce ta katse mata tunani ta ce, " Ai ni nace kar Daddynka ya sanar da kai dan nasan rigimarka ka dinga takuramun da tambayar yaushe zamu ta so " juyawa yayi da niyyar yiwa Daddy magana idanunsa suka kai kan Indo dake gefe cikin mamaki yace, " What a Beautiful Momma ina kika samo wannan " ya ƙarasa magana yana nuna Indo.

Indo cikin zuciyarta ta ce, " Kut wai wannan yana nufin bai sanni bane? Ko bai taɓa ganina ba? "

_CAKWAKIYA_🤪

*ASSALAMU ALAIKUM ƳAN UWA KAMAR YANDA NA SANAR DA KU ZANYI LITTAFIN GASA MAI SUNA SHAFAFFU DA MAI,A DA WAKILAN GASAR SUN BADA UMARNIN KOWA YA SAKI LABARINSA AMAN DAGA BAYA SUN CANJA TSARIN AKAN RANA-RANA NE INSHA ALLAH LABARI NA SAI NAN DA KWANA HUƊU ZAI SAUKA,DAN ALLAH KU TAIMAKA MUN DA SHARE KUMA AKWAI RANAR ZAƁE ZASU BAMU LINK MU BAKU KU MASOYA ZAKU SHIGA KUYI MANA VOTE DAN ALLAH KU NUNA ƘAUNARKU GARENI TA HANYAR ZAƁEN LITTAFINA NGD.*

_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
[05/08, 18:29] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

*INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️
*BY*
*AMEERA ADAM*

*FOLLOW ME @WATTPAD*
_*AmeeraAdam60*_
Chapter 26 · 0% Book details