Sashe 29
Indo Sarƙa Complete Hausa Novel · about 8 min read
Lokacin da Indo ta shiga ɗaki kan katifa ta faɗa tana lumshe idanu, wani irin nishaɗi take ji acikin zuciyarta. Fuskar Yaseer ce take mata yawo acikin ƙwayar idanunta, ɗagowa tayi tana murmushi a fili ta furta, "Yaseer kenan..."motsin ƙofar ne ya katse mata maganar da ƙoƙarin furtawa, Baba Mariya ce ta shigo tana faɗin, "Tsohuwa ana hutawa" Indo ta amsa mata, Baba Mariya zama tayi gefen katifa ta fara jan Indo da hira.
Tun daga ranar Indo ta fara wasan ɓuya da Yaseer ko sun haɗu a hanya gaisuwa ce kawai take haɗasu, ko da ya ja ta hira sai dai ta bashi amsa sama-sama ko ta ce masa zata shiga ɗaki tana da abinyi.
Tun abun baya damun Yaseer har ya fara damunsa sai yayi niyyar yiwa Indo magana sai kuma ya fasa dan bayasan duk wani abu da zai ɓata mata rai ko ya takurata, amma matakin da ya ɗauka na barazanar sanya rayuwarsa cikin wani hali. Wata rana Indo na zaune a garden zaune a kan kujera da alama tana cikin damuwa, Idanunta a rufe suke daga gefen idanunta hawaye na gangarowa. Ya jima a tsaye yana kallonta yana jin babu daɗi a zuciyarsa, duk ɗigon hawayenta ɗaya dai-dai yake ya bugawar numfashinsa, zuciyarsa ta kasa sukuni kamar zata hudo ƙirjinsa, Indo na daga zaune kamshin turerensa ne ya fara fusgar numfashinta, a hankali ta sauke ajiyar zuciyar tana juya ƙwayar idanunta da suke rufe, wani irin farin ciki ne ya ziyarci zuciyarta amma ko buɗe idonta batayi ba saboda kar Yaseer ya fahimci ta san da zuwansa.
Murmushi Yaseer yayi saboda ya fahimci sarai abinda Indo take nufi, handkee ɗinsa ya ɗauko ya ɗora mata a dai-dai fuskarta yana cewa, "Ki goge hawayenki bana buƙatar ganin su" Sautin muryar Yaseer yayi dai-dai da bugawar ƙirjinta, jiki ba ƙwari ta buɗe darara-dararan idanunta karaf suka haɗo. Da ƙyar ta samu sukunin sauke ƙawar idanunta ƙasa haɗe ta miƙa hannu ta karɓi handkee ɗin ta fara goge fuskarta, lumshe idanunta tayi saboda daɗin kamshin turaren da take shaƙa sannan ta miƙa masa.
Janyo kujera yayi ya zauna yana fuskantar Indo ya watsa mata manyan idanunsa, Indo ji tayi duk da tsargu ta fara wasa da zara-zaran ƴan yatsunta, Yaseer kallanta yake cikin murmushi saboda yadda yaga duk ta dubur-duburce. Indo ɗago da kanta tayi suka ƙara haɗa ido da sauri ta kauda kanta gefe tana ƙoƙarin miƙewa, Yaseer ƙafarsa yasa ya tokare hanyar da zata bi yana murmushin gefen baki, Indo cikin wata iriyar murya ta ce, "Ya Yaseer ni ka bani guri zan shiga ciki" Daidaita nutsuwarsa yayi cikin nutsuwa ya ce, "Idan naƙi fa?" Indo turo baki gaba tayi ta ce, "Nidai ka matsa zan wuce" Yaseer tsuke fuska yayi cikin wata iriyar murya ya ce, "Ki koma ki zauna" da sauri Indo ta kalleshi suna haɗa ido a zuciyarta ta ce, "Wallahi shi ne" jiki a sanyaye ta koma ta zauna. Yaseer murmushi yayi ya ce, "Matsoraciya kinji tsoro ne?" Indo ɗauke kai gefe tayi ta ce, "Ni ai bana tsoron kowa sai Allah" tun da ta fara magana ƙwayar idansa na kan ɗan bakinta sannan ya cigaba da cewa, "Humaira me yasa kike neman wahalar da rayuwata?" da sauri ta kalleshi tana mamakin maganganunsa.
Ya ci gaba da cewa, "Na rasa laifin da nayi miki da kike share ni kina azabtare da ruhina, kin daina hira dani kin daina bani tatsuniyarki mai daɗi ko kinasan na kai ƙararki gurin Momma?" Indo wani kallo ta watsa masa cikin zuciyarta ta ce, "Kai ƙara na nawa kuma? Banda ƙara ta da ka kai wata zaka kuma kaiwa" a fili ta ce, "Ba komai" Yaseer ya kuma jefo mata tambaya, "Humaira ni ne bakyasan na dinga raɓarki?" da sauri Indo ta kalleshi tana girgiza kai, murmushin gefen baki yayi sannan ya ce, "To idan bakyasan na kai ƙararki ki daina yi mun waɗannan sababun halayen naki" Indo hannunta ta sa a baki murya a sanyaye ta ce, "To na daina Ya Yaseer" shima murmushi yayi ya ce, "Gaskiya ban alama ba dan banga kinyi mun murmushi ba" da sauri Indo ta rufe fuskarta tana dariya, Yaseer dariya yayi daga nan suka cigaba da hira cikin farin ciki.
Tun daga wannan lokacin Yaseer da Indo suka ɗinke suka koma kamar yadda suke a baya, duk lokacin da Yaseer ya dawo daga gurin aiki bayan ya huta zasu zauna ya ƙara yiwa Indo bita akan karatun da akayi mata na ranar, bayan sun gama karatu sai ta zubo musu ruwan tea suna sha suna hira, Yaseer da Indo sunyi matuƙar shaƙuwa Momma har mamakin wannan shaƙuwar tasu take, duk lokacin da gurin aiki suka tura Yaseer wani garin idan zaiyi kwana biyu sai Indo tayi ta jin wani iri saboda damuwa, bata da sukuni ko walwala sai Yaseer ya dawo.
Indo sosai take fahimtar karatun da ake koya mata hakane yasa Daddy ya nemi wata private school mai suna Al-manar Collage yayi mata registration, makarantar haÉ—e take da islamiyya wuni suke tun bakwai na safe sai biyar na yamma suke dawowa. Kullin idan yaseer zai tafi aiki shi yake sauke Indo a bakin gate, da yamma kuma driver ne yake É—aukota ya dawo da ita.
A jss1 aka saka Indo saboda a yanayinta tayi girma a ce tana primary school, duk da haka malaman da suke zuwa biya mata karatu suna zuwa shiyasa karatun baya bata wahala sosai, a wannan lokacin ne Jikokin Baba Mariya su biyu suka dawo hakan ne yasa aka warewa Indo nata É—akin da toilet É—inta aciki.
Lokacin da su Indo suka cinye first term a result ɗin ta ita ta ɗauki ta goma sha bakwai acikin su talatin, gabannin zasu koma school Lubna ƴar ƙanin Daddy tazo karatun jami'a nan garin Abuja, a gurin Momma zata zauna har ta gama karatunta na shekara huɗu. A ɗakin Indo Momma ta sauke ta hakan sam be yiwa Lubna daɗi ba dan tana ganin kamar an ƙasƙantar da ita ne agurin wacce bata kaita gata ba.
Bayan Momma ta fita daga ɗakin su Indo Lubna a ya mutse ta kalli Indo ta ce, "Ke! Kamar kece mara asalin nan wacce muka ji labarin kece ƴar gudun hijara ko" Indo ji tayi kamar an buga mata guduma a ka, take idanunta suka kaɗa sukayi jawur, haɗiye ɓacin ranta tayi ta ce, "Eh nice, ke kuma wace ce?" Lubna taku biyu tayi tana watsawa Indo wulaƙantaccen kallo sannan ta ce, "Ni ƴa ce ga Alhaji Nasir ƙanin mai gidan nan, a taƙaice zan iya ce miki nan gidanmu ne" Indo cikin halin ko'in kula ta ce, "Ok, hakan yayi" tana gama faɗa ta tashi ta fice daga ɗakin.
Tana fita kai tsaye garden ta wuce tun kafin ta ƙarasa ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya, sai da tayi mai isarta sannan ta ji sanyi a zuciyarta. A hankali ta furta, "Me yasa na zaɓarwa kaina wannan rayuwa? Anya bazan koma gurin su Baba Huwaila ba?" ɗaya daga cikin tsagin zuciyarta ya ce, "Idan kin koma kina da abin da zaki goge wannan mugun tabon da kike da shi?" shiru tayi ta rasa bawa kanta mafita, gabaɗaya ji tai zaman gidan Momma ya fita daga ranta, ta jima a gurin tana saƙa da warwara sannan ta taso jiki ba ƙwari ta koma ciki.
Bayan kwana biyu su Indo suka koma makaranta, sai dai yanzu gabaɗaya bata sakewa saboda Lubna ta matsa mata, kodayaushe cikin faɗa mata magana take Indo ta rasa wannan dalili na tsangwamar da Lubna take mata, wannan dalilin ne yasa ko yaushe tana falo idan yamma tayi bayan ta gama karatu sai ta wuce garden ta zauna, idan ta gaji da kaɗaicin sai ta tafi gurinsu Baba Mariya tayi zamanta suyi ta hira. A yadda Indo ta lura Lubna batasan alaƙarta da Yaseer shiyasa ta fara takatsantsan dan gujewa abin da zai sa taci mata mutumci, dan ta lura rashin mutumci da wulaƙanci yafi komai sauƙi a gurin Lubna. Duk wanda ya san Indo a baya ya ganta yanzu sai yayi matuƙar mamakin irin sanyin da tayi, ta koma wata shiru-shiru mara san magana zagin wulaƙanci babu irin wanda Lubna bata yiwa Indo, sai dai ta ji ta da kunne idan ta ga maganar zata ɓata mata rai sai ta tashi ta bar mata gurin. Duk ranar da Lubna ta ga Yaseer da Indo a zaune guri ɗaya suna hira to a ranar sai tasan yadda tayi ta takalo Indo da faɗa, dan ta samu ta zage tas. A haka rayuwa ta cigaba da cuɗawa Indo har suka shafe wani lokaci tare.
Wata rana suna zaune suna a falo Yaseer ya shigo, yana shiga Lubna ta kalleshi tana sauke ajiyar zuciya, ba ƙaramin kyau Yaseer yayi mata ba, tana shirin magana ya ce, "Humaira ɗauko mayafi ki rakani shopping" take annurin dake ɗauke a fuskar Lubna ya ɗauke, a fakaice Indo ta kalli Lubna murmushin mugunta tayi a cikin zuciyar, ɗan yamutsa fuska tayi ta ce, "Ya Yaseer Assignment fa gareni kuma banyi ba" Kwaɓe fuska yayi kamar ƙaramin yaro ya ce, "Minti nawa zamuyi mu dawo ba fa daɗewa zamuyi ba, Lubna kema taho mu tafi" Lubna kamar jira take ta ce, "Ok, muje kawai Yaya" Indo haushi taji ba haka ta so ba amma cikin rashin damuwa ta koma jikin kujera ta kwanta, harara ya watsa mata ya ce, "Bazaki ba ko?" Dama haka Indo take so a hankali ta miƙe kamar ranta bai so ba ta wuce ɗakinsu, acen ɗakin tana shiga Lubna ta fara yadda habaici tana faɗin, "Nan gani dai nan bari duk cusa kan mutum bazai taɓa amsa sunan ɗan danginmu bane?" Indo bata kulata ta ɗauko mayafinta ta fito daga ɗakin tana fitowa tuni Yaseer har ya shiga mota su yake jira, Lubna haushi ne ya kamata rashin kulawar da Indo tayi mata, Indo ta fito baranta Lubna ta sa mata ƙafa ta baya cikin tsautayi Indo ta zame ta faɗi, kanta ne ya bugu da bango ya fashe wani irin zafi Indo taji cikin azaba ta ƙwalla ƙara, da sauri Yaseer ya fito daga mota yana zuwa ya ɗaga hannu ya zabgawa Lubna mari.