Sashe 32
Indo Sarƙa Complete Hausa Novel · about 7 min read
Gabaɗaya falon shiru yayi banda shashsheƙar kukan Indo babu abinda yake tashi, Lubna yatsina fuska tayi ta ɗauke kai gefe cikin zuciyarta fes kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha, Yaseer jin kukan Indo yake har cikin ransa lokaci-lokaci yake furzar da iska mai huci, Momma ce tayi ƙarfin halin yin magana ta ce, "Humaira shin abinda Fahad ya faɗa gaskiya?" Indo goge hawayen Idanunta tayi ta gyaɗa kai muryarta na rawa ta furta, "Eh Momma! Gaskiya ne abin da ya faɗa" Yaseer ji yayi maganar Indo kamar saukar aradu a tsakiyar kansa, da sauri ya ɗago ya kalleta yana mata wani irin kallo mai wuyar fasaltuwa, suna haɗa ido da ita ta sunkuyar da kai tana jin babu daɗi a zuciyarta, wani irin abu ne ya tokare ta Momma cikin ɓacin rai haɗe da mamaki ta kalli Indo ta ce, "Humaira dama duk abin da kika gaya mana ƙarya kike? Yanzu a ƙananan shekarunki har kin iya tsara zance irin wannan? Meye ribarki ta barin gaban iyayenki? Kina tunanin akwai mutanen da zasu maye miki gurbinsu ne? Gaskiya kin bani mamaki" Indo rushewa tayi da wani irin matsanancin kuka mai ratsa zuciyar mai sauraronta, Yaseer dukda yana cikin jin haushin haushin Indo hakan bai hanashi jin kukanta na ratsa jijiyoyin jikinsa ba, Lubna taɓe baki tayi ta ce, "Ai dama bahaushe yayi gaskiya da yace tsintacciyar mage bata mage, Allah ya tonu asirinki sai ki bi wani sarkin ba wannan ba" wannan karan Yaseer bai dakatar da Lubna ba saboda bashi da hujjar kare Indo, sunkuyar da kansa ƙasa yayi yana jin ɗaci a zuciyarsa. Indo sai da taci kuka mai isarta sannan ta tashi ta ƙarasa gaban Momma ta tsugunna ta ce, "Dan Allah Momma kiyi haƙuri ki yafeni akan ɓoye muku ainihin labari na da nayi, tabbas nayi kuskure amma dan Allah karkuyi mun mummunar fahimta. Babu ko tantama a maganar Fahad tabbas ni ƴar garin Kura ce kuma a cen muka taɓa haɗuwa da Fahad da Mommy lokacin da suka je gidan Maigarin garinmu, na taso a garin Kura gurin wata baiwar Allah da ta riƙeni tun ina ƙarama har na fara girma, daga baya Allah karɓi rayuwarta na koma hannun Aminiyarta da zama, sai dai inda Fahad yake tunani nan ne gidanmu sam ba mutanen gidan ne asalin mahaifa na ba..." Indo gabaɗaya ta kwashe labarinta ta basu har tahowarta garin Kano da yadda ta ƙwaci kanta agurin samarin da suka biyota, zuwa gidan Aunty da haɗuwarta da Fahad a resturent har zuwa tahowarsu garin Abuja da dalilinta na zuwa ƙofar gidansu ta zauna." Indo na rufe baki Daddyn Yaseer ya shigo jiki a sanyaye saboda yaji duk abinda Indo take faɗa, zama yayi a kan kujera Indo ta cigaba da cewa, "Tabbas nasan zamana a gidan nan yazo ƙarshe, amma ko da zan tafi zan shiga duniya ne domin naci alwashin bazan koma gurin Baba Huwaila ba har sai na nemo ainihin iyaye na, Momma da Daddy tabbas kun nuna ƙauna da hallaci agareni Allah ya saka muku da mafificin alheri, Ya Yaseer tabbas ka nuna mun kulawa ka ƙaunace ni ba zan taɓa mantawa da kai a shafin rayuwata ba, Allah ya baka wacce ta fini Ubangiji ya dauwamar da kai cikin farin ciki kamar yadda a kullin kake ƙoƙarin faranta min rai."
Indo na zuwa nan ta goge hawayen Idonta ta miƙe tsaye ta ci gaba da cewa, "Na barku lafiya Allah ya sada fuskokinmu da alheri" ta ƙarasa faɗa tana tunkarar bakin ƙofa, Cikin muryar damuwa Daddy ya ce, "Dakata Humaira! Baza ki bar gidan nan ba ki shiga duniya ba, domin muddin mukayi haka Allah bazai barmu ba. Idan Allah ya kaimu gobe gabaɗayan mu zamu ɗunguma zuwa garin Kura domin nemo inda wannan Baiwar Allah ta koma a garin Kano, na tabbata a faɗin ƙauyen baza'a rasa sanin inda ta koma ba, zamu je gurinta bayan mun sameta akwai hukuncin da ya kamata mu ɗauka" Indo jiki babu ƙwari ta juyo ta ce, "Amma Daddy..." katseta yayi da, "Wuce ki tafi ɗaki banasan musu" Indo labulen ɗakin ta ɗaga ta fice wani irin kuka na taso mata, Lubna tsuke fuska tayi saboda bataji daɗin hukuncin da Daddy ya yanke ba, Daddy ne ya kalli Fahad ya ce, "Allah yayi maka Albarka Fahad Allah ya ƙara haɗa mun kanku" Mommy da Momma jiki ba ƙwari suka amsa da Ameen. Lubna tashi tayi fuuuu ta fice daga ɗakin ta nufin ɗakinsu da niyyar cashewa Indo, tana fita Yaseer yabi bayanta sannan Fahad ya mara masa baya.
KUYI MANEJI SBD RASHIN CAJI
*MASU TAMABAYATA LINK INSHA ALLAH GOBE DA ƘARFE TARA NA DARE ZA'A SAKI NAMU ZUWA TARAN DARE NA RANAR ASABAR, INA FATAN ZAKU BANI HAƊIN KAI TA HANYAR DANGWALA MUN VOTE, A WANNAN NE ZAN GANE ZALLAR SOYAYYAR DA KUKE YI MUN.*
_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
[17/08, 12:57] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀ï¸
*INDO SARƘA*🤸ðŸ¼â€â™€ï¸
*BY*
*AMEERA ADAM*
*FOLLOW ME @WATTPAD*
_*AmeeraAdam60*_
GARGAÆŠI BANYAR WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.
_*WANNAN LITTAFIN GABA ÆŠAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE UðŸ¤*_
_SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._
*Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.*
59&60
Indo tana shiga ɗakin su ta faɗa kan katifa ta rushe da wani irin kuka mai tsuma zuciya, sosai take kuka tun ƙarfinta saboda wani irin zugi da raɗaɗi da zuciyarta take mata, Baba Huwaila ce ta faɗo mata take taji zaman su Yaseer ya fice mata daga ranta, tana nan kwance taji shigowar Lubna amma kasancewar halin da take ciki ya sa bata bi ta kanta ba dukda irin baƙaƙen maganganun da Lubna take gaya mata.
Lubna na cikin magana Yaseer ya shigo cikin ɗakin fuska babu walwala, tana daga kwance ƙamshin turarensa ne ya bugi hancinta wanda yayi dai-dai da bugawar zuciyarta, ƙarasowa yayi daf da ita ya zuba mata manyan idanunsa wanda yayi dai-dai da ɗagowar Indo karaf suka haɗa idanu, da ƙyar ta samu sukunin janye ƙwayar idonta hawaye na ci gaba da gangarowa.
Yaseer kallan tsaf ya yiwa Indo cikin wata irin murya mai ya ce, ''Humaira me yasa kikayi haka? Kinbani mamaki meyasa zaki yi mana ƙarya alhalin mun ɗaukeki zuciya ɗaya tsakaninmu da Allah? Na tsani maƙaryaci bana mu'amala da mayaudari, bantaɓa tsammanin zan samu makamancin wannan daga gareki ba, amma bamu kika yiwa ba kanki kika yiwa" yana gama maganar ya juya ya fita zuciyarsa tana suya. Lubna zuciyarta ƙal saboda farin cikin abin da Yaseer ya yiwa Indo, sai da ta leƙa ta tabbatar da Yaseer ya fita ya ƙaraso gurin Indo ta ce, "To anyi walƙiya mun ganki sai a bi wani sarkin, da ansamu guri har ana shuka iya shege ansamu gidan daɗi har anmurje ancanja kala, dole a koma ƙauye a ci gaba da cin tuwon dawa" Indo ɗagowa tayi kamar zata yiwa Lubna magana, amma sai ta ɗauke kai bata tanka mata ba. Lubna ba haka taso ba sai ta kuma cewa, "Ƴar gudun hijira ashe ƴar kwararo ce yooo ƴar kwararo mana tunda ba'asan asalin mutum ba" Indo ba ƙaramin ciwon maganar Lubna taji ba, ɗagowa tayi ta kalli Lubna murya a shaƙe ta ce, "Lubna kina yawan shiga gona ta karki bari ki take shukokin da suke ciki, a kullin ina ƙara gargaɗarki da ki kiyayeni har yanxu bakisanni ba bakisan wacece ni ba" Lubna shewa tayi harda tafa hannu ta ce, "Yooo dama ta ina zan sanki ƴar kwararo wayasan iskancin da tsohuwarki ta shuka har ta jefar da ke, tunda gudun abin kunya ne yasa ta jefar da ke a titi..."maganarta ce ta maƙale lokacin da Indo ta tsinke ta da wani irin azababben mari, kafin ta ɗago Indo ta ƙara wanke ta da mari. Hannu biyu Indo ta sa ta shaƙe wuyan Lubna ta turata jikin bango tana buga kanta da shi, idanun Lubna ne ya furfuto wani irin tari ya sarƙe ta. Dukda haka Indo bata saurarawa Lubna ba, ƙara tsaurara riƙon wuyan Lubna tayi har numfashinta na ƙoƙarin ɗaukewa. Sai Lubna ta galabaita Indo ta sake ta ji kake yaraf ta faɗi a wahalce tana jan numfashi da ƙyar, Indo tsugunnawa tayi kusa da Lubna da sauri Lubna ta ja baya tana haɗa hannuwanta guri ɗaya alamun roƙo, Indo bata saurare ta ba ta ce, "Tun da kika zo gidan nan ban taɓa shiga harkarki ba saboda nan gidan a Humaira nake, karki bari na zo miki a INDO SARƘA bazaki ji daɗin haɗuwarmu ba." tana gama faɗa ta koma kan katifa ta janyo fulo ta shiga tunanin rayuwa.