← Book details Indo Sarƙa Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 76

Sashe 54

Indo Sarƙa Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fahad wani abu ne ya tsarga masa baisan lokacin da ya shagala da kallonta ba, sai ji yayi ta ce, "Ya Fahad yanzu kuma me ya kawo ka ɗakina? Ko yanzu ma zuwa zakayi ka dake ni" sai ta nutsuwarsa yayi ya ce, "Ki fito akwai mai ruƙƙiya a falo" Indo ɗan tsorota tayi, da sauri ta ce, "Me ya haɗani da me ruƙiyya ko nice na koma maka magen?" maganar Indo taso bashi dariya amma sai ya kanne ya ce, "Ai da zaki koma magen ma da nafi kowa murna, inɗaukeki inkaiki cen waje na yar ko na huta" yana kaiwa nan ya fice daga ɗakin.

Indo kanta tsaye ta fito itama falon, lokacin da ta ƙaraso Falon Malam Khalid na zaune da sallama, ta shigo falon ta nemi kujera ta harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya. Fahad da ya shiga kitchen domin ɗebo ruwa a kofi, yana zuwa falon ya bugawa indo tsawa, "Ke! Baki da hankali ne? Wuce ki sako hijabinki" Indo ta ɗan tsorota da yanayin da ta ga Fahad a ciki, amma sai ta shanye tsoronta ta ce, "Ya Fahad ruƙiyar ce har sai na sa wani hijabi meye haɗin aljanu da hijabi na ko..." tun bata rufe baki ba ya tunkaro gurin da take a hassale ya ce, "Zaki wuce ko sai na karya ki a gurin nan" nan take fuskar Fahad tayi jawur jijiyoyin wuyansa duk sun tashi, Indo shiru tayi gabanta sai faɗuwa yake, wannan karan ba ƙaramin tsoron Fahad taji ba. Ganin bata da niyyar tashi yasa ya ƙarasa gurin ya fisgi hannunta, ya wuce da ita har ɗakinta. Yana shiga ya ce, "Wallahi idan kika kuma fitowa a haka sai na baki mamaki" yana faɗa ya bar gurin ya koma falon.

Bayan Fahad ya koma ya ce, "Malam kayi haƙuri kasan lamarin mata sai a hankali ." Malam Khalid ya ce, "Malam Fahad kasan mata sai da lallami, tunda matarka ce ka dinga janta a jiki bare kaga da ƙuruciya, sai kana kauda kai. Yanzu ka je ka lallasota ku fito tare, kasan ko jinnun jikinta zasu iya sata wasu abubuwan"

Fahad tashi yayi ya wuce ɗakin yana jin zafin Malam dan ya dangantashi da mijin Indo, sai dainta wani fannin tausayinta yaji da ya tuna aljanin da suke jikinta, yana zuwa ya same ta zaune akan katifa ta rafka tagumi kamar wata mutuniyar kirki, cikin sanyin murya yace, "Ki sako hijabinki ki fito Malam yana jiranki" bata ɗago ta kalleshi ba, itama muryarta a sanyaye ta ce, "Ni ka ƙyaleni na fasa zuwa, a ƙyale aljanun su mun duk abinda zasu mun kowa ya huta, tunda dama ba sona ake ba." bakinta yake bi da kallo da yadda take motsa su, lumshe ido yayi ya girgiza kai. Har zai mata faɗa sai kuma ya tuna maganganun Malam, ƙasa-ƙasa ya ce, "To ni da ba mijinta ba? Meye zan wani lallame ta" sai wata zuciyar ta ce masa, "Amma ko ba komai ƴar uwarka ce ta jini" tsugunnawa yayi gabda ita har suna jin numfashin juna ya ce, "Kinsan mutumin nan saboda mu yazo, idan yaga baki fito ba bazai ji daɗi ba. Kuma wa yace miki bama sanki? Da bama sanki zamu nemo miki mai maganin warakar lalurarki?" Indo ware manyan idanunta tayi ta shagala da ƙarewa Fahad kallo, da yadda yake sarrafa laɓɓansa yake mata magana, cikin zuciyarta take ayyana dama Fahad ya iya tausasa murya wajen kalamai? Amma komai yake mata cikin masifa da hantara." ganin ta shagala da kallonsa yasa hannun saitin fuskarta, yana murza ƴan yatsunsa.

Sai a lokacin Indo ta farga wata ƴar kunya ce ta kamata, shi kuwa tsuke fuska yayi kamar zai yi mata magana sai ya tuna, yana mata magana yasan zai iya wargaza komai zata iya ƙin fita. Miƙewa yayi ya ce, "Sauri ki fito yana jiranki" yana fita Indo ta lumshe ido tare da sauke ajiyar zuciya. Nan take ɗaya daga sashen zuciyarta ya ce, "Me yake damunki? kin manta waye Fahad? Kawai dan ya tausasa miki harshe na lokaci ɗaya, har zaki fara tunaninsa." guntun tsaki tayi a filinta ce, "Ko meye abin tunani akan wancen oho, dukda kamar su ɗaya da Yaseer amma Yaseer ya fishi komai" tana gama magan ta ɗau hijabi ta fice.

Tana zuwa ta hau kan kujera ta ƙame guri ɗaya, Malam Khalid alwala ya ƙara ɗaurowa sannan ya zauna ya fara karatun alƙur'ani. Sai da Malam Khalid ya shafe awa ɗaya cif amma ko motsi baiga Indo tayi ba, kallan Fahad yayi ya ce, "Malam Fahad muje inasan magana da kai" Malam na gama maganar ya nufi bakin ƙofar, da sauri Indo ta ce, "Malam angama ruƙiyyar zan iya tafiya?" Malam yace, "Eh! Zaki iya tafiya" Indo kamar dama jira take tun bai rufe baki ba, ta tashi zata wuce sashenta su Momma suka fito. Da mamaki suka bi Indo da kallon ganin tasha zumbulelen hijabi, barka da hutawa tayi musu ta wuce ɗakinta.

Malan ya gaida su Mommy sannan ya koma suka zauna gabaɗaya, ya fara musu bayani akan ruƙiyyar da aka kirashi yayi. Sai dai sam babu wasu ginnu a jikin Indo, mamaki sukayi suka kawo kuɗi suka bashi tare da yi masa godiya, ya yi musu sallama ya tafi. Mommy ce ta kalli Momma ta ce, "Amma lamarin da mamaki fa" Momma ta ce, "Wallahi nikam banyi mamaki ba idan kika tuna da lamarin da su Baba Huwaila suka bamu, wallahi nifa dama jikina bai bani aljanu bane shaƙiyancin yarinyar nan yawa gareshi" Fahad dake gefe ya ce, "Amma wallahi yarinyar nan data gane kurenta" yana gama magana ya nufi ɗakin, Indo ta cire hijabi kenan Fahad ya ja hannunta ko magana babu, bai dire ta a ko'ina ba sai gaban su Mommy. Aunty Safna ce ta rufe da faɗa ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, Mommy ce ta karɓe zancen cikin lallami da nasiha.

Nasiha mai kashe jiki Mommy tayi mata tare da nuna mata illar kwaikwayon abinda takeyi, sosai jikin Indo yayi sanyi nadama ƙarara ta hau kan fuskarta. Su Mommy sun lura da haka ita kanta Aunty Safna ba ƙaramin daɗi taji ba, ganin yanayin da Indo ta shiga na nutsuwa. Fahad kallan Indo yayi ya ce, "Allah sa dai ta ɗauki faɗan da akayi mata, dan Allah Aunty ji yadda take sunne kai kamar ta kirki" Aunty Safna ta ce, "Kaima dai ka faɗa Fahad, wai a haka Yaseer yake so da wannan sakarcin nata" Indo zumɓurar baki tayi gaba ta ce, "Dan Allah Ammi ku daina faɗa a gaban Ya Fahad karya rainani" Indo ba ƙaramin dariya ta bawa su Mommy ba, Aunty Safna ta ce, "Wane raini kuma bayan shi ya fara saninki a lokacin da kike ƴar ƙauyenki, ba yanzu da kike waye ba. Ai wallahi kome kika zama yanzu Ɗana Fahad ne sila" Fahad kansa murmushi yayi, ko ba komai ya samu abin gori nan gaba, Indo kamar zatayi sabida takaici. Mommy ta ce, "Rabu da su Humaira, kice asalin kowa ma ai ƙauye. Kuma cen ɗinma ai a gida kike tunda kin rayu da Kawunki Maigari" Indo kamar wata yarinya ta yiwa Fahad gwalo, sannan ta ce, "Yauwa Mommy naji kince Maigari ɗan uwanku ne, amma banji kun gaya mun alaƙarku da shi ba rannan" Mommy ta ce, "Mahaifinsa da Mahaifin abokan wasa suke, lokacin da Mahaifinmu zaizo garin saida ya yiwa mahaifin Maigari tayin zuwa amma yaƙi, sai wani zuwa da Mahaifinmu yayi suka taho tare, har dai Allah ya sa shima yayi tunanin dawo da iyalinsa garin nan. Amma shi Mahaifinsa sai ya fara safarar kaya yana kaiwa garin Kura, har aminci ya haɗasu da Maigarin wancen lokacin. Humaira labarin yana da tsayi a takaice dai Maihafin Maigari ya zamu zama a wancen garin kuma mutum ne me amana, da tsoron shiga haƙƙin wani. Lokacin da Maigarin wancen garin ya fara wata jinya, sai yayi sanarwa tare da saka sojojin masarauta, ya sa hannu akan ko da bayan ransa Mahaifin Maigari, shi zai cigaba da mulkarsu saboda tausayinsa da amanarsa. To kinji yadda akayi, banda ma zumuncin yanzu ya zama yadda ya zama, dama duk cikin ƴan uwana ba yabon kai ba nafi su ƙoƙarin zumunci, kuma da har zuwa Kura muke muna zuwa mu shafe watanni a cen. Ni da kike gani a cikin garin da kikayi rayuwa babu inda bansani ba, idan na fara baki labari sai mu kwana anan." Indo ajiyar zuciya ta sauke ta ce, "Taɓ amma wallahi Maigari nasha da ƴan ƙauyen nan sam be ɗauko halin mahaifinsa ba, zalinci a cikin mutumin nan kamar..." da sauri Mommy ta ce, "Gidanku Humaira" Fahad yayi karaf ya ce, "Ku barta ta faɗa dan ni kaina wani zuwa da mukayi inaji wasu mutane na zaginsa, wai ya cinye wata gonar gadonsu" Aunty Safna ta ce, "Ƙaniyarka ana kwaɓar ƙanwarka kana kuma sakin bakinka" Fahad dariya yayi ya tashi zai shiga ɗakin, Indo ta ce." Ai wallahi nina saita shi sai da ya mayar musu da dik gonakinsu" da mamaki ta fara suka kalleta, gyaɗa kai Indo tayi basu labari tun daga lokacin da aka damƙawa Maigari takardunta, da ɓadda kamar da sukeyi ita ƙawayenta. Hatta ludayin da suka dinga ranƙwalawa Maigari sai da ta faɗa da umarnin da suka bashi akan ya mayar wa da mutane dukiyarsu.

Fahad duk gimtsewar da yakeyi sai da ya dinga ƙyalƙala dariya, su Mommy dariya suke harda hawaye sai da suka tsaida, Mommy ta ce, "Dama Humaira ke kika rikitamu ɗan uwa lokacin da muka je" Indo dariya tayi ta ce, "Mommy nima ai Ya Fahad tasoni yayi saura kaɗan asiri na ya tonu, wallahi da ya kamani da na kaɗe dan ƴan garin nan sai mun tofin Allah tsine" Fahad me zaiyi banda dariya, Aunty Safna ta ce, "Ikon Allah wato mu duk shakiyancin ƙuruciya da mukayi muna yara, bamu kama ko rabinki ba Humaira. Allah ya ƙara shirya mana ku gabaɗaya." gabaɗaya suka amsa da Ameen, suna nan zaune Daddy mahaifin su Fahad ya shigo hannuwansa riƙe da su Aseem, zama sukayi suka cigaba da hira cikin barkwanci.
Chapter 54 · 0% Book details