← Book details Indo Sarƙa Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 76

Sashe 13

Indo Sarƙa Complete Hausa Novel · about 8 min read

A zabure ta miƙe tana sosa kai harara ta watsawa Jamilu tana murguɗa baki ta ce, " Wallahi ka daina cin zalina idan ba haka ko..."

Jamilu ya katse ta, " Idan ba haka ba me? Ramawa zakiyi? " ƙeya ta juya masa tana ɗan girgiza jiki kamar me jiran kaɗan ta fara dambe, Jamilu kallan Indo kawai yayi takaicin ta ne ya kamashi, juyawa yayi ya wuce ciki ya na faɗin, " Zaki shigo gida zaki mun bayani "

Indo ta ce, " Idan na shigo karka barni da rai "

Zulai ce ta cewa Indo, " Sarƙa dan Allah ki daina yiwa Jamilu wannan abun, duk garin nan anshaida baida abokin faɗa, ni wallahi har cikin zuciyata nake jin ƙaunarsa dama yace yana sona "

Da sauri Indo ta juyo tana kallan Zulai cikin mamaki tafara tafa hannuwa tana salati, Zulai waigawa tayi tana duba hanya taga babu mai ganinsu, ƙasa tayi da murya ta ce, " Ke Sarƙa meye dan nace inasan Jamilu "

Da sauri Indo ta fisge hannunta da Zulai ta dafa ta cikin zallar tsoro Indo ta ce. " Zulai ashe kin koma ƴar iska ban sani ba? Wallahi mun raba hanya babu ni babu ke tun kafin Goggo ta rasu ta ce mun duk wanda yace yana sona ɗan iska ne ashe kema kina cikinsu? Kuma wallahi ina shiga zan gayawa Baba Huwaila kuma ko ƙofar gidan nan karki ƙara zuwa " cikin zulai ne ya ɗuru ruwa tsoro da fargaba suka kamata sai yanzu take ganin abinda ta faɗa ba dai-dai bane, ita ta ɗauka ba laifi bane dan kace kanasan mutum saboda taji Yasiran gidansu ta ce tanasan Muɗɗafa, cikin tsoro ta janyo Indo tace.

" Dan ALLAH Sarƙa kiyi haƙuri ni bada wata manufa na faɗi haka ba, naji rannan Yasiran gidanmu tace tanasan Muɗɗafa shima ya ce yana santa kuma Innarmu bata mata faɗa ba " Sototo Indo tayi har Zulai ta gama magana sannan ta ce, " Wato agun Yasira kika koyi iskanci ko to wallahi ni babu ruwana, mu gidanmu ba ƴan iska bane daga yau babu ni babu ke " Indo na gama magana ta tura ƙauren gidansu ta shige ta bar su Zulai a tsaye.

Zulai duk ta firgice da ka kalleta zaka gane tana cikin tashin hankali, kallan Saude tayi ta ce.

" Saude wallahi bansan meyasa na faɗawa Indo inasan Jamilu ba " Saude jiki a sanyaye tace, " Zulai kema me ya kaiki ni kaina Innarmu ta ce duk wanda yace yana sona ɗan iska ne amma wai yau da bakinki kike faɗa " Zulai ƙasa tayi da murya ta ce, " To amma bazaki gayawa kowa ba ko? "

Saude shiru tayi kamar mai nazari sannan ta ce, " Amma wallahi kika ƙara ko nima na daina hurɗa da ke " daga haka rankayawa sukayi suka wuce gida Zulai kamar wata mara lafiya.

Fahad na zuwa gidan Mai gari Fuska ba walwala ya kalli Mommy ya ce, " Mommy ya kamata muzo mu wuce saboda yanzu aka kirani a waya ina da wani uzuri " Mommy kamar taso ta fahimci Fahad amma sai tai tunanin Fahad bai saba ƙarya ba hasalima baya shiri da maƙaryaci, murmushi tayi ta ce, " Ɗan gidan Mommy ko gajiya kayi da garin namu? "

Girgiza kai yayi ya ce, " A'a kawai dai ina da wani uzuri ne "

Mommy ta ce, " To shikenan bari muzo mu fara shiri amma mu da gida sai dare " Shiru yayi saboda yasan Mommy ta faÉ—a ne dan bataso tafiyar yau ba.

Mai gari taje ta samu ta sanar dashi ta É—ebo kudi masu É—an dama ta bashi, haka matansa ma tayi musu alheri sannan suka fara shirin tafiya.

Lokacin da Indo ta ƙarasa cikin gida kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki, jiki ba ƙwari taje ta zauna ta zuba uban tagumi, Baba Huwaila ce ta fito daga ɗaki ta ƙarewa Indo kallo ta ce.

" Indo lafiya naga kin zuba uban tagumi ko wani abun kika aikata kafin ki shigo gidan? " A sanyaye Indo ta É—ago ta ce, " Baba Huwaila kafin Goggo ta rasu ta ce mun duk wanda yace yana sona É—an iska ne? " Baba Huwaila ta ce.

" Eh, waye yace yana sanki? "

Indo sai da ta leƙa ɗakin Jamilu ta hango labulensa a sauke yake sannan ta ce, " Wallahi Zulai ce tace tanasan Jamilu nikuwa nayi mata tas dan nace ko gidanmu karta ƙara zuwa " Baba Huwaila zama tayi kusa da Indo zata fara magana Jamilu ya fito daga ɗaki.

" Tana ganinsa ta ɗauke kai gefe takowa ya farayi cikin zuciyarta tace, " Jibeshi wani soɓoɓo mugu azzalumi " Jamilu takowa yayi yazo har kusa da Indo ya zauna juyo da ita yayi, yasa hannunsa ya haɗa hannuwanta biyu ya riƙe cikin shammata ya zuba mata rankwashi, so take ta fisge hannunta ta kasa ga azabar rankwashi.

Tamke fuska yayi sosai ya kalleta ya ce, " Indo rainin da kuka min keda sauran shaiɗanun ƙawayenki har ya kai haka? " Baba Huwaila da sauri ta fisge hannun Indo ta rufe Jamilu da faɗa.

" Meye laifinta aciki ita tace tana sanka ko ƙawarta? Saboda zalinci ko Jamilu? Wallahi ka fita harkar yarinyar nan idan ba haka ba ranka zaiyi mummuna ɓaci, da ka samu akace ana sanka ma har wani kyau gareka da zaka tsaya zaɓen budurwa, Ina laifin Zulai yarinyar arziƙi "

Haushi ne ya kama Jamilu ya ce, " Ai duk tsiyar da Indo take shukawa ku kuke ɗaure mata, ni me zanyi da ƙawayen Indo? Inrasa wacce zanyi soyayya da ita sai ƙawayen Indo tir Allah ya tsareni " yana gama faɗa ya tashi ya fice daga gidan.

Cikin faɗa Baba Huwaila ta ce, " Ka zauna ruwan ido har ka rasa wacce zatayi da ka sakaran banza sakaran wofi meye aibunsu " juyowa tayi ta kalli Indo ta ce, " Goge hawayenki kinji Indo na, ita kuma Zulai karki daina kulata ai ba kowa ne idan yace yana sanka ya zama ɗan iska ba, idan mutum yace zai taɓa ka shine ɗan iska " Sai a lokacin Indo ta fahimci abinda Baba Huwaila ta sanar da ita.

*INA KUKE MASOYA LITTAFIN WANDA BAIJI BARI BA BOOK2 YA KAMMALA, KAMAR YANDA NA GAYA MUKU BOOK1FREE NE, DA NAIRA 100 ZAKI KARANTA BOOK2 ÆŠINKI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKI BIYA NAIRA 100 DA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 0706 206 2624*

_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉

[26/06, 19:42] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

*INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️
*BY*
*AMEERA ADAM*

*FOLLOW ME @WATTPAD*
_*AmeeraAdam60*_

GARGAÆŠI BANYAR WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.

_*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_

31&32

Goge hawayen idanunta tayi ta miƙe ta shiga ɗakin Baba Huwaila, kan gado ta faɗa tayi rufda ciki tana nazarin irin abinda zata shukawa Fahad dan ta fanshe abinda yayi mata, kamar wacce aka tsikara haka ta miƙe da sauri ta fito ta shuri takalmanta ta fice, Baba Huwaila kallanta tayi tana girgiza kai a fili ta furta, " Oh nidai na godewa Allah, Allah ka shiryamun Indo ko yaushe yarinyar nan zatayi hankali? Yarinya harta fara ƙirgen dangi amma babu saurayin kirki da ta taɓa tsaida ta "

Jamilu da ya shigo gidan ya riski maganar Baba Huwaila ya ce, " Yaushe zatayi hankali bayan ku kuke ƙara sangarta yarinya, idan kuka cigaba da tafiya a haka to wallahi sai an aurar da ƴan matan garin nan gaba ɗaya idan tayi kwantai ma nemi wani tsohon mu bashi,Tsohon ya raka da ita " a hassale Baba Huwaila ta ce.

" Bakinka ya faɗa kanka sakarai, kai Jamilu ka fita harkar yarinyar nan to bari kaji Indo ko mai mata bazan bawa ba bare kuma tsoho cen sai dai idan kai zaka auri tsohuwa kai da kullin cikin ruwan ido kake " Jamilu bai tankawa Baba Huwaila ba ya shiga ɗaki ya ɗauko jakarsa har yazo tsakiyar gida ya ce, " Baba Huwaila zan wuce na canjowa Indo Uniform dan na gaji da ganinta da wannan tsangalallen wandon kamar mai shirin tsallaka ruwa, kuma wallahi wannan karan bazan laminci rashin zuwa makarantar da batayi ba, ace yarinya a sati baifi ta je makaranta sau ɗaya ko biyu ba kuma ana kallanta, shiyasa gata nan da kwakwalwa kamar ta kifi babu tsiyar da take tsinanawa a makarantar " Indo dake ɗakin tayi farat ta fito tana riƙe da ƙugu ta ce, " Wallahi badai ni ce mai kwakwalar kifi ba kuma daga yau wallahi na daina zuwa makarantar tunda ba ta Allah da Annabi bace " ta ƙarasa maganar tana murguɗa baki, da sauri Jamilu ya zabura zai juya gurinsa Baba Huwaila ta dakatar da shi, cikin jin haushi ya ce.

" Wallahi karki bari na kamaki kuma makaranta babu fashi mu zuba nida ke mu gani " yana gama faÉ—a bai jira cewarsu ba ya fice.

Baba Huwaila ƙarasawa tayi gurin Indo ta ce, " Indo ina rabaki da rashin kunya Jamilu fa kamar yaya yake a gurinki, kinga dan ina hanashi ne amma wata rana ya kamaki bana kusa wallahi zai miki dukan tsiya " Zumɓurar baki Indo tayi ta ce, " To bakiji me yace ba, wai nice mai Kwakwalar kifi "

Baba Huwaila ta dafa Indo ta ce, " Kyaleshi ya faÉ—a ne kawai amma ba wata kwakwalwar kifi da kike da ita, Keda zaki hadda ce mana izifi sittin " Murmushin jindaÉ—i Indo tayi ta faÉ—a É—aki ta koma kan katifa, har zuwa wannan lokacin nazarin abinda zata shukawa Fahad takeyi.

Indo bata jima a kwance ba tayi wani nazari lokaci guda ta bushe da wata irin dariya, tun tanayi a hankali har ta fara kyakyatawa harda riƙe ciki, Baba Huwaila ɗagowa tayi tana kallan Indo da mamaki sannan ta ce, " Indo karfa harsashen mutane ya tabbata akanki da suke miki take da ƴar uwar Aljanu, banda haka ke kaɗai ki dinga ɓaɓɓaka dariya sai kace mai hauka sabon kamu? " Indo kuma tuntsirewa tayi da dariya ta kalli Baba Huwaila ta ce.
Chapter 13 · 0% Book details