← Book details Indo Sarƙa Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 76

Sashe 25

Indo Sarƙa Complete Hausa Novel · about 8 min read

Honourable banda tamola da soshe-soshe babu abinda yakeyi,yanasan yayi ihu domin neman agaji yana tsoron abinda zai janyo hankulan mutane har su fahimci abinda yake faruwa,sanin shi waye da matsayinsa yasa ya ja bakinsa ya rufe banda roƙo da hannu babu abinda yakeyi,domin yasan muddin yayi ihu har aka kawo masa ɗauki ko yaƙi ko ya so sai labarinsa ya fita duniya musamman da ɗaukan abu da yaɗashi a waya bashi da wuya,yana tsaka da wannan tunanin yaji Indo ta ɗaure masa ƙeya da wayar Tv, wata uwar ƙara ya saki yana dafe ƙeya haɗe da hawayen wahala,cikin tashin hankali ya fara buga ƙasa da tafin hannunsa yana cewa, " Dan Allah Humaira kiyi haƙuri kimun rai karki illatani wallahi komai kike buƙata zan yi miki shi " Indo juya idanunta tayi ta kuma kallan gefe da gefe sannan ta kalli Honourable ta ce, " Bazamu barka araye ba sai mun farke hanjin cikinka mun cinye saboda ka taɓo ƴar sarkin Aljanun farisa,hukuncinka mai tsanani ne " Kamar ƙaramin yaro Honourable hawaye ne yake bin fuskarsa cikin tashin hankali yace, " zan iya mallakar da dukiyata akan rayuwata amma dan Allah kumun afuwa wallahi sharrin sheɗan ne kuma ba halina bane..." da sauri Indo tayi sufa ta faɗa kan katifa tana cizgarta, Honourable cikin zuciyarsa yace, " Yarinyar nan ashe annoba ce na ɗaukowa kaina bansani ba amma..." yana tsaka da tunani Ya ga Indo ta ɗaga katifar gadon ta jingineta, da gudu ta nufi wajen ƙofa tana wani irin jijjiga kai sannan ta fara cewa, " Zamu buɗe ƙofa mu gayyato sauran dakarun Aljanun domin mu sanmusu hanjin cikinka " Indo ta ƙarasa maganar tana ƙoƙarin buɗe ƙofar, da sauri Honourable ya rarrafo lokacin jikinsa duk yayi tsami ga shatin bulala ruɗu-ruɗu ajikinsa, cikin magiya ya fara roƙon Indo, " Ku yiwa Allah da Annabi kuyi haƙuri dan Allah karku tonamun asiri wallahi ni babban mutum ne a ƙasar nan,muddin labarin nan ya fita kashina ya bushe " Indo wani irin layi tayi irin na ƴan shaye-shaye kamar zata faɗi cikin shammata ta kaiwa Honourable duka da ƙafa a ƙirji,ji kake ƙwal ƙeyarsa ta bugu da center table.Wani irin yuuuu yaji kansa ga wani irin zugi da yake ji dama gurin da ta buga masa plate har ya fara tashi,cen ya faɗa gefe yayi ɗai-ɗai yana sauke ajiyar zuciya,Honourable gabaɗaya ya gama laushi magana yake amma da kyar ake iya jin abinda yake faɗa, wani kukan kura Indo tayi sa gudu ta ɗauko jakar kayanta ta fara kai duka ta ko'ina, tana ƙarasawa gurin Honourable ta dinga jibga masa iya ƙarfinta tun yana iya magana har ta kai saidai ya dinga girgiza kai daga kwance,miƙewa tayi ta ƙara ƙwallah ƙara sannan ta faɗi a cen gefe tunda ta faɗi bata ƙara motsi ba,Honourable a hankali ya juya kansa gefe ya hangota gefe warwas jiki ba ƙwari ya yunƙura ya ja jiki jikin bango yana maida numfashi.

Bayan wasu mintuna Indo ce ta yunƙura a hankali ta tashi zaune cen gefe ta hango Honourable har lokacin yana jikin bango,kallan ɗakin ta farayi da mamaki take bin ko'ina da kallo miƙewa tayi tsaye da sauri Honourable ya ja baya,a ɗan tsorace Indo ta kalleshi ta ce, " Honey lafiya me ya faru ne? " Honourable girgiza kai yayi gabaɗaya ya jeme idanunsa sunyi zuru-zuru murya ƙasa-ƙasa ya ce, " Ba komai Humaira " Indo ƙara kallan gurin tayi sannan ta ce, " Amma ai naga gurin kafin nayi bacci ba haka bane nidai tsoro nake ji dan Allah mu bar gurin nan ka azo acutar damu, naga duk anfarfasa abubuwa " Da sauri Honourable ya ce, " Yanzun nan kuwa yanzu zamu tafi kwaso kayanki " Indo zuciyarta fes ta juya ta fara neman ɗankwalinta da mayafinta, jakarta ta ɗauko ta ajiye ta ce, " Ka tashi mu tafi dan Allah Honey muje gidan rediyon ka kai cigiyar " Honourable bai ce uffan ba ya yunƙura jiki ba ƙwari babbar rigarsa kawai ya ɗauka ya zura ya nufi hanyar fita, har ya ja ƙofa ya tuna bai saka sauran kayansa ba, agurguje yasa kayansa ko saka babbar rigar baiyi ba ya waurgar da ita gefe, ko hularsa bai ɗauka ba wayarsa ya ɗauka ya wuce fuskarsa murtuk ba fara'a suka fice,Indo cikin zuciyarta banda dariya babu abinda takeyi.Key ɗin ɗakinsu Honourable ya bawa ma'aikata yace musu zaije ya dawo,lokacin da suka fito tuni anyi sallar Isha'i motarsa ya ɗauka ya fara shawagi dasu a titi shi tunaninsa ɗaya inda zai kai Indo,gashi bayasan Matarsa tasan yana cikin garin Abuja,gabaɗaya tsoron Indo yake ko motsi yaga tayi zai zabura yaja gefe,wata dabara ce ta faɗo masa kallan Indo yayi ya ce, " Humaira muje gurun cin abinci daga nan sai muje gidan Rediyon " Ita ɗinma yunwa take ji da sauri ta amsa masa " kai tsaye wani resturant suka wuce, shigarsu ba wuya aka kawo musu list Honourable ne ya zaɓar musu ba jimawa aka cika musu gabansu da Abinci, sun fara ci ba jimawa Honourable ya fara wayar bogi tashi tsaye yayi ya cewa Indo, " Humaira ina zuwa zan amsa waya " Indo ko ajikinta ta gyaɗa masa kai, Honourable na fita da sauri ta shiga motarsa ya bata wuta da gudun gaske ya bar gurin.

Indo gama cin abinci tayi tana ta jiran Honourable ya dawo amma shiru,tun tana jiransa harta fara gajiya kwashe kwanunka gabanta ma'akanta sukayi hamma take ta zabgawa tana leƙensa,mutanen da suke gurin duk sun watse wasu ma sunzo sun tafi, gajiya tayi da zama ta tashi zata fita da sauri ɗaya daga cikin ma'aikatan yayiwa Indo magana, " Hajiya zaki tafi baki sallamemu ba " da mamaki Indo ta ce, " Bangane ban sallameku ba? " Murmushi yayi ya ce, " Ina nufin baki bada kuɗin abinci ba " Indo gyara tsayuwa tayi ta ce, " Tare nake da Honey shi zai biya ya fita yin waya waje bari na duba shi " kusan tare suka fita dashi Indo na fita ta nemi motar Honourable sama ko ƙasa, wani mutum ta gani jikin motarsa da alama zuwansa kenan bai daɗe da zuwa ba, da saurinta ƙarasa gurinsa ta ce, " Dan Allah Malam baka ga motar Honey ba ɗazu ya fito waje ya ce mun zai amsa waya " Indo na rufe baki taga anturo ɗayan murfin ƙofar cikin masifa wata kyakykyawar mata ta fara magana, " Malama lafiya me ya kawoki gurun mijina, ƴan iska kawai da kunga maza kun dinga kwarkwasa kenan, zaki matsa daga gurin nan ko sai na ci mutumcinki " Cikin tsiya Indo tace, " Allah ya kiyaye me zanyi da wannan buhun alabon ko maza sun ƙare wallahi bazan aureshi ba " tana gama faɗa ta matsa cen gefe tana dube-dube aikuwa matar ta cigaba da bambamin faɗa sai da mijinta ya rarrasheta, kallanta yaron Mai resturent ɗin yayi yace, " Hajiya mufa ba wani Honey ke muka sani Honey ya gudu ya barki cen ku kuka sani, mudai kuɗinmu zaki bamu " ya ƙarasa magana yana matsawa kusa da Indo, Idanunta ne suka ciko da ƙwallah sannan ta ce, " Wallahi Malam ni baƙuwa ce daga Kura nake kuma bansan kowa agarin nan ba Honey ne ya taho dani " Kallan sheƙeƙe yayi mata yace, " Lallai ashe kema ƴar hannu ce muje kiyiwa Hajiya Bayani " yana gama magana auja juya cikin resturent ɗin daga wani ɓangare, matar na zaune a hakimce kan kujera ɗan risinawa yayi yai mata bayanin Indo tun daga farko har ƙarshe, kallan tsaf tayiwa Indo sannan ta ce, " Lallai yarinya kin rainawa kanki Hankali wallahi ba Honey ba ko Uban Honey ne ya kawoki Abuja sai kin biyani kuɗi na " kallan sa tayi ta ce, "Abinci nawa aka haɗa musu? " Cikin girmamawa yace, " Abinci dubu Huɗu da ɗari biyar ne "

_INDO FANS HOW MARKET🤣🤣🤣_

_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
[19/07, 08:53] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

*INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️
*BY*
*AMEERA ADAM*

*FOLLOW ME @WATTPAD*
_*AmeeraAdam60*_

GARGAÆŠI BANYAR WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.

_*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_

_SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._

*Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.*

*ASSALAMU ALAIKUM BARKANKU DA WANNAN LOKACIN DA FATAN KOWA YANA LAFIYA,INA MUKU FATAN ALHERI MASOYA ALLAH YA BAR ƘAUNA,JIYA NA MANTA BAN SANAR DA NA TAFI HUTUN SALLAH BA AMUN AFUWA,KAR AMANTA DA KABARBARI DA ADDU'O'I ALLAH YA DATAR DAMU AMEEN.*

*ZAN CIGABA DA SANADIN RAGON LAYYA INSHA ALLAH,MASU WATTPAD SU DUBA TA CEN XASU SAMESHI COMPLETE,LITTAFIN BA SABO BANE TUN LAST YEAR NA RUBUTA SHI KAWAI NA DAWO DASHI NE YANZU.*

INA MUKU FATAN ALHERI DA FATAN ZA'AYI SALLAH LAFIYA😉

_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
[29/07, 18:21] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

*INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️
*BY*
*AMEERA ADAM*

*FOLLOW ME @WATTPAD*
_*AmeeraAdam60*_

GARGAÆŠI BANYAR WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.

_*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_

_SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._

*Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.*

49&50
Chapter 25 · 0% Book details