← Book details Indo Sarƙa Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 76

Sashe 41

Indo Sarƙa Complete Hausa Novel · about 7 min read

*Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.*

71&72

Lokacin da Alhaji Khaleel yazo nan a zancen sa, a firgice mutanen falon suka ɗago suna kallonsa. Momma, Mommy, Daddy da Aunty Safna ne basu wani nuna alamun firgici ba, amma kana kallan fuskar Mommyn Yara, zaka fahimci launin fuskarta ya sauya cikin damuwa. A tsorace Fahad ya ce, "Dan Allah Uncle karka kace mini Mommy ce ta aikata wani mummunan abu akan jaririyarku, domin nasan bazata taɓa aikatawa ba." Alhaji Khaleel ya ce, "Fahad kenan! ai duk gaggawar Unguwar zoma ta jira haihuwa. Ka jira ci gaban labarin mana, nasan kowanne ɗan Adam yana matuƙar ƙaunar mahaifiyarsa dan haka sam banga laifinka ba Son. Amma ka sani nina san wace Mommynku ko kwatankwacin haka bazata iya aiwatarwa ba." Wata nannauyar ajiyar zuciya Fahad ya sauke yana lumshe ido, Indo dake gefe cikin tausayin iyayenta ta ce, "Dan Allah Abba wace ta aikata muku haka, Allah idan na gano ta zata gane zakaran da Allah ya nufa ko ana muzuru ana shaho sai ya yi. Kuma sai na koma mata Sarƙa, tunda yanxu na koma Aishatul humaira." Yaseer kafe ɗan bakinta ya yi da kallo yana murmushi haɗe da mamaki, saboda gabaɗaya sanin da ya yi mata bata da hayaniya. Jamilu shima murmushi ya yi da ya tuna wace Sarƙa da shuka tsiya da take yi a baya sannan ya ce, "Ayusher zan tayaki da bada shawara kawai kiyi mata fatalwar me..." tun kafin Jamilu ya ƙarasa faɗa, Indo da sauri ta miƙe tsaye tana sa hannunta a baki alamun yayi shiru, murmushi ya yi sannan ya ce, "Sai kin bani cin hanci amma" ɗaga idanunta sama tayi alamar tunani da sauri ta ce, "Ka tuna dukan da ka mun akan gonar Ɗan Iya?" Jamilu jim ya yi yana nazari saboda ya daki Indo ba adadi, zuwa cen ya ce, "Eh na tuna, wacce kukai masa ɓarna ko?" Yaseer tsuke fuska yana tsaki ƙasa-ƙasa.

Indo ta ce, "Yauwa to dama naci alwashin wannan dukan, da akwai abin da niyyar zanyi maka amma yanzu kawai ka fanshi kanka, nima kayi shiru basai ka faɗa sun ji ba" murmushi Maigari yayi ya ce, "Kai jama'a Sarƙa kin daɗe kina shuka tsiya wai Jamilun ma bakya raga masa? Lallai Baba Huwaila kunyi ƙoƙari" Ɗan shiru ne ya biyo baya sannan Alhaji Khaleel ya ci gaba da cewa.

"Ganin za'a ɓata lokaci yasa Momman Yara ta fice da yarinya, a lokacin muna gate cikin tashin hankali, bamuyi wata-wata ba muka wuce asibiti. Muna zuwa aka karɓeta aka shiba bata kulawa, kwanan mu ɗaya a asibiti aka sallamemu muka koma gida. Mommyn yara ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba, najin labarin ɗankwalinta aka gani naɗe a wuyan Aisha. Banda kuka babu abinda takeyi, Ƴan uwana ne suka zauna muka tattauna sukayi mana nasiha akan kada mu zargi Mommyn yara ko kaɗan, tunda a lokacin da abin ya faru ma ta tafi rakiyar wasu ƙawayenta da sukayi kara suka xo suna. Kuma har yau har kwanan gobe Allah shi ya barwa kansa sanin wanda ya aikata wannan abun. Abin da muka ɗauka kawai duk wanda yake mana wannan abun ba ƙaramin maƙiyinmu bane, kuma Allah shi zai mana sakayya. Haka muka ci gaba da al'amuranmu yarinyar mu na ƙara wayo, gwanin ban sha'awa gata da farin jini duk inda muka je da ita mutane na sha'awar ɗaukanta. Alokacin da ta cika wata biyu cif, idan ka ganta zaka rantse tayi wajen wata huɗu. mun ɗauki soyayyar duniya mun ɗora akan ƴar mu Aisha. Ƙwatsan wata rana da daddare muna tsaka da bacci mukaji harbe-harbe, daga baya sai Ihun maigadin gidanmu muka fara ji. Ta window muka leƙa muka hango mutum biyu sun saka shi a tsakiya ga jini na zuba a gefen kafaɗarsa, muna nan tsaye muka ji anfara buga ƙofar falonmu, bugun ƙofar ne ya tashi Aisha ta fara kuka. A firgice na fara neman wayata domin kiran ƴan sanda, amma akayi rashin dace na barta a falo jikin caji. Ɗaya daga cikinsu ne naji ya ce, "Kai Babba idan bazasu buɗe ba mu doke ƙofar Ƴarinyar kawai akace mu karɓo idan kuma sukayi gardama duk mu kashe su" muna jin haka gabaɗaya tsoro ya kama mu bamuyi aune ba, mukaji sun karya ƙofar falon haɗe sakin harbi. Kallan Safna nayi na ce mata, "Kishiga cikin ɗakin cen zan tsaya akan koda sun shigo ɗakin nan bazasu sameki ba, zan roƙesu alfarma ko kuɗi ne na basu su tafi." cikin firgice ta miƙomin waya tana faɗin, "Bazamuyi haka ba ga wata maza ka kira ƴan sanda" karɓar wayar nayi sai dai kash ba lambar DPO a wayarta, wata dabara ce ta faɗo min na kira wayar Yaya Haruna, sai a kira na uku ya ɗauka na sanar masa. Da hanzari ya kira lambar DPO ya sanar masa halin da mike ciki da adireshin gidanmu, kuma akan dole badan Safna ta so ba na turasu cikin ɗaki ina me gargaɗinta da duk rintsi karta sake ta buɗe ƙofar ta fito, tunda tsakaninmu da ofishin ƴan sandan ba nisa cen sosai, nasan kafin su shiga gurinsu Safna folisawan sun ƙaraso. Safna na kuka haka na rufosu na dawo dakin na tsaya ina jiran ikon Allah. Aikuwa ina nan tsaye har suka samu nasarar karya itama wannan ƙofar suka shigo su wajen biyar, fuskokinsu duk a rufe. Suna shigowa na ce musu, "Dan Allah ku tsaya muyi magana da ku, duk iya kuɗin da kuke buƙata zan baku amma karku ɗaukar mun ƴata" Babban cikin su ne yayi wata dariya sannan ya ce, "Ka ɗauka bamusan kana da kuɗi ba? Munsan kana da amma ƙwandalarka baza mu ɗauka ba, ƴarka ita aka turo mu mu ɗauka idan kuma kuka yi mana gardama zamu kasheku gabaɗaya." shiru nayi ban tanka musu ba wani daga cikin su ya ce, "A ina ka ɓoye uwar da ƴar?"

A wannan karanma shiru nayi ban tanka musu ba, banyi aune ba sai ji nayi sun sakar min bindiga a ƙafata, cikin azaba na kurma ƙara ina ambaton sunan Allah, daga cikin ɗakin naji Safna ta kurma ihu tana ambatar sunan, cikin azaba nake ƙara gargaɗinta da karta sake ta fito. Suna jin gargaɗina suna ƙara sakarmin harsashi a gefen kafaɗa ta, cikin tsananin jin zafi na ƙara kurma ihu. Anyi haka babu jimawa sai ga Safna ta fito, hannunta ɗauke da Aisha tana kuka ta miƙa musu ita tana faɗin, "Inda ƴa ce ga ta amma dan Allah karku kashe mini mijina, ina matuƙar ƙaunarsa." Ɗaya daga cikinsu ne ya ƙarɓe yana murmushi ya ce, "Shikenan fa abin da zakuyi ka tsaya yi mana gardama" Ɗago da kaina nayi na ce mata, "Safna me yasa kika yi haka?" Kafin ta bani amsa Ɗaya daga cikin su ne ya shafo wuyanta yana lashe baki ya ce, "Gaskiya wannan hajar tayi ku wurga min ita ɗakin da ta fito"

zan dinga typing ko ba yawa ne sbd bana samun tym idan nace sai da yawa zan jima banyi ba.

Kuyi hkr da rashin replay kwana biyu network ke rikeni dan posting É—in jiya ma da kyar ya tafi.

Mommy, mmn naseer, mmn rauda kuna da yawa wallahi naga comments É—inku na muku replay yaki tafi ina muku fatan alheri.

Wattpad ina gdy kulawa🥰

_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
[13/09, 19:27] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp

*INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️
*BY*
*AMEERA ADAM*

*FOLLOW ME @WATTPAD*
_*AmeeraAdam60*_

GARGAÆŠI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.

_*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_

_SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._

*Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.*

73&74
Chapter 41 · 0% Book details