← Book details Indo Sarƙa Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 76

Sashe 55

Indo Sarƙa Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alhaji Mahmud Lamiɗo shine ainihin sunan Mahaifin su Fahad, asalinsa Fulanin daura ne. Sai dai kakanni da iyayensa a buɗi ido ya gansu a cikin garin Kano, Iyayensa sun rasu bayan haihuwar su Fahad babu jimawa, Su uku ne rak a gurin iyayensa. Shine babba sai ƙannensa mata biyu, Alhaji Mahmud ɗan kasuwa ne saboda baiyi wani zurfi a karatun boko sosai ba, Allah ya bunƙasa kasuwancinsa har ƙasashen waje yana fita sarin kaya. Mutum ne mai matumci da karamci gashi da zumunci da taimakon marasa ƙarfi, uwa uba gashi da alheri da sakin fuska.

MU KOMA LABARI

Kwanan su Indo biyu suka wuce garin Kaduna, wannan karan ma ba tare da Fahad suka wuce ba, saboda wani uzuri da zai gabatar kafin komawarsa. Indo ji tayi kamar ta je ta ajiye masa takardar da ta É—auka, amma sai kawai ta share har suka koma.

Makaranta me kyau Mahaifinta ya nemar mata idan tare da direban da yake kaita, yana dawo da ita. Wannan karan a JSS3 aka sakata tare da É—aukan malam da suke yi mata lesson a gida, makarantar su Indo haÉ—e take da islamiyya basu suke dawowa gida ba, sai gabanin magriba. Wannan dalilin yasa koda Fahad ya koma basu cika wani haÉ—uwa ba.

Indo batasan yadda akayi Yasir ya samu lambarta ba, amma kodai mene ne tasan a gurin Momma ya ƙarɓa, Indo tun tana fushi da Yasir har ta sakko suka cigaba da mutumci, kamar yadda Indo ta ɗauka tunda har yau Yasir bai taɓa furta mata kalmar soyayya ba.

Wata ranar Asabar Indo na cikin garden Yasir ya kirata a waya, sun shafe awa guda suna waya banda murmushi babu abinda take, wani lokacin sai dai ta tuntsire da dariya, kome Yasir ya gaya mata ta miƙe tsaye tana murna harda tsallenta.

Dun abinda takeyi Fahad na tsaye yana kallanta wani ƙululun takaici ne ya rufeshi, Bai ankara ba yaji tace, "Wallahi nima nayi missing ɗinka Ya Yasir, amma kasan me zaka siyo mun idan zaka zo?" Kafin Yasir yayi magana Fahad ya ƙaraso a zafafe ya fusge wayar, kasheta yayi gabaɗaya fuska a tamke yace, "Ƙaramar yarinya da ke har kin iya soyayya ko? Shi kansa Yasir ɗin zamu gauraya dashi, zanga wanda zai ƙara baki waya yanzu" Indo batasan lokacin da hawaye ya fara zubar mata a fuska ba, da gudu tabi ta gefensa ta wuce ɗakinta. Iska mai zafi Fahad ya fesar ya wayar a aljihu ya bar gurin.

AKWAI ƘURA🙊🤣😂

KUYI HAƘURI DA KURAKUREN CIKI.

WANNAN SHAFIN SADAUKARWA NE GA ƳAN GROUP ƊINA NA *AMEERA ADAM FANS GROUP* DA MUTANENA ƳAN AMANA TA *WATTPAD*

_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
[02/10, 19:30] Omu Aslam Bint Adam✍🏼: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp

*INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️
*BY*
*AMEERA ADAM*

*FOLLOW ME @WATTPAD*
_*AmeeraAdam60*_

GARGAÆŠI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.

_*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_

_SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._

*Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.*

85&86

Aunty Safna na falo Indo ta shiga falon da gudu, da ido ta bita da kallo har ta shige ɗaki. Bata bi ta kanta ba saboda tasan wataƙila ita da Fahad ne, faɗansu kuwa bata shiga dan baya ƙarewa daga wannan sai wannan.

Fahad ɗaki ya shiga banda zarya babu abinda yakeyi, wayar ya ciro daga aljihu ya kunna domin ya shiga ciki yaga abinda take shukawa, sai dai password ɗin da yaci ƙaro dashi ne ya dakatar da shi. gwada lambobi ya farayi amma babu wacce tayi dai-dai, sai yayi tunanin bari ya sa 1234 yana sakawa ta buɗe. yana shiga cikin gallery ɗinta ya shiga ɓangaren camera, banda hotunanta dana su Aseem babu komai, whatsapp photos ya duba nan yaci karo da hotunan Yaseer ne birjik, har sai ɗaiɗaikun hotunan Jamilu, da wasu tsurarin ƴanmata wanda da alama ƙawayenta na makaranta ne.Da sauri ya fita ya koma cikin Whatsapp ɗinta, Ya Yaseer ya gani da sauri ya shiga, baiga wata doguwar hirarsu banda gaisuwa, sai kuma Assignment da take rubutawa take tura masa sai ya koya mata. fita yayi ya koma cikin lambar Jamilu da yaga anrubuta, Abokin Faɗa. Yana shiga ya fara duba hirarsu wacce rabi Voice note ce ba typing ba, ɗaya bayan ɗaya ya fara buɗewa yana saurara. Yawanci hirar tasu ta ƴar tsama ce sai wani lokacin gaisuwa ce, wani lokacin kuma labarin makarantarsu da take yawan bashi. Shima tana tura masa Assignment da yake koya mata, amma abin da ya dagula zuciyar Fahad da kodayaushe zaiji Jamilu na cewa Indo yayi missing ɗinta, wasu Voice note da ya ji Jamilu da Indo sunyi ya kunna su yafi a irga wanda Jamilu ya ce, "Ayusher yaushe zaki zo mana hutu ne?Saboda na nayi missing ɗin tsiwarnan taki" Indo ta ce, "Ya Jamil dama wai kana sona amma da sai kayi ta dukana" Jalimu ya ce, "Ayusher meyasa kika tambayeni?" Indo murmushi tayi ta ce, "Naga Baba Huwaila ce kawai take so na duk faɗin ƙauyen nan, bayan har kaini kake gurin Maigari ya dokeni" Jamilu ya ce, "Ayusher ni kuwa nake sanki! Bazan taɓa fasalta irin ƙaunar da nake miki ba. Amma lokaci na gabda zuwa da zan sanar dake abinda ya daɗe yana cimun tuwo a ƙwarya. Kina da Saurayi kuwa" Gaban Indo ne faɗi, murya a sanyaye ta ce, "Ya Jamil ba kai kake hanani kula kowa ba bayan su Zulai duk da samarinsu, kace har ansa ranar su." Jamilu ya ce, "Ai ba a ƙauye nake nufi ba, ina nufin anan Kaduna" da sauri Indo ta ce, "Cab bana kula kowa, bare mugun nan Ya Fahad yana nan ina zai barni na kula kowa" Gaban Jamilu ne ya faɗi amma sai ya basar ya ce, "Kintuna dai a ƙauye abinda ya taɓa faruwa da Hansa'u ko? To karki yadda ki kula kowa da sunan soyayya, idan lokacin yayi ni zan gaya miki, ko kuma na samo miki miji mai hankali kuma ɗan gayu ko bakya so?" Indo kunya taji kamar yana ganinta ta rufe fuska sannan ta ce, "To ya Jamil, amma karka samo mun mai mugunta kamar kai, kuma kyakykyawa nake so kamar kai ko wanda ya fika " ba ƙaramin dariya ta bawa Jamilu ba, Saboda ya lura har yanzu da sauran yarinta a kan Indo, yace "To shikenan ai dai-dai ke zan samo miki" sun jima suna hira sannan sukayi sallam.

Fahad ba ƙaramin shaƙa yayi ba, kashe wayar ya ƙarayi sannan ya koma kan katifarsa ya kwanta.

Bayan Magriba su Indo na zaune gabaɗaya suna cin Abinci, Fahad ya shigo da kofi a hannu da alama tea yake sha, Bayan ya zaune Indo miƙewa tayi zata bar falon Aunty Safna ta ce, "Humaira wai me akayi miki kike ta ɓata rai kamar wacce taci kashi?" Indo kamar jira take nan take idanunta suka ciko da ƙwalla, murya na rawa ta kalli Fahad ta ce, "Haka kawai ina zaune Ya Fahad ya karɓe mun waya, kuma waya muke da Ya Yaseer nasan yanzu haka ya neme ni bai same ni ba" Fahad ɗan zaro ido yayi wato ita bata ma kunyar faɗar wayar da take yi, har take jimamin kar Yaseer ya kira bai samu ba. Yana cikin tunani Aunty Safna ta ce, "Da abinda kikayi dan ruwa baya tsami banza" ganin angoyi bayan Fahad yasa Indo bata ƙara magana ba ta wuce ɗakinta.

Tunda Fahad ya karɓi wayarta bai bata ba. Kuma itama bata tambayeshi ba, sai bayan wasu watanni sannan ya bata wayar tare da canza mata layi, da kamar bazata karɓa ba ta karɓe abarta tana watsa masa harara.Tun daga lokacin Indo bata kuma shiga sabgar Fahad, shi ɗinma bai cika shiga sabgarta ba. Sai dai duk wani moshi da Indo takeyi akan idonshi takeyi.

BAYAN SHEKARA BIYU

Watarana Indo ta dawo daga makaranta da yamma liƙis, tana shigowa kamar a mafarki ta hangoshi zaune akan kujera da waya a hannunsa yana dannawa, cikin bazata gabanta yayi mummunar faɗuwa. Dukda shi ba fari bane amma ba ƙaramin canjawa taga ya yi mata dukda batafi wata shida rabon da tayi tozali da shi ba, kyawunsa ya ƙara fitowa har wata ƴar ƙiba taga ya yi. cikin murna ta jefar da jakarta gefe ta zuba da gudu kamar zata rungumeshi sai kuma ta tsaya, murmushi ɗauke a fuskarta ta ce, "Ya Jamil kaine! Wow dama zaka zo amma ko jiya a waya baka gaya mun ba, ina My Baba Huwaila wallahi nayi missing ɗinku gabaɗaya, Ya Jamil ka ga yadda ka ƙara kyau kuwa" tana faɗa ta ɗan taɓe baki ta cigaba da cewa, "Inama yadda ka ƙara kyau haka ka daina mugunta amma ina wallahi nasan halinka yana nan, Yauwa ya wajensu Zulai yanzu ƴaƴanta nawa?" Kafeta yayi da kallo, wani abu na tsarga masa cikin jikinsa. Ganin ya tafi duniyar tunani yasa Indo ta hura masa iska a fuska, lumshe ido yayi yana sauke ajiyar zuciya ya ce, "Yanzu Ayusher wacce tambaya kikesan na fara amsa miki?" ya ƙarasa faɗa yana harɗe hannuwa a ƙirji.
Chapter 55 · 0% Book details