Sashe 3
Indo Sarƙa Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ganin zaman bazai kaita ba yasa ta tashi ta fice daga gidan ko su magajiya bata yiwa sallama ba, tana tafe tana hawaye har ta ƙarasa gida zamanta babu wuya Indo ta shiga gidan tana ƴar waƙarta, " kujerar tsakar gida gun zama na mata wacce duk ta hauta......." turus tayi ganin Baba Huwaila na sharɓe hawaye da gefen mayafi, sauke ruwan kanta tayi ta ƙaraso gurunta ta tambayeta, Baba Huwaila zayyanawa Indo tayi duk abinda yake faruwa tsakaninta da Mai Gari, amma bata gaya mata cewar Goggo tsintota tayi tana jaririya ba, tana gama ji ta ƙyalƙyale da dariya da mamaki Baba Huwaila ta kalleta ta ce, " Nifa sakarcinki yasa bana san gaya miki maganaganu masu muhimmanci "
Tsagaitawa da dariyar tayi ta cewa Baba Huwaila, " Dan Allah Baba Huwaila ki daina zubda hawayenki a banza Ni Indo Sarƙa na Rantse miki da girman Allah Mai Gari sai ya bada takardunan cikin ƙasa da kwanaki ƙalilan, ki barni da shi wallahi sai ya bada su kuma babu wanda zai je ya karɓa da hannunsa zai bayar " tana gama faɗa ta shige ɗaki tana cigaba waƙar, " Ahayye dawo dawayya, dawo masoyiyata dawayya.... " da idanu Baba Huwaila ta rasa Indo dashi tana mamakin maganganunta.
*KACOKAN WANNAN SHAFIN NAKI NE MUM AMNASH ( MARUBUCIYAR DAFTA A'IYA💉💊) BARKA DA DAWOWA KWANA BIYU MUNYI KEWA DA FATAN KIN DAWO LAFIYA🥱.*
_Ummou Aslam Bint Adam_😉
[17/06, 03:30] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀ï¸
*INDO SARƘA*🤸ðŸ¼â€â™€ï¸
*BY*
*AMEERA ADAM*
*FOLLOW ME @WATTPAD*
_*AmeeraAdam60*_
GARGAÆŠI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.
_*WANNAN LITTAFIN GABA ÆŠAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE UðŸ¤*_
5&6
Indo har ta shiga ɗaki tai farat ta fito ta ce wa Baba Huwaila, " Yauwa Baba Huwaila nasan yanzu zakiji Sa'ar malam Sani ta kawo ƙara gurinki wallahi karki biye mata Lantan ce ta tsokane ni nikuwa na rama " Jamilu da tun farkon fara maganar Indo ya shigo gidan ya ce, " Munafuka wani abun kika aikata kenan shi ne kike kandagarki tun kafin akawo ƙararki ko? " Zumɓura baki gaba Indo tayi tana ɗauke kai gefe sannan ta ce, " Idan ma ƙarar tawa aka kawo ayba gunka za'a kawo ba " da sauri Jamilu ya ƙaraso gunta yana faɗin, " Rashin kunya zaki mun wallahi zan wanke ki da mari "
Da Sauri Baba Huwaila ta katseshi, " Kai wai wane irin azzalumi ne Jamilu? Kullin baka da magana sai ta zaka mareta, to yanxu kai take gayawa ba ni take gayawa ba " Haushi ne ya rufe Jamilu yayi gaba yana cewa, " Indai indo ce ba ƴar goyo bace ina zaune zan jiki idan ta janyo miki wata masifar " yana sa kai zai shiga ɗaki yaji sallama daga ƙofar gida juyawa yayi ya nufi hanyar waje dan ganin mai yin sallamar.
Mlm Sani da dogarawan Mai gari ya gani cikin sakin fuska yayi sallama yana miƙa musu hannu dan su gaisa, Mlm Sani Fuska a murtuke ya ce wa Jamilu, " Kai yaro dube mu da kyau ba gaisuwa ce ta kawo mu " Ado ne yayi karaf ya cewa Jamilu, " Shaiɗaniyar gidanku ce ta kusa ɓanɓarewa Lantan ƴar wajen Mlm Sani goshi suna cen gaban Mai Gari yanxu haka ku ake jira kayiwa Kakarka magana yanzun nan ta fito mu wuce " afili Jamilu ya furta, " Ay nasan ruwa baya tsami banza, amma ina zuwa " juyawa yayi cikin gida a bakin ƙofar soro yaci karo da Indo laɓe aykuwa batayi aune ba ya zuba mata ranƙwashi aka yana faɗin, " Almura dama nasan kame-kamen da kikeyi akwai tsiyar da kika shuka ni dama nasan wannan tuban da kikayi tuban muzuru ne bana Allah da Annabi bane "
Tun lokacin da Jamilu ya damƙi hannun Indo ta fasa wata uwar ƙara da ihu kamar wacce akewa yankan naman jikinta, Baba Huwaila tun tana zaune take ƙwalawa Jamilu kira jin ihun Indo yaƙi ci yaƙi cinyewa yasa ta taso tana tafe tana masifa.
" Wallahi Jamilu ka kiyaye ni da yarinyar nan tunda yarinyar nan ta dawo gidan nan ka sata gaba, yanxu abun har yakai da duka wallahi kaji tsoron Allah ka daina zalintar marainiyar Allah " Tana ƙarasowa Jamilu yayi ƙwafa ya ce, " Wallahi Baba Huwaila na ga alamar tarbiyyar da Goggo tayiwa Indo ita kike niyar cigaba da ɗorata akai " Baba Huwaila daƙuwa ta yiwa Jamilu ta ce, " Gidanku Jamilu, wato wata tarbiyya ta daban muke bawa Indon.... " daga cen bakin ƙofa aka katse Baba Huwaila ana cewa, " Wai zaku fito bane ko sai mun shigo mun ɗauke ta aka " Jamilu ne ya tasa ƙeyar Indo da take ta cika tana batsewa Baba Huwaila na biye da su.
Suna fita Ado ya kalli Indo yace, " Maƙira ƙanƙanuwa da ita sai hatsabibanci yarinya kamar jikar Aljanu " Indo harara ta galla masa ta ce, " Idan ni jikar Aljanu ce sai dai inkaina Kakan nawa dan ka fini kama da siffar Aljanu " doguwar bulalar hannunsa ya tsulawa Indo a baya, yana cewa, " Shashasha mara tarbiyya da bata ganin girman manya" dafe baya Indo tayi tana susa saboda yanda bulalar ta shigeta tana shirin magana Baba Huwaila ta ce, " Kai Ado ka fita ido na rufe wallahi karka ƙara taɓa mun yarinya tunda ba wani laifi tayi ba zalincin naka da ake faɗa zaka gwada agabana " Indo da ta gama susar bayan ta ce, " Ƙaleshi Baba Huwaila wallahi shima sai jikinsa ya gaya masa Sarƙa ce fa " haka suka tafi suna yi har suka ƙarasa fadar Mai Gari.
Fadar Mai Gari cike take da mutane Lantan na zaune da busassun hawaye anÉ—aure mata goshinta sai mahaifiyarta Sa'a dake gefe tana ta harare-harare, gefe Iyayen Zuwaira ne sai su Zulai suma da Iyayen su Goggo sallama tayi ta zauna Jamilu ya koma cen gefe yana watsawa Indo Harara, Mai Gari ne yayi sallama sannan ya kalli Indo ya fara magana, " Ke Indo mai ya haÉ—a ki da Lantan har kika ji mata wannan mugun raunin? "
Indo kallan Lantan tayi ta murguɗa mata baki tana ƙwafa, jin tayi shiru yasa Audu ya buga mata tsawa yace, " Indo Magana ake miki " karaf Indo ta ce, " Naga Lantan ɗin ta rigani zuwa mai yasa baza'a fara tambayarta ba sai ni saboda ni aka raina? " Mai Gari kallon Indo yayi ya watsa mata daƙuwa yace, " Ke fitsararriya kalleni kinci gidanku waye ya raina ki anan gurin? Kaga Yarinya mara kunya "
Indo ɗauke kai gefe tayi ta ce, " Allah ya baka nasara ya ƙara girma muna tafiya zamu ɗebo ruwa Lantan ta take mun takalmi har na faɗi naji ciwo da nace ta ban haƙuri shi ne ta gayan ba suga nikuwa na bita na rama tunda nima har ciwo ta ji mun, ko ba haka akayi ba Karime? " Karime tai sauri ta amshe zancen, " Eh haka ne ni har cizo na ma Zuwaira tayi garin dambe "
Mai Gari ne ya ce, " Ke Lantan haka akayi " Lantan girgiza kai tayi ta ce, " Ƙarya take ni bansani ba na bige ta kawai sai ji nai ta rufe ni da duka shi ne ta ɗauki bokiti ta buga mun kaina, kuma ni ban ji mata ciwo ba.... " karaf Indo ta katse Lantan, " Kuturun uba Allah ya tsine uwar mai ƙarya wallahi Ranka shi daɗe ƙarya take " Tsawa Audu ya buga musu ya ce, " Kai karku maida mutane sa'anninku mana, Ke Indo Ina ciwon da kika ce anji miki? " Indo kamar jira take ta fiddo hannu tana nuna musu gurun data kwaile sannan ta ɗora da cewa, " Kuma wallahi ko yanxu yarinya ta kawo mun raini sai jikinta ya gaya mata " Mai Gari ne ya kalli Indo yace, " Ke Sarƙa kike ko wa? Wallahi idan baki iya bakinki ba zansa a hukuntaki yanxun nan, kuma mai yasa da ta ji miki ciwo baki zo kin kawo ƙara ba kika ɗauki doka a hannu? "
" Ay wallahi nasan ko nazo na faɗa ba abinda za'ay mata sai dai ace inyi haƙuri daga haka kuma ta samu guri gaba ma abinda yafi haka zata mun " cewar Indo. Mai Gari Kallon Baba Huwaila yayi yace, " Baba Huwaila zaku biya duk kuɗin da za'a wankewa Lantan ciwo kuma duk maganin da za'a siya ku zaku saya mata, Ke kuma Indo idan na kuma samun makamancin irin wannan wallahi sai jikinki ya gaya miki " Baba Huwaila sunkuyar da kai tayi ta ce, " Na amince zan biya amma itama Lantan aja mata kunne karta kuma shiga sabgar Indo tunda bama sa'o'i bane, yoo banda ma rashin kamun kai ina Lantan ina Indo nawa Indon take ni bana san ma ta kuma takalarta harta kaisu ga haɗa ƙashi haka kawai yarinya ta dinga haɗa jiki da tsohon ƙashi "
Sa'a kamar jira take ta ce, " Ahayye ay gwara mu tsohon ƙashi ne ita waya sani ma ko ta gaba da alfatiha ce shiyasa ma ta addabi mutanen gari " Mai gari ne ya buga musu tsawa sannan ya ce, " Banasan shashancin banza da wofin fada ba gurin kace-nace bane Mlm Sani faɗi abinda kake so abiyaku kuɗin magani " Indo sam bata fahimci inda zancen Sa'a ya dosa ba shiyasa ma ko kaɗan bata kawo komai aranta ba.
Mlm sani kallan Mai Gari yayi ya ce, " Allah ya taimakeka abani dubu biyar ma sun isa " Indo karaf tai tace, " kambu lallai ma sai kace wacce aka cirewa ƙafa ko hannu zamu biya dubu biyar... " Jamilu daga gefe ne watsa mata daƙuwa shiyasa ta ja bakina tai shiru tana harare-harare, Baba Huwaila kallan Mlm Sani tayi ta ce, " Haba Mlm Sani wane irin ciwo aka ji mata da har zan biya dubu biyar " Sa'a ta karɓe zancen, " Wallahi haka zamu ƙarɓa ko sisi bazamu kankare ba "