← Book details Idon Naira Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 100

Sashe 99

Idon Naira Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin hakan sai Zainba tajanye daga nuna AQEEL nata ne ta zabi nuna Amal itace tata sai abin yasake musu qaimi suna sake nuna soyayyar dansu da cikin da basuda zabi Bayan so indai har suna son AQEEL din da gaske.

Basuyi wani zaman tone toneba sbd Babu wannan shakuwar ko sakewar har lokacin Amma dai kowa ya watsarda makaman yaqinsa gabaki daya hankalinsu yakoma akan cikin, mufeeda ce kawai tarage cikin kunci da baqin ciki

Su yanzu dasuka watsar sun samu sassauncin quncin zuciya Dama abun duk wahalar da Kai ne,

Idan ka dauki tsanar wani ko baqin ciki kasawa zuciyarka Kaine zakayita wahala kana shiga qunci har sai kacire ka huta,

Idan ka dauki lamura da sauki suzo maka da sauki idan ka dauka da wahala Kaine zakasha wahalar.

Su yanzu zaman Amal acikinsu sungano hakan sbd hankalinta kwance take da familynta da Mijinta,

AQEEL koyaushe a wayarsa da ita suna jiyo farin ciki da kwanciyar hankalinsa da Haka idan Suka matsa yanda yake sonta dinnan tana daukeda cikin daya qwallafa Rai suna tsanantawa rasashi zasuyi,hausawa sukace da Babu gwara ba Dadi, Dan Haka dasu rasashi duka gwara su lallaba a zauna lafiya.

Zaune yau a Palo habiba nayiwa Amal din gashin qafafunta dasuka Dan fara kumbura kadan wayarta ce a hannunta tana chatting da siddi ba zato taji qamshin turarensa.

Ajiye wayar tayi ta juya tana kallon kofar shigowa ga mamakinta ganinsa tayi tsaye Yana kallonta cikin wasu navy blue Cartier wears yayi wani irin kyau da haske na kwanciyar hankali da hutu harda wani kyakkyawan qasumba ya Tara daya qara Masa wani sanyin kyau da nutsuwa.

Murmushi ne dauke a fuskarsa Yana kallota cikin wani madaukakin sonta da kaunar abinda yake cikinta Wanda ya qara girma sosai.

Kallonsa takeyi sbd kasa dogon motsin datayi,

Ahankali ta sauke ajiyar zuciya tana lumshe fararen idanuwanta ahankali.

Da ido yayi mata" Hi love"

Sake sauke ajiyar zuciya tayi tareda janye kafafunta daga hannun habiba da Basu lura dashiba Dan tun farko sallamarsa Babu Wanda yaji

Itama qamshinsa dayake haddace cikin kanta da zuciyarta yasata dagowa ta kalli kofar.

Miqewa tsaye tayi ta nufesa ahankali tana kallonsa cikin tsananin farin ciki da sonsa Mai tsanani da kewarsa data Gama dawainiya da ita.

Bata qarasaba ya tako yashigo gabaki daya Yana sake kallonta da cikinta cikin kewarsu shima..

Gabansa ta tsaya tana kallon cikin idonsa ya bude Baki zaiyi magana ta daqa qafafunta ahankali takai fuskarta ta Dora bakinta kan nasa tafara kissing dinsa ahankali cikin sanyi.

Rungumeta yayi tareda Kama bakinta da nasa din yakarbi kissing din sbd sanyi da nutsuwar Wanda take Masa zai iya zautashi a gurin.

Tsotsan bakinta yayi tsawon minti daya da seconds kafin ya saketa ahankali Yana kallon fuskarta datake bayyanarda galabaituwan datayi da sonsa da kewansa.

Juyawa sukai palon habiba ta Dade da barin palon a rikice Kai aqasa

Haj Maryamah Daman tana daki tana fitowa tun bataga me sukeyiba ganinsu a jone yasata juyawa qafafunta na rawa tareda mamakin dawowar tasa.

Umman Cameroon kuwa qyam tayi a palon zaune abunta tareda qurawa tv Ido batareda tana fahimtar komaiba sbd duk ta rikice da wannan diban albarkar dasukai musu a palon.

Hannunta cikin nasa ta riqe cikin farin ciki suka qaraso tana Masa shagwaban ya dawo ba sanarwa.

Duk neman susucesa takeyi daqyar yake kamo nutsuwarsa da kamewarsa Yana gaisawa dasu umma dasuke Masa barka da dawowa Suma cikin kulawa da farin cikin ganinsa Amma duk Amal din tagama susutasa dauriya kawai yakeyi Yana amsa musu suna cigaba da magana.

Hararar duniya umman Cameroon tayiwa Amal akan ta sakesa karya rude da abinda yake fada Amma Amal ta fuske a gefensa taqi kallon umman Dan Jin takeyi duk ta narke da ganinsa kawai.

Daqyar tabarsa dasu umman ta nufi kitchen sbd girkin dataketa sake koya a gurin habiba sbd Idan ya dawo din.

Sharp sharp Suka hada Masa simple abinci Suka jera da komai ba kunya taje Tai wanka ta shirya cikin doguwar Leyla A casual gown mara nauyi ta fito tana qamshi lokacin ya tafi sallar laasar.

Baki sake su umma Suke kallon ikon Allah harta Gama wayoyinya dasu Mommy ta sanar musu da isowarsa.

##MAMUH#77

*_Arewabooks@Mamuhgee_*

77

LAST PAGE

Yana dawowa daga masallaci su umma Suka shige dakunansu sbd kaucewa ganin abinda Bai Kamataba Dan yanda Amal ke narke Masa suna gudun ta sakasa kunya a gabansu,

Dukkaninsu mamakinsa ma sukeyi Dan su ba Haka sukasan AQEEL ASAD dinsuba,

Mutum Mai kunya da kamewa zama cikin zuriar Idon Nera ta fedare musu shi.

Babu kowa a palon daga ita sai shi ta jasa dining ta zaunar dashi sai janyota yakeyi Yana shinshinawa kaman Wanda zai cinyeta.

Kaucewa ta ringa Yi tana zuba Masa abinci Wanda tana Gama zubawa ya janyota kan qafafunsa Yana da shafa cikinta Yana kokarin cusa Kansa cikin wuyanta ta Dan janye tana kama fuskarsa tayi kissing bakinsa tana cewa,

"Girkina ne wannan fa,nice nayi maka.

Murmushi yayi Yana kallon abincin yace,

"Mmmmn really??

Gyada Kai tayi tana murmushi tareda miqewa daga kafafunsa ta fara debowa ta Kai bakinsa.

Itace tayi Masa Bismillah tareda saka Masa cikin Baki.

Jinjin Kai yayi Yana cewa,

"Thank God Matata ta iya abinci.

Qara Masa tayi Yana basa ahankali Yanaci Yana shaqan qamshinta dayayi masifaffen missing.

Lokaci Mai tsayi suka Bata kafin Gama cin abincin Suka dawo palon Suka zauna tana Masa fira da sakalci daban daban tareda mantawa dasu umma na daki makure.

Sai magrib ya fice zuwa sallah.

Bai dawoba sai Bayan ishi lokacin Dole itace tabarsa ya gana dasu mahaifiyarsa.

Abinda Bata taba zaunawa tayi da danta bane sukayi a yau din wato fira cikin kauna da kulawa da sakewa ba kaman baya da iyakacinsu magana cikin girmamawa da da'a kawai Babu sakewa Babu zama free.

Daqyar ya iya barinta a sashen ta kwana bayan sun Gama shiriricewa a palon tana Masa shagwaba da narkewa iri iri duk yabi ya birkice Haka yaso lallabata suje sashensa Amma taqi Dan har cikin ranta zafin kishinta bazai barta ta bisa can bangaren daya gama rayuwar komaima da matarsa.

Ko bayan datazo ta kwanta Hana umman Cameroon bacci tayi da waya dashi akai akai daqyar umman taga safiya tayi ta baro Mata dakin.

Da safe suna kallo ta ringa neman Dama Masa lissafi da sakalcinta har harya fice gidan.

Akwai ayyukan dake jiransa Dan Haka can ya wuce Bai samu zuwa gurin Maminsa ba har yamma ya dawo ya huta tukuna ya fito zuwa sashensu umman.

Bayan sallar magrib sai ga Yan gidansu sunzo gabaki daya yimasa barka da dawowa harda uncle Lulu Wanda duk lokacinda Haj Maryamah zata gaisa dashi saita Jinjina yau itace ahali daya hardasu Dan daudu.,

Ita Siddi dasuka San yanda aka sameta tun suna duba lamarin qarfi da yaji dai Suma sun saje yanxu har mantawa sukeyi da yanda take shiyasa wani lokacin suke mamakin Wanda yake rayuwa free Bayan yasan yanada abin fada to ya yake rayuwar?

Ashe abin daka barwa Allah ka watsar shikenan mantawama kakeyi.

Gashinan yanzu Suma mantawar sukeyi da waye siddi,

Waye Lulu hakama waye Zainab wadda zuwa yanzu sun fara manta zancen sunan karuwancin dasuka santa dashi batareda anfada musu gaskiyartaba sbd AQEEL daya zabi su kaunace yanzu a yanda take sbd Allah ba Dan anfada musu ba abinda suke tinani bane idan sun sani daga baya shikenan dai.

Tayi murnar zuwansu Haka shima yayi farin cikin zuwan Mamin nasa Nan Suka zauna aka gaggaisa A mutunce.

Anty Fareedah da Amal daki Suka shige

Shikuma dasu Mamin da uncle Lulu harma dasu umman akai maganar tarewan Amal din da zatayi jibi.

Anan sukai dinner tareda mutan gidan Kai waye,

Haj Zainab da uncle Lulu da Anty Fareedah harma da Amal kansu a waye yake sosai shiyasa sukeda sakewa Dan Haka a waye ba damuwa Suka sakewarsu musamman uban gayyar shi Daman a sakensa yake indai Amal na kusa dashi.

Haj Maryamah da umma dasuka ga suna komawa kaman Yan kallo

umma Cameroon tasake rutsawa tana nuna Suma a wayen suke tunda sunyi yawon kasashe.

Murmushi kawai Haj Zainab tayi sbd tsakaninta dasu Babu wannan sakewar ta Yan uwan jini saidai girmamawa kawai irin ta sirikai Dan yanzu sabuwa alaqa ce aka kulla Basu dawo data Bayan ba tukuna kila sai gaba kokuma wannan sabuwar alaqar ta auren 'yayansu itace ta kamacesu Kuma itace zata zama sabuwar alaqarsu sbd ta Bayan Allah baiyi itace zata doreba.

Da zasu tafi Dole tareda Amal Suka tattara suka tafi gida sbd daga can ne zata tare gidanta.

Bayan tafiyarsu saiga su umma da kewan Amal da cikinta sbd tanada sanyi da nutsuwar da Basu taba tsammanin samu daga garetaba,

Ko makaranta datake zuwa kullum Ahmed yakaita ya dawo da ita Babu inda take qara zuwa idan ba gidan mommynta ba itama sai jifa jifa sbd AQEEL din da bayason yawo,

Habiba kuwa dasukai sabo fiyeda kowa Jin Tayi ta matsu Amal ta tare takoma gidanta dan tace da ita zata.

Haj Zainab ba qaramin dadin barinsu tafiya da Amal dinba dayayi taji Dan harga Allah tanason takai yarta dakinta da kanta.

Itama Amal tayi farin cikin dawowa gida duk da kwana biyu ne zatayi ta tare din.

Washe gari Haj zainab bata tsaya bata lokaciba tafara shirya yarta duk da babu daman manyan shiri sbd ciki dan haka aka fara yimata na skin da sauransu,

Gidan karatunsa dama key na hannunsu tun wancan lokacin da aka gama gyara aka Zuba sababbin luxury furnitures da komai

Dayake kusan komai shine ya zuba a gidan sai sukuma sukai Kayan kitchen masu shegiyar tsada da aji da sauran abubuwan da baa rasaba.

Siddi ma dole tadawo sbd kar ayi hiduman yar uwarta batanan,

Tunda tadawo gida tayi busy mommynta ta hanata ko saukowa shima yayi busy sosai sbd ayyukansa daya Bari hakama akwai wata tafiyar gabansa amma tareda matarsa zaije dan Haka saiya bawa su Mamin daman yanda takeso baijeba bare hankalin Maminsa ya tashi da ganinsa Dan ya lura yanzu idan yaje gidan ta dinga rarraba ido kenan Dan kada yayi wani Abu gidan da Amal tunda ba sanin inda Suka Saba kebewa suka samu ciki ba tayi.
Chapter 99 · 0% Book details