← Book details Idon Naira Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 100

Sashe 86

Idon Naira Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mommy da kanta ta tayar da ita tasata tayi wanka jikinta a sanyaye ta shirya Suka fito siddi ce ta fidda Mata kayanta suna fitowa Bata gansaba yariga ya fice sbd bayason Yana ganinta a yanayin datake agaban mutane coz a yanda yake jinta dinnan zai iya rungumeta gabansu Kuma yasan bazataso hakan ba.

Tea kawai tasha sama sama har lokacin batada walwala ko kadan
Ita kanta mommyn zuwa yanzu tanason Amal din taje taga likitan tunda ya buqata hakan
Daga nasa likitan har nasu basusan Ina Saar samun lafiyar takeba.

Mommyn daga na palon tayi bankwana da ita Takoma sama sbd batasan rakiyar me zatayi Mata har waje ba.

Siddi ma daga kofa ta tsaya ta Dan rungumeta tareda Mata sallama ta juya tana cewa,

"Amal Dan Allah ki Dan sake Masa fuska kafin kudawo.

Batada energy na iya amsawa zancen siddin Dan Haka ta shareta kawai kafin tayi wani motsin tajisa a bayanta ya qaraso cikin nutsuwa.

Juyowa tayi ta kallesa da idanuwanta dasukai jajir take taji jikinta yasake mutuwa da wani irin damuwar halinda ya sakata a yanzu.

Hannunta ya Kama ahankali batareda yace komaiba ya nufi mota da ita tana tafiya kaman Mara lafiya ba kuzari ko kadan,
Tun kafin su qaraso Ahmed yabude masu mota
Shine yafara shigar da ita ya rufe Mata kafin ya zagaya ya shiga nasa bangaren Ahmed ya rufe Masa.

Suna barin harabar gidan Kai tsaye airport suka nufa duk da akwai sauran 1 hour kafin tashin kirjinsu.
#MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR_*

*RUMBUN K'AYA*🔥
Hafsat Rano

*DAUDAR GORA*🔥
Billyn Abdul

*IDON NERA*🔥
Mamuhgee

*A RUBUCE TAKE*🔥
Safiya huguma

*KI KULANI*🔥
Miss xoxo

Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200

ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN

0022419171
Maryam sani
Access bank

Shedarka ta 09033181070

MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*Thanks for choosing us*🔥*_Arewabook@Mamuhgee_*
66
Koda suka Isa Al-Amin na airport din tareda tickets da sauran abubuwan nasu na tafiya da alama taredashi zsuyi tafiyar wadda Daman akwai abinda zasuyi acan zuwa jibi Amma AQEEL ASAD ya zabi tafiyar da wuri kawai.

Ahmed na parking din motar dakyau ya bude ya fito yabar gurin gabaki daya Dan Basu guri yabi Al-Amin dashima baiso tafiyar tasu yanzuba yaso sai jibin.

Juyowa yayi yana Mata wani irin kallon da baisan wane iri bane,

Zuciyarsa tariga tagama dadewa da ita manne acikinta har bazaice ga lokacinba.,

Tazama Kamar itace rauninsa da qarfinsa tareda kuzarinsa da akalarsa Amma sam ita bata gane hakanba,

Ayau yatashi da azumi ne na nunawa ubangijinsa tsananin godiyarsa da babban arzikin dayayi Masa na abinda Dr tayo ta sanar dashi jiyan,

Yashiga wani yanayi ne Mai hadeda shock da zallan wani yanayi Mai tsananin girma a cikin zuciyarsa alokacinda kalmar Amal din na daukesa cikinsa ajikinta ta shiga kunnesa,

Ya Dade zaune shiru cikin nutsuwa alokacin da Dr tayo take cigaba da Koro Masa bayanin Yana sake kokarin kame Kai daga shiga firgicin zancen Dan arzikin daga Allah ne daya basa a lokacinda Bai taba tsammanin wannan kyautarba Dan kuwa Amal tagama basa duk wani abun a duniya dayake buqata bayan gamawa lafiyada cikawa da Imani.

Idan Bai samu ya dauketa yaje inda zai dauki lokaci Yana Jinta da cikinsaba to duk yanda yake biya Mata gurin Hana kowa ganesu dan kada ranta ya baci tashiga damuwan kunya to tabbas idan bai bar Nan da itaba komai bayyanuwa zaiyi Dan tsakanin jiya zuwa yau din daqyar yake controlling Yana nutsar da Kansa akanta,

Buqatan rungumeta yakeyi ajikinsa ya sauke Ajiyar zuciya ya shaqi qamshinta Da numfashinta dake fitowa da 'dansa ko 'yarsa ajikinta.

Hannuwanta ya riqo cikin nasa ya sarke ahankali tareda sauke ajiyar zuciya ya kalleta itakuma har lokacin taqi kallonsa daga zuciyarta har jikinta ba Dadi.

Bazai iya shigar da ita jikinta ya shaqi qamshinta ba sbd azuminsa Dan Haka hannunta kawai yakai bakinsa yayi kissing sai alokacin ta juyo ta kallesa batareda tace komaiba.

Shima kallon nata yakeyi da idanuwansa dake neman qarasa rikitata ahankali cikin wata murya Mai sanyi da Dadi tareda nutsuwa yace,

"Congratulations Mrs AQEEL ASAD...

Wani kallo tayi Masa jikinta na qarasa mutuwa da mummunan halinda takejin tana ciki tareda mamakinsa Akan ta tabbata dai Dr tayo ta sanar dashi tana daukeda ciki,
Meyasa zaiyi congratulating nata bayan ko a kallo ya kalleta yana iya hango mummunan tashin hankalin datake ciki,

Idan yasani to meyasa zai dauketa suje ganin wani likitan?
Akan me zasu ganin liktan?

Fuskarta ya shafa kadan Yana sake cewa,

"Idan kina mun wannan kallon Zaki karyamun azumi fa.

Juyar da kanta tayi ahankali tana rintse Ido cikin damuwar data dameta.

Al-Amin ne ya iso ya sanar dasu su fito lokacin tafiyan yayi.

Hannunta cikin nasa a riqe yake tafiya da ita ahankali ba gaggawa ba garaje cikin nutsuwa da kwanciyar hankali Al-Amin ne janyeda kayansu.

A jirgi ma Haka ya zaunar da ita da Kansa kafin ya zauna Yana kallon yanda duk tayi sanyi batada walwala ko kuzari ko kadan.

Ajiyar zuciya kawai ya sauke Yana Hana Kansa yimata rarrashin dayake buqata sbd azuminsa,
Ayanda yake jinta Acikin Ransa Dole Yana buqatan janyewa da nesanta Kansa da ita aduk lokacinda zaiyi ibada irin wannan ta azumi.

Ciki ba ruwansa da damuwa Dan Haka suna tashi wani bacci Mai dadi da Dan nauyi ya kwanshe hannunsa daya Yana manne da nata.

Bayan isarsu Kai tsaye beach Villa resort aka kaisu Kai tsaye dakinsu yakaita Wanda yake kusan zagaye da ruwa da abubuwan hutawa da asalin iskan ruwa Mai dadi.

Al-Amin gabaki daya baa resort din nasa masaukin yakeba Dan Haka shi juyawa akai aka wuce dashi nasa masaukin dayake kusa ba nesa sosaiba.

Bakin manyan windows din dasuke kaman kofofi ta tsaya tana shaqan iskan dake kadawa Mai sanyi da rashin hayaniya.

Ajiyar zuciya ta sauke ahankali tana kokarin barin kanta ya warware yasamu salama ko zata Samu sassaucin komai.

Waya yakeyi Mai mahummanci Sosai tunda Suka shigo makeken dakin dayake daukeda komai na tsadaddiyar luxury rayuwan Jin Dadi da kwanciyar hankali da hutawa.

Tunda yake wayar idanuwansa akanta suke Yana kallon sauyinta na haske data qara da wani irin kyau Mai sanyi saidai daga hankalinta datayi a jiyan zuwan yau din yasa duk ta Dan rame.

Gurin cikinta dake cikin doguwar Rigar jikinta ya zubawa Idanuwansa Yana cigaba da wayarsa.

Koda ya Gama tashige toilet tayo alwala ta tana fitowa yasa ta jirasa ba musu ta jirasa din Yana fitowa sukai sallan tare,

Da Kansa yayi Mata order na abinci kusan kala uku da drinks marasa sanyi aka kawo,.

Kaman yanda yasabar Mata idan har suna tare zataci abinci shine yake Bata abaki,

Haka ya janyota ya zaunar gabansa yabata abincin taci sosai ba laifi sbd yinwar da cikinta yake ciki gashi kwanakin sosai takecin abinci dama Ashe da dalili.

Tana Gama cin abincin Takoma ta zauna ta rafka tagumi tana sake shiga tunani Mai zurfi daga Nan Bata jimaba bacci ya dauketa Mai qarfi.

Tanayin baccin ya dauketa yakai tsakiyar lafiyayyan gadon dakin ya kwantar da ita ya zare Mata doguwar abayan jikinta yabarta da leggings da qaramar singlet din dake jikinta ya rufe ta da lallausan duvet me taushi ya fice daga dakin Yana nufi makeken qaton corridor dinsu budadde Yana cigaba da amsa wayoyi sbd abubuwan dasuka danganci aiki da wasu mahimman abubuwan daya baro sbd tafiyar ta Babu tsammaninta kusa.

Bacci sosai tayi sai yamma ta farka ta sauko gadon ahankali tana kallon cikinta dayake kukan yunwa.

Toilet ta nufa ta tadda tuni an kawo duka abubuwan dayasan tana amfani dasu an jere a toilet din,

Brush tasake Yi tayo alwala tafito ta saka abayan tayi sallar laasar tana idarwa Yana shigowa sanyeda qananun Calvin Klein's isowa yayi gabanta tareda miqar da ita Yana cewa,

"Barka da tashi Yar Mommy.

Juyawa tayi ta kalli abincin datake hangowa jere a lafiyayyan 2seat dinning din dake dakin.

Gurin abincin ya nufa da ita still shine yasake feeding nata Yana tarairayarta dan mantar da ita damuwarta wadda tarasa Ina mafitar take.

Yana gama Bata abinci ko dining din basu dagaba lokacin Shan ruwansa yayi,

Kai tsaye yace Mata ta zuba Masa tea ya nufi toilet Dan yin alwala.

Ajiyar zuciya ta sauke ahankali sbd batada zabin daya wuce yin abinda yace din,

Tea din tafara zuba Masa tareda janye plates daya gama abinci ta gyara table din Dan samun space yanda yakamata Dan abincin kusan gab da magrib din aka kawosu aka jera.

Yana fitowa tablet din yake kalla da mamaki ganin ta gyara komai tana janye wainda suka Bata da farko.

Zaunawa yayi ahankali ya Dan sha fruits da tea din kafin yamiqe sukai sallan magriba a tare suna idarwa ya jata da Kansa yace shima itace zatayi feeding dinsa.

Zamewa takeyi tana neman kaucewa Amma Bai Bata Daman hakanba ya dauketa cak ya nufi dining din suka zauna tana jikinsa ya gyara Mata zama jikinsa Yana shinshinata idanuwansa dasukai tsananin kewanta a jikinsa da qamshinta suna lumshewa,

Sake zagayeta yayi dakyau Yana zira Kansa cikin wuyanta ya sake shaqo qamshinta Yana shafa wuyanta da fuskarsa.

Ita kanta lumshe fararen idanuwanta tayi tana dan motsawa tsikan jikinta dayake neman tayarwa da fuskarsa dake shafan fatan wuyanta wuwa kirjinta.

Fuskarta ya tsayar da tasa a saiti Yana shaqan iskan numfashinta dake sauka akan fuskarsa ya kalli cikin idanuwanta da itama ta dago tana kallonsa,

Harshensa yakai kan lips dinta ya laso yasake lasowa ya lumshe Ido Yana sauke ajiyar zuciya kafin ya Dora bakinsa akan nata din gaba daya ya kamo harshenta da nasa yayi nasa wata irin kyakkwar tsotsa Mai sanyi da nutsuwa kafin ya Ciro bakinsa ya dago ya sake kallon fuskarta cikin matsanancin sanyin sonta dake riqe da dukkanin zuciyarsa da wata kasalalliyar murya qara qasa yace,

"I Love you MARYAMAH Amal Sanda,
Nagode da wannan farin cikin da Zaki bani na zamowa uba.

Kasa motsawa tayi sai idanuwanta dasuka narke data zuba Masa tana mantawa da halinda ma take ciki da damuwa.

Sakinta yayi Yana gyara Mata zama a jikinsa yafara cin abincin Yana tsokanarta Akan ta basa da hannunta Amma taqi.
Chapter 86 · 0% Book details