← Book details Idon Naira Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 100

Sashe 80

Idon Naira Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Kaman yanda ya dawo da ita jiyan Haka ya dawo da ita a yau Amma yauma harsunyi latti kadan ya rage Basu hadu da Uncle Lulu daya fita yau din tunda safeba.

A kwanakin komawa yayi Yana raba kwana a tsakaninta da Bilkees batareda Bilkees din Tama tsaya ta fahimci duk Bayan kwana biyu baya kwana a gidaba hakama Amal data manta gabaki daya da yanada wata Matar.

Ana cikin hakan yayi tafiyar dazata daukesa kusan sati biyu ko uku ma.

Ranar dazai tafi acan suka kwana dagacan school ya ajiyeta Koda kowa ya farka Bata gida Bilkisu tace musu ta wuce school tunda safe dayake exams Sukeyi.

Yana ajiyeta airport suka wuce shida Al-Amin Ahmed yakaisu yakoma makaranta jiranta.

Karfe uku ta fito makarantar Suka dawo gida wanka kawai tayi taci abinci ta kwanta sbd Dan zazzabin datakeji tun shekaran jiya sama sama.

Koda maraice yayi jikinta yayi zafi Sosai Haka ta Dan daure aka Bata magana tasha,

Hankalin mommy tashi yayi sbd lurada wata yaqare ciwon marartane na period zaizo wannan karonma kaman ta gota harda kusan sati daya,

Mamakin lamarin mommy tayi Amma dai ganin tafara zazzabin Mai zafi saita San ciwon ne zaizo.

A sukwane ta wuni kwance hakama washe gari ta tashi da zazzabin dayake sun Saba da ciwon nata sai akaci gaba da Bata maganin datakesha hakan saiya fara sata ciwon Mara ahankali batareda itama tayi wani tunaninba ta dauka period dinne zaizo dan harta manta da ciwon nata dataga lokaci ya wuce batai period dinmaba kwata kwata.

****Haka kawai Bilkees ta zowa su umma a wuya ta tsaya sbd gabaki daya ta tattara zancen lamarin Mijinta da aurensa ta watsar tamaida hankali gurin rayuwar Matan manya dasukeyi itada qawayenta su Nafee data dawo Suka sake dinkewa abinsu ganin kowa ya watsar da kwallon mangwaro ya huta da quda,

Ita Nafee tana sane da AQEEL ASAD Yana tareda aurensa da Amal Bai rabuba Amma taqi fadawa Bilkees din sbd kada tayi rigima auren ya mutu tasan Amal na rabuwa da aure wallahi Allah ne kawai zai Hana Mijinta aurenta Dan Haka ta zabi yin shiru tana sake Dora Bilkees din a hanyoyin da bama zatasan akwai aurenba bare tayi wani yunqurin.

Umma Babu safiyar da Bata debewa bilkees akan wawanci da haukata gashi Suma yanzu sunaji suna gani AQEEL yake qin kwana a gida wasu lokutan Wanda sune kadai sukasan inda ake gashi ba damar magana saidai Ido da guni a zuci Wanda yafi komai ciwo.

Haj Maryamah kuwa ganin da gaske suna zaune zasu iya samun mugun labarin sabuwar hadin zuria da Zainab da Haka tafara dagawa Bilkees hankali akan sake haihuwa sbd Daman can Dan ana Zaune kalau ne bata maganar asake Amma har cikin ranta 'yaya takeson AQEEL ya Haifa musu masu yawa tunda ita Shi kadaine, itama ita kadaice agun ummanta gwara shi ya hayayyafo da yawa tunda akwai arziki Mai yalwanda ko 'yayansu bazasuyi talauciba da yardar Allah hakama Shi kansa tasa yanada masifan son yara tunda sungani tun haihuwar Zainab datai ta Amal dn yabi ya rikice.

Bilkees ganin masifar dasuka bullo Mata da ita ta maganar haihuwa ba arziki Ido a rufe gabaki daya sun sauya Mata Dan ita umma harda maganar Daren farkon Nan tana ranta takasa cirewa ace matar dasuka kawo Masa Babu Wani motsi salin alin Amma 'yar karuwa anzo Anata neman madinka da likitoci hardasu gashe gashe Dan Haka akwai zance a qasa tsakaninta da uwar Bilkees idan Takoma Cameroon bata yarda dasuba rufa rufa sukai Mata aka bata ta aurawa jikanta.

Bilkees da mufeeda dataji abinda sukewa mahaifiyarta binsu suka ringa Yi da magana

Bilkees Babu ranarda Bata debewa tsufan umman Cameroon albarka tana fatan ta tattara Takoma Cameroon sbd itace mahadin komai.

##MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR_*

*RUMBUN K'AYA*🔥

Hafsat Rano

*DAUDAR GORA*🔥

Billyn Abdul

*IDON NERA*🔥

Mamuhgee

*A RUBUCE TAKE*🔥

Safiya huguma

*KI KULANI*🔥

Miss xoxo

Littafi daya---400

Biyu---600

Uku----800

Hudu-----1k

Biyar din duka----1200

ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN

0022419171

Maryam sani

Access bank

Shedarka ta 09033181070

MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪

*Ina yan uwa 'yan nijer?*

*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA

biyu---650CFA

uku----850CFA

hudu----1050 CFA

Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*Thanks for choosing us*🔥Mamugee
63
Chapter 80 · 0% Book details