← Book details Idon Naira Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 100

Sashe 92

Idon Naira Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wane irin kike maganar zaa hada da Idon Nera????

Kai tsaye umman Dan qunsa Mata baqin cikin datake fatan yasa kanta ya juye gabaki daya su huta tace,

"Tsohon cikin Mijinki ne a jikin Amal Yar gidan Zainab....

Mufeeda dake jinsu a firgice ta fito mota tana isowa gurin qafafunta na neman hardewa zatayi magana.
##MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR_*

*RUMBUN K'AYA*🔥
Hafsat Rano

*DAUDAR GORA*🔥
Billyn Abdul

*IDON NERA*🔥
Mamuhgee

*A RUBUCE TAKE*🔥
Safiya huguma

*KI KULANI*🔥
Miss xoxo

Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200

ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN

0022419171
Maryam sani
Access bank

Shedarka ta 09033181070

MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*Thanks for choosing us*🔥*_Arewabooks@Mamuhgee_*
71
Kallon takaicin umma tayiwa mufeeda data iso gabanta jiki na rawa tana sake Tambayar umman abinda ta fada,
Bilkees da kunnuwanta ke Jin wata jiniya na qara cikin kanta itama sake maimacin maganar umman take jira sbd abinda ta fada a kwai Yar rudarwar tsufa suke gani.

Al-Amin dake gudun ta tambayesa da kanta yakasa Mata qarya juyawa yayi ya shige mota da hanzarinsa yabar gidan Yana Jinjina rigama irinta umman Cameroon Dan yanda ta fada din da gayya yasan so takeyi ta cinnawa Bilkees din hauka.

Mugun kallo umman ta sake jifan mufeeda dashi tana cewa,

"Da kikaji ubanki zai sake haihuwar wata 'yar ko 'dan shine Kika fito kikazo gabana sbd muguwar tarbiyar da uwarki tai Miki kenan Amma farko da Kika hango ni ranga ranga ko kallo ban ishekiba,

Wlh Bilkees kinci Amanar AQEEL da Kika lalata Masa tarbiyar 'ya,

Ai duk hakan mukewa kukan wannan cikin na zuriar Zainab ance azabarwa 'yaya uwa ta gari gashinan Muna gani akanki
Duk iliminsa da addininsa da iya kokarinsa akan tarbiyantar dake da 'yarsa bayan idonsa wargazawa kikeyi.,

Ai Allah yaqarama da Amal din tasamu ciki tunda ke kinzama shashashar banza da wofi.

Mufeeda ce ta katse umman da cewa,

"Haba umman Cameroon sai magana kikeyi kina tsine tsine batareda kinsan komaiba,.wayace Miki Amal Idon Nera nada ciki?

Cikin wata nannauyar murya me kokarin Hana Kai bugawa Bilkees ta katseta da cewa,

"Idanma tanada ciki wlh ba na mijina bane saidai idan a wajen mazan dakewa uwarta rawar qafa ta samoshi.

Sabon kallon firgici umma tayi Mata tana sake tabbatarda Bilkees rufa rufa akai Mata ta amsowa jikanta ita Dan akuwa alamu sun sake nunawa batada hankali,

Wannan masifa tayiwa 'dansu yawa Mata biyu Babu wadda ta fito hannun albarka gashi zaa Tara musu 'yayansu,

Ita Bilkees hanyar komawa Cameroon take daukowa kanta Dan kuwa ko su dasuke iyayensa duk abinsu bazasu iya sheganta cikin Amal ba Dan yanda taga AQEEL akan cikin ko ita tsaf zai maidata Cameroon ita data haifi uwarsama bare wannan mahaukaciyar matar tasa.

Kallon Bilkees tayi tace,

"Wallahi tallahi haukarki ta tsaya a iya Nan
Idan Kika qi Allah yasa kiyiwa kanki duk mu huta Daman ke mungaji dake,.Ina dalili Haba,mata kullum sai hauka daban daban kinbi kin ishemu mun rasa da balai da masifar Zainab zamuji kokuma da taji jarabar.

Ciki dai Amal Idon Nera cikine da ita Kuma na AQEEL ne, dan Allah ki haukace a kaiki gidan mahaukata sai kowa ya huta muji da masifar Zainab kawai.

Gaba tayi abinta tana hadawa daga Bilkees din da uwarta data cuceta akai Mata rufa rufa har Zainab da sunan duka Idon Nera tana debe musu albarka abin ya isheta ya ishi tsufanta.

daga Bilkees har mufeeda kasa motsi sukayi sbd kashesu da umman tayi da maganganunta da Babu wadda suka gane fes kaman maganar cikin AQEEL a jikin Amal Idon Nera..

Mufeeda da batada taurin zuciya irin na umminta Hannu ta Dora akai tana fasa kuka tace wlh umme shege Suka kwaso zasu maqalawa daddyna,

Umme Dan Allah karki Bari ta laqawa daddyna a hadani da wani jinin ace ubanmu daya Dan wlh ban yarda babyn daddyna bane.

Bilkees gabaki daya kanta da hankalinta tsayawa sukayi cak Bayan jiniya Babu abinda takeji a kunnuwanta da cikin kanta..

Tabbas an gunguma Mata babbar cuta da munafurci a gidan Nan,

Su umma suna sane da AQEEL Yana tareda Amal idan har umman Cameroon Kai tsaye zatace cikin AQEEL ne tabbas
To suna saneda meyake faruwa kenan akai shiru aka munafurceta sai yanzu taji wani maganar ciki kawai Rana tsaka,
Cabdijam
Ai kuwa wallahi tallahi bazata yardaba tafison a masifa ayi balain da kullum umman Cameroon ke kira idan yaso daga cikin ya zube,masu hawan jini ya Haye Suma su zube,masu bugawan zuciya su buga su wuce ita kanta dasukewa kirarin mahaukaciya tayi haukar a kaita gidan mahaukata Amma wlh saita Rama wannan abin.

Wato har tsohon ciki kaman yansa umma tafada.
Sbd sunason haihuwar batayiba shine suka juya gurin Amal tasamu sbd mutuwar zuciya irin tasu....

Huhmmmnn" ta sauke numfashi Mai tsananin zafi da tiririn zuciya ta fizge key din mota dake hannun mufeeda daketa faman kuka komai batace ba ta nufi mota ko ganin gabanta sosai batayi.

Tana fadawa motar ta tada
Da sauri mufeeda dake hawaye ta iso ta shiga itama ko Gama rufe motar batayiba Bilkees ta fizgeta da mugun gudu daman masu gadi sunbar Mata gate din bude sbd Al-Amin daya fita da mota itama sunga fitar zatayi shiyasa Basu rufeba.

Tana Hawa titi Kai tsaye ta daga wayarta takira Habib daya Saba Mata aikin Yan Media.

Yana dauka muryarta na fidda wani zafi tace,

"Yan media zaka tura gidan Idon Nera tonan asiri zaayi musu 'yarta Amal tasha nono daya da AQEEL ASAD yanzu Kuma tayo ciki wani gurin tace nasane,

Ka tabbatarda wannan labarin ya yadu a ayau dinnan Kuma a yanzu bada jimawaba a tura Yan media gidan suyi Mata tonon asiri da wannan labarin..

Shiru Habib yayi yana cewa,

"Bakowane labari fa Yan media ke zuwaba,
Wannan abinda kika fada bekai ace sunje dnba sbd abune da kusan koina Ana samun hakan,
Suna daukan labaraine akan abubuwan dasukasan Yana zama tamkar abin al'ajabi,
Sai Kuma idan na manyan masu kudine da duniya ta sani,
AQEEL ASAD Yana daya daga cikinsu Amma Kuma fidda wannan labarin ga media wlh babban hatsarine garemu da wainda ma zasu buga labarin dukanmu AQEEL ASAD bazai barmuba.

Cikin baqin ciki ta katsesa da cewa,

Ina ruwanka da abinda zai biyo baya kawai ka tabbatarda an watsa zancen yanzu Yan media din su tafi gidanta Dan suna samun labarin gidanta zasu nufa yanzu Dan wlh yau sauna cinnawa gidan Nan wuta.

Ko nawa ne zanbada,
Zanbaka kudinda zaka bar qasar kaje hutunda sai komai ya lafa yanzu nakeson wannan aikin banason Bata lokaci.

Kashe wayarta tayi tareda wurgi da ita bayan motar zuciyarta na wani irin tafasa kanta na neman kuncewa.

Mufeeda ma Jin abinda umminta zatayi saitaji sanyi ta dakatarda hawayenta sbd hakan zaisa koina cikin bazaikaiba da duniya ta sheganta auren da cikinma,
Daddynta ma idan yayi fushin Dan lokaci zai yafewa umminta tunda Yana sonta itakuma Daman baya fushi da ita kasancewarta tilon yarsa idanba yanzu da akeson kawo Mata wani mugun zancenda bazai karbu ba ta hada uba daya da 'dan karuwa ko 'ya.
Gidan Idon Nera ta nufa tana zuba wani irin gudu da mota kaman wadda ta rasa kanta gabaki daya,.
Babu abinda takeson gani kaman tai ido biyu da cikin jikin Amal tagansa.

Al-Amin kuwa ganin umman Cameroon ta fadawa Bilkees maganar yasan akwai matsala Dan Haka yana baro gidan Kai tsaye asibiti yakoma ya tadda Haj Maryamah ma ta Dan dawo daidai Amma numfashinta ahankali take yinsa ta nace akaita gida kawai.

Ganin yanda AQEEL din Kansa ya Dan dauki zafi yasa Bai sanar dashiba Kai tsaye yayi shiru tukuna Saida suka shiga mota suka Kama hanyar gida.

Shiru yayi yanata juya zancen to Amma ganin idan saisunje gida Kuma yafada Masa su dawo kaman lokacin kila wani abun yafaru to Amma sbd baida tabbacin ko Bilkees ta fita ko tana gida sai yabari idan sun Isa yaga batanan din ya fada Masa ko kila gidan IDON NERA ta nufa Dan yasan Allah ne kawai zai Hana Mata zuwa gidan.

Suna Isa Ana nude musu gate ko shigowa basuyiba ya hango ba motarta a harabar gidan Kai tsaye ya juyo ya kalli AQEEL din cikin damuwa da fargaban inda taje yafada Masa abinda ya faru.

"Wat" AQEEL yafada Yana kallon harabar gidan ba motarta ko umma Basu tsaya ajewaba Dan ko qarasa shigowa basuyiba yace Al-Amin ya juya zuwa gidan Maminsa.

Shiru AQEEL yayi Kansa na daukan wani irin zafi Wanda irin hakan idan ta faru shiru yakeyi Dan alamar tsananin bacin Rai ko tashin hankalinsa shiru yakesashi.

Kallo daya Haj Maryamah tayi Masa tasan yau 'yar wahalar matarsa tayi haukan taba wannan jarababben cikin kila harsu saisun sheda fushinsa da ita kanta Bata taba ganiba Dan na yau din yafi na kullum.

Dedeta numfashinta tayi dan dolenta ta Kama kanta sbd Allah ya hutar dasu Cikin sauki mahaukaciyarcan zata musu fadansu da bazasu iyaba Dan gudun fushi da bacin Ransa.

Wayarta ta daga ahankali ta saka Kiran ummanta taca a Aiko Mata driver yanzu yazo gidan Idon Nera ya daukota ya dawo da ita gida Dan ita ko gidan bazata iya shigaba gwara driver yazo ya juya da ita.

Ummanta najin hakan tasan wani balain Yakuma bullowa tunda taji Maryamah a gidan Zainab Dan Haka da kanta ta biyo driver din sukaje daukan Haj Maryamah din.

Bilkees dayake ta tsaya cire kudi masu yawan gaske tabawa Habib kafin ta wuce gabaki daya baa hayyacinta takeba shiyasama har lokacin Bata Isa gidanba.

Amal data Gama kuka ta rarrashin kanta tayo wanka tareda alwala tayi sallah tana idarwa ta fito ta nufi dakin mommynta jikinta a sanyaye.

Tana tura kofar dakin mommyn zata fito itama.

Kallonta tayi tana sake kallon cikin daya fito a straight doguwar Rigar data Sanya da hula.

Ita kanta Mommy kunyar cikin takeji shiyasa abin yazo Mata a wani iri.

Sun shammaceta,sun Kuma Bata mamaki iya mamaki wlh.

Wucewa zatayi Amal din ta riqota da sauri tana sake Mata hawaye cikin sanyin murya tafara Bata hakuri tana kokarin fada Mata lokacinda AQEEL yafara saninta...
Chapter 92 · 0% Book details