← Book details Idon Naira Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 100

Sashe 56

Idon Naira Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cutatarta akeda niyar Yi kome?

Boye Mata zaayi kamar yanda suka boye Mata alaqarsu da zuwansu gidan IDON NERA tun farko?

Hummmmm" ta sauke wani numfashi Mai nauyi da zafi..

Indai kuwa boye Mata akeda niyar Yi tabbas akwai wuta a qasa kwance Dan kuwa zataga yanda zaayi rayuwa a wannan zuriar da wannan auren da kowa yake maqiyin kowa.

Tashi tayi a haukace zata nufi kofar fita wata zuciyar ta hanata
Ta dawo qafafunta na wata irin rawa takai kanta dakinta tana Shiga ta rufe ta zube qasa tareda sake fasa kuka Mai qarfi tana dafe kirjinta dake tafarfasa.

Dannar zuciyarta tayita yi tana kuka sbd tasamu bin komai ta fahimci abinda ake nufi da ita Dan tasan Idan tayi haukar Komai lalace Mata zaiyi batareda tasan Ina makamar zancen takeba.

Wani zafi da radadin zuciya ta kwana dashi tana kuka,
Yanda taga Rana Ido biyu Haka taga Daren Idon tsaye,

Jin takeyi zuciyarta na tafasa da tsanar duk Wanda yake gidan na zuriar AQEEL da Idon Nera gabaki dayansu.,

Mufeeda ma Ido biyu taga safiya cikeda damuwa da kukan datasha qarshe ma da wani irin zazzabi ta tashi umminta Kuma da ciwon kai Mai tsananin gaske dayasa ko fitowa taqi yi,.

Taga Kiran AQEEL ASAD a wayarta da safen Amma yaqi daukan wayar karshe kashe wayar tayi gabaki daya.

Daga ita har mufeeda Babu Wanda ya fito yaje gaidasa kaman yanda suka saba suna sake kowace ta rufe dakinta Tama wi fitowa.

Yasan abinda yake damunsu Dan Haka Bai takura neman nasu ba yabari su sauko tukuna.

Baiyi breakfast ba qarfe goma yafito a shirye cikin milk luxury yadi Mai taushi.

Kai tsaye sashen ummansa yaje yafara duba umman Cameroon wadda itama Sam taqi yarda tagansa taqi fitowa daga dakinta tace ace Masa yaje kawai batason ganinsa sai uwarsa tadawo zatayi lokacinsa.

Yana fitowa malam Rabiu ya taso ya bude Masa mota ya shiga suka nufi gate securities na matsowa gurin motar suka Masa barka da fitowa cikin girmamawa.

Suna fitowa daga gate din gidan malam Rabiu yahau titi Kai tsaye hanyar gidan IDON NERA ya nufa sbd yasaba zuwa yanzu kusan kullum saisun biya da safe kafin AQEEL din ya wuce office dinsa.

Tun Basu qarasoba Securities suka hango lafiyayyar motarsa a tafe
Dan Haka suka tashi sa sauri suka bude Masa gate suna Masa barka da zuwa cikin girmamawa.

zaune suke a Palo suna Shirin yin breakfast daqyar siddi ta shawo kan Amal ta fito da ita yin breakfast din fuskarta babu walwala ko kadan saidai ta Dan sake daga kumburin kukan datayi jiyan sbd Bata sake wani kukanba tayiwa kanta alqawarin hakan.

Kayan bacci ne fafare qal ajikinta Riga da wando gajeru masu tsantsi
ba bra ajikinta hakama ko Babu komai akanta daga ita sai slippers farare masu laushi.

Siddi ce a gaba sai ita a baya fuskarta takoma Yar Qarama sbd rashin isasehn bacci.

Anty Fareedah ce da Haj Zainab a zaune suna jiran saukowarta uncle Lulu yayi tafiya yau din tunda safe sbd akwai da abinda zai kaisu kaduna Amma sbd halinda ake ciki Dole shi kadai sai salahudden yabi jirji ya wuce.

Qamshinsa daya fara shiga hancin Haj Zainab Bayan Bilkisu ta bude Masa kofa yasata waiwayawa ta kalli kofar alokacin ya shigo take ya sauya musu iskar palon da kamshinsa Mai dadi.

Anty Fareedah ma kallo daya tayi Masa ta miqe tsaye tana kasa sake kallonsa sbd cika idanun dayakewa mutane.

A natse tana Dan sake fuska ta gaidasaa shima ya amsa batareda ya kalleta sosaiba.

Maminsa ya qarasa gurinta itama ta miqe tsaye tana kallonsa kafin ta amsa nutsatsiyar gaisuwarsa tace,

Muje breakfast kayi breakfast tukuna.

Cikin yanayi na kulawa ya kalleta sbd ko a yanayin fushi yasan Mami Bata qin basa kulawa.

Magana zaiyi su Amal da basu lura dashiba Saida ta iso tsakiyar palon taji qamshin data tabbatarda nasa ne ta kame fuskarta nauyin zuciyarta na neman dawowa.

Siddi ce itama cikin sakin fuska da girmamawa tace Masa Good morning.

Waiwayowa yayi ya amsa batareda itama ya kalleta sosai dinba..

Maida kallonsa yayi kan Amal ya zuba Mata fararen idanuwansa yayi mata kallon sakanni kafin ya dauke Kansa ya dawo da kallonsa kan Mami datake kallon Amal tana jiran taji ta gaidasa kosa a maqoshi ne.

Ta gabansa tabi ta wucewarta Kai tsaye zuwa hanyar dining batareda ta damu da kallon da kowa yabita dashiba musamman Anty Fareedah dake kollon kayan jikinta da suka lafe ajikinta.
##MAMUH#
#LOVE/HOTLOVE
#AQEEL ASAD#AMAL SANDA

*_ZAFAFA BIYAR_*

*RUMBUN K'AYA*🔥
Hafsat Rano

*DAUDAR GORA*🔥
Billyn Abdul

*IDON NERA*🔥
Mamuhgee

*A RUBUCE TAKE*🔥
Safiya huguma

*KI KULANI*🔥
Miss xoxo

Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200

ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN

0022419171
Maryam sani
Access bank

Shedarka ta 09033181070

MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*Thanks for choosing us*🔥*_Arewabooks@Mamuhgee_*
43
"Amal"
Haj Zainab ta Kira sunanta alokacinda take gap da qarasa barin gurin.

Dakatawa tayi batareda ta juyoba Saida Haj Zainab din tace,

"Dawo Nan.

Juyowa tayi ahankali ta dawo har lokacin Bata sake kallon inda yake shima tun kallon farkon da yai Mata Bai sake kallontaba saima time daya kalla daga Cartier watch dake daure a hannunsa.

Siddi da Anty Fareedah wucewa sukai sukabar gurin sbd ganin yanda mommyn ta Dan kame fuska.

Amal na zuwa Kai tsaye tace Mata,

"Meye hakan?

Kasa magana Amal tayi sai dagowa datayi ta kalli mommyn cikin Dan mamaki da muryarta Mara nauyi tace,

"Me nayi mommy??

Maganarta yasashi sake Dan kallonta kafin ya maida kallonsa kan Maminsa sbd time dinsa na tafiya yanada abubuwan Yi ayau din.

A natse Kai tsaye yace,

Mami ba buqatan komai
Karki damu tako Ina,
Zanji da komai,
Zan tafi inada baqi dasuke jirana yau.

Juyawa yayi har zai wuce ya dakata tareda juyowa yakalli kayan jikinta dakyau kafin ya maida kallonsa kan Haj Zainab data rasa abin cewa
Cikin nutsuwarsa da kamewa yace,

"Mami next time kada takuma fitowa ahakan.

Juyawa yayi ya wuce yabar Amal tana binsa da kallon mamaki da takaicin maganarsa.

Harya fice Bata Dena bin hanyar dayabi dinba da kallo tana tausan juciyarta akan damar daya samu.

Haj Zainab ma tashiga mamakin sbd qarfin ikonsa akan Abun dayakeda Isa dashi hardashi yake Bata tsoro da shakkar idan zai aminta yabar Amal din har zuwa gaba.

Boye shakkarta tayi tareda kallon Amal data dawo da kallonta akanta itama idanuwanta na sauyawa.

Gaba tayi tana cewa,

"Kinji abinda ya fada ai
nxt time din saiki hada harda gaisuwa sbd wannan haline Zaki nuna wainda yake nuni da irin tarbiyar da Kika samu,

Bansan meyasa Zaki wahalarda kanki ki wahalar daniba akan maganar Nan,
Nace Miki ki nutsu ki Cire komai a ranki Ina Nan zanji da komai Amma kin kasa tausan zuciyarki,

Wannan zafin kan naki ba komai bane agaban nasa zafin kan,

Idan kikai danyen Kai wahala Zaki fara Sha da wuri dan kuwa alokacin ne zakiga cikakken ikonsa akanki Dan koni bazan hanasaba tunda yariga yasha gabanmu.

Dining ta nufa tabar Amal din a tsaye tana binta da kallo itama,

Kasa qarasawa gurin cin abincin tayi sbd apatite data rasa take,
Juyawa tayi ta koma dakinta tareda wucewa toilet Kai tsaye.

Tubewa tayi tayo wanka ta fito ta zauna gaban mirror sai alokacin ta samu ta nutsu tadawo daidai ta fizge tunaninsa kwata kwata daga kanta.

A natse tayi shirinta na makaranta Dan idan ba ficewa tayi daga gidanba bazata Dena Jin iskarta tadawo daidaiba sbd qamshinsa daya barmusu.

Riga da skirt ta saka na embellished atmp coffee brown sai qaramin veil iya wuya Wanda take saka irinsu.

Handbag da key din motarta kawai ta dauka ta sauko.

Mommynsu ta fita itama tana saukowa ta fice.

School ta Isa Kai tsaye sbd tanada lectures har biyu a ranar.

Da farko Babu kusan kowa yayi mamakin zuwant da Kuma shigarta wadda tasaba normally sbd sun dauka tunda tana auren AQEEL ASAD shigarta zata sauya wasu harsuna matsuwa da ganinta Acikin su jallabiya masu rufe jiki sosai.

Kaman yanda tasaba batada wasu friends na musamman saidai wainda take Dan gaisawa dasu Dan Haka Babu Wanda yaga Fuskar zuwa gurinta Dan samun qarin bayani akan aurenta Haka suka wuni suka Gama ta juyo a matuqar gajiye ta nufo hanyar gida,

Sai data biya makarantar Fahat ta daukesa sbd 6 ta wuce Daman 6 din suke tashi.

Koda suka iso gida angama sallar magrib Dan Haka tana parking Fahat bangaren su mum dinsa ya wuce ita Kuma tana kokarin rufe motar Aka bude gate motar AQEEL ASAD ta shigo harabar gidan.

Shine ya tuqo motar da Kansa bama wadda ya Saba zuwa da ita bace watace daban.

Saiti da tata motar yayi parkin
Bude motar yayi yafito sanyeda black jallabiya Mai tsadar gaske daya kwanta matuqa sai kyalli takeyi ajikinsa gashi kalar ta fidda hasken fatarsa sosai.

Juyawa tayi batareda takuma kallon inda yakeba bare ta nuna tagansa zata wuce abinda duk duniyarta Bata taba tunaniba shine Jin hannunta daya riqo cikin tattausan tafin hannunsa.

Tsayawa tayi cak ba tareda ta juyoba ta fizge hannunta zata wuce ya riqo qugunta gabaki daya ya dawo da ita bayanta na gap da haduwa da kirjinsa saidai ya Hana hakan faruwa sbd bazaizo jikinsu ya Hadu dinba.

Zafi zuciyarta keyi tana Mata tafarfasa tareda faduwar gaba sbd wani namiji kaf rayuwarta Bai ta'ba taba jikintaba irin hakan,

Hannuwansa dasuka riqo qugunta takeson Kai hannunta ta cire Amma bata son hannuwanta su taba nasan Dan Haka ta sake qwacewa da qarfi saidai kaman tasake tura kantane ta hade bayanta da kirjinsa abinda baisoba ko kadan Dan Haka yayi saurin sakinta tareda dauke kallonsa akanta gabaki daya yaja baya kadan kafin ya dago ya sake kallonta da Idanuwansa datakejinsu ajikin ahankali cikin nutsuwa yakai bakinsa saitin kunnenta daga bayanta qasan makoshinsa ya janyo muryarsa ahankali yace,

"Next time kada ki Kuma fita koina batareda saninaba,

Kayan jikinta yakalla tareda sake janyo muryarsa zaiyi magana sai kawai ya fasa ya miqe tsaye tareda rabata ya wucewarsa gaba batareda ya waiwayo ba kaman bashine yayi maganaba.
Chapter 56 · 0% Book details