← Book details Idon Naira Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 100

Sashe 93

Idon Naira Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dakatar da ita Haj Zainab din tayi tana cewa Bata buqatan jin lokacinda suka zama Ma'aurata.

Siddi ce ta fito ta qaraso tareda riqe mommyn itama tana Bata hakuri tareda tinatar da ita jikan datake buqatane yazo maimakon tayi murna Kuma sai tana fushi Bayan itace taketa rokon Allah yabata jikan gashin yabata tunda gurin roka jikan kawai take fada bawai tace ga wadda takeson ta haifo jikanba.

Batace komaiba amma yanda ta Dan sake kallon Amal da cikin yasa Suka fahimci bawai cikin ne batasoba kwata kwata yanda komai na yanayin yazo.

Saukowa sukayi Suka nufi dining Siddi na riqeda Amal datace batajin cin abincin Amma sbd kallon da mommy tayi Mata yasata saukowa taredasu cin abincin.

Suna saukowa Anty Fareedah da uncle Lulu suka shigo palon ko dining Basu qarasaba Bilkisu ta shigo tana kallon Uncle Lulu tace,

"Hajiyar Mahaifiyar Sir AQEEL ce ta iso tana harabar gida.

Rintse Ido Haj Zainab tayi ahankali sbd tasan Daman zaa Rina,
Tasan saisunzo gida sbd bazasu taba karban cikin nanba,
Tasani sai sunzo sun aibata cikin da ita da yayanta a gidanta Dan Haka itace tafara nufar kofa tareda uncle Lulu kafin su Amal din gabaki dayansu Suma Suka bi bayanta.

Umma kuwa isowarta kenan daukan Haj Maryamah da Basu Riga sun isoba Dan tafisu kusa da hanyar gidan akan ta inda suka biyo su.

Motarta Suka nufa dukkaninsu itama tana ganin sun tinkarota ta fito fuskarta a daure tana kallon cikin Amal dayake tsole idanuwanta.

Kafin suyi wata magana motar Bilkees ta kunno kai cikin harabar gidan da baa Gama rufe gate dinba cikin wani mugun gudu daga nesa ta hango Amal da mommynta da umman Cameroon guri daya ga cikin da idanuwanta tsabar baqin ciki da fita hayyaci suke nuna Mata kaman yanzu zaa haifesa Kai tsaye Bata tsayaba ta danne motar tayi kansu
Mufeeda wani razanannan ihu tasake tana Kiran sunan ummin tata Amma idanuwan Bilkees sun rufe so take tayi cikinsu da motar matsalarta taqare daga yau din idan yaso taje gidan yari ta yarda, Dan kuwa Amal Idon Nera da Zainab Idon Nera sai umman Cameroon sune babbar matsalarta a yanzu.

Cikin mummunan tsoro da tashin hankali da gigicewa mufeeda ta fizge steering motar Suka daki motar Haj Zainab dake gurin take duka motacin suka farfashe da tasun data Haj Zainab.
##MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR_*

*RUMBUN K'AYA*🔥
Hafsat Rano

*DAUDAR GORA*🔥
Billyn Abdul

*IDON NERA*🔥
Mamuhgee

*A RUBUCE TAKE*🔥
Safiya huguma

*KI KULANI*🔥
Miss xoxo

Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200

ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN

0022419171
Maryam sani
Access bank

Shedarka ta 09033181070

MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*Thanks for choosing us*🔥*_Arewabooks@Mamuhgee_*
72
Umman Cameroon datayi suman tsaye tareda saddakarwa zuwa lahira tuni qafafunta Suka fara rawa tana zare Idon hankalinta na kasa dawowa jikinta da abinda taga Bilkees taso aikata musu,

Haj Zainab ma gabaki daya ta shiga mummunan tsoro da tashin hankali tareda rungume 'yarta datasan sbd ita Bilkees din takeson kashesu,

Amal kuwa tsabar tashin hankali da firgita kullewa mararta tayi take ta rige cikin tana neman durqusawa jikinta na rawa.

Al-Amin da kusan saura kadan shima yayi cikin su Uncle Lulu gurin buge mota Bilkees din daga Yi kansu Amal bugun motar Bilkees din yayi tasu suka tadan fashe daga gaban.

Haj Maryamah data rikice gabaki daya alokacinda Suka dannowa motar Bilkees data rigasu shiga Dan kusan tare Suka shigo layin Amma tarigasu Shigewa gidan akan idonsu tayi kansu umma tini jinin haj Maryamah yakusa kaiwa dari biyu da 'dori sbd ganin ummanta da zata tafi lahira ba shiri sosai ta firgita tashiga mummunan tashin hankali.

AQEEL daya Gama girgiza matuqa shima Yana fitowa motar Kai tsaye Amal dasu Mami ke tallafowa ya nufa ya taro jikinsa Yana Kiran sunata da wani wata shaqaqqiyar muryar da tsananin bacin Rai da zafi Mai tsanani suka dashe Masa ita.

Ganinsa yasata bude idanuwanta akansa tanajin tsiwon mararta na qaruwa kafin kace me sai jini yafara biyo qafafunta.

Wani mummunan tashin hankalin da Babu Wanda ya taba Tunanin zai shiga duk ya shigesu musamman mommy da ahalin Idon Nera din dukkaninsu ita kanta Haj Maryamah da umma tashin hankali suka shiga
Yau kowa yasan da cikin Kuma ace yau idin zai bare,Babu Wanda zaiso hakan,.shi Mai cikin ko maganarsa baayi Dan Haka Bai tsaya jiran kowaba ya dauketa Kai tsaye Yan nufi mota da ita tun kafin yaqaraso Al-Amin ya bude Masa yashige da ita a jikinsa

Wani mugun ribas Al-Amin yayi dashi ya fita gate din gidan kafin ya juya yahau titi da mugun gudu suka nufi asibiti.

Uncle Lulu da Ransa yagama mummunan baci fiyeda yanda ake tunani Kai tsaye Yan SARS yakirawa Bilkees da 'yarta tsabar baqin ciki da takaici.

Ita kanta Haj Zainab Bata damu da matakin da uncle Lulu din yadaukaba kafin suyi wani motsi saiga ya Media din data Kira sun iso kofar gidan tareda shigowa harabar datake bude sbd masifar data afku.

Daga ita har mufeeda sun Dan bugu Amma bawani ciwo sukaji ba fitowa mota sukayi tana bude Idon inda zataga Amal Dan batasan AQEEL yazo ya dauketaba Dan Saida kanta ya dawo daidai daga buguwar da yayi Suka iya fitowa motar.

SARS office na kusan kusa da Anguwarsu Dan Haka kafin kace me Suma sun iso ba wata wata suka cafketa Yan media kuwa abin yaqara musu armashi take guri yacika aka wuce da ita abin baqin ciki su haj Maryamah na kallo rayuwar dansu da Mai mutunci da qima da girma a idanuwan mutane tazama abar daukan media da Allah wadai sbd rashin matar albarka.

Asibiti Haj Zainab dasu Siddi da hankalinsu ya tashi Akan Amal Suka nufa itama Haj Maryamah asibitin Suka nufa itada umma a motar da umma tazo da ita
Har lokacin umma Bata Gama dawowa hannyacintaba daidai Bayan ajiyar zuciya akai akai Babu abinda takeyi sbd ta girgiza ta firgita matuqar gaske,
Duk haukar dasuke Kiran Bilkees da ita Bata dauka Dagaske dai batada hankalinba sai ayau data kusa hadata da malaikun azaba Dan kuwa kafin ta hadu da malaikun rahama ta tabbatarda azabar markadar da motar zatayi Mata ita zata fara Sha kafin ranta ya fice.

Kalma daya takasa fitowa daga bakinta sbd Bata Gama fitowa daga shock ba,
Sai yau sukasan asalin yanda shock yake ba irin Wanda Suka Saba shigaba na bacin Rai Ashe.

Ita kanta Haj Maryamah yau ta dandani asalin shock in gaske data hangi mahaifiyarta zaa niqata da mota da tsufanta Bilkees taso gana Mata azabar da ko a labari ba Dadi.

Koda suka Isa asibiti Kai tsaye har Amal na labour room su Dr tayo na kanta Ana dubata Dan cikin Kam ya zuba.

Har Suka zo Suka tsaya taredashi a office din Dr tayo suka zazzauna jigum jigum Babu Wanda ya iya cewa komai sai Satan kallonsa sukeyi sbd yanda gabaki daya Babu Wani rahama ko fuskar da wani zai iya magana a gurin sai kallon kallo kawa sukeyi gasu aguri daya yau din Amma Babu damar fada da juna Dan yau duk Wanda yai fadama kila AQEEL yafesa zaiyi tunda sunkoma kaman sune 'yayan shine uban sbd rashin tinaninsu.

Dr tayo Allah yabasu nasarar Hana cikin zubewa Ya tsaya saidai zuban dayayi kawai Dan Haka Dr tayo tace Gaskia zata riqeta a asibiti sai tasamu qarfi sosai Dan ta fahimci akwai rigimar da akeyi a gidan.

Jin ansamu daga Amal din har cikin suna lfy yasa Suka samu damar fitowa kurmanci wucin gadin dasuka shiga Amma still dai Babu Wanda ya iya yiwa AQEEL magana sbd shima dai baicewa kowa komaiba.

Uncle Lulu da aketa kira sbd zancen kamun Bilkees din daya fara fita sunan AQEEL na neman baci aciki yasa yaje da Kansa SARS aka saketa ta hau motan haya ta nufi gida da yarta datasha kuka har idanuwanta basa gani,

Suna zaman zamansu ta rasa meya jawo musu wannan wagararriyar rayuwarba.

Tsoronta abinda daddynta zai musu idan yaji wannan abin da umminta takusa aikatawa.

Gashi kusan kila kowa yaji abinda sukayi tunda a Media din dasuka Kira sun hada hardasu sun dauki rahoton sun hada da Wanda Suka Basu.

Suna Isa gida ba kowa har lokacin su umma suna asibiti tareda AQEEL dayake cikin wani irin Hali na qunci da bacin Rai tareda baqin cikin rayuwar dake gudana a familynsa,

Kobai fadaba dukkaninsu sunga halinda yake ciki Kuma sun tabbatarda Yana cikin qunci Mai tsanani,

Bayan daidaituwar Amal shi kansa saida Dr tayo Suka dubasa tareda Dr Abdulsamad salees yayan Dr Inayah A majeed sbd kirjinsa dake ciwo Wanda alamu ne dake nuni da gap yake da kamuwa da ciwon zuciya koma zuciyar ta buga kowama ya huta sai suci kansu.

Haj Maryamah da umma da Zainab dasuka ji wannan mummunan labarin hankalinsu tashi yayi
Umman Cameroon datafi kowa saurin kuka fasa kuka tayi tana tsinewa zuriarda Bilkees ta fito tana tsinewa aurenta dabai qaresu da komaiba bayan haihuwa daya.

Haj Maryamah ma kuwa kasa cewa komai tayi Dan tunanin Mijinta ne yadawo Mata matuqar wani Abu yasamu AQEEL ya bar Mata duniyar to me zata zauna tayi.,

Ita rayuwarta a qunci ta taso a qunci tayi rayuwa gashi haryanxu a qunci take takasa samun farin cikin rayuwa sbd balai da masifar abinda yake zuciyoyinsu.

Haj Zainab ma sanyi jikinta yayi da 'yayan nata suke cikin wannan masifun daga wannan sai wannan gashi yazo ya Hadu da mahaukaciyar Mata ya aura zata kashesu taja Masa masifa sukuma ta kashesu lokacinsu Bai qarasa yiba,

Son zuciyarsu umma yakaisu ga kwaso Masa masifa gashinan masifar harsu tana neman gagararsu.

Sai dare suka tattara suka koma gidajensu gabaki dayansu aka bar Anty mommyn a asibiti tareda Siddi sune zasu kwana da Amal.

Shi kansa shawara likitoci suka basa na ya kwana anan asibiti taredasu su samu su qara duba yanayinsa Dan Allah ne kawai ya tsaresa ya Hana zuciyarsa bugawa a yau din.
Chapter 93 · 0% Book details