← Book details Idon Naira Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 100

Sashe 42

Idon Naira Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wannan ba Zainab maminka bace da kakeso da alfahari da ita
Wanna Zainab IDON NERA ce,
Nice uwar dakin karuwai,
Nice nakeda gidajen karuwai da qungiyarsu,

Sunana qaurarrene a duniya yanzu,
Banda baqin ciki Banda kunya banda takaici ko Dana sani na hakan,

Kamar yanda kaji Ana fada 'yayana basuda uba,
Babu Wanda yasan ta yanda na haifesu Dan Haka bamuda wani abin bugun gaba ko alfahari daya wuce dukiya da muke rayuwarda mukeso da ita,

Kai din babban mutum ne a yanzu,
Babban masani addini ne da ake alfahari dashi koina,
Kanada mutunci da suna,
Kanada girmanda Bazanso alaqarka daniba ya zubar maka da duka wainnan abubuwan,

Kayi nesa Dani,.
Ka nesanta kanka da duka ahanalina,
Sunanka zai lalace zaka rasa mutuncinka a addininsa idan ka bayyanawa duniya alaqarka da hamshaqiyar karuwa IDON NERA........

Wasu irin hawayene suka gangaro Masa daya kasa riqewa,
Kowace kalmar data furta deep yanka sukewa zuciyarsa,

Wane mutunci da radadi yafi sunanda take ambata din,
Wane mutunci da girma yakai ya tsaya akan tsamota daga wannan mummunan suna da duniya ta santa dashi..

Hawayensa suka saka jikinta sanyi Amma Dole ne ya nesanta Kansa dasu.
Zubewa yayi gabata tareda sunkuyar da Kansa Yana tsiyayar hawayen dayake riqewa a Ransa tsawon shekaru na rashinta.

Wallahi ayanzu daya gansu kome suka zama bazai iya rabuwa dasuba.

Maimakon tayi fushin da yanke sauran alaqarta dashi kasawa tayi zuciyarta ta karshe sbd ganin hawayen babban mutum kamarsa
Duk da agurinta shi din yarontane datake goyawa tana basa abinci abaki.

Kasa riqe kanta tayi daga kaunarsa Mai tsanani dake qasan ranta ta bayyanar Masa da kaunar tata a fili ta tsiyayo da hawayen kewarsa da tuno muguwar rayuwarta ta baya.
##MAMUH#
#LOVE/HOT
#SISTERSLIFE

*_ZAFAFA BIYAR_*

*RUMBUN K'AYA*🔥
Hafsat Rano

*DAUDAR GORA*🔥
Billyn Abdul

*IDON NERA*🔥
Mamuhgee

*A RUBUCE TAKE*🔥
Safiya huguma

*KI KULANI*🔥
Miss xoxo

Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200

ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN

0022419171
Maryam sani
Access bank

Shedarka ta 09033181070

MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*Thanks for choosing us*🔥*_Arewabooks@Mamuhgee_*
31
Lokacinda suka dauka batareda sun saniba yasa Koda suka Ankara da time din lokacin tafiya ya wuce sbd karfe biyu harda mintina,

Malam Rabiu Kam tuni ya shige cikin securities yayi kwanciyarsa tuni bacci ya daukesa.

A yanda ya takura Mata da Kuma kwarjini da girmansa yasata ta sanar Masa kadan daga cikin rayuwarta Amma Bata sanar dashi waye MARYAMAH ba har lokacin hakama Bata sanar dashi dalilinta na barin gidaba da yankewar alaqarta da mahaifiyarsa ba har abada.

Amincewa dashi da Tai kawai yasashi Jin wani babban nauyi ya saukar Masa daga zuciyarsa Dan Haka bazai takurataba zaibita ahankali ya samu damar gani da Kuma Jin inda MARYAMAH take sbd itace zai fara janyewa daga rayuwar tadawo hannunsa ta hakan yasan Mamin zata dawo hannunsa itama sbd matuqar ba dawowa sukai hannunsaba bazai taba samun kwanciyar hankali da wannan rayuwar dasuke cikiba,
Fatansa ma ya kansace da gaske MARYAMAH din aure takeyi baa mata wannan mummunan shedan da akewa Maminsa wadda kome zaa ce akanta bazai taba kaucewa ko gudintaba duk da asalinsa ya kasance Mai tsanani kaucewa da gujewa qazantacciyar rayuwa ko qazantaccin mutane,

Amma gashi ayau Allah Yana jarabtarsa ta wanna hanyar.

Sai bayan sallar asuba Haj Zainab ta tashi ta nufi sama Dan gabatar da sallan,

Shima kasancewar Babu masallaci a kusa yasashi yin alwala yayi sallah taredasu malam Rabiu da dayan security dinsu dayake musulmi a harabar gidan harma da Uncle Lulu Wanda Dama tare suke sallah da Taju kullum asuba.

Suna idarwa gari yafara haske AQEEL yayi magana sosai da Uncle Lulu Wanda shima Bai fada Masa wacece MARYAMAH ba kawai dai ya bude Masa zance sosai na sanadin barin Zainab din gida da shariarta da ummansa harma da zamanta gidan yari kusan so biyu ko ukuma.

Sosai hankalinsa ya tashi ya girgiza da duka zantukan da kusan yakejinsu Kamar a mafarki.

Palon yakoma jikinsa a mace Dan kuwa sai yanzu yakejin kunya da takaicin Kansa daya takurawa Mamin harsaida ya tado Mata da quncin data Jima da dannewa da rufewa cikin ranta...

Shigowarsa palon yayi daidai da saukowar AMAL Idon Nera daga sama,

Sanye take da fararen kayan baccin Riga da wando masu tsantsi..

Bata lura dashi ba kamar yanda Bai lura da ita dinba wayarsa zai dauka ya bar gidan sbd Kansa dake sarawa da maganganun dayaji.

Itace tafara ganinsa
Cikin mamaki Mai tsananin gaske da tsoro tace,

"Ya Salam,
Meyake faruwa Anan??

Juyowa yayi Jin muryarta data sauka kunnensa kamar ta Maminsa a dah,

Fararen idanuwansa dasuka na sauya sbd rashin bacci da damuwa da ciwon
Ya zuba Mata gabaki daya Ya kalli fuskarta datake fresh sbd tashinta kenan daga bacci..

Dauke idanuwansa yayi daga kanta sbd aqidarsa ta rashin kallo
Musamman ita da kayanta kusan koyaushe hakan suke.

Juyawa yayi zai wuce saiya dakata cak tareda juyowa da muryarsa Mai taushi da nutsuwa yace,

"You are??????

Wani kallo Tai Masa tana mamakin shi din waye dazai shigo har ciki bayan ba kowa mommyn ke shigowa dashiba..

Rashin amsarta yasa ya juya zai wuce kamar daga sama yaji itama Kai tsaye cikin muryarta Mai rashin hayaniya tace,

"AMAL IDON NERA......

Cak ya dakata daga fitar dayake dap dayi...

Bai juyoba baikuma tafiba Saida yagama juya muryarta cikin Ransa dake Masa sautin muryar Maminsa..

Kenan dai itama Yar Maminsa ce...

Wucewa yayi batareda ya juyoba.

Yana fitowa harabar gidan malam Rabiu da zuwa lokacin yagama saddakarwa tunda gasu da kwana gidan IDON NERA ya taso ya bude Masa kofar mota sukai ribas suka fice daga gidan.

Suna fita abin mamaki abin mamaki saiga wasu Yan jarida biyu suna bin motarsu da hotuna.

Gudu malam Rabiu ya qarawa motar suna barin ikeji din.

Gida suka nufa Kai tsaye,

Yana fitowa motar ko qarasawa sashen ummansa baiyiba ya nufi bangarensa.

Bilkees dake zaune a babban palon tana jiran isowarsa
Yana shigowa ta miqe tsaye tana kallonsa cikin tsananin mamaki da tashin hankali..

Kallo daya yayi Mata ya nufi hanyar palonsa zuwa bedroom dinsa..

Binsa tayi Abaya tana cewa,

"Tafiya kayine baka sanar Mana ba??
Ina kaje harda kwana Haka?
Tunda safe naje wancan gidan baka can Kuma Babu alamar acan ka kwana?
Please kace wani Abu man.....

Dakatawa yayi daga zare kaya dayakeyi ya juyo ahankali ya kalleta cikin rashin son daga hankali yace,

"Calm down please Bilkees
Meye ne? Ba gani nadawo ba,
Banajin Dadi Ina buqatan nutsuwa kaina na ciwo,
Idan na nutsu Zan sanar dake koma okay???

Rungumesa tayi ahankali tana gyada Kai da cewa,

"To please kada ka sake irin hakan
Banyi bacci ba yau,
Inata tunanin inda kake,
Kuma dai zaka fadamun kace???

Gyada Mata kai yayi ahankali tareda Dan shafa fuskarta yakai soft lips dinsa yayi kissing kumatunta.

Zarewa yayi ya nufi toilet.

Yau baiyi workout ba sbd ba gidan ya kwana ba Dan Haka brush da wankan ruwan zafi yai ya fito ya shirya cikin White fendis ya kwanta sbd Yana buqatan baccin dazai warware Kansa.

Bayan yakwanta ficewa Bilkees tayi ta nufi kitchen ta bawa masu aiki umarnin kalar abincin dazasu dafa ta wuce gurin ummansa takai Mata labarin bayajin Dadi ne ya kwanta shiyasa Bai shigoba gaidata.

***AMAL kasa hakura tayi ta tsare mommynsu da tambayar waye wannan din,

Yanke zancen Tai da cewar wani 'danta ne datake kauna tun lokacinda tana Reno Ana biyanta da abinci kafin tasamu aikin Yi.

Abin mamaki Amal kuwa sai gashi da daddare yasake zuwa gidan nasu,

Dinner ta musamman akai a gidan dominsa Wanda yasa Mamakin AMAL qaruwa akansa.

Sanyeda white hoodie Balenciaga yazo Wanda suka maidasa kamar sabon matashin saurayi,

Fari ne shi sosai shiyasa duk kayansa kusan kaloli masu duhu ne Haka yake saka abinsa,

Tunda yashigo palon qamshinsa ya doke duka qamshin turarukansu,

Kwarjininsa yasa Shi kansa uncle Lulu basa girma yakeyi sbd daman manyane abokansa kamar yanda akace yaro da kudi abokin manya,

Uncle Lulu yafisu sanin waye AQEEL ASAD din shida yake Shiga manyan sosai yasan yanda suke da AQEEL ASAD tunda kudi sungama shiya Masa girma da matsayi.

Saida kowa ya zauna cin abincin AMAL ta sauko sanyeda doguwar Riga Mara hannu kamar yanda ta Saba saka abinta.

Qamshinsa ne yasata kasa basarwa ta dago ta kalli gurinda yake zaune ya gama gauraya musu koina da qamshinsa.

Isowarta Bata saka ya juyo ya kalli gefenta ba sbd Haka Allah yayisa,

Itama Bata damu da sake sanin meyasa yasake zuwa gidanba ta zauna suka fara cin abincin.

Uncle Lulu ne kawai ke magana sai mommyn wadda take kallon yanda yakecin abincin cikin nutsuwa da kwanciyar hankali..

Sama sama Amal taci abincin ta miqe tabar gurin sbd bazata iya Bata lokacinta gurin ganin yanda uncle Lulu da mommyn keyiwa baqon ba.

Tana tashi Anty Fareedah ma tagama ta tashi shima goge bakinsa yayi da tissue ya tashi.

Yau magana yayi sosai da Mamin akan duka abinda yasani gameda barinta gida...

Ya nuna Mata yanason ta dawo garesa Kamar baya..

Kai tsaye ta dakatar dashi da wannan zancen kafin ta Dora Masa sharadin duk ranarda yayi Mata maganar mahaifiyarsa ko komawarta rayuwarsu daga ranar zata sake yanke alaqarta dashi har abada..

Ganin irin bacin Rai dayake cikin maganarta yasashi barin zancen a lokacin Amma Kuma alqawarin daya dauka Yana Nan saiya dawo da ita rayuwarsa itada MARYAMAH.

Tun daga lokacin ya maida gidan IDON NERA gurin zuwansa batareda laakari da sunansa dazai baci ba da mutuncinsa da girmansa,

Aduk zuwansa gidan saiya roki Maminsa MARYAMAH Amma har lokacin taqi sanar Masa inda take,

Bai taba kawo tunanin AMAL ba
Ya yarda da MARYAMAH itace yarta daya da batanan,..

Amal gabaki daya Babu ruwanta da duka zuwan dayake gidan sbd lura da miskilin mutum ne na karshe,

Takasa gane alaqarsa da zuwa gidan koyaushe Amma dai koma menene kamar yanda ta lura da halayyarsa ko kallo biyu baya Mata duk kyau da daukan hankalinta da ake fada,

Shine mutum na farko dayake hulda da gidan IDON NERA Amma Bai taba yimata kallon burgewaba ko bayyana shaawar aurenta.
Chapter 42 · 0% Book details