← Book details Idon Naira Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 100

Sashe 23

Idon Naira Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Meya hadata da zuwa kotu Kuma?

Lauyanta takira shine yayi Mata bayani Kai tsaye cewar wani Dan daudu da karuwarsa aka Kama shine akan rikicin gida tace ke Yar uwartace mahaifinku daya.

Kusan yanke jiki Haj Maryamah tayi zata Fadi Saida tayi saurin zaunawa tana Jan numfashinta dake sarkewa.

Bata taba tunanin kowa sai zainab,
Haka Bata taba tunanin zainab zata zaba wannan rayuwar ta sabon Allah ba akan ta bawa umma yarta..

Umma takira muryarta ko fita batayi sosai sbd azabar da zuciyarta keyi Mata,.
Cikin ciwo da baqin ciki Mai tsanani tayiwa umma bayanin komai.

Umma ma kasa cewa komai tayi sai data Gama zaunar da zancen cikin zuciyarta tace"

Rayuwar da zainab din ta zaba kenan akan ta bamu yarta ko????
Tunda ta zaba bariki Allah ya kyauta,
'yar tata ma saita tashi da rayuwar datafi wadda take tunanin zamu Bari tayi anan ta lalacewa...

Idan ta lalata mutuncinta da sunanta to meyasa zatayi kokarin lalata Miki mutunci da suna ta hanyar cewa ta sanki?
Taje tayi rayuwarta Ina ruwanki aciki da zaa nema zubarda mutuncinki Dana familyn Mahaifin Aqeel harma Dana mijinki ayanxu Dan dukkaninsu sai mutuncinsu ya tabu idan sunanki ya bayyana a kotu.

Babban bacin Rai da tashin hankali suka shiga daga Haj Maryamah din har umma Dan kuwa yanda dangin mahaifin Aqeel suke neman hanyar cin mutuncinta suna Jin abinda zai faru zasu tarar Mata gabaki dayansu.

Umma kuwa ta tsinewa zainab yafi so ashirin tana aibatata da 'yarta akan wannan abin,
Ita Haj Maryamah baqin ciki da damuwa ya hanata tunanin komai qarshe a gadon asibiti taqare.

Kwanciyarta asibitin yasa aka daga zaman kotun Amma dai daga baya haka aka juya lamarin lauyanta yakai takarda kotu cewar Haj Maryamah batada alaqar komai da zainab rashin lafiya bazai barta tazo kotun ba.

Dayake kotun kusan dai qaramace sai aka karanto bayanin sako daga Haj Maryamah tace batada alaqa da zainab da Lulu.

Tunda zainab take Bata taba mutuwar tsaye da mamakin Haj Maryamah ba da umma sai wannan karon,

Kasa motsi tayi sbd lamarin ya Gama shallake tunaninta,
Hawaye takeson Yi Amma takasa zuciyarta nauyi da bushewa takeyi.

Suna umma ta bada wato mahaifiyar Haj Maryamah din a gabanta aka Kira  umma itama ta fada abinda haj Maryamah din tafada tareda qarin cewar 'yar malam din ce Amma su basuda alaqa da ita,

A taqaice batai bayanin gamsashsheba
Dama jira kawai akeyi a tozartasu akan zalinci sai kawai aka yanke hukuncin komawa dasu gidan yari su Gama zaman hukuncinsu na batawa ds da Haj Maryamah suna idan sun fito zaa bawa zainab nata kason haqqin gadon Wanda Haj Maryamah ce zata Bata kudin gidan gabaki daya tunda sun bada ne ayi masallaci basuma tsaya sun bincika ko anyi dinba gashinan Mai anguwa ya Saida ya cinye kudin.

Lulu yayi baqin ciki da Dana sani matuqa na daga zancen sbd halin dayaga zainab din tashiga na wani irin quntataccen baqin ciki da nauyin zuciya,

Gabaki daya ta Dena gane komai bayan daskarewa da zuciyarta tayi Bata iya tunanin komai...

***Wata daya sukai cif suka fito gidan yarin,

Rungume 'yarta tayi cikeda kauna da kunci da baqin ciki da damuwa,
Tabbas a yanzu taga wani bangare na rayuwa Mai matuqar wuyar koya....

Siddi tayiwa godiya da ido sbd magana ma ayanxu wuya take Mata sbd shock daya Gama sakar da rayuwarta.

Sidda ta kula da MARYAMAH sosai tamkar 'yarta hakama Koda yaushe itace take ziyartarsu gidan yarin har suka fito.

Tunda suka dawo Shi Kansa Lulu sai rayuwarsa tayi sanyi Dan Jin kamar shine ya lalatawa zainab Yar sauran rayuwar tata da nufinln nema mata 'yanci..

Kokarin nemawa zainab din wani gurin zama can wata anguwar daban yayi sbd taje tayi rayuwarta mai kyau itada 'yarta.

Ranarda suka samu wani qaramin gida Mai daki daya da Palo qarami sai bandaki da kicin..

Kudinsa bai cikaba Dan haka Dole suka hakura suka dawo gida,

Kulawa da kaunarda Bata taba samu daga jinintaba Lulu yake Basu itada MARYAMAH,
Dukkanin kokarinsa yanzu akansu yakeyi sbd yakasa daukewa Kansa shine sanadin quncinta a yanzu Wanda yafi na baya,

Ta bangare daya har cikin Ransa kaunarta yakeyi a matsayin Yar uwa jininsa sbd mahaifiyarsa.

Ita kanta tasan bayan Mijinta da Aqeel to Lulu ne mutum na uku dayake kaunarta fiyeda komai Kuma yake shirye dayayi komai da inganta rayuwarta data 'yarta.

Fafutikan nema kudi Lulu yafara sbd hadawa a kamawa zainab din can tabar Nan sbd gabaki daya Takoma Kamar dutse batada walwala da komai,
Tunda suka fito gidan yarin rayuwarta ta canja Takoma kamar me ciwo,
Ita kanta MARYAMAH yanzu agurin siddi tafi zama sbd zainab din bayan tunanin babu abinda take a rayuwa yanzu.

Lulu na cikin wannan Fadi tashin neman kudin Samar Mata gurin zama barayi suka shiga gidan DS suka kashe Mai gadinsa tareda yiwa 'yarsa daya fyade suka ko sata basuyuba suka gudu.

Babu tunanin komai akaiwa Lulu mummunan sharri akan da saka hannunsa a lamarin,

Ds da Kansa ya bada tabbacin Lulu ne kawai zai iya yimasa hakan
Sbd fyaden kanwarsa yasa anyiwa shima tasa yar
Kuma a ranar da abin zai faru kowa ya shaida fadan maigadin gidan DS da Lulu akan taron da Lulu yayi da jamaarsa har kofar gidan ds din mutanensa ne.
##MAMUH#
#IDON NERA
#AQEEL ASAD
#LOVE/MARRIAGE

*_ZAFAFA BIYAR_*

*RUMBUN K'AYA*🔥
Hafsat Rano

*DAUDAR GORA*🔥
Billyn Abdul

*IDON NERA*🔥
Mamuhgee

*A RUBUCE TAKE*🔥
Safiya huguma

*KI KULANI*🔥
Miss xoxo

Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200

ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN

0022419171
Maryam sani
Access bank

Shedarka ta 09033181070

MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*Thanks for choosing us*🔥*_Arewabooks@Mamuhgee_*
18
Tunda Lulu yake baa taba Masa zargi ko sharri Mai girma da munin wannan ba,
Kisa da fyade fa ake magana....

Innalillahi wainna ilayhi rajiun""" shine abinda zainab da siddi suke nanatawa cikin mafi girman tashin hankali lokacinda akayiwa Lulu mummunan kamu.

Gabaki daya jamaar anguwa kowa da abinda yake tofawa lamarin wasu alkhairi wasu sharri da mugun kalami.

Zainab ce da siddi suka fara yawon neman mafita Amma babu sai wahala da qara gurbacewa da lamarin keyi.

Tun lamarin na wasa harya girmama Dole suka nema lawyer da taimakon wani saurayin siddi..anan suka fara kashe kudi sbd case din babba ne sosai tunda kisa ake magana.

Zainab Bata ankaraba ta samu kanta dumu dumi a wani bangare na ruyuwa irin wannan ta kaida kawon cikin maza nagari da Bata gari,

Lulu shine Dan uwanta daya da bazata iya gani cikin wannan halin ba Dan haka itada siddi suka Dage dan ganin sun taimakesa alokacinda yakeda buqatan hakan.

Tun Ana iya ganin lulun har andena barinsu ganinsa,

Sannu ahankali komai da siddi ta mallaka yaqare Daman ita zainab batada komai sai nauyin restaurant din lulun daya dawo kanta sbd kallon uwa daya uba daya da ake musu ita dashi,

Tun suna iyawa harsunkai basa iyawa haka aka Saida restaurant dinsa da komai suka bada kudin Dan a fiddo lulun Amma babu sauki.

Komai na Lulu Saida aka Saida suka bada kudin Amma babu wani sauki sai agurin ubangiji.

Ds suka koma gurinsa roko da neman alfarmar akan case din.

Da farko kin kulasu yayi sbd tsanar dayayi a gansa da karuwai sbd tsoron abinda zai taba mutuncinsa da siyasarsa.

Daga baya Kuma dasuka ci gaba da roko da magiya akoda yaushe saiya nuna raayinsa akan zainab..

Kai tsaye ta sanar dashi ita din ba karuwa bace sbd kadama su batawa juna lokaci,

Siddi ce ta miqa Masa kanta a maimakon zainab din yayi abinda zaiyi da ita qarshe yaqi Yi musu abinda yace din saima kamasu daya saka Yan hisbah sukai akan suna bibiyarsa da mummunan dabiarsu akan ya asaki Dan uwansu...

Yayi musu hakan ne da a kamasu su ta yanda babu Mai sake kokarin tada maganar Lulu.

Hisbah ta kamasu tareda kaisu gidan gyara Hali na tsawon sati uku kafin aka sakosu,..zuwa wannan lokacin Lulu anriga an yanke Masa hukuncin zama gidan yari har ankaisa da hakan aka rufe case din.

Bayan fitowarsu wata muguwar qaddarar ta samesu ta bayyanar ciki a jikin siddi Wanda yake tabbas na DS ne,

Sun shiga tashin hankali da damuwa sbd siddi tai duk yanda zatayi cikin yaqi fita sai zainab tace ta hakura tabarshi tunda hakan Allah ya qaddaro.

Rayuwar zainab da sunanta sun Jima da lalacewa daga ranarda ta saka kafarta a anguwar,

Kowa da sunan karuwa yake kiranta Wanda ita masifar datake ciki Bata barinta Jin zafi ko takaicin sunan,

Babu ta yanda zata iya wanke kanta sbd ba yarda zaayiba,
Wayema ya damu da mutuncinta da zata tsaya wanke kanta..

Rayuwarta data MARYAMAH ta sauya
Babban burinta shine fitowar Lulu da saukar siddi data koma yau lafiya gobe ciwo,

A ayanxu da siddi Takoma cikin duk ya Gama lalatar da rayuwarta sbd tsananin ciwo da laulayi kala kala
Zainab itace take dawainiyarsu,

Itace take karban kudin hayar kowane daki na gidan da karuwan ciki ke biya,

Itace take sanaar Saida kayan planning da siddi keyi a gidan harma da wasu abubuwa da karuwan gidan ke siya komai ya dawo kanta
Duk tabi ta qara hargitsewa,

Siddi ta rayuwarta ta koma abin tausayi gabaki daya sbd cikin yazo da matsala sosai...

Zagi da zunde tareda bacin suna babu wanda baa musu akan ita ta Haifa shegiyar da baasan ubataba,
Lulu ankamasa sbd yayi fyade da kisa,
Siddi Kuma tayi shege lafiya ta gagareta.

Zainab dakejin irin wannan zagin da cin fuskar Bata damuwa sbd abinda yake gabansu yafi qarfin tsayawa biyewa zagin mutane.

Cikin siddi Yana fita wata takwas tafara zubar jini
Tun Yana zuwa kadan kadan daga Baya yafara zuwa da yawa
Hankalinsu ya tashi suka nufi asibiti.

Zuwansu asibiti yasa yanayin tsanananta nan hankalin Zainab ya tashi ta rasa was zata nema,
Wa zata tinkara.

Jikin siddi tsanani yayi kuwa qarshe dai ta haifi 'ya mace itama saidai take ta rasu bayan haihuwar tata.
Chapter 23 · 0% Book details