← Book details Idon Naira Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 100

Sashe 38

Idon Naira Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Umma ta basa tabbaci da rantsuwar cewa da kanta Dan raayinta tabar gida,

Data bar gidan meyasa Bata tafi kota tsaya inda idan yadawo zai sametaba,

Tasan cewan rayuwarsa gabaki daya ta sauya Babu farin ciki aciki daga ranarda ya dawo ya samu bata ba MARYAMAH¿

Duka tsawon wannan lokacin rashinsu,
Da rashin sanin halinda suke ciki shine qunci da farin cikin daya rasa a rayuwarsa duk da Yana tareda mahaifiyarsa da matarsa da 'yarsa Amma farin ciki yakasa walwala a rayuwarsa,

Su din amanarsace,
Su din haqqine dayayi alqawarin ya ratayawa Kansa bayan baba malam sanda dinsa daya rataya masa amanarsu,

Ta Ina? Tayaya zai kalli tsakiyar Idon Maminsa da ake Kira da shahara a wannan rayuwar Mai muni da radadin fada a Baki.

Amma koma menene a yanzu tabbacin itadin Maminsa ce yakeso sbd bayyanarsu garesa shine mafi girman nutsuwa da farin cikin dazai samu.

***Da safe qarfe Tara ya fito a shirye qamshinsa Mai Dadi da sanyi Yana tashi.

Cikin kulawa Bilkees ta riqo hannunsa tana cewa,

"Daddyn mufeeda please kayi breakfast kafin ka fita.

Da kallonta yayi Yana kokarin kunna wayarsa data kwana kashe..

Bayason tauye haqqin kowa duk uzurinsa kuwa Dan Haka ya juya suka nufi dining atare tana sake shige Masa da tambayar Allah yasa lafiya yayi dare jiyan Bai dawo da wuri ba.

Bai amsa wanna tambayar ba Dan Dama tasan bayason tambaya da Basu shafekaba.

Black tea da ships yaci sai dafaffen kwai daya ya goge bakinsa da tissue ya miqe Yana cemata bye.

Kafin ya Isa kofa mufeeda ta fito daga bedroom dinta sanye cikin Riga da wando na bacci masu Dan kauri ta qaraso gurinsa tana cewa,

"Good morning Daddy.
Ka tashi lfy??

Cikin kulawa da kauna ya kalleta tareda sake fuskarsa dake kashe jikin Matan dasuke mutuwa akansa harma da matarsa wadda akoda yaushe zai fita zuciyarta saitayi Mata Dan wani qaiqayi.

"Morning mufeeda Aqeel,
Kin tashi lfy?

Lafiya kalau,
Daddy fita zakayi tun yanzu?
Kaman lokutan futarka basuyiba.

Dan gajeran murmushi ya saki Yana wucewa yace,

"Akwai wani abun Mai mahummanci ne sosai..

Ki wuce school in time,
Banda rough driving..ok???

Ok daddy, take care,
Allah yabaka saar koma menene wannan Mai mahummanci.

Dakatawa yayi sbd sanyi da dadin adduar nata,
Ahankali ya waiwayo ya kalleta cikin nutsuwa da Dan sakewar fuska yace, "Amin" ahankali kafin ya juya ya wuce.

Bangaren ummansa ya nufa wadda take zaune kan dining an jere dining din da kayan breakfast da abinci.,

Doguwar free Kuwait Riga ce ajikinta ash data Dan fiddo kyanta da farar fatarta saidai fuskarta na Dan bayyanarda damuwa da rashin farin cikin datake ciki a yau din sakamakon rashin zuwan AQEEL ASAD gareta jiya kafin shigewarsa a karo na farko duk tsawon shekarun Nan dasukai a tare gida daya ahali daya.

Shigowarsa yasata kallonsa dakyau tana qarewa fuskarsa dake nuni da Bai wani samu dogon hutuba a jiyan..

Tasowa tayi daga dining din ta dawo palon ta zauna batareda ta kallesaba ta amsa gaisuwarsa Kai tsaye ta Dora da cewa,

"AQEEL akwai damuwa ne ko matsala?
You don't look ok kwata kwata?

Kallonta yayi tareda Dan kokarin dawo da yanayinsa daidai cikin nutsuwa yace,

"Stress na aikine kawai Amma inshallah zanyi kokarin taqaitawa.

Sake kallonsa tayi dakyau tana kasa karantar yanayinsa,

Ace 'danta datayi renon cikinsa wata Tara ajikinta ta haifesa Amma batada kusanci,shakuwa ko sanin halayyarsa da dabiunsa sosai,

Zainab ta cuceta,
Taci Amanar rayuwarta,
Ta lalata Mata rayuwa gabaki daya sbd 'danta shine rayuwarta Kuma gashinan ta rabata dashi,

Yana tareda ita a gabanta Amma Kuma Kamar da gangar jikinsa kawai suke tare..

Ya Allah yayi Mata sakayya akan abinda Zainab tayi Mata,

Har abada Allah kada Allah yasa AQEEL din yasake ganin zainab sbd ma rayuwarta Tintini ta Dade da zama abar qyama da gudu,

Dan Haka zuwa yanzu tasan duk inda Zainab din take tagama gurbata da lalacewa a waccar muguwar qazamar rayuwar data zabarwa kanta da 'yarta harma da abinda ta Haifa ta hanyar a shekarun bayan.

Sallama yayi Mata ya fice Kai tsaye motar dazai fita da ita ya nufa inda Mal Rabiu ke tsaye Yana jiransa,

Yana qarasowa ya bude Masa motar ya shige.

Tada motar malam Rabiu yayi suka fice daga harabar gidan da aka bude musu babban gate din.
##MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR_*

*RUMBUN K'AYA*🔥
Hafsat Rano

*DAUDAR GORA*🔥
Billyn Abdul

*IDON NERA*🔥
Mamuhgee

*A RUBUCE TAKE*🔥
Safiya huguma

*KI KULANI*🔥
Miss xoxo

Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200

ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN

0022419171
Maryam sani
Access bank

Shedarka ta 09033181070

MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*Thanks for choosing us*🔥*_Arewabooks@Mamuhgee_*
28
Lauyanta ne a gaba kafin ita da uncle Lulu a baya suka shiga..

Gurinda za zasu zauna aka nuna musu suka zauna gefe daya tareda lauyyinsu,

Ajiye Hermes handbag dinta tayi a gefenta tareda fuskantar jamaar dake babban offishin taron.,

Kai tsaye ta gaidasu gajerar gaisuwa batareda ta tsaya qare musu kalloba ta maida hankalinta gurin sauraron bayanan da aka fara korowa na munanan Lefuka da barnar da akeda tabbacin tana aikatawa kuma ake aikatawa a qarqashinta..

Batason Jan zance da batawa juna da zaman sulhun lokaci Dan Haka Kai tsaye Babu boyo ko shakka ta zayyano abubuwan da ake aikatawa da sunanta wainda tasan batada alaqa ko hulda dasu ko bayanansu Bata kawoba sbd Bama yarda zaayiba dan Haka atafi ahakan..

Lauyanta ne ya karba zancen da fara bada hakuri dakuma godiyar yarda da sulhun da akai,

Kallon Haj Zainab din yayi wadda itama ta dago lokacin zatayi magana idanuwanta suka sauka akan Fuskar data sakata sarqewa da yawun bakin da zatayi magana dashi...

Tari Mai qarfi ne ya rufeta hannuwanta na daukan rawa a hankali..

Cikin kulawa da mamakin abinda ya sametan uncle Lulu ya kalleta Yana Dan tasowa da bayansa dake jingine jikin kujerar dayake kai ahankali yace,

"Yar uwa Yaya dai?
Are you ok??

Kasa magana tayi sbd tsananin da tarin ya qara sosai
Take idanuwanta suka fara ja ta dafe kirjinta tanayi..

Da sauri Barr Salahudeen ya leqa waje yace Salis yakawo Mata ruwa da sauri...

Ko awane masifaffen Hali take na dimuwa ko ciwo ko hauka
Bazata taba kasa gane AQEEL ASADULLAH ba,
Kamai girma da manyanta da zaiyi da sauyawar da zaiyi kuwa bzata taba kasa ganesaba..

To Amma meya kawo hardashi a wannan zaman?

Koma menene batada alaqa ko wani hadi dasu Dan Haka Babu amfanin tabari ya ganta,..

Rawa zuciyarta da jikinta ke dauka tareda wani irin sanyi na shekaru data Dade batajiba,

Rintse idanuwanta tayi cikin wani irin nauyi da zuciyarta ke sauka Mai qarfi,

Bata so ko buqatan sake kallonsa a yanda takeji zuciyarta na bubbugawa da da sauri da karfi.....

Tsanananta tarinta yayi Wanda ya Hadu da bugun zuciyarta dayake qarfi da sauri....take tafara neman fita hayyacinta.

Da sauri uncle Lulu ya Kamata suka miqe sbd Dole zaman ya wargaje sbd gabaki daya ta fara fita hayyacinta idanuwanta tini sukai jajir hannuwanta sai rawa sukeyi.

Kai tsaye aka miqawa lauyoyinta bayanan matsayar zancen da aka Kai Wanda akaso karantawa gaban kowa a zaman Wanda take nuqatar saka hannun amincewa Dan Haka tunda zaman ya lalace sbd zuwan tsautsayin sai aka bawa lauyoyinta daga baya ta karanta su saka hannu itada Lulu lauyyinsu su dawo dashi a miqa kotun shikenan.

AQEEL ASAD Wanda ya kasa dagowa ya kallesu sbd ba halayyarsa bace yawan kallon bare Kuma ga mace irin wannan dayaji Ana fada,

Yanada kiyaye ganinsa akan abubuwan da kallonsu zasu damu Kansa da zuciyarsa shiyasa duk abinda yasan baida mahummanci kokuma zai taba Masa nutsuwar Kansa baya kalla sbd kaucewa damuwa da ciwon kai.

Koda IDON NERA tayi nata bayanin kwata kwata Bai dagoba hakama jinsa ba sosai yake akantaba...

Miqewa sukai Lulu na gefenta Barr Salahudeen na dayan gefen da handbag dinta a hannunsa sai sannu suke jera Mata tana dafe da kirjinta dake zafi da nauyi matuqar gaske kamar zai fado...

Tana gap da kaiwa kofar ficewa data matsu tabar dakin sbd suffocating takeji....

"MAMI"

Taji Nutsatsiyar muryarsa ta sauka akan kunnuwan duka Wanda yake dakin..

Babu Wanda yajuya ya kallesa sbd tunanin waya yakeyi
Itakuma datasan menene Bata juyoba ta wucewarta Kai tsaye batareda ta nuna alamar Jin sunan ba..

Motarta ta nufa har lokacin hannuwanta da kirjinta rawa sukeyi Kuma tarin ya sarqi makoshinta sosai ta yanda ko magana Bazata iyaba.

Kasa yarda da idanuwansa yayi alokacinda ya dago yaga matar da batada bambamcin kamanni da Maminsa,

Baisan lokacinda bakinsa ya furta kalmar Mamin ba,
To Amma meyasa ta dakata alokacinda ya Kira sunan kafin daga baya ta wucewarta Bata juyoba....

Miqewa yayi da sauri ya nufi kofar yabi bayanta da sauri Kansa na daukan wani irin zafi da juyawa,

Yana gap da Ida jikin motarta Yana kallo tace aja motar awuce.

Maminah ce wannan da gaske?
Maminah ce nake gani?
Am i hallucinating?

Dafe Kansa yayi daya Wani irin sarawa Yana sake daukan zafi...

Morarsa ya nufa kai tsaye da drivernsa harya bude Masa.

Yana Shiga cikin wata shaqaqqiyar murya yace,

"Muje office yanzu Nan.

Jan motar Rabiu driver yayi cikin Dan speed sbd ganin yanda Mai gidan nasa yake kamar a zafafe.

Wayarsa ya daga ya saka Kiran PA dinsa Kuma na hannun damarsa Al-Amin tajudden.

Al-Amin na daukan wayar Kai tsaye yace,

"Ina son bayanan komai da hoton Idon Nera yanzu Nan..

Ok done Sir" Al-Amin din yace Yana janyo Apple tab dinsa dake gefensa yafara dubawa kafin ya saka Kiran Wanda zai Basu sauran bayanan komai da bazai samu a internet ba.

AQEEL ASAD da yagama fita gabaki daya tinaninsa akan lamarin dayake kamar kyaftawar ido a mafarki ace yaga Maminsa,

Maminsa fa yake tunanin yagani...

Shi gabaki daya bayama kawo a matsayin datake din idanma mamin tasa ce,
Sam zancen wata karuwa ko karuwai ya fita Kansa shidai fata da buqatan sanin itace 'dince kokuwa.
Chapter 38 · 0% Book details