← Book details Idon Naira Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 100

Sashe 77

Idon Naira Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin lafiyayyan love yayi Making da ita a dakin Mai nutsuwa da gigitarwa,
Duk yanda takai ga tsoro da firgita Saida ta Dan shagala da yanayin ta manta da a gidanda suke Saida suka Gama ta Ankara da hakan ta kasa juyowa ta kallesa hankalinsa kwance yayi bacci abinsa cikin nutsuwa ajikinta.

Tsoro da fargaban zuwa wani dakin yasata kasa baccin ita gashi takasa tadashi shima Dan Haka ta zame jikinta ahankali tareda janyo towel dinta dake qasa yashe ta daura ta nufi kofar bedroom din nata ta saka key tadawo ya nufi toilet ta sakarwa kanta ruwa tana rintse idanuwanta da tinanin meyake faruwa a rayuwarta ne?

Wanka tayo ta fito daureda wani towel din daban tayi drying gashinta ta shafa mai tareda turarikanta ta saka doguwar Abaya milk ta daura qaramin silk scarf na Versace akanta tayi sallah kafin ta bude dakin ta sake saka key ta waje ta zare key din ta sauko qasa har lokacin Babu Wanda ya dawo a gidan ta nufi kitchen takai gurinsa suka Sha kankana ta samu kanta da dauko ruwa Takoma saman dasu.

Tana shiga ta nufi kujera ta zauna tana kiran su Siddi Dan taji lokacinda zasu dawo gidan.

Bayansu mommynta takira itama tace Mata da yamma kaman yanda su siddin sukace.

Dan boyayyan numfashi ta sauke tana sake Satan kallon kan gadonta tana adduar yatashi kan lokaci ya tafi kafin yamman sbd Shi ko mommy samunsa tayi a gidan ta tabbarda Babu abinda zaiji ita kuwa kila har mutuwa saita kusa Yi sbd kunya da rashin abin fada.

Sai laasar ya farka cikin sanyi ya bude idanuwansa ya kalleta itama bacci ya dauketa a kwance kan kujera tana gadin ya tashi Kuma tana gadin kofar dakinta da Wanda zaiyi knocking.

Lumshe idanuwansa yayi Yana kallon innocent face dinta datake qyallin Zamanta cikakkiyar mace ayanzu.

Addua yayi ahankali cikin Ransa kafin ya tashi zaune ya ziro qafafunsa qasa ya sauko gadon ahankali,

Cikin nutsuwa ya Isa inda take ya durqusa ya dauketa ya maidata kan gadon ya rufeta tareda juyawa ya shiga toilet dinta Yana kallon yanda komai na yan Mata masu aji 'yayan gata suke buqata akwai toilet din a jera kana shiga kasan toilet din Mata ne.

Sabon brush ya fasa cikin wainda baa fasaba yayi brush kafin yayi wanka da ruwan dumi ya fito da towel dinta da Bai gama rufesaba ya goge jikinsa ya shirya cikin kayansa dasuka Gama Dan yamutsawa Sosai.

Yana Gama shiryawa ya juya gurinta ya Isa bakin gadon ya ranqwafo yayi kissing goshinta ya juya yadauki wayarsa batareda shakka ko gudun kada wani yaga fitowarsaba yabude key din data saka ya fice daga dakin ya sauko ya fice Dan har lokacin gidan tsit basu dawoba
Balkisu Kuma Daman idan ba ganin fitowarsa tayiba bazata iya dogon motsiba.

Yana fitowa harabar gidan yakira malam Rabiu da shima yasha baccin Rana dakin Securities din gidan bayan Bilkisu takawo musu abincinsu sunci sun koshi da kyau.

Malam Rabiu da sauri ya shigo ya taho ya bude Masa mota Yana Satan kallon kayansa dasuka Gama fita hayyacinsu sbd squeezing.

Jan motar yayi suka bar gidan Kai tsaye yace a nufi gidan karatunsa.

Suna Isa ya nufi ciki ya sauya kayansa zuwa wani tsadaddiyar luxury yadi Mai taushi ya fito Yana zuba qamshi ya nufi masallaci yayi sallar laasar tukuna Suka nufi office da ake jiransa tun safe sbd yana fitowa gidansa qarfe Sha dayan Rana can gidan ya wuce.

Al-Amin da yayita kiransa baya samu yakira malam Rabiu ya tambayesa inda suke ya fada Masa suna Idon Nera gum yayi Yana satar kallonsa shima Dan kuwa dai Ogan nasa yayi wani Dan fresh yaqara kwarjini da kyau.

Baqin dake jiransa ya qarasa office dinsa Yana musu barka da zuwa a natse kaman ba Wanda ya gamo komaiba a fuske a kame yake.

***Itama sai lokacinda su Siddi Suka dawo ta farka ta tashi tana duba dakin da idanuwanta Bata gansaba,

Saukowa gadon tayi ta dauki wayarta zata duba time taga sakonsa na cewan ya wuce ta tashi lfy.

Ajiyar zuciya ta sauke ahankali jikinta dayayi Mata tsami Yana sakewa,
toilet ta nufa tayo alwala tayi sallar laasar da Bata samu yiba.

Tana gamawa ta sauko ta samesu a Palo ta zauna tasa Bilkisu ta kawo Mata abincinta anan tanaci suna fira Siddi na tsokanarta ta rage fita sbd bazata taba iya kallon AQEEL ASAD ta tambaya izininsa ta gwammaci zaman gidan.

Shiru kawai tayi musu batace komaiba akan zancen Jin Anty Fareedah na cewa ita mamakin wannan auren nasu ma takeyi ace ko juna basa kalla kamar ma ya Manta da yanada Mata a gidan nasu Dan mommy kawai yake zuwa gidan sbd ita.

Har lokacin dai Bata iya cewa komaiba shiru tayi tana cin abincinta jikinta ba wani qwari sosai.

Suna palon su mommy suka dawo tareda Fahat da Suka biya suka dauko daga makaranta Anty Fareedah ta tashi ya nufi sashenta gurin Mijinta.

Fahat kuwa kan Amal ya fada da qarfi Yana Bata labarin wani wasan da sukayi a school.

Cikin kulawa ta gyara Masa zama tana cewa,

Sweetheart idan kana mun wannan dirar ballani zakayi fa.

Dariya yayi yana cewa,

"Anty Amal kin rage karfima keda kike dagani da kanki.

Murmushi kawai tayi tana cewa,

"Ko yanzu Dan nadawo school na gaji ne shiyasa Amma ai Idan na sake Zan iya daga ka.

Mommy Bata tsayaba sama ta wuce Dan a matuqar gajiye take Dan gaskia saima ta kwana biyu bata fita koina ba tana buqatan hutawa.

Da daddare Bai zo gidanba text yai Mata sbd Idan yazo zaa iya samun akasi.,
Itama Jin nutsuwa da rashin zuwan nasa tayi sbd tsoron abinda zai iya Yi din.

Washe gari qarfe goma ta fita school
Can ta wuni sai yamma sosai ta dawo

Bata tsaya komaiba Saida tayi wanka da sallah ta fito sukaci abinci tareda Anty Fareedah da itama lokacin ta dawo Suna gamawa Suka nufi sashen Anty Fareedah gabaki dayansu Banda mommyn.

Suna can sashen har dare batama San yazo gurin mommy ba harya wuce saidai taga txt dinsa
Ba qaramin Dadi tajiba da Bai sameta acan din ba.

Washe gari ma Bata fita school ba gurin gyaran Kai dasu qafa da dai sauransu dasuka zaba zuwa itadasu Anty Fareedah din da Siddi zasu,.

Tun safe take juye juyen yanda zatayi fitar sbd batason Ahmed yazo din Dan da motocinsu suka Saba fitar kokuma motar daya daga cikinsu.

Qarfe goma Sha daya Ahmed yazo sbd Shi kansa ya riqe time table dinta yasan lokacin zuwa a kowace Rana.

Yana kiranta a waya sai tace Masa kawai ya tafi yau bazata school ba akwai inda zasu tafi.

Yana barin gidan ya maida motar gidan karatu ya dawo gate ya zauna tareda securities sbd Shi aikinsa natane kawai idan batada gurin zuwa shi a ranar baida aikin komai.

Samun kanta tayi da Yi Masa txt din fitar tana turawa ta kashe wayarta gabaki daya Dan batama son Jin yace kada ta fitan.

Shiryawa sukayi qarfe biyu suka fitawarsu Haj Zainab bama ta saniba tana can sama tana bacci Dan ba qaramar gajiya take fama da itaba kwanakin.

Yawonsu dasuka Dade basuyiba a tare kaman yanda Suka Saba shi Suka Sha kafin suka Isa Beauty Box spa.

Suna gurin har yamma kafin suka Gama suka fito kowaccensu an gyarata Amal harda kanta ta gyara sbd ruwa data saka Masa kwana biyun kaman ya Dan Dama kan.

Suna gurin Mommy ta Kira Siddi akan Ahmed yazo Yana neman Amal wayarta Bata Shiga Kuma.

Fada Mata inda suke siddi tayi tana cewa Amal din tana taredasu.

Kallon Bilkisu tayi tace,

"jeki kice Masa tana beauty box spa taredasu Siddi.

Bilkisu na zuwa ta fada Masa yaja motar Ya nufi inda tace din Yana duba map da zata kaisa gurin.

Yana Isa yaga motar Anty Fareedah ya gane motar gidan IDON NERA din ce Dan Haka yayi parking a gefe Yana jiran fitowarsu tunda wayarta a kashe take Kuma maigidansa yace yaje ya dauketa ya maidata gida.

Yana gurin har yamma AQEEL ASAD yakirasa yana tambayarsa koya dauketa din,

Fada Masa yayi Yana gurin Yana jiran fitowarsu.

Address din yace a tura Masa take Ahmed ya tura Masa.

Kusan awa daya da Gama wayarsu saiga AQEEL ASAD din ya iso gurin ya kalli malam Rabiu yace yakoma waccan motar ya karba yamaida gida shikuma Ahmed yadawo wannan din.

Malam Rabiu na barin gurin da waccar motar suna fitowa kowaccensu na cikin shigar alfarma Mara takura.

Ita doguwan rigar wani plain lace Mara nauyi da tsada ne ajikinta sai mayafinta Dan Mara girma sosai kaman yanda ta Saba.

Tana ganin motar ta kalleta cikin mamaki kafin tasake kalla Ahmed ya fito cikin Bata girma Yana Mata barka da fitowa.

Kasa magana tayi lokacinda ta hango waye Acikin motar ta juya ta kalli Siddi dake cewa school Zaki shigane da yamman Nan? Batareda sun lura da waye a motar ba.

Anty Fareedah ma ita take kallo tana jiran amsarta.

Rasa abin fada tayi Kuma bazataso su gansaba gashi idan ta fuske tace Ahmed ya tafi kawai tasan fitowa zaiyi ya jata koya dauketa gabansu Anty Fareedah din.

Dan sanyayyan numfashi ta sauke tana Dan basarwa ahankali tace,

"Eh zan biya school din Ahmed zai kaini ku wuce din.

Mota Suka shige Anty Fareedah na cewa,

Ki kula to.

Siddi ma cemata tayi take care Suka wuce sukabar gurin.

Saida ta sauke Ajiyar zuciya a boye Mai zafi bayan wucewarsu ta Dan juyo takalli Ahmed daya bude Mata mota kafin tashiga ahankali batareda ta juyo ta kallesaba.

Rufewa Ahmed yai ya zagaya yashiga motar ya tada suka bar gurin.

Suna tafiya ahankali Babu Mai magana Dan tunda tashigo motar yake waya ahankali cikin rashin daga hankali bare murya komai nasa a natse.

Hanyar dataga sun dauka ne yasata juyowa ta kallesa da idanuwanta da take Suka fara narkewa
shikuma har lokacin wayarsa yakeyi da wani abokin aikinsa dake Europe.
##MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR_*

*RUMBUN K'AYA*🔥
Hafsat Rano

*DAUDAR GORA*🔥
Billyn Abdul

*IDON NERA*🔥
Mamuhgee

*A RUBUCE TAKE*🔥
Safiya huguma

*KI KULANI*🔥
Miss xoxo

Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200

ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN

0022419171
Maryam sani
Access bank

Shedarka ta 09033181070
Chapter 77 · 0% Book details