← Book details Idon Naira Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 100

Sashe 48

Idon Naira Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Hafiz kaje babban police station ka daukomin motar Yan Sanda suzo gidan IDON NERA kame zasuyi Ana can Ana dambe da fashe fashen Kaya..

Mufeeda kuwa Yan jarida ta boye number ta Kira itama ta turasu gidan tana cewa,

"Su umman zanga yanda zaayi sulhun yanzu idan kota Ina mutuncinsu da sunansu ya bayyana a gidan IDON NERA tareda sanin alaqarsu da ita da basason asani.

Hafiz ne ya Kira yabata tabbacin an isarda sakonta kowane time police zasu Isa gidan.

Burki taci a zafafe tareda yin ribas tayi kwana ya juya Dan kuwa yau so take a gaban idonta sunan kowa ya baci ayi barnar da zaayi zumunci da alaqar taqarasa yankewa kowa ya koma rayuwar data fi masa IDON NERA tayi nesa da Mijinta babu ruwanta da ita din Maminsa ce
Karuwa tasanta
Kuma ahakan zataci gaba kallonta.

*****Amal kallon mommynta tayi wadda idanuwanta suka sauya da qunci da baqin cikin dake kwance cikin ranta na shekaru,

Riqo hannunta tayi tana matsawa jikinta tace,

"Mommy Allah ya Dade da kawar da baqin ciki rayuwarki tareda duk wani qunci,
Karki damu da tsayawa sakawa kanki damuwar wahalan wasu,
Kece Haj Zainab Idon Nera bakya buqatan daukan reni ko wulaqancin kowa..
Koma su din su waye a rayuwarki na tabbatarda basuda mahummanci tunda Kika rufe shafinsu arayuwarki.......

Wannan da kike magana cikin rashin girmamawa sbd rashin tarbiyarki da rayuwar da kuka taso ita din yayar uwarkice uba daya,
Jini daya ne yake yawo ajikinsu
Saidai ita Bata Mai tsafta Bai gurbata da kowane jinin qazantaba..

Ita din jinin mommyna ce naji
Kefa waye ce?
Jininta ce?

Cikin nutsuwa Haj zainab ta katse Amal din da cewa,

"Amal ya isa, shekarunta sun wuce amsa duka maganganinki,
Kije ciki
Sungama tafiya zasuyi ai tunda sun Gama.

"Zainab kin nuna tsintacciyar mage Bata mage,
Kin nuna har abada halak daban take da Haram,
Yau nice Kika tsaya gabana kikaci mutuncina da 'yarki,
Kin nuna Mana babancin tarbiyar titi zuriar titi wadda takeda dogon Nisan banbanci da tamu rayuwar Dan Haka ki saka aranki ki ajiye
AQEEL har abada rayuwarsa ta wuce qanqantar rabar inda wannan rayuwar taki takeba,

Me kikeso?
Me Maryamah tayi Miki Bayan alkhairi da Zaki saka Mata da wannan muguwar sakayyar?
Meyasa Kika zabi rabata da 'danta?
Baga taki 'yar ba anbarki da itaba a gabanki idanma Mara tsarkin ce idanma Mai tsarkin ce.

Zuciyar haj Maryamah data kasa daukan komai ce ta fara dauke wuta tana neman kasa bugawa...

Juyawa tayi ta nufi kofa tana cewa,

"Umma bazan iya qara ko second dayaba anan
Bazan iya shaqar numfashin gidan Nan ba
Zanje nayi da Wanda nakeda iko akansa idan nice na haifesa to zai zaba tsakanin ni da Idon Nera da qazantarta.
##MAMUH#*_Arewabooks@Mamuhgee_*
36
Kofa ta nufa Kai tsaye idanuwanta basa gani sosai sbd zuciyarta kowanne lokaci bugawa zata iya yi,

Ita kanta umma zuciyarta bugawan take neman Yi tana kokarin dannewa,
Hawan jininta kuwa tanaji yarigada ya hau Amma bazasu iya bayyanarda rauni ko tashin hankalinsu agaban Zainab ba da 'yarta,

Dukkaninsu Babu Mai gani suka tinkari kofa suka fice Babu Mai sassauci a zuci...

Haj Maryamah ce agaba umman na bayanta qafa ba qwari,

Motarsu suke kokarin nufa kawai ba tsammani aka fara daukansu hotuna Ana jeho musu tambayoyin dasuka kusan sumar da Haj Maryamah datayi mutuwar tsaye cikin mummunan tashin hankalin da Bata taba shigaba,

Umma tsabar firgici rudewa Tai tana neman faduwa cikin tashin hankali.

Innalillahi wainna ilayhi rajiun
Innalillahi wainna ilayhi rajiun
Meye Haka?
Me Zainab take nufi da hakan?
Tozarci mafi Muni ne tasa ayi musu¿

Innalillahi wainna ilayhi rajiun"
Kasa magana Haj Maryamah Tai sbd numfashinta dake kokarin daukewa tana kokarin kamosa Amma lamarin yafi qarfin abinda zuciyarta zata dauka,..

Isowar Bilkees ne tareda motar Yan Sanda yasa kallo komawa kansu Ana sake daukan hotunan da rahoto
Yau dai ga Yan Sanda mota guda a gidan IDON NERA
Hakama ga familyn AQEEL ASAD a gidan,uwarsa da matarsa da 'yarsa,
Kenan dai ga gaske akwai alaqa a tsakaninsa da IDON NERA...

Isowar Lulu a guje da mota yasa Yan sandan dakatawa daga waje suna jiran isowarsa Dan kuwa basu dauka gidan IDON NERA dinne da gaskeba sukazo.

Babu Bata lokaci kallonsu kawai yayi yacewa Barr Salahudeen yaji da matsalar,

Ciki yayi da sauri Yana mamakin abinda yake faruwa..

Bilkees kuwa haukace take cewa Yan sandan su shiga su Kama Idon Nera sbd itada yarta sun Zaga iyaye Mijinta tareda cin zarafinsu...

Umma Bata taba jin ta tsani hada zuria da Mai sunama Bilkees ba bare wannan datake gabanta ayanzu,

Allah ya tsinewa wannan Bilkees da Allah yayota mahaukaciya,

Wannan 'ya anyi mahaukaciyar asararra,

Wayace takira Yan Sanda da jarida,
Su tayiwa mummunan tonan asiri da tozatawa ba Idon Nera ba,

Yau tayi musu abindama yafi Wanda akayo musu daga ciki batareda kowa yasaniba,

Yau balkees taja musu abin kunyar dasukai ta gujewa shekara da shekaru na boye alaqarsu da Zainab Idon Nera da basa kaunar Koda Wasa wani yasan alaqarsu da ita.

Haj Maryamah kasa dago Kai tayi Saidai taji muryar AQEEL ASAD akanta Yana Kiran sunanta ahankali cikin kulawa da damuwa Mai tsanani....

Daga hakan ta Dena Jin komai sai numfashinta dake gizga Yana neman daukewa take ta yanke jiki ta Fadi...

Bilkees da batasan ta Ina AQEEL ASAD ya sauka ya bullo ba sai ganinsa sukayi a gabansu sumewa takusan Yi tsabar firgita da tashin hankali Sabo,

Mufeeda hannu ta Dora akai tana neman kurma ihu Amma takasa,

Umma dataga 'yarta a jikin AQEEL Rai hannun Allah itama sarewa kafafunta ke neman Yi Saida uncle Lulu ya riqota aka sakasu mota da gudu akai asibiti dasu.

Securities ne suka Kori Yan media daga gurin wainda suka kwasa wasunsu suka bi asibitin da aka nufa da cika rahoton nasu tunda ga Mai gayyar Nan ya iso daidai lokacinda sukaso.

Bilkees da mufeeda Securities ne suka fidda su a gidan bayan umarnin da Amal ta Basu cikin takaici da mamakin hauka dake yawo a familyn AQEEL ASAD din.

Haj Zainab kuwa sama ta koma ta rufe kanta Dan tana buqatan kadaicewa kanta ya warware,

Yau sun sosa Mata wani tsohon fami dake zuciyarta,
Sun goga ciwon data Jima da rufewa a ranta,
Meyasa zasu dawo rayuwarta Bayan ta Jima da binnesu a tata rayuwar?

Meyasa komai yakeson ya dawo baya rayuwar kowannensu ta lalace ya baci Bayan kowa ya samu Kansa a rayuwar daya zaba?

Ayau Amal tafara sanin komai na rayuwar baya to idan siddi tasani hartasan itace wadda suke Mata cin Fuskar ta Haifa a titi
Yaya zatai?
Tayaya zata iya sanar da siddi ita wacece,
Mahaifinta shine Wanda tafara aura Acikin aure aurenta
Tama Yaya zata cewa siddin ba itace ta haifetaba mahaifiyarta karuwa ce data haifeta sanadiyar komai daya faru.

Duk wannan akan dawowar AQEEL rayuwarta ne,
Tana rayuwa da 'yayanta Amma komai na neman juyewa lokaci daya akansa,
Itace masifar rayuwarsu dasuke fada kokuwa sune masifar tata rayuwar,

Tabbas kasancewarsu ahali daya ba alkhairi bane garesu su dukan Dan Haka akaro na biyu itama ta zabi yanke alaqar kowa yayi rayuwarsa Babu ko inuwar Tina akwai wata alaqar tazama tarihi..

Kamar yanda mahaifinsa suka fada Dole a yanke alaqa Babu abinda zaiyi saura tsakaninta dasu,
AQEEL daga wannan lokacin ta yafesa idan har sunanta Idon Nera to tabbas ta yanke alaqa dashi.

****Amal data Gama sauraron tarihin uwarta a gurin uncle Lulu Bata taba Jin akwai abinda ta tsanaba a duniya kamar sunan daya kasance asalin sunanta itama,

Jajir fararen idanuwanta sukai tanajin hawaye na taso mata Amma tana dannewa sbd idan ta zubda hawatenta akai kamar sunyi nasarar sakata kukane da Mugayen halayensu,

Jin takeyi ta tsani jinin dayake yawo ajikin mommynta Yana yawo jikin Haj Maryamah,

Sunan AQEEL ASAD ma Jin takeyi Yana yankar zuciyarta datakeda taushi da sanyi,

Shine Sila asalin matsalar rayuwar mahaifiyarta,
Me yakeyi a rayuwarsu haryanxu da bazai barsuba,
Mahaifiyarta batada alaqa dashi kamar yanda batada alaqa da tsohuwa umma
Mahaifiyarsa ce jinin tata mahaifiyar Kuma sunja layi sun yanka jinin to meya rage tsakaninsa da mommynta??

Sungama sakawa mahaifiyarta ciwo da quncin zuciya,
Duk Wanda ya sake zuwa gidansu da niyar cin mutuncin mommynta to tabbas zata nuna musu banbancin tarbiyan karuwa dasuke fada.

Mommynta ta sama har daki Bata iya cewa komaiba sai qarasawa datayi ta rungumeta cikin tsananin so da kaunarta tareda tausayinta,

Ahankali hawaye masu zafi suka gangaro idanuwan Haj Zainab din tana rintse idanuwanta dasuke ja tin dazu.

Zubar hawaten mommyn Amal taji a kafadarta, ta rintse idanuwanta tanajin radadin hawayen mahaifiyarta har cikin zuciyarta...

Raunin datake dannewa itama a zuciyarta ya bayyana sbd Jin 'yar uwarta datake tsananin so Siddi ba uwarsu dayaba,
Qaddarace ta Samar da ita,
Meye laifin siddin Dana mommyn da ake kokarin aibatasu akan hakan,

Yaya 'yar uwarta Siddi zatai alokacinda zatasan mommynta datake tsananin so ba itace ta haifetaba..

Ahankali zuciyarta ta karye tafara wani irin kukan tausayin mommynsu da Siddi..

Ita kanta Haj Zainab din kuka takeyi ahankali Wanda yake Sosa zuciyarta,

Kuka wani abune data manta yanda akeyinsa Bayan shekarun sai yanxu,
'yarta AMAL Bata taba kuka ba tun girmanta bayan na ciwo Wanda takeyi duk wata Amma yau bayyanar AQEEL da iyayensa rayuwarta Yana neman dawo da qunci da kuka arayuwar datasha wahala kafin ta ginata.

Uncle Lulu dayake Jin kukansu har cikin Ransa Jin yayi shima alaqar AQEEL ASAD da Haj Zainab ta fita ransa
Gwara su ciresa rayuwarsu tun kafin komai ya lalacewa kowa harsu har shi din da familynsa.

Asibiti kuwa Ana Isa aka karbi Haj Maryamah cikin gaggawa Dan kamar heart attack ne tasamu.,

Umma ma Dole aka shiga da ita Dan dubata Dan ita jininta mugun Hawa yayi.

Bilkees ma miqa kanta tayi a dubata Dan kwakwalwarta ta tabbatarda tana rawar Dena aiki,

IDON NERA ta zama masifar rayuwarsu a taqaice,
IDON NERA ajalinsu zatayi daya Bayan daya kenan,
Wadda ta haifi Idon Nera ta haifo musu masifa da balain rayuwarsu
Hadda ita da batajina Bata ganiba batasan anyiba Amma masifar ta shafeta dumu dumu.

Securities aka Aiko Masa asibitin sbd Yan media da aketa fama dasu asibitin gashi Kansa ya dauki wani irin zafin dabai taba daukaba,
Chapter 48 · 0% Book details