← Book details Idon Naira Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 100

Sashe 67

Idon Naira Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Miqewa Bilkisu tayi ganinsa
Cikin girmamawa ta gaidasa tareda sulalewa tafice daga palon.

Dauke kanta tayi daga bangarensa taci gaba da cin abincinta ahankali cikin nutsuwa tana Hana kanta sake waiwayowa.

Ahankali ya qaraso ya durkuso kadan ba zato yayi kissing kumatunta tareda furta Mata Saida safe ya juya ya fice sbd Idan yayi Wasa zai iya raba dare a gidan baisaniba.

Harya fice Bata dagoba Bata Dena cin abincinta ba.

Dawowar Bilkisu ce ta tabbatar Mata daya bar gidan gabaki daya Dan Haka tana gamawa batai wani doguwar firaba ta shige ta kwanta.

Washe gari Kiran Ahmed tayi qarfe goma ya iso Suka wuce makaranta.

Acan ta wuni sai yamma sosai ta dawo
Shima ranar wani irin busy ya zama Dan Haka Bai samu zuwa gidanba saida daddare bayan harta kwanta yashiga har dakinta yayi kissing goshinta tana jinsa harya fice tukuna bacci ya dauketa.

Washe gari ma Haka ta wuni makaranta sbd zaman gida Babu Dadi tunda Babu kowa,

Haka ta ringa rayuwar kadaici agidan Babu kowa shiyasa take wuni makaranta sai yamma ta dawo,

Shima ayyukane masu zafi suka Sha Kansa shiyasa iyakacinsa yazo da safe yaganta kokuma da daddare,

Su Haj Maryamah kuwa ganin sun nuna Masa tuba da sallamawa akan komai Yana nuna Mata kauna da kulawa fiyeda kowane lokaci Dan tausayinta yakeji yanda ta Hana kanta sukuni,
Ita kanta umma Cameroon yanzu ne suke gane Masa sai suka gano masifar wani lokaci batayi,

Da wannan Haj Maryamah ta ringa lafewa yau ciwo go lafiya ta ringa cinye lokacinsa tana hanasa zuwa gidan Zainab batareda ma sunsan Bata qasar ba.

Ita kanta Bilkisu ganin yanda yake da iyayensa sun shirya sosai taga hankalinsu kaman ya kwanta saita hau murya Dan kuwa tasan warwarewarsa dasu Zainab ne kawai zaisa su umman su sake Haka Dan Haka itama saita kwantar da hankalinta ta ringa zuba Masa iyayi da kissa kala kala duk da Bai dawo yanda yake a baya da itaba sbd zuciyarsa dake shakkar kishinta ysata fidda zancen nan Amma dai duk da hakan lafiya kalau suke zamansu Babu tauyewa ko wani dogon sauyin.

Sanin ya Saba zuwa duk dare yasa yanzu tasamu kanta da Bata shigewa sa wuri bacci saiyazo sbd batason Yana shiga dakinta Dan Bilkisu dake iya gani karta fadawa mommy kosu Anty Fareedah da Siddi ayi tinanin wani abin.

Yana wucewa take Shigewa ta kwanta Kuma har wannan lokacin magana dai bata hadata dashi Dan haryanxu Bata karbi auren nasaba.

Satinsu Haj Zainab biyi da kwanaki suka dawo
Tayi farin ciki da murnan dawowarsu sbd Ba'a taba tafiya batareda Babu dayansuba acikinsu sai a wannan karon Kuma Suma sunyi kewarta.

Ranar dasuka dawo baizoba sbd tafiyar Rana daya dashima yayi.

Jikin mommynta ta lafe tana zuba Mata shagwaban barinta dasukai.

Ita kanta Haj Zainab din daqyar tayi kwanakin sbd tunanin yanda Amal din take rayuwa ita kadai duk basa Nan gashi AQEEL dinma yayi tafiya alokacin tasan ba lallai yasamu time din zuwa dubatab.

Washe gari qarfe goma ta ajiye siddi airport ta wuce Abuja gidanta
Suna ajiyeta Ahmed ya juya da ita zuwa school.

Da wuri ta dawo yau din Dan Haka tan yin wanka ta fito sukaci abinci a dining atareda Anty Fareedah da itama ta fita sai alokacin tadawo.

Suna gamawa gurin mommy suka dawo suka zauna suna fira.

Da daddare kowannensu ya halarta a dining zasuci abinci Banda ita sai gashi ya shigo a natse sanyeda fararen hoodie Balenciaga sweater da wandonsu.

Kyansa da sauran kuruciyarsa ne suka bayyana sosai qamshinsa yana tashi ahankali.

Cikin farin cikin ganinsa Haj Zainab ta tarbesa tareda jansa Suka nufi dining Daman Bai samu yaci dinner ba sbd ayyukan da sai ayau yasamu sakinsu ya sallama.

Anty Fareedah ma gaidasa tayi cikin sakewar fuska da girmamawa,
Hannu ya miqawa uncle Lulu suka gaisa kafin ya zauna gefen Maminsa data ja Masa kujeran da kanta.

Haj Zainab ta zuba Masa abincin da kanta kafin ta zauna.

Amal ce ta sauko sanyeda farar chiffon blouse da skinny jeans blue sai qaramar hula akanta da wayarta a hannunta.

Bata Ankara dashiba Saida tazo zata zauna taji qamshinsa agurin ahankali ta dago Kai tana dubawa idonta ya Shiga nasa.

Satar kallon Mommy da uncle Lulu tayi taga hankalinsu na kan abincinsu Dan Haka ta zauna ahankali tanaqin kallon inda yake.

Abincin sukeci ahankali Wanda kowa yayi tsit sbd AQEEL dake table din.

Suna kammalawa ita tafara miqewa tabar gurin text yashigo wayarta tana dubawa taga abinda aka rubuto Wanda yasata dakatawa gabanta na faduwa sbd gane Wanda ya turo din.

"Yaya zaayi da goodnight kiss Din Matata yau?

Kasa juyowa tayi sbd mamaki da tsoron kada wani ma ya iya fahimtar meyake faruwa.

Sama take kokarin hayewa wani sakon yashigo.

"Ko a bedroom dinki ne zanzo na Bata sbd na Saba kuma.

Ahankali ta juya ta wuce kitchen sbd tasan Babu abinda zaisa ya shigo kitchen Dan wlh ta gwammaci kwana a kitchen din har sai yabar gidan,

Ko kallonta batason yanayi gabansu mommy bare a dauka wani abin
Sam ta tsana hakan.

Ahankali ya saka hannunsa cikin plate din daya Gama cin abinci ya Dan shafa maiqo ya dago ya kalli Haj Zainab cikin fuskewa yace,

"Mami Ina buqatan wanke hannuna inaga maiqo ya taba.

Miqewa tayi cikin kulawa tana cewa,

"Ohh akawo ruwan anan inaga saika....

No Mami inaga Bari naje kitchen kawai.

Miqewa yayi Yana cewa,

"Zaunawanki zanje da kaina inaga.

Anty Fareedah ce ta taso tana cewa,

"Let me lea.....

Itama katseta yayi cikin nutsuwa da cewa,

"No thanks Zan iya.

Dawowa tayi ta zauna tana cewa ok.

Kitchen din ya nufa a natse ya Shiga.

Tsaye take jingine da fridge tana sake karanta sakonsa wani irin kunya na dabaibayeta ita kadai
Batasan dashiba sai jinsa tayi ya dagata ya Dora ya zaunar kan freezer dake gefen fridge din.

Tsayewa yayi gabanta tareda janyota jikinsa suka hade ya cusa Kansa cikin wuyanta yafara shaqar kamshinta ya lumshe Ido tareda sauke ajiyan zuciya Mai sanyi kafin ya dago Yana kallon fuskarta data sauke idanuwanta taqi kallonsa zuciyarta na bugawa.

Hade fuskarsa yayi da tata ya sakar Mata numfashinsa Mai dumi a kan fuska kafin ya goga Mata hancinsa ya bude Baki ahankali yace,

"Gudowa kikayi Nan boyo kokuma godowa Nan kikayi dan nasameki??

Dago Idanuwanta tayi ta kallesa batasan lokacinda ta bude nata bakinba itama ahankali tace,

"Waya nazo Yi anan.

Yana kallon bakinta ya zira hannunsa daya ya zare wayar dake hannunta ahankali ya saka cikin aljihunsa Yana cewa,

"Kodai numberna kike kokarin haddacewa??

Dukansa tayi a kirji da sauri tana neman Bata fuska da abinda ya fada din...zatayi magana ya Dora bakinsa akan nata tareda kamo harshenta Yana tsotsa..

Shiru kitchen din ya dauka sbd shaanin dake wakana acikinsa

Bilkisu data kwaso kayan da aka Gama cin abinci dasu a dining ta shigo kitchen din Kai tsaye Bata ankaraba sai data kawo tsakiyar Kitchen din
A rikice ta saki kayan hannunta tana sauke Kai da sauri ta juya zata koma
Amal tayi saurin dirowa da gudu ta riketa tana hanata juyawa.

Anty Fareedah ce tashigo da sauri Jin barin kayan tana shigowa ya fice hankalinsa kwance kaman Babu abinda yake aikatawa.

Yana fitowa Saida safe yayiw Maminsa da uncle Lulu yafice.

Tambaya lafiya Anty Fareedah takeyi tana kallon kayan dake qasan
Amal hade fuska tayi tareda Hana Bilkisu magana ta juya ta fice daga kitchen din itama ta haye sama tana gyara rigarta data juye sosai.

Bilkisu cikin daburcewa tacewa Anty Fareedah Babu komai Bari ne kawai tayi.

Dan fada sama sama anty Fareedah tayi Mata kafin ta juya ta fice.
##MAMUH#

INTRODUCING UNIQUE AND AFFORDABLE PART-TIME DIPLOMA AND DEGREE PROGRAMMES IN HEALTH RELATED COURSES.

The Directorate for Consultancy Services and Continuous Education of the Kazaure School of Health Technology, Kazaure, Jigawa State, Nigeria wishes to inform the general public that it now offers the underlisted Health courses at its Kazaure centre.

DIPLOMA

1. Dental Surgery Technician

2. Medical X- Ray Technician

3. Health Information Technician

4. National Diploma Biomedical Engineering

5. Public Health Technician

6. Junior Community Health Extension Worker (J-CHEW)

7. Community Health Extension Worker (RE-TRAINEE)

DEGREE

1. Health Information Management

2.Public Health

3.English Language

4.Public Administration

5.Business Administration

6. Economics

7. Accounting

8.Computer Science

9.Mass Communication

10.Agricultural Economics

Interested applicants can call the following phone Numbers for the application forms.(WhatsApp) 08035298851, Calls Only 07066542055

*_ZAFAFA BIYAR_*

*RUMBUN K'AYA*🔥
Hafsat Rano

*DAUDAR GORA*🔥
Billyn Abdul

*IDON NERA*🔥
Mamuhgee

*A RUBUCE TAKE*🔥
Safiya huguma

*KI KULANI*🔥
Miss xoxo

Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200

ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN

0022419171
Maryam sani
Access bank

Shedarka ta 09033181070

MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*Thanks for choosing us*🔥*_Arewabooks@Mamuhgee_*
53
Tana Shiga bedroom dinta toilet ta wuce Kai tsaye ta fara wanke fuskarta da ruwan sanyi sbd wani dumi datakeyi Mata na kunya da faduwar gaban ba mommy ko Anty Fareedah bane suka shigo kitchen din alokacin.

Ajiyar zuciya ta sauke tareda janyo qaramin towel tana goge fuskarta ta fito jikinta ba qwari ta nufi kujera ta zauna tareda lalaban wayarta zata duba Abu sai Bata gantaba,

Tashi tayi tana sake dubawa dakin Bata gantaba sai ta nufi kofa ta fito Kai tsaye ta sauko kasa
Su mommyn na Palo zaune suna fira ta wucesu ta nufi kitchen ta duba wayan a inda suka tsaya Amma Bata gantaba.

Bilkisu dake wanke kayan da aka Gama cin abinci dasu tana ganin shogowarta ta fara sinne Kai tana kunyar hada Ido da Amal din sbd mugun ganin datayi musu.

Itama Amal din kunyar kanta da hada Ido da Bilkisun takeyi Dan Haka batareda ta kalletaba tace,

"Bilkisu wayata Bata kitchen dinnan?
Baki gantaba?

"Banganiba Anty Amma ko Zaki Kira da wayata saikiji inda take.

Saka kiran wayar sukai da wayar Bilkisun Amma baa dagaba tanata ringing.

Mamaki ne yakama Amal ta juya tana tunanin inda ta ajiyeta.

Dakinta takoma tana kokarin sake dubawa sai tunaninta ya dawo Akan lokacinda AQEEL din ya zare wayar a hannunta.
Chapter 67 · 0% Book details