← Book details Idon Naira Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 100

Sashe 27

Idon Naira Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai tsaye Siddi ta nacewa momynsu akan aurensa Dole aka samu daqyar takai 300 level akai auren Wanda shima akaci uwar NERA ta watsar da karatun tabi Mijinta sukai Cyprus.

Auren siddi yasa AMAL komawa kamar ita kadaice Yar IDON NERA tunda Takoma ita kadaice 'ya a familyn sai Anty Fareedah da Allah yayi Uncle lulunsu zai haihu.

AMAL lokacinta take bugu dakya yanda ya Kamata sbd irin motocin datake Hawa da sitirar datake duka masu tsada,

Komai nata na musamman ne a rayuwarta,
A tsari take komai nata,

Suna tayi sosai kamar yanda mahaifiyarta tayi,...

Suna ne da ake fassarashi da sunyisa ne sbd suna tareda manya,
Su din yayan uwar karuwai ne,
Su din IDON NERA ne babu abinda suke ganewa fiyeda NERA,

Duk dukiyar da suka Tara Bata isarsu kullum qari suke nema,

Auren mahaifiyarsu baya qirguwa kamar yanda na Yar uwarta Siddi yafara qirguwa Dan kuwa ta rabu da Mijinta ta sake auren wani Wanda yaci ubansa a maiqo...

Dukkaninsu duk wainnan maganganun da ake binsu dasu Bai taba damunsuba sbd sundan daukakarsu ce da sunan dasukai a duniya yazo da hakan...

Shiyasa suke zuba rayuwarsu yanda suke so su taka yanda sukeso babu Wanda ya Isa ya tanka musu...

Zainab da Lulu sunyi rayuwar garari da qunci a garin Lagos kafin zuwansu nan dasuke yanzu,

Sunyi kwanan bola,
Sunyi na gangayen gida,
Sunyi na shaguna,
Sunyi na qarqashin gada,
Sunyi yawo a garin Lagos da Yaya goye a bayansu,
Shi AMAL ita siddi,

Har kamensu antaba Yi Amma baa taimakesuba,
Sunyi kuka atare, sunyi a bacci, sunyi a farke,

Arzikinsu ba a lokaci daya suka yisaba,

Shekaru suka debo masu nauyi da wahala da qunci masu yawa kafin sukayisa Dan Haka basuda daukan Renin dazaisa a iya tozartasu a dare daye ko rana daya komai nasu da yardar Allah sunyi gaba ranakun kuka da damuwa tini suka shude musu
Kuma gashi komai ya wuce yanzu Dan Haka babu wani malami dazai kirasu yayi musu waazi Kai tsaye su fahimcesa....sbd malaman ne yanzu suketa kutsen rayuwarta suna kokarin dawo da ita hanya dan girmamar da bariki tayi ta yayan musulmai hausawa a qarqashinta lamarin yanata ciwa manya malaman addinin dake can tuwo a kwarya...

Anyi kamen,
Anyi nasihar,.anyi baraza Amma babu sauki ko nasara sbd hukumar dake tareda manya,
Manyan Kuma tare suke da Haj Zainab din Dan Haka suketa kokarin ganin ta inda zasu bullowa lamarin Dan Haj Zainab IDON NERA din Koda suke malamai Bata gane yaren nasu tunda basuda nerar dazata bude kanta ta fahimcesu.

Ta bangaren Mata da karuwai da ake magana kuwa bayan maganar Haj Zainab din su kansu basa gane komai..
Duk da kusan karuwai da Matan set set ne wasu duk ta aurar dasu ga manyan mutane sunacan suna rayuwar aurensu hankali kwance cikin aminci shiyasa dai kota Ina tanada connection dinta yanda takeso...
Wannan shine Asalin wacece Haj Zainab IDON NERA da ahalinta datake so da kauna fiyeda komai data mallaka wato,
'yarta jininta AMAL IDON NERA da 'yarta 'daya SIDDI IDON NERA
Sai 'dan uwanta Rabin jikinta LULU IDON NERA da matarsa Fareedah jarma IDON NERA da sabon farin cikin gidan da aka haifo Fahat IDON NERA.
##MAMUH#
#AMAL IDON NERA
#LOVE/MARRIAGE/ROMANCE

*_ZAFAFA BIYAR_*

*RUMBUN K'AYA*🔥
Hafsat Rano

*DAUDAR GORA*🔥
Billyn Abdul

*IDON NERA*🔥
Mamuhgee

*A RUBUCE TAKE*🔥
Safiya huguma

*KI KULANI*🔥
Miss xoxo

Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200

ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN

0022419171
Maryam sani
Access bank

Shedarka ta 09033181070

MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*Thanks for choosing us*🔥*_Arewabooks@Mamuhgee_*
21
AMAL Idon Nera ayanzu datake cikin cikakken lokacinta kaf familyn IDON NERAn tafi suna sbd irin Yanda take rayuwarta a yanda takeso a yanda tayi raayi..

Kuma ayanzu da ita kadaice budurwa a gun momyn kusan duka abokan huldarta manya Neras AMAL din suke ta sakon aura shiyasa kowa ke sakarwa Haj Zainab din kudi,

Uncle Lulu ma ta nasa bangaren akwai masu son auren nata Amma duka AMAL din batada raayin auren a yanzu sukuma su Haj Zainab basa takurawa yayan nasu ko kadan shiyasa Bata takurataba,
Shima uncle Lulu din Bai takura Mata dinba,..Suma masu son auren nata Basu takura dinba sbd ba abune na gaggawa ko daga hankaliba tunda Daman karatu takeyi Dan Haka ko ajikinsu kudaden dasuke sakarwa Haj Zainab din da Lulu Idon Nera.

Siddi a Abuja take da aure Amma kusan duk baya wata biyu tana hanyar Lagos cikin jirgi idan tazo ma takanyi sati biyu,uku koma fiye a gida suna hutawarsu sbd Mijin nata nada Mata kowacce da gidanta ita tana maitama dayar matar tana gwarimpa..

Aurene babu takurawa sukeyi irin na masu kudi da yayan masu kudin,
Bata wani zama sbd batada kowa abujan sai Mijin da danginsa wainda Suma kusan hakan suke basa wani zama Dan Haka take hanyar Lagos kusan ko yaushe
Kuma momynta basa ganin laifinta tunda Mijinta Bai hanataba Dan ba komai bane agunsa.

AMAL na final year dinta a karatunta na Amma har lokacin raayinta Bai sauyaba akan mazan dake shirye da aurenta,

Duk yanda mutanen duniya ke musu kallon musu kallon ahalin Yan bariki karuwai masu lasisi Mai tsada wannan tunanin a iya gurin Yan wahala ne sbd mutanensu na arziki babu abinda ya damesu da wannan zancen basama jinsa sbd iya gurin Yan wahalar mutane ya tsaya zancen sukam duk wani matsayin mutunci Haj Zainab da ahalinta sunkai tunda suma sunada arzikinsu Kuma tanada 'yaya masu daukan hankali dasukeso hakama Koba 'yayanta ba tanada 'yan Mata masu inganci harma da manya Matan masu aji a qarqashinta da zata baka ka aura idan kanaso,

Ga iya business da sanin hanyoyin hada harqallar business tsakanin manya Wanda take qaruwa da hakan sosai Dan Haka su a gurinsu Haj Zainab IDON NERA mutuncinta yafi musu na kowa ma.

SSG Hayat Nasir shin mafi mutuwa a soyayyar Amal IDON NERA,

Ya gama mutuwa tareda wani irin nisa a sonta Wanda kusan da yawan mutane sunsan da hakan,

Matarsa da 'yayansa sun sani,
Yan uwansa da abokansa sun sani hakama media ta sani Dan duk zamansa Mai fada aji to hidima ta Haj Zainab IDON NERA data Amal IDON Nera baya hadata da komai,

Komai zai iya dakatarwa akan hidimar AMAL da haj Zainab...

Ita dukiya kuwa kamar su ya Tarawa Dan iyalansama duk yanda suke Jin Dadi da rayuwa basa wulaqanta dukiyarsa Kamar yanda ahalin IDON NERA keyi,

Uncle Lulu kuwa jinsa yake kamar uban daya haifesa tsabar biyayya da 'barin dayake Masa shima.

Duk wanna abin AMAL Bata taba sonsaba,.
Bata taba Kuma Jin zata so shi dinba,
Shi kadaine yake kidansa yake rawarsa,

Ba tsoho bane bakuma dattijo bane irin matasan da kudi yasa suka zama dattijai ne,
Abokin manya ne,
Kyakkyawane ba laifi gashi yasan sutura Yana dukanta yanda yakamata.

Matarsa da yayansa Idan akwai abinda duniya ta tsana a fada a gabanta ko a mafarkine shine sunan AMAL IDON NERA,

AMAL itace babbar masifar rayuwarta,
Amal itace quncinta,
Itace baqin cikinta,
Itace damuwarta..duk yanda zatayi ta raba Mijinta da zafaffiyar soyayyar AMAL a Ransa tayi ta kasa,

Har rabuwa tayi dashi ta kwashe yayanta tabar qasar gabaki daya akan hakan Amma takasa rabasa da AMAL

abin baqin ciki da haushi da takaici ma shine duk lokacinda zata tunkari AMAL din saita tozartata ta qunso Bata baqin ciki Mai tsanani ta Kuma fada Mata ko so daya Bata raba son Mijinta ba shine yaji zai iya yake nacinta.

*********Kwance take tana bacci cikin bargo iya kanta ne kawai a waje..

Tun baccin bayan sallar asuba ne data koma Bata tashiba gashi kusan karfe goma na safe.

Kofar bedroom din nata aka bude Kai tsaye aka shigo
Dayake baccin yafara sakinta tashi take son Yi Amma Bata tashinba tanajij shogowa dakinta Kai tsaye tasan Siddi ce sbd masu aiki basa shigo Mata daki Kai tsaye.

Ahankali ta bude manyan idanuwanta masu haske dasukai Dan duhu sbd bacci ta zubawa Siddin wadda ta nufi gaban madubinta zata dauki Abu...

Lumshe idanuwanta tayi ahankali tareda yaye bargon datake ciki ta tashi zaune ahankali...

Idanuwanta akan siddin ta ziro qafafuwanta qasa tareda miqewa tsaye kyakkwar surarta ta bayyana..

Cotton fararen kayan bacci ne ajikinta Riga da wando na Asceno ko hula babu akanta sai safa Qarama a qafarta....

Fresh take koina jikinta na bayyanarda hutu da kafiyar dayake da ita..

Daga inda take tsaye ta bude baki cikin muryarta Mai tafiye Kai tattare da class tace,

"Siddi,me yasa kullum idan kina gidan Nan kece kike tashi na¿??
Ke ko knocking bazakiyiba kike shigomun Kai tsaye...me zakimun gurin Kuma???

Washe Baki siddin Tai batareda ta juyoba tana cigaba da duba key din motar AMAL din tace,

"Zan fita da motanki ne sbd mommy ta fita tunda safe da nata,
Uncle ma ya fita Anty Fareedah ma ta tafi aiki na nata nakin shine a qasa sai dayar motar mommy na duba koina Banga key din ba nakira wayar a kashe may be tana wani gurin ma mahummanci...

Qarasowa AMAL tayi ta gurin tana cewa"

Inada gurin zuwa Nima kije ki shirya Zan ajeki inda Zaki na tafi idan nadawo Zan tsaya na daukeki kokuma Idan kingama ki Kira Sharif yaje ya daukoki Yana gurin gyara da dayar motan wani ya buga mun ita jiya a makaranta.

Juyowa siddi tayi tana kallonta tace,

"Asibiti fa zanje inason confirming ne kaman inada ciki...

Dakatawa Amal tayi tana kallon siddin cikin Dan mamaki da takaita farin cikinta sbd ba yau suka Saba jiran cikinba Amma yaqi samuwa...

Kin tabbata kinajin alaman ciki Siddi???

Ina tunanin hakan Amma dai sai abinda asibitin suka gano...

Ki shirya Zamuje asibitin tare muga likitan.""Amal ta fada hakan tana ajiye key din data karba hannun siddin ta nufi toilet na bedroom din nata.

Tubewa tayi tareda jefa kayan data cire a qaramin laundry basket bag din dake toilet din.

Brush tayi kafin tayo wanka ta fito tana qamshin asalin original makari bath gel.
Chapter 27 · 0% Book details