Sashe 84
Idon Naira Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
janye nata tana kallonsu Anty Fareedah da hankalinsu ke kan zancen dasukeyi na wani kayan da zasu siya a waya. Gurin mommy da uncle ta maida kallonta sukuma magana sukeyi dashi bilhaqqi batareda sun lura da idanuwansa na kanta ba. Sake kallonsa tayi ganin kallon nasa kusan ya banbanta dana koyaushe..Wani tunani ne yashigeta na ko Dr tayo tayi magana dashi take gabanta yay wani irin mummunan faduwa jikinta ya dauki rawa a boye tasake kallonsa taga irin kallon dayake binta dashi idan Bata bar gurinba zai iya tasowa ya dawo gurinta agaban kowa Dan Haka ta janye Fahat daga jikinta ahankali tareda miqewa tsaye tana gin sake kallon gefensa ta daga gafafu a sanyaye cikin toro da fargaba ta nufi stairs zata Haye.. "MARYAMAH" ya ambaci sunanta cikin wata irin nutsuwa hankali kwance Wanda fadan sunan yasa dukkaninsu kowa ya juvo Yana kallonsa sbd Babu Wanda ya taba kiranta da sunan sun ma manta da ance sunan nata na asali MARYAMAH ne Dan har lokacin Hai Zainab Bata fadar sunan a bakinta Koda na wanine daban ta yafe fadarsa. Ita kanta cak ta tsaya bugun zuciyarta na wata irin tsananta take idanuwanta suka ciko hawaye matugar ya bude Baki yayi maganar data danganci abinda take boyewa to zata iya yanke jiki agurin tsabar tashin hankali da mummunar kunyar duniya.Fatanta da adduarta a lokacin shine ya kasance baiyi magana da Dr tayo ba Dan kuwa tsabar tashin hankalin data Shiga yasa ta manta Bata fadawa Dr tayo din karta sanar da kowaba. •Ha Zainab kallonsa tayi lokacinda ya dawo da fararen idanuwansa dasukai wani irin sanyi akanta Yana kallonta Kai tsaye yace, "Amal zataje gain likitan da nay alqawarin zataje akan matsalarta, Ta shirya gobe da safe zamu wuce Zan kaita da kaina... Daga Hai Zainab harsu siddi da Anty Fareedah da uncle Lulu kallonsa sukai Ita kanta Amal din juyowa tayi ta kallesa cikin yanayi biyu sod tariga ta saddakar maganar cikin jikinta zaiyi saikuma taji wanna zancen Wanda shima ta tabbatarda idan akaje duk likitan da zata gani take zai tabbatar da cewa akwai ciki ajikinta.•Hai Zainab kuwa Dadi da akasinsa ne tareda mamakin Yaya Amal zataje taga likita Babu kowa atareda ita saishi Kuma bawani sabo ko magana sukeyi da junaba babu yanda tafiyar zata yiyu a hakan Dole saidai idan ta shirya ta bisu kokuma Fareedah ko Siddi. Magana zatayi uncle ya dakatar da ita da cewa, "Amal dawo zo. •juyowa tayi ahankali jikinta na sake mutuwa da wannan abubuwan wani bayan wani datake shiga, Shikuma uncle ko ya taba ganinsu ne kila shiyasa shima yace tadawo. Innalillahi wanna ilayhi rajiun" tafada cikin ranta hannuwanta na rawa ta saci kallon AQEEL dayake kallonta Kansa tsaye da alamar yariga yagama magana takuma sani tafiyar Nan sai Allah idan baayita ba Amma itama batason zuwa koina yanzu ta cikin jikinta take tukuna. ##MAMUH# * ZAFAFA BIYAR **_Arewabooks@Mamuhgee_* 65 Kasa qarasowa sosai tayi tsakiyar palon ta tsaya daga gefenda su Anty Fareedah suke tana Dan sauke kanta qasa,abinda yasake bawa kowa mamaki kenan ganin kanta a qasa Abinda Basu taba ganiba kenan,