Sashe 1
Idon Naira Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*_IDON NAIRA_*
_Mamuhgee_
*_ZAFAFA BIYAR 2023🔥_*
1
_Bismillahir rahmannirRaheem_
_*Uba daya ne ya haifesu, yabasu tarbiya daya,kauna daya,matsayi daya..*_
*_Qaddara ta bambamta rayuwarsa ga bangarora guda Kashi biyu Wato haske da duhu,_*
_*haske da duhu shine qaddarar data zama tazara a rayuwarsu har suke tsananin qyamatar junansu,*_
*_qaddararsu ta gangaro har kan 'yayansu Wanda suke tamkar black and white maana baqi da fari suma gurin bambamci fiyema da iyayen nasu,_*
*_kaman yanda haj Maryam ta fada har abada babu alaqa ko kusancin dazai hada zuri'arta tsarkakka mara najasa da daudar zina da zuriar Yar uwarta dasuka kasance gewaye cikeda daudar rayuwa mara kyau da amfani ta karuwanci.._*
*_Labarin IDON NERA kenan Wanda yazo cikin wani qayataccen salo da sabon tsari tareda nutsatsiyar kauna da soyayya kaman yanda muka saba wannan karon salon na musamman ne._*
_ALLAH YABAMU IKON GAMAWA LAFIYA KAMAN YANDA ZAMU FARA LFY.Amin_
**************
Daga kwancen da ta ke bisa kan gadon ɗakin baccinta, ta kai hannu ta shafa cikinta ɗan watanni bakwai zuwa takwas, tana jin tarin ƙauna da soyayyar cikin na sake huda zuciyarta.
Sai dai a duk lokacin da ta tuna irin zaman da ta ke yi da uwargidan mijinta da kuma ƴarsa, sai ta ji wani tsoro na shigarta na yadda za ta haifi ɗa ko ƴa su rayu irin kalar rayuwar da ta ke yi a cikin gidan.
Wata iriyar rayuwa me sanya kewa da ƙunci wanda ba a taɓa ɗaga ido anyi mata duba na sassauci, bare har ta sanya rai watarana za a ƙaunaceta ko abinda za ta haifa ba.
Basu taɓa faɗa da juna ko musayar kalamai a tsakaninta da kishiyarta ko ƴar kishiyar ba, sai dai irin zaman shariya da wofintar da ita da suke yi a cikin gidan, ta gwammace ace faɗa su ke yi kullum ko banza a ce suna musayar kalamai marasa daɗi a tsakanin junansu.
Amma zaman da ta ke yi dasu zama ne na ba ruwan wani da wani a cikinsu, idan sun haɗu sai dai su kalli juna kawai, don ko ta kwantar da kai ta gaida abokiyar zamanta, ba za ta taɓa tada kai ta dubeta ba bare ta sanya ran za ta amsa mata gaisuwarta,
Kazalika Maryamah wacce ke amsa matsayin ƴar mijinta tilo da ta zo ta tadda a gidan budurwa me kimanin shekaru sha bakwai a duniya, wacce ta fi uwarta nuna mata zafin kishi da tsana tamkar ita ce kishiyarta ba uwarta ba,
Maryamah nada kishin abinda takeso take Kuma ganin nata ne,
Kaunar datakewa mahaifinta yasa takejin kishin aurensa sbd zai Haifa wasu yayan ya hada da ita,
A duniya abinda tafi tsana shine 'yan ubanci,
Tanada wata irin fitinanniyar qyama da qyanqyami akan a hada Jininta da wasu shiyasa take Jin rashin kaunar matar mahaifinta.
Sam bata shiga duk wani sabga da zai haɗata da ita, kallo ma bata ishe ta ba bare ta sanya rai wani abu zai iya shi ga tsakaninsu,
Babu abinda hafsatu ta ke hangowa a cikin idanun Maryamah face qyanqyaminta da kishinta me zafi,
Ko mahaifiyarta takan jisu wasu lokutan tanawa maryamah din fadan rage qyamar shiga mutane Wanda ita Kuma tamkar halittace hakan Allah yayita idan tanason Abu tanaso,
Idan tana kaunarsa to tana kaunarsa
Idan batason Abu to da gaske take qin ko son kallonsa.
Hannu hafsatu takai ta shafa cikinta dake juyawa ahankali cikin cikinta tana sake jin wani irin abu na danne zuciyarta,
''Shin za su ƙaunaci abinda za ta haifa?
ko shi ma ba zai samu arziƙin ko kallon banza daga gare su ba? Maryama za ta rungumi ɗa ko ƴar da za ta haifa a matsayin ƴan uwanta na jini ko kuwa ƙiyayyarta da ta ke bangowa a idanunta shi zatawa abinda za ta haifo?"
Waɗannan tunanikan suka sake sanyaya zuciyarta har ta ji hawaye na biyo fuskarta ta Dan gyara kwanciyarta daidai lokacin da muryar mijinsu Malam Adamu ke ratsa kunnuwarta lokacin da ya ke kiran sunanta,
"Hafsatu! Hafsatu!"
Sai ta yi saurin kai hannu ta share ragowar hawayen da suka zubo mata tana amsawa da cewa,
"Na'am Malam gani nan fitowa
Daga haka ta nufo hanyar fitowa falon gidan wanda yake na tarayya ne kuma anan suke haɗuwa su ci abinci kowane lokaci sai dai idan randa Malam ɗin ya yi balaguro ne kawai ba a zaman cin abincin.
Ta samu wajen zama daga gefensa na dama ta zauna idanunta na satan kallon yadda Maryama ta ɗauke kai daga duban sashin da zata zauna ma baki ɗaya ta maida idanunta kan mahaifiyarta da ke hidiman zubawa Malam Adamu abinci a plate.
Ajiyar zuciya ta sauke a boye sbd takasa sabawa da wannan yanayin na Maryamah sbd rashin ko inkulan Maryamah yafi damunta akan na kishiyarta sbd ganin Maryamah itace Yar uwa kuma jinin abinda Zata haifa zatafi son kome Zata Haifa yasamu kauna da kulawa daga Yar uwarsu wadda Zata iya Zama kaman uwa a garesu tunda babban Yaya kaman uwa ko ubane.
Ta mayar da dubanta kan uwargidarta wacce sam ba ma asalin ƴar ƙasar bace daga can Cameron ya aurota shekaru ashirin da biyu da suka wuce, kuma Maryama kaɗai ta haifa masa bayan ita ba ta kuma haihuwa ba sai yanzu ne da ya aurota ita za ta sake haifa masa wata ƴar ko ɗan.
"Bismillah Hafsatu zuba abincin mana."
Malam Adamu ya yi maganar idanunsa akanta waccce yasan ta kasance shiru shiru mara son haniya kyakykyawa bafulatanar asali da ya aurota daga jihar Adamawa Marainiya ce da ta rasa uwa da uba tun tana tsummar goyo a yanzu bata da wani cikakken dangi ko gata da ya wuce Malam Adamu dayake mijinta Kuma zai zamo uban yayanta.
Hafsah ta zuba tuwan ɗanyar shinkafa miyar kuɓewa ɗanya da Hadeeza ta yi (Wato Uwargidarta) Ta sanya hannu cikin robar ruwan da Malam ɗin ya wanke hannunsa a ciki ita ma ta wanke nata hannun tare da sanyashi cikin plate ɗin tuwan ta fara ci.
Shiru ya ratsa falon daga ƙaran fankar da ya fara gajiya da ya cika falon ba ka jin sautin komi sun yi tsit suna cin abincin babu me kallon kowa a tsakanin junansu sai Malam Adamu kaɗai da ya kan bi matan nasa da kallo yana takaicin yadda har yau gidansa ya rasa walwala da farin ciki kaman kowane gida sbd Hadeeza ta kasa haɗa kanta da Hafsatu domin duk irin kallon rashin Inkula da suke gwada mata yana sane da shi.
Maida kallonsa yayi kan Maryamah wacce zuwa yanzu ta ke matakin kammala karatun diploma ɗinta akan harkan kasuwanci da ta ke karanta wato (Business Administration)
Ya ɗauke idanunsa daga gareta yana jinjina kai ganin yadda gaba ki ɗaya ta juya musu baya tana cin abincinta a natse ko kaɗan bata so ma ta kalli direction ɗin da Abban nata suke zaune sabida kada ta damu kanta ta Kuma damesu,
Ta kasa gane dalilin rashin son kula da matar duk irin sanyin halinta da rashin kwaramniyarta da hakurinta duk da ko so daya gidan Basu taba ko gardamaba bare hayaniya sai dai tana yawan bai wa kanta amsa da cewa jininta ne bai haɗu da matar ba.
Maryamah ita ce ta fara tashi ta shige ɗakinta bayan ta kammala cin abincin Abbanta ya rakata da ido yana jinjina kai ba tare da ya ce komi ba Hafsatu ta miƙe da ƙyar sabida nauyin da jikinta ya fara sosai ta dubi su Malam Adamu da matarsa ta ce
"To Allah ya bamu alkhairy zan shiga daga ciki Malam,
Anty Hadiza Saida safe.
Malam Adamu ya bi ta da kallon ƙauna yana tausayin yadda ta riski rayuwarta a cikin gidansa ba tare da ta samu walwala da sakewa cikin iyalinsa ba ya ɗaga sautin muryarsa ya ce,
" To Allah ba mu alkhairy Hafsatu, Allah Ya tashe mu lafiya."
Hadeeza kuwa da qaramin sauti itama ta amsa Tai Mata Saida safen kafin ta Dan daga murya ta kira Maryama don ta zo ta kwashe kayan zuwa kitchen.,
Abbanta ma kaman yanda ya saba Saida yakuma Yi Mata 'yar nasiha akan su yaqi shedan su tsarkake zuciyoyinsu duk da yasan tana taimakon hafsatu da wasu ayyukan kamar yadda ta ke wa uwarta duk ranar girkinta,
Zata tayata ayyuka da dama Amma Babu wata doguwar magana shiyasa itama hafsatu Bata takurawa Maryamah din da magana sbd tasan ko ahakan yarinyar tanada tarbiya sosai tunda ko kallon wulaqanci bare rashin kunya batai taba mataba.
Tana kwashe kayan ta kai madafin ta aje ta dawo ta wuce ɗan ƙaramin ɗakinta ta kwanta ba bacci za ta yi ba wayarta ta ɗauka Android me arhar kuɗi wanda Abban nata ya siya mata ta hau chatting sai wajen 11:30pm ta kashe wayar ta kwanta don tana da lactures ɗin safe 8 za ta bar gida.
Washe gari karfe takwas daidai Maryama ta fito cikin shirin fita makaranta tana sanye da riga da zani da suka amsa jikinta ta yafa mayafi me Dan girma sbd Maryamah ba laifi tanada ilimin addini sosai hakama tanada irin yanayi na rayuwar uztazan Yan mata.,
Baƙace Maryamah amma kyakykywace sosai tanada jiki Mai kyau da kyakkyawar fuskar Mai kyau itama.
A falon nasu ta samu Abbah da su Ummanta suna kalacin safe ta tsuguna ta gaida su gaba ɗaya a jam'i tana ɗauke idanunta daga duban sashin da Amarya Hafsatu ke zaune ta zauna daga gefen Ummarta ta zuba kunun tsamiya da ƙosai ta fara ci.
"Maryamah ƙarfe nawa za ki dawo daga makarantar yau?"
Abbanta ya tambaya idanunsa a kanta, sai ta ɗaga kai ta dubesa tana amsa shi da cewa,
"Ƙarfe biyu Abbah."
Malam Adamu ya gyaɗa kai yace"
Madallah, Ga kuɗin motarki na kwana biyu zan baki don tafiya Lokoja ya kamani sai jibi zan dawo idan Allah Ya yarda.
Ya yi maganar yana zura hannu ya zaro kuɗin ya miƙa mata
Maryamah ta amsa kuɗin ta yi godia tana cigaba da cin abincin har ta kammala Ta yi wa Abbah da Umma sai ta dawo ta fice daga falon.