← Book details Gov Wife Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 38

Sashe 8

Gov Wife Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kafin ya bar office yasa an binciko masa duk abinda ya faru kuma ya samu bayanai kan cewa Asiya ce ta aiko da hotunan Lami Ninja wanda ya nuna ita
in tun asali 'yar bariki ce, sannan script
inta da aka samo an saka wani Professor ya duba marking
in kuma ya tabbatar abinda Saifuddeen ya bawa Lami Haladu, shi ta ci.

Ko da ita ta sa aka yiwa Mr Silas duka saboda ya fa
i gaskiya, to tayi ne domin shi.

She went this far just for him.

"Come here Darling, na saka an girka maka favourite food
inka"
Bilkisu ta katse shi.

Da ta yi maganar girki
walwarsa tuno masa tayi da kwana biyu da ya
ani girkin Asiya matarsa.

Akwai professional Cook da yake musu girki a gidan, amma albarkar dake girkin mata ga mijinta yana da yawa.

Bilkisu ta kama hannunsa ta wuce da shi
aki dan ta taya shi kimtsawa...

Har
arfe tara na dare Asiya na jiran kiran Gwamna.

Abu biyu take juyawa a ranta.

Ko dai idan Gwamna ya kira yace ta dawo gida ko kuma idan ya kira yace ya saketa.

Tun tana jiransa har ta fara gyangya
arshe bacci ya sace ta.

Da Asuba da ta tashi wayarta ta fara dubawa, babu missed call sai text message guda
aya wanda aka tura
arfe sha
aya da rabi na daren jiya.
*Bello zai zo ya
auke ki
arfe goma na safe*
"Shikenan kawai" ta furta ranta a
ace.

Da safe ta shiga ban
aki tana wanka ta jiyo ihun Ali da Gwani.

Da sauri ta watsa ruwa ta sanya hijabi a saman zanin wanka ta fito.

"Mi ya sameta?, mi kuka mata?" Asiya ta daka musu tsawa.

"Ta fito daga kitchen ne zata shiga
aki kawai muka ga ta fa
i" Ali ya fa
a kaman zai yi kuka.

Abba ne ya nemo mai mota aka saka Umma suka wuce da ita Asibiti.

Saura ka
an Asiya ta fita da zanin wanka Abba ya ce ta koma ta shirya, kafin ta fito sun riga sun wuce dan haka ita da Sumayya suka tsaida Keke suka bi bayansu.

Sai da aka basu damar ganin Umma data shiga
aki sannan ta cire ni
ab da ya zama mata dole yanzu, indai bata son idon mutane akanta.

Sai yanzu ta lura da wata rama da Umman tayi.

A tunaninta laulayin cikin ne ya figar da ita haka.

Bayan Umma ta farfa
o Asiya take tambayarta miyake damunta?.

Umma ta kauda kai gefe.

"Dama kin da
e ba lafiya Umma, amma shine kike ta
oyewa.

Ranan da kika koma Asibiti mi Likita yace?"
"Asiya ki barta ta huta" Asiya ta kalli Abba sannan ta kalli Umma dake kwance.

Maganarsa yai mata kamar akwai abinda suke
oyewa, da alama wannan jinyar ba ba
onsu bane.

"Abba mi yake damunta?"
"Zamuyi magana idan mun koma gida"...
arfe goma da 'yan
mintuna Yaya Bello ya iso
akin da suke, yaje chan gida ance suna Asibiti.

Ya gaida Umma sannan yacewa Asiya Gwamna ne ya turoshi ya zo ya
auketa.

"Yaya Bello ina zan je kana ganin Umma a kwance"
Umma dake kwance ta yafito ta tace ta tashi ta tafi tunda Sumayya na wajen.

"Sumayya zata tafi makaranta"
au wayarta ta danna numbar Gwamna wanda ta rasa dalili amma da *His Excellency* ta saving numbarsa.

Bayan ta amsa sallamarsa tace "Umma tana Asibiti, kayi ha
uri ba zan iya zuwa ba"
"Allah ya bata lafiya, a isar min da gaisuwa"
Ganin idon kowa akanta yake yasa tace "za ta ji, mungode"
Zuwa dare aka sallamesu saboda Umma ta takura akan zata tafi wai ta samu lafiya.

Lokacin da suka koma gida Abba ya samu daman yiwa Asiya bayanin ciwon Umma.

Haka Asiya ta tsaya galala tana kallon Abba cikin rashin fahimta.

Umma na da ovarian cancer sai kace shirin film.

Tukunna ma yaushe suka sani amma suka sakata a duhu babu wanda ya gaya mata?.

Kusan watanni biyar kenan da suka san da zaman ciwon a jikinta, tana shan magani amma yanzu cikin daya shiga jikinta bazata shi yake galabaitar da ita.

Asiya haushin kanta ta fara ji sannan ta maida haushin kan ciwon Umma, kan Abba da Ubayd da suka
oye mata ciwon, kan jaririn da bai tashi zuwa ba sai yanzu, bayan kusan shekaru goma da suka wuce tana cikin
oshin lafiya.

Abba yace "Tana zuwa check-up amma yanzu suna maganar kaman ya shiga stage IV, amma basu tabbatar ba sai sun sake yi mata wasu gwaje gwaje"
Asiya ba ta ce masa komai ba ta mi
e ta wuce
aki, gefen Umma ta kwanta ta
ameta ta fashe da kuka...

Sai da Asiya ta
ara kwana uku kafin ta koma gida, chan asalin gidan Gwamna.

Bata so tafiya ba, Umman ce ta tursasata akan matu
ar bata tafi ba sai ta sa
a mata, akwai aure akanta ba zata zo ta tare mata a gida ba.

Ganin ta samu
warin jiki Asiya ta tafi da niyyar kullum za ta zo ta dubata kafin su sake komawa Asibiti.

Ranan data koma gidanta Gwamna bai le
ota ba, bata damuba saboda yanzu lafiyar Umma ne a gabanta.

Wasu mata da suka zo dubata ma
in fita tayi.

An fara Kamfen suna neman matsuguni a jikinta, bata da
arfin yin hayaniya yanzu.

Ta godewa Allah data samu ta yanke ala
a da Umaru Kwom sannan aka wanke sunan Gwamna.

Ita yanzu koda zai saketa bata da matsala saboda burinta yanzu shine ta kasance kusa da Umma.

Washegari Gwamna ya shigo da safe misalin
arfe takwas saura kwata.

Asiya na
aki Sumayya ta shigo tace mata Gwamna ya zo yana jiranta a sama.

Rigar bacci ne a jikinta dan haka ta
aura hijab ta fita.

Lokacin data gaisheshi, fiskarta da ke kumbure ya fara lura da shi, sannan idanunta da suka
ance.

"Ya jikin Umma?"
"Alhamdulillah" ta amsa tana jujjuya wayar hannunta.

"Ina so a fita da ita waje, akwai wanda zai zo gobe saboda passport
inki ke da ita da kuma mutum biyu maza da za su iya binku"
Da ba Umma bace
ila zaginsa za ta yi akan yadda suka maida fita Asibitin
asar waje kamar tafiya anguwa,
ila tace masa bata son sadaka da ku
in talakawa,
ila kuma tace masa bata son burga da nuna isa.

Amma lafiyar Ummanta ake magana ba za tayi wasa da wannan dama ba.

Asiya ta
aga ido ta kalleshi, shima ita
in yake kallo, ta rasa dalilin dayasa kaifin idanunsa ke tsoratar da ita, take kasa jure kallon cikin fararen idanunsa.

Ta maida dubanta ga wayanta tace
"mun gode, Allah ya saka da alkhairi"
Shiru ne ya biyo bayan haka kusan minti uku kafin tace " ina so naje na shirya
arfe tara zamuje ganin Likita"
"Bismillah" ya fa
a yana mata nuni da hannu alamar zata iya tafiya.

Akwai maganar da ya ke so suyi, akwai tambayoyi daya ke son yi mata amma a yanayinta baya tunanin zata fahimci koma minene yake son fa
a dan haka zai bari zuwa lokacin da take cikin kwanciyar hankali.

A ranan da Gwamna yazo gidan Asiya, a ranan aka sace wasu
alibai 'yan Sakandare su goma sha
aya daga wata makarantar gwamnati dake cikin jahar Congo.

Irin haka ya faru farkon hawan marigayi Gwamna Saminu Bacchi inda aka sace wasu
alibai hu
u a hanyarsu ta zuwa Makaranta, an samu an kar
o yaran kuma daga nan ba a sake sace
alibai ba.

Maganar satan
alibai ya kara
e jaha ya kara
asa baki
aya.

Ko'ina sai maganar satan ake.

Kwana
aya kwana biyu shiru babu labarin za a sako
aliban sannan kidnappers
in basu fito sun bayyana mi suke bu
ata ba.

Bilkisu Kachallah ta dawo daga taron mata da aka yi ta tsaya a tsakiyar falonta tana kallon TV saboda kanun labaran da ta ji ya ja hankalinta.

Umaru Kwom ne a wajen Kamfen ya jefi Gwamna da rashin bawa rayukan al'umma mahimmanci, taya za ayi a sace raya
anana 'yan
asa da shekaru shabiyar kusan kwana biyar amma babu abinda Gwamna ya iya yi akai?.

Ba a ji daga jami'an tsaro ba balle 'Yan kidnappers da suka sace yaran, mi hakan ke nufi?

"He's behind this.

Shine da wannan aikin, Umaru Kwom yanzu kuma dirty tricks ka fara?

Mu zuba mu gani" ta snapping hannunta, daga haka ta
au gyelenta ta wuce
aki.
angaren Gwamna kuwa ya kasa zaune ya kasa tsaye saboda wannan lamari.

Ya dakatar da fita Kamfen saboda ya bada hankalinsa ga case
in sace yaran nan.

Daga wajen Alhaji Sani ya fara fuskantar matsin lamba saboda ajiye fita kamfen da yai a gefe, yayinda Umaru Kwom na chan yana fita Kamfen yana kururuta maganar satan
aliban da aka yi.

Ya yi meeting da Commisioner of police ya fi sau ba adadi amma duka shiru ne domin kwana bakwai kenan babu labarin yaran da aka sace.

A kwana na goma sha
aya da
atan
alibai jikin Umma ya tashi, cikin dare aka wuce da ita Asibiti.

Ba a sanar da Asiya bama sai washegari...

"Umma ya jikin?.

Umma an kusa gama ha
a takardun, naki ne ma ya bada matsala, Insha Allah da zaran an gama harha
a takardunki zamu fita"
Tana yiwa Umma bayani ne da hannu, Umma da ke rigingine a kan gado ta kalli Asiya ta mata murmushi.

Duk da bata da
arfin jiki haka ta fara mata bayani da yaren Kurame.

"Ki kwantar da hankalinki Asiya, sau
i na Allah ne.

Idan da yiwuwar na samu waraka to ko a nan
inma zan samu, dan haka babu inda zan je, idan Allah zai
au raina ina son kasancewa kusa da iyalina"
"Babu abinda zai sameki Umma, ba abinda zai sameki, zaki warke, cancer ba mutuwa ba ce, ki dena fa
in haka"
"Allah ya miki albarka Asiya.

Ina alfahari da ke, ko ba na nan na san za ki zama uwa ta gari ga
annenki."
"Umma ya isa haka, dan Allah ya isa"
Asiya ta fa
a tana goge hawaye.

"Ki bari na yi magana Asiya Shahidan Gwani.

Kinada kyakykyawan zuciya amma kina da taurin kai, kinada ri
o.
Chapter 8 · 0% Book details