← Book details Gov Wife Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 38

Sashe 25

Gov Wife Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk yadda taso
oye
acin ranta hakan ya faskara dan kuwa fiskarta babu walwala kwata kwata har aka gama taro.

Ihu da ta dinga yi ma ba kamar na kullum ba domin gwiwarta ya sace babu
arfin gwiwar
aga murya.

Ta yi
arin danne
acin ranta da tunanin zobenta zai isota nan bada jimawa ba.

Shri Hari Bansari ya gama bautan ranaku masu alfarma a gareshi.

Idan zobe ya zo, ba Gwamna Saifuddeen ba, gaba
aya jahar za su dawo
ashin ikonta.

Sai da Umaru Kwom ya rufe kamfen
insa kafin Gwamna Saifuddeen ya rufe nashi.

A bayyane take mutane na tareda SSK sama da Umaru Kwom.

Hatta wa
in za
e na SSK yafi na Umaru Kwom da
i musamman wanda wani hazi
in mawa
i ya rera yana yabon Gwamna da amaryarsa Asiya Shahidah.

Asiya na zaune gefen Junior Gwamna ya shigo.

Asthma
insa ce ta tashi
azu bayan ya gama tsalle-tsallensa a waje shi da wasu yaran ma'aikata na gidan., ba inhaler kusa da shi shine ya shiga mawuyacin hali kamar zai shi
e yaran suka gudu, sai da wani security ya ganshi ya kawo shi cikin gida wurjanjan.

Aka ci sa'a Gwamna na kusa ya fito da inhaler
insa ya matsa masa a baki, still ya jima kafin yaron ya dawo dai dai
"Ya jikin na shi?"
Gwamna ya zauna gefen Asiya bayan ya kissing goshin Junior
"Da sau
Bata ankara ba taji ya kamo hannunta, yanzu kam har ta saba da irin haka dan indai suna tare baya rabo da ri
e hannunta ko kuma ya kissing goshinta ko kumatunta.

"Zan fita, zan je wajen Baba"
"Allah ya kiyaye hanya"
"Amin" ya kissing goshinta sannan ya mi
e ya fita.

Ta cigaba da kallon Junior tana tuno yadda kwanaki suka dinga tafiya da sauri har haka.

Gobe Jummu'a za'a
aura auren Ubayd da Salma, jibi Asabat za a yi za
en shugaban
asa yayinda sati biyu na gaba kuma za ayi za
en Gwamnoni.

Tunda ta gama kamfen
inta bata sake fita daga gidan ba.

Duk wani shirye shiryen biki da ake yi ta
i zuwa gidan.

Ta dai aikawa Inna Yaha ku
i, sannan ta turawa Faty ma ku
in gudummawa saboda hidimar bikin da za a yi.

Ba zai kyautu ba idan bata halarci ko
aya daga cikin hidimar bikin ba, idan tayi haka zata zama butulu.

Ko babu komai, Yaya Ubayd Yaya ne a gareta, sannan ko dan darajan Abba dole ta je.

Ba wai tana jin haushin auren bane amma ta rasa ya akayi zuciyarta ya rasa samun sukuni tunda satin bikin ya shigo.

Ta mi
e ta koma
akinta saboda ta fara shiryawa domin shai
an ke jefa mata wannan wasu-wasi.

Matu
ar tana auren Saifuddeen, Ubayd ya haramta mata har abada.

Soyayyarsa ta fara gushewa a zuciyarta sai dai abinda ba za a rasa ba daga shai
an wanda ke motso mata rayuwar soyayyarsu ta baya a wasu lokutan.

Ta kan tsinci kanta da damuwa idan Gwamna bai kirata ko ya mata text ba a kwanakin da ba nata ba.

A ranakun da ya kasance nata, idan har tafiya ta kamashi ba zai kwana a gari ba gadonta na mata fa
i.

Duk da idan yana nan
in, filo take jerawa tsakaninsu, kasancewar su kwance a gado
aya yana sa mata nitsuwa.

Duk ranan da ba su kwanta tare ba, tana yin kewar numfashinsa,
anshinsa, tusarsa idan ya shiga ban
aki da Asuba zai yi fitsari, abin mamaki har
walwarta ya haddace sautin tusar ta yadda a ko'ina ta ji zata ce tasa ce.

Ta kan yi kewar wata rana da take al'ada suna kwance tayi tusar gaba ba su jima da bacci ba dan haka sarai ta san ya ji tusar amma ta kafse ta rintse idonta tana Allah yasa kada yai magana.

Ko sakan arba'in bai cika ba ta sake wata tusar mai
ara, wannan karan ta fita ta baya ne dan haka bayan
aran da tayi har da wari.

Asiya ta ji kaman ta nitse cikin gadon saboda kunya.

"Gaskiya za a ciki tara.

Domin daga yanzu Gwamna ya saka dokar hana tu..." Asiya ta sa hannu ta toshe masa baki, tana ji a ranta kaman ta fasa ihu.
arin cire hannun yai amma ta hana sai ma
ara matsowa da tayi tana fa
in "ai kaima kullum kana yi idan ka shiga ban
aki, nima idan ka sake yi zan ci tarar ka ehe"
Ganin ta dage da danne masa baki dan kada yai magana hakan yasa ya fara mata cakulkuli, nan da nan ta sake mai baki tana
arin ri
e hannunsa tareda fa
in ya dena, bai denan ba kuwa har sai da ta birkice tana dariya sosai tama manta cewa dare suke.

Tuni ya samu daman ha
e bakinsu ya shiga kissing
inta passionately.

Jikinta ya riga yayi la
was dan haka ta kwanta shiru tana kar
an zazzafan sa
o daga Gwamna.

A hankali kuma ba tareda ta shirya ba ta shiga maida masa da martani tana kwaikwayon yadda yake mata.

Sun jima suna kissing junansu, sun manta da duniyar da suke ciki dama wani damuwar dake cikinta, sun manta
iyayya ko soyayya domin all that matters a lokacin shine wannan kiss
in, wanda sha
ar numfashine ka
ai ke raba bakunan su.

Kusan minti takwas suka
auka a haka kafin Asiya ta yi saurin juyar da kai gefe tana fitar da numfashi da sauri sauri saboda hankalinta ya fara dawowa jikinta.

Ganin haka yasa Gwamna ya janye jikinsa yana fa
in "sai da safe"
Dukkansu sun tsinci kansu cikin wani sabon yanayi.

Gwamna ya shiga jin wani matsananciyar bu
atarta, ya dinga sauke ajiyar zuciya yana
arin saito nitsuwarsa,
arshe ya mi
e ya shige ban
aki ya sakewa kansa ruwan sanyi.

Sai da ya shige ban
aki Asiya ta samu damar motsawa, ta mirgina gefenta ta lullu
e duk jikinta da duvet sannan ta sa yatsu uku ta danne lips
inta tana ajiyar zuciya akai akai.

Ba zata iya fassara yanayin da ta shiga ba, duk da tana jin kunyarsa amma yadda jikinta da ruhinta ya amsa wannan sa
o, ji take kamar ta mi
e ta bishi ban
aki ta ha
e bakinsu su dawwama a wannan yanayi har abada.

Haushin kanta ma ta fara ji data katse wannan da
in, at least da ta bari sun
ara koda minti
aya ne, kai koda sakan talatin ne.

Zuciyarta ya shiga
iyasta mata abubuwa dayawa har Gwamna ya dawo ya kwanta.

Deep down tana fata ya sake yi mata chakulkuli, ya sake kissing
inta ya sake fa
in "i didn't know you are a good kisser" wanda sai yanzu ta tuno in between kissing
inne ya fa
i hakan.

Ko mi itama ta fa
a masa cikin yanayin nan oho.

Haka ta dinga tariyo komai a zuciyarta, tun daga cin abinsu tare zuwa kwanciyar da ta yi, zuwa shima shigowar sa
aki, wanka da yai da kuma kwanciya da yai yana mata addu'ar Allah ya tashe su lafiya bayan tace masa sai da safe, zuwa tusar da ta yi, chakulkuli and then...kiss.

Washegari ita ta fara tashi ta bar
akin da wurwuri tun kafin ma alarm
inta ya buga dan ba wani baccin kirki ta yi ba.
arfe biyu da rabi ta isa gidansu.

Gidan ya cika da 'yan biki, ana ganinta aka shiga ihu ana mata kirari.

Inna Yaha ta shiga nan nan da ita, yadda Asiya take bata girma bayan ta san irin zaman da suka yi da Ummanta, hakan yasa ta ke jin kunyan abubuwan da ta aikata a baya.

Yarinyar da ta ke wa gori da Agola itace ta ke da matsayin da ya
aukaka darajan gidansu a anguwa.

Gidansu ya koma abun kwatance.

Sai dai ka ji ana cewa Muna layin gidan su matar Gwamna.

Gidanmu na daura da gidansu matar Gwamna.

Gidan da zanje da ka wuce layinsu matar Gwamna ka
an sai ga layinmu.

Wasu masu abin hawar ma kana cewa gidansu Asiya Kachallah to a
ofar gidan Abba za a saukeka.

Asiya ta halarci walimar Amarya amma bata jima a wajen ba.

Haka kawai kuma data ga Amarya sai ta ji zuciyarta yayi sanyi.

Ta sani Salma na son Ubayd kuma zata kula da shi.

Nan da lokaci ka
an tsakaninsu zai daidaita, Ubayd zai manta da cewa sun ta
a soyayya.

Asiya bata koma gida ba sai
arfe tara na dare.

Ba ita ke da kwana ba shiyasa kawai ta wuce
akinta ta mur
a key ta kwanta bayan tayi wanka.

Sumayya bata nan anyi hutun za
e ta koma gida.

Koda tana nan ma tsakaninsu har yanzu basu daidaita ba.

Suna dai magana kam, amma babu wannan walwala kamar da, ko
akin Sumayya bata shiga sai da dalili itama kuma Sumayyar hakane.

Yanzu a gidan Junior ne ya maye mata gurbin Sumayya domin indai yana gidan to yana ma
ale da ita, wannan nema yasa ta jajirce wajen koya masa karatu na addini saboda ta nan ne yake da na
asu.

Malamin dake zuwa koyar da shi ba kullum yake zuwa ba, kuma kaman yana koyarwar ne da tsoro tunda baya iya tsawatar masa saboda Bilkisu Kachallah ta gindaya masa sharu
a lokacin da aka kawo shi.

Dalilinta ne yaron ya fara sake jiki da yaran ma'aikatan dake gidan duk da yasan idan Mommynsa ta sani ya ka
e dan fa
a zata masa sannan tasa a zane yaran(Allah Sarki basu da gata)a ganinta sune zasu
ata mata yaro, sannan a dalilin yaran ne ma har Junior ya fara magana da Hausa sosai.

Bilkisu ta yiwa Asiya magana akan ta dena shiga harkan 'ya'yanta tun ranan da ta gansu a wajen kamfen
inta.

Asiya ta yi banza da maganar.

Bilkisun bata zama a gidan balle ta sanya musu ido, shima yaron da ya gane mahaifiyarsa bata so ya dinga zuwa jikin Asiya sai ya dena fa
a mata abinda suka yi da Asiya, ko wani abu ta siya masa baya fa
a mata sai dai ya fa
awa Daddynsa...
an tsurkukin kwanakin daya rage ayi za
e aka fara ya
a jita-jita wai Gwamna Saifuddeen bare ne ba
an asalin jahar Congo ba.
Chapter 25 · 0% Book details