← Book details Gov Wife Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 38

Sashe 7

Gov Wife Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani
angare na zuciyarta na tunanin
ila Saifuddeen ya san da maganar za a kashe tsohon Gwamna amma bai iya yin komai ba, saboda ba shi da za
Koma minene gaskiya, yanzu ta gane cewa al'amarin 'yan siyasa sai su.

Idan ta samu ta wanke kanta a wajen Gwamna zata rabu da shi hankalinta kwance.

Sai dai kuma akwai wani
aramin gurbi a cikin zuciyarta da ya fara kwa
aito mata rayuwa tareda Saifuddeen Kachallah.
ila tunanin da wannan gurbin yake ne ya hanata bacci, amma Asiya ba za ta ta
a yarda da hakan ba...

Ta fa
awa Umma da Abba cewa Gwamna da kansa ya ce ta zo gida amma ba ta gaya musu akan wani dalili ba ne.

Ga sauran 'yan gidansu cewa ta yi saboda bikin Faty da za ayi ne ta zo.

Sumayya ma bata san ainihin dalilin zuwansu gida ba, amma kamar yadda Inna Yaha da Hindatu ba su yarda cewa saboda biki ta zo ba, haka itama ta yarda cewa akwai matsala ne tsakaninta da Gwamna.

Ranan Monday aka watsa labarai cewa kaso biyu cikin uku na majalisar jaha sun za
i ayi watsi da maganar tsige Gwamna, sun fa
i cewa abubuwan da ake tuhumar Gwamna da shi shati fa
i ne na 'yan adawa.
agaren Umaru Kwom kuma jaridar sa ta Climax ta cigaba da fitar da labarai marassa da
in ji gameda Gwamna.

Alhaji Kwom ya
aura aniyar a zama na gaba a kotu zasu kawo Mr Silas ya bada shaidah.

Ranan Laraba aka yi Primary election.

Gwamna mai ci Saifuddeen Sa'ad Kachallah ya zamo
an takarar Gwamna a jihar Congo a za
e mai zuwa a
ashin jam'iyyarsu.

Duk wannan bidiri da ake yi tsakanin Bilkisu da Alhaji Sani Kachallah da ma mutanen da ke goya masa baya, shi Uban gayyar hankalinsa ba a kwance yake ba, babu nitsuwa a tattare da shi.

Kowacce rana yana wuni ne da abinda ya dace yai wa Asiya.

Duk ta inda ya
ullowa lamarin sai ya ga zuciyarsa ta kasa gamsuwa da shawaran daya yanke.

Ya aureta ne da niyyar rabuwa da ita amma yanzu ga dalilin rabuwan yana da shi amma zuciyarsa ta
i amincewa da hakan.

Duk wani hidiman biki da aka yi, Asiya ta yi shine cikin rashin jin da
i.

Ta
auka da House suka janye maganar tsige shi Gwamna zai nemeta, amma shiru, yanzu fatanta kawai komai ya tafi dai dai ranan da za ayi zama na gaba a kotu.

Ranan
aurin auren Faty, Fou'ad Salisu ya kirata, ba yadda za ayi ta fita dan haka sai Queen Bee ta aika ta kar
o sa
on.

Ranan Alhamis.

Alhaji Umaru Kwom yana zaune a falo ya
urawa TV ido jira yake a gama yanke hukunci ya ji sanarwar da za a yi.

Yana da mutanensa da za su halarci zaman kotun duk da kuwa zama ne za a yi ba tareda 'yan kallo ba.

Duk da ba a tsige Saifuddeen Kachallah ba, yana da dama a kansa idan shari'ar ta tafi yadda ya tsara.

Idan kotu bata wanke Saifuddeen Kachallah ba yana da damar da zai soke shi a lokacin ya
in za
Sama da awa
aya bai samu labari daga mu
arrabansa ba, haka duk tasoshin da yake jira su kawo labari da
umi-
uminsa, har yanzu ya ji shiru.

"Hello Halliru, mi yake faruwa ne?

Al
ali bai fa
i hukunci bane har yanzu?"
Halliru yace " akwai matsala, Ranka shi da
e komai ya lalace.

Yanzu dai an tafi hutun rabin lokaci idan an dawo Al
ali zai zartar da hukunci"
"Wani matsala kuma?

Mr Silas yana nan, Lami na nan, wani shaida kuma suke nema?"
"Allah ya taimaki Excellency.

Ga sa
o nan ance a kawo maka"
Alhaji Umaru Kwom ya dakatar da mai maganar yana cigaba da bibiyan bayani daga bakin Halliru.

Amma Halliru ya
i fa
a masa komai,
arshe ma wayar yankewa tayi.

Ya duba mai aikinsa da ya kawo sa
on yace " sa
o daga ina?"
"Ance daga wajen Matar Gwamna"
"Matar Gwamna?" Ya dai kar
i dogon envelop
in daga hannunsa.

Yana yaga envelop
in ya duba abinda ke ciki.

Hoton Lami Ninja ce tana zaune akan wani mutumi, shigar da tayi a hoton ya bayyana cewa ita
in ba kamilalliyar mace bace.

Hoto na gaba kuma ita ce ri
e da sigari a wajen party, wannan tsohon hotone ma, dan zai iya kaiwa shekaru shatakwas baya.

Takardun gaba kuma photocopyn script ne na jarrabawar da Lami tayi aka bata carryover take i
irarin Prof Kachallah bai bata dai dai bane saboda abinda ya faru tsakaninsu.

Sai wata takarda kuma da itama photocopy ce wanda rubutu ne da Mr Silas yai ya bayyana duk abinda ya auku shekaru shabiyar da suka wuce, tareda fa
in cewa Lami Ninja ce ta biya shi dan ya aikata komai.

Takardar
arshe kuma anyi rubutu ne da hannu inda aka rubuta
*idan ka ga sa
ona ka kira* a
asa akayi signing da initial A wanda ke nuna Asiya ce.

Cikin ki
ima ya kira numbar Asiya wacce dama kiransa ta ke jira.

"Ka ga sa
ona?"
"Kin yi
ari kam" ya fa
a da
arfin hali
"Kar ka damu babu wanda zai kira sunanka cikin Mr Silas da Lami Ninja, amma ka shirya, Jaridar Climax za ta biya tara na rubutun bogi da ta buga ta
atawa Gwamna suna"
"Kina tunanin zan tsorata ne?"
"A'ahhh!

Alhaji Umaru tsoro kuma.

Ni dai ina son tabbatar maka ne kawai kujerar Gwamna ta maka nisa, ka shirya congratulatory speech wa Gwamna Saifuddeen Sa'ad Kachallah"
Kafin ya kashe wayar ta riga ta kashe.

Tabbas ita ce Malam Nawaso yake nufi.

Ta ya zata shammace shi haka?.

She completely make a fool out of him, taya ma haka ta faru?...

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci Alkali ya zartar da hukunci.

Lami Ninja ta rintse ido lokacin da ta ji hukuncin da Alkali ya karanto.

Ita Lami Ninja wacce take cin karanta ba babbaka a chan Lagos shine yanzu ake maganar za ta yi shekaru bakwai a kurkuku, sannan za ta biya tara ku
i miliyan goma na
atawa Gwamna suna da tayi.

Tana da sirrikan mutane dayawa a tafin hannunta, mutanen da akwai jarinsu acikin sana'ar da take yi, idan suka juya mata baya za ta tona musu asiri...

"Mi zai faru idan mutanen Gwamna suka samu hujja a kaina?, mi zai faru idan Alkali ya turani kurkuku?"
"Wannan ba zai faru ba, idan kuma aka samu akasi hakan ya faru to za a nemi
aukaka
ara.

At most ki biya tara, ko da za a turaki kurkuku ba zai wuce na wata shida ba"
"Ka san akwai abinda zan fa
a ya zamowa wasu mutane matsala"
"Ba abinda zaki fa
a Lami.

Rayuwarki da ta shegiyar 'yarki yana da mahimmanci a gareki"
Hirarta da Umaru Kwom kenan.

Ba dan kanta za ta yi shiru ba, sai dai ba za ta so a ta
a lafiyar 'ya
aya tal data mallaka ba.

Ta san mutane irinsu Umaru Kwom ba wani abu bane a wajensu su sa a kashe rai.

Mr Silas zai yi shekaru uku a kurkuku amma shi ba zai biya tara ba.

A hakan kotu ta masa sassauci ne saboda halin da ya ke ciki wanda yai i
irarin wasu 'yan kidnappers ne suka kama shi suka laka
a masa duka, da suka ga bashi da komai suka sake shi.

Dukkansu biyun kowa da nashi dalilin na
in ambaton sunan Umaru kwom.

"Gobe za a bu
e Kamfen
in Saifuddeen, muna bu
atar goyon bayan ku" Alhaji Sani ya fa
a yana kallon Yalla
"Alhaji Sani, jam'iyya tana tareda Saifuddeen
ari bisa
ari sai dai dole ne ya
au alkawari akan ba zai juyawa Jam'iyya baya ba idan aka rantsar da shi" Alhaji Macci
o ya fa
a yana kallon Alhaji Sani Kachallah da ke fuskantarsa.

"Dole ne ya
au alkawari, idan ba haka ba we'll not support his campaign" Mr Paul yai maganar yana jijjiga hannu, jijiyoyin wuyansa har sun fara tashi.

"Da mutane nake magana, ban saka dabbobi cikin maganata ba" Alhaji Sani ya fa
a yana yiwa Mr Paul mugun kallo
"Alhaji Sani are you calling me an animal?"
"So?"
"Enough!" Yalla
ai ya buga sandarsa da
arfi.

"Muna magana mai mahimmanci kuna mana zancen yara.

Wata uku muke da shi wajen tabbatar da cewa Saifuddeen Kachallah ya samu matsuguni a kowanne lungu da sa
o na jihar nan"
"Sorry Yalla
ai, Ka san akwai tsohon banza a cikinmu" Mr Paul ya fa
a yana dariya
Alhaji Sani ya mi
e tsaye, cikin fushi yace "ba zan zauna yaron bayana yana gaya min magana ba.

Yalla
ai za mu ha
u a zama na gaba"
"Alhaji Sani, Alhaji Sani..." Alhaji Macci
o ya shiga kira amma ina, tuni Alhaji Sani ya cikawa babbar rigansa iska.

Bayan tafiyarsa Yalla
ai yaiwa Mr Paul fa
a saboda ko ba komai Alhaji Sani Kachallah ya girmeshi nesa ba kusa ba.

Damuwar Mr Paul dai shine a san yadda za a yi Saifuddeen ya saka hannu a bu
atun jami'iyya saboda kar ya zo ya hau a samu matsala.

Gwamna na tareda COS lokacin da aka bayyana hukuncin kotu a talabijin.

"Congratulations your Excellency"
"Thank you Mr Lamara"
"Yanzu babu wata matsala sai mu fara Kamfen kawai"
"Allah ya shige mana gaba"
Har ya bar office bai daina mamakin Asiya ba, bai san takamaimai mi tayi ba amma ya san tanada hannu wajen yadda komai ya warware.

Lokacin da ya shiga gida yana isa falo Bilkisu ta mi
e da sauri ta zo ta rungumeshi tana fa
in "Congratulations Darling, we won.

Yanzu bamuda wata matsala sai ta Kamfen.

Ita kuma tsinanniyar nan Lami na so life imprisonment aka rubuta mata"
Chan
asan ransa yake tunanin babu wacce ta dace da wannan rungumar sai Asiya.
Chapter 7 · 0% Book details