← Book details Gov Wife Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 38

Sashe 36

Gov Wife Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dan a wajenta da a kashe rai gara an haifi cikin, tunda dai ba laifin yaron bane, laifin iyayensa ne.

A haka Kimberly ta raini cikin har ta zana jarrabawarta na WAEC.

Watanni biyu bayan ta zana jarrabawar ta haifi
anta namiji wanda ya
auko kamanninta.

Ashe tun kafin ta haihu ta riga ta yankewa kanta abinda za ta yi.

Dan haka kwana goma shauku da haihuwar ta gudu daga gida, ta bar yaron a wajen iyayenta.

Ba a san inda ta shiga ba, haka kuma iyayenta basu nemeta ba tunda sun fahimci guduwa tayi.

Godiya Kimberly
asar Ghana ta je wajen wata distant cousin na mahaifinta da ke zama a chan.

A nan ta samu scholarship na karatu a
asar America.

Ta yi karatu tun daga digiri na farko har na uku.

Sai data zauna da
afafuwanta kafin ta waiwayi iyayenta da
anta, lokacin shekarunta biyar da auren wani baAmurke amma ba su ta
a haihuwa ba, kuma likitoci sun tabbatar mata da cewa da wuya idan ta sake haihuwa.

Ga mijinta Mark Anderson, rashin haihuwa ba matsala bace a wajensa dan bai damuba, ya ta
a haihuwa da matarsa ta farko amma yarinyar ta mutu tun bata fi shekara shida ba.

A yanzu karensa Jerry yafi masa mahimmanci sama da samun
a ko 'ya na cikinsa.

A wajen Kimberly wacce ta kasance 'yar Nigeria, 'yar Africa.

Rashin haihuwa matsala ce a gareta musamman idan ta tuno
an data haifa a lokacin
uruciyarta tayi watsi da lamarinsa ko ya rayu ko bai rayu ba batada masaniya saboda shekaru ishirin cur bata waiwayi gida Nigeria ba, bata waiwayi iyaye ko 'yanuwanta ba.

Lokacin da ta zo Nigeria ta samu mahaifinta ya mutu,
aninta yayi aure da yaransa biyu sannan Clement ya zama saurayi, yana aji uku a Jami'a.
an da ta yi yun
urin kashe shi lokacin yana cikinta,
an da tunda ta tafi bata damu ta san wani hali yake ciki ba balle ta waiwayeshi...

Shekaru goma da suka biyo bayan zuwanta Nigeria ko ka
an babu wani jituwa tsakaninta da Clement.

Mahaifiyarta da
aninta sun yafe mata kuma sukan gaisa a waya lokaci zuwa lokaci amma banda Clement.

Zuciyarsa, zurfin cikinsa da ri
o sun hanashi yafe mata balle har ya kirata da kalmar Uwa.

Har yau babu wannan mu'amala ta uwa da
a tsakaninsu.

Kimberly ta yi kukan ta yi magiyar amma Clement ya tsaya kan bakarsa cewa uwarsa ta mutu tun yana jinjiri bai da ala
a da ita ko ka
an.

A koyaushe tana saka tsammanin Clement zai yafe mata har kuma ya dawo gareta sai dai kuma yana
ara girma yana
ara tsanarta ne, but she's ever hopeful zuwa lokacin da zuciyar
anta zai karkato gareta.

A yanzu data
auki kiran Clement kuma ta ji muryansa farin ciki ne ya mamayeta, in dai har saboda matar nan Asiya Clement zai kirata ya ro
eta alfarma to ba
aramin mahimmanci take da shi a rayuwarsa ba dan haka zata gayawa mijinta ayi duk abinda za ayi akan wannan maganar.

A Babban ofishin NDLEA na Abuja kuma cecekuce ne ya kaure tsakanin Agent Vic da kuma Agent Dahlia.

Kowannensu gani yake abinda yake akan gaskiyarsa ce shiyasa babu wanda yaiwa waninsa uzuri.

"It could be a set-up, she's innocent"
"Oh please Vic!

Kar ka kawo min maganar banza.

Ba a rubuta criminal a goshin mutane balle ka ganesu.

I will lead this investigation to the end and i will make sure she rots in jail"
Daga haka Agent Dahlia ta juya ta bar ofishin Vic a fusace.

Agent Vic ya sauke ajiyar zuciya, tabbas babu mai iya dakatar da Dahlia saboda ta kowanni fanni tana da kariya.

Mahaifinta babban mutum ne a
asar sannan ita
in American citizen ce kuma babbar jami'a a hukumar DEA.

Bai san dalilinta ba amma tunda ta zo she's being obsessed with tracking drug traffickers.

Amma a wannan case
in gaskiya yana ganin akwai lauje cikin na
i saboda a iya tunaninsa Asiya seems innocent.

Gwamna Saifuddeen Kachallah ya
urawa agogon da ke manne a bangon
akinsa ido yana bin kowanni tik tik tik da agogon ke yi.

Cikin kwanakin nan yadda yake ganin rana haka yake ganin dare.

Maganin baccin daya ke sha ma duk a banza ne, dan sai dai jikinsa ya mutu amma baya iya yin barci.

Bai san dalilin daya sa yai wannan
aran-
aramar ba ranan da ya fito yai jawabi wa duniya gameda case
in Asiya ba.
*"Banida hannu cikin binciken NDLEA.

Hukumar NDLEA tanada damar kama duk wanda ta samu da laifi, ko wanni irin matsayi gareshi.

Ina tabbarwa jama'a cewa Gwamnatinmu ba zata yiwa kotu katsalandan ba, zamu bata goyon baya tayi duk wani bincike daya dace"*
Ba abinda yake son fa
a ba kenan, it was what Bilkisu wanted.

Saboda haka ne ma tace lawyansa ba zai wakilci Asiya ba.

Wani
angare na zuciyarsa na gaya masa cewa cire hannunsa a case
in Asiya was a betrayal amma kuma ya rasa
arfin aiwatar da wanni abu a kai.

Barrister Zaytoonah Tijjani Abubakar ta ja dogon numfashi sannan ta sake gwada sa'arta a wajen maigidanta wanda ya kasa-ya-tsare tun
azu.

"Daddyn Alinah ka sake duba batun nan dan Allah.

I want to help..."
"Adaeze ki ha
ura da wannan case
in Dan Allah, for my sake.

Ki duba condition
inki, this is not an ordinary case da zaki je sau
aya sau biyu, this can take a long while"
"Zunnoon, please!" Ta fa
a tana marairaice murya tareda ri
o hannunsa
aya
Justice ya sauke ajiyar zuciya yace "Adaeze da condition
in ki zaki dinga jeka ka dawo tsakanin Congo da Abuja?

Idan baki damu da lafiyarki ba think about our baby"
"We'll be fine my love" ta
arisa maganar tana kwantar da kanta a
irjinsa.

Jin bai sake cewa komai ba Zaytoonah ta sani yanzu kam ya ha
ura.

"Hajiya Bilkisu Kachallah ta gyara zamanta da kyau sannan ta dubi Madam Bintu ta ce "kina tunanin zan bari a bata special treatment ne?

No no no, you know me ai"
"Shegiya Bilkisu kenan yadda kowa yake rayuwa a kurkuku haka zata yi?"
"Of course, ita wacece da za a
agawa
afa"
Madam Bintu da gatse tace "Matar Gwamna ce"
Bilkisu Kachallah ta fashe da dariya har da tafa hannu.

"Idan akwai Gwamna a cikin prison to Asiya zata amsa sunan matarsa, otherwise, ni ka
ai zan amsa sunan har ya gama tenure
insa biyu"
Madam Bintu ta saka ihu "ina yinki tawan"
Suna cikin
yatawa da dariya wata mai aiki ta shigo ta rusuna gabansu tareda fa
awa first lady cewa Uwani staff
inta na chan gidan Gwamna tana son ganinta.

"Uwani?" Bilkisu ta maimaita da mamaki.

"Ok ki shigo da ita"
"Lafiya dai ko?" Madam Bintu ta tambaya tana kur
an juice
"Bari ta zo mu ji"
Minti biyu sai ga Uwani ta shigo jiki a sanyaye.

Bayan ta gaishe da matan biyu sannan ta du
ar da kai
asa tana tunanin ta ina zata fara bayani musamman gashi ba Bilkisu ka
ai bace a falon.

"Miya kawo ki?"
"Dama dama..." Uwani ta fara inda-inda
"Banida lokacin wasa, ki fa
i abinda ya kawoki ko kuma ki bamu waje"
Uwani ta sauke ajiyar zuciya sannan tace "ina son komawa garinmu"
"A wani dalili?" Bilkisu ta tambaya fiskarta
aure.

"Hankalina zai fi kwanciya idan nayi nisa da nan garin"
"Babu inda zakije.

Ke Uwani!"
Uwani sai da ta ji hanjin cikinta sun ka
a dan ba
aramin firgita tayi da tsawar da Bilkisu ta mata ba.

"Babu inda zaki je"...

Har Uwani ta koma chan gidan Gwamna bata daina rawar jiki ba.

Babu yadda za ayi ta ku
uta daga hannun Bilkisu.

Lokacin da Bilkisu ta tunkareta da maganar saka
wayoyi cikin akwatunan Asiya ba ta bata damar cewa e ko a'a ba.

Umurni ta bata kuma ta san rashin bin umurnin akwai matsalar da zai jawo tunda babu abinda Bilkisun bata sani ba gameda ita.

Tun da aka kama Asiya ta kasa yin bacci, duk da umurnin Bilkisu ta bi, randa gaskiya ta bayyana itama za a iya turata kurkuku.

Wani mafita gareta daya wuce ta yi shiru da bakinta ta zubawa sarautar Allah ido.
*Congo state Prison*
Ko a mafarki Asiya bata ta
a tunanin zaman kurkuku ba, kafin a kawota nan ta ta
a zuwa gidan kurkuku na Congo lokacin tana Jami'a ta zo
aukan rahoto na wani assignment da aka basu.

A rahoton data kawo tayi nuni da yadda gidan kurkukun ke cikin yanayi na neman agaji:
azanta, rashin ruwa mai kyau da kuma abinci wadatacce, ga kuma uwa uba cikowa da wajen yai.

Sai gashi wai an wayi gari ita Asiya Shahida Faru
Baba ta fara irga kwanaki a gidan yari, yau kwana na shida kenan.

Kwana shida tana kulle kamar wacce tayi kisan kai, kwana shida babu wani daya zo dubata koda kuwa lawya ne, kwana shida bata san miyake faruwa a wajen dogon katangar daya zagaye kurkukun ba.

Hakanan kwana shida na wani sabon babi a cikin rubutacciyar
addara wacce tun kafin zuwanta duniya an riga an rubuta.

Kwanaki biyun farko,
akinta ita ka
ai ne kuma abinci mai kyau ake kawo mata duk dama ba wai ci take ba dan azumin dole ta
aurawa kanta.

Sai kuma a kwana na ukun aka zo aka chanja mata
aki, a hasashenta
akin da aka ajiyeta shine mafi muni a cikin kurkukun.

Tana cikin
aki wata warden ta zo ta bu
ofa tace " Hajiya Asiya akwai wata lawya dake son ganinki" warden
in mai suna Bisola ita ka
aice ke yi mata magana cikin girmamawa da kuma tausasa harshe, amma sauran kaman wanda aka musu karatun rashin mutunci musamman kwanaki ukun nan.

Lokacin da aka fito da Asiya tana cikin tafiya ita da warden Bisola ta ji an kira sunanta.

"Asiya Kachallah"
Kaman ta wayi mai muryan hakan yasa ta juya, ai kuwa sai idonta ya gane mata Hansa'u cikin kayan firsina ri
e da fartanya a hannu.

"Hansa'u" Asiya ta fa
a da
arfi.
Chapter 36 · 0% Book details